KUDIN RUWA DA BASHIN BANKI

KUDIN RUWA DA BASHIN BANKI A MUSULUNCI KASHI NA BIYU

Sponsored Links

    
                            بسم الله الرحمن الرحيم

       BASHI DA MATSAYINSA A MUSULUNCI :

          (1)    Ma’anar Bashi A Musulunci:

  Bashi shine dukiyar da mabukaci yakan karba daga wajen mai hali don biyan bukatar sa, da sharadin zai biya abin da ya karba ko kimarsa. 1 Dukiyary nan tana iya zama kudi ko abinci, ko dabbobi, ko duk abinda yake a matsayin kadara a masulunce.

              (2)   Hukuncin Bashi A Musulunci

Shari,ar Musulunci ta halatta wa wanda yake da wata bukata bashi da yadda zai iyi, ya cin bashi domin ya biya bukatar sa. matukar yana sa ran akwai yadda  zai iya biya shi.

  kuma wanda aka nemi bashin daga wurinsa lallai ya kamata ya taimaka yabayar saboda Allah. watau mustahabi ne a kansa ya taimaka.

     Domin Annabi (S. A W )yace:
  wanda ya yaye wa dan;uwansa wata damuwa daga damuwa irin ta duniya, a dalilinta, Allah zai yaye masa wata damuwar daga damuwa  irin ta  ranar kiyama  wanda kuma ya saukaka wanda yake cikin matsala Allah zai saukaka masa a duniya da lahira, Allah yakan taimaki bawa matukar, yana taimakon dan uwan sa.   

      (3) KULUWAR BASHI DA RUKUNANSA

   Bashi yana kulluwa, da cewar mai neman bashi “Ina son bashi” shi kuma mai bayarwa sai  ya mallaka masa. ko Kuma mai bayarwa yace ” Na baka abu kaza bashi” shi kuma yace : [ Na karba] ta nan za mu iya fahimatar cewa rukunan bashi [ Biyu ne] watau mai karba da mai bayarwa.

              (4)   HIKIMAR HALATTA BASHI

  Musulunci ya halatta bashi ne saboda Musulmi su zama   masu tai makon juna da rufin asirin ‘yan’ uwa such Musulmi da tabbatar da kaunar juna a tsakanin su. Domin bayar da bashi ga wanda ke cikin halin matsuwa yakan san ya kauna da dankon zumunci tsakanin mai bayarwa da mai karba. ka ga ke nan ta haka za ‘ a sami tausahi da soyayya a tsakanin jama’a.

           (5)   NAU’ I’IN BASHI A MUSULUNCI

     Bashi a musulunci iri biyu ne :

A – na farko shi ne bashin da za’a bayar domin taimakawa, da rufa asirin wanda ke cikin matsi wanda aka yi don neman yardar Allah kawai. irin wannan bashin shi musulunci yake son a rika taimakawa  ana bai wa mabukata, kamar yadda na yi bayani a baya.

B- Na biyu kuwa shi ne wanda za’a bayar da Sharadin a kawo kari a kan abin da aka karba. watau. [Riba] wanda aka fi sani da [bashin Ruwa] ko [interest] a turan ce Babu abin da ke kunshe da irin wannan bashi sai zalunci da tsabagen rashin [imani]. A saboda haka ne musulunci ya harmata irin wannan bashi ya kuma tanadi azaba mai radadi ga masu ta ‘amali da shi.
     Ta wani fanin kuma za muga cewa bashi ya kasu kashi uku ne, kamar yadda [Bukhari] ya rawaito Abdullahi dan umar yana cewa :-
   ” Bashi yana da fuskoki uku :

1 – Bashin da ka nufi Allah da shi, sai ka sami sakamako daga Allah.

2- Bashin da kabayar domin wanda ka bai wa ya saka maka, To shi din zai saka maka.

3- Da kuma bashin da kabar domin ka karbi mummuna wato [A karbi kari]wannan shi ne Riba.

A  duba  [As-sunanul Kubra Juzu’i na 5 shafi na 351.].

                              وبالله التوفيق.

Insha Allah zamu ta shi 

      A [ RUBUTU BASHI]  A KASHI NA UKU.

Leave a Reply

Back to top button