ILIMIN HADISI

ILIMIN HADISI A SAUKAKE KASHI NA SHIDA

Sponsored Links

                           بسم الله الرحمن الرحيم

       (16)  MENENE HADISI MAUKUFI?

     Hadisi maukufi shine hadisin da aka danganashi da sahabi. na daga fadi ko aiki, ko jinginansa ya sadu ku bai sadu ba (wato ga sahabi) misalin Hadisin ya kasu biyu na fada dana aiki.   kamar ace. Abdullahi Ibn Abbas yace  kaza. misalin hadisi maukufi  na aiki. kuma shine kamar ace Abdullahi Ibn Umar Aikata kaza.

            (16)  MENENE HUKUNCINSA.?
   Hukuncinsa shine ko dai ya zamo sahihi. ko ya zamo hasani. ko kuma ya zamo Ra’ifi.

                                        وما أصفته إلى الأصحاب من
             . قول وفعل فهو موقوف زك

          (17) MENENE HADISI  MURSALI?
   
   Hadisi mursali shine hadisin da tabi’i yace Manzan Allah (S A W) yace kaza gashi kuwa baiyi zamani da Annabi ( S A W) ba.

        (17)     MENENE HUKUNCINSA?
   
   Hukuncinsa daya da ra’ifi a wajen mafi yawa daga malaman Hadisi daga cikin su  akwai Imamuna shafi’i. amma Imamuna maliki yace ana kafa hujja da shi a cikin hukunce- hukunce. kuma wannan shine mafi shahara wajen Imamu maliki. da kuma Ahamadu Ibn Hambali.
                                         
                     .  ومرسل منه الصحابي سقط

            (18)  MENENE HADISI GARIBI?

    Hadisi garibi shine hadisin da ya kadaita da ruwaya daya. yanda ba wani wanda ya rawaito shi. ko kuma ya kaidaita da kari a cikin tantagaryar hadisin (wato matani) ko kuma wajen isinadinsa.

              (18)  MENENE HUKUNCINSA?

     Hukuncinsa hadisi Garibi shine yana kasancewa Sahihi. yana kasancewa Hasani. yana kasancewa Ra’ifi wannan shine yafi yawa. {wato Ra’ifi}.
                                          .وقل عريب ما روى راو فقط

                                     وبالله التوفيق.

daga dalibin ku
musa s zage.

Mai Karatu Amma Ka kula Karatu Aje Wajen Mallami ya Fi Alheri da kuma fahimta wannan kawai haska ma Akayi . Allah ya datar da mu duniya da lahira.
     

Leave a Reply

Back to top button