Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 65

Sponsored Links

CHAPTER 65

Kansa sukayi da mugun sauri har rige rigen tambayasa da”lafiya lafiya?shide Alh bala ba baki sai ido wuƙil wuƙil ganin suna tambaya sa be amsa musu yasa Alh surajo ɗaukan wayan yaduba yagani shi dawa,lokacin da Maƙwa yasha wannan naushi be gama zuwa daidai ba wayansa rayi ringin ganin numba ce basuna hakan yasa Goga ɗaukan wayan danson sanin waye keda hannu cikin ɗauke musu ƴar oga shima Alh bala yakira ne yaji haryanzu basu ƙaraso bane koya dan shi yana gudun samun matsala kasancewar sa matsoraci dakuma raunin zuciya tsaɓanin su Alh sunusi da oga kwata kwata Alh surajo dan su zama suyi kisa dan ganin cikan burin su.

Muryansu yaji sanda suke tambansa lafiya hakan yasashi kashe wayan yana ɗan tafa fuskan Maƙwa dayayi suman wucin gadi yana bude idon sa yamiƙa masa wayan da masa alama dayayi magana idan ko yakuskura yayi wani abunda zesa sugane da wata matsala yamasa alama da yankashi zeyi,ai kuwa cikin rawar murya data jiki yashiga bawa Goga hakura yana hada hannuwansa guɗaya yace”dan Allah oga kayi hakuri wallahi bansan wannan yarinyar ta wajenka bane da ban karɓi wannan aikin ba.

Suɗin banza suɗin wofi wallahi ko nawa zasu bani baxan amshi aikin nan ba,taɓa wannan yarinya
hatsarine gareni amun afuwa maigida wallahi duk abunda kakeso zanyi mashi da yardan ka dakuma amincewar ka maigida babban oga da girman kugeranka oga yanda yakema Goga kirari kaɗai hakan ze tabbar maka da yasansa farin sani,shide Goga shiru kawai yayi yana sauraron sa yana cikin zuba aka sake kiran wayan a karo na biyu bayan kashewan da Goga yayi ɗazu”wani ɗan balamin ne?muryan Alh sunusi ta daki dodon kunne su dayake wayan a hands free yasata”oga nine Makwa ya amsa”kaine wa?”nine wanda kabawa aiki ko baka ganeni bane?ajiyar zuciya Alh sunusi yasauke yana duban Alh bala da ɓacin rai yace”kadeji da kunnen ka amma katashi ka ɗaga hankalinka dama namu baki daya.

******
Aisha bata tashi farkawa ba daga suman da tayi ba sai can cikin dare,daddy Ishaq duk hankalin sa a tashe yake yasata a gaba yana zaune bayan tafiyan dr daya kira yaduba ta,yakuma sanar masa da ta farfaɗo saide anmata alluran bacci dan tana bukatar hutu sabida firgita datayi kuma yasake tabbatar masa da zata farka lafiya yayi ƙuri ya zuba mata ido bayaso ko kiftawa yayi,salati dauke a bakinta tashiga buɗe idon ta a hankali a hankali ta sauke shi saman fuskarsa zabura tayi zata mike yayi saurin riƙeta jikinta ne yashiga karkarwa wani irin rawa jikin ta kiyi zuciyarta sai sama da ƙasa yake tsananin rudewa datayi sakamakon ganin sa datayi rintse idon ta tayi tashiga karanta duk addu’a da tazo bakin ta karfi dan ita a tunanin ta fatalwa take gani dan fa bata yarda da Abbanta na rayeba tasan tabbas idan yana raye baze taɓa barinsu tsawun wannan lokaci batare da sunji labarin sa ko yanemi inda suke ba koda khadija ranan da tace yana raye jinta kawai tayi badan ta yarda dayana rayen bane ko faisal dayace mata babanta na raye jinsa kawai tayi dan ganin kaman yanaso yayi amfani da faɗa mata hakan dayayi dan aikin da yasa gaba saboda ita tasan wasu daga cikin abunda yake aikin akai kuma tace dashi zata taimaka masane akan aikinsa dan son ceto rayukan ƙananun yara daga shiga maraici sannan da tsiratar da mata daga shiga zawarci ko banza tasan idan aka kawo karshen su Alh sunusi yakasance tamkar guɓane daga cikin al’umma.

Luuu tayi zata koma baya saurin tarota Daddy ishaq yayi yashiga kiran sunan ta”Aisha Aisha Aisha bude idanunki ki kalleni nine Abbanki Aisha karki sake ritsa idonki ina da bukatarku kusa dani riƙo mata hannu yayi yashiga tofa mata addu’a duk yarikice yama rasa abunda zeyi kawai sai yafara zubar da hawaye matsowa lukman yayi yace”oga kayi hakuri ka karfafa zuciyarka kama gode Allah dayasa basuyi mata komai ba,na tabbata akwai abunda Aisha tasani na sirrin su ƙila hakan yasa suka farauce ta.

Jin yanda suke tabashi baki hakan yasake tabbar mata da ba fatalwa bane ashe yana raye to idan yana rayen ina yashiga tsawun wannan shekaru ya barsu yabar Anna da wahala da ɗawainiya dasu tsawon wannan shekarun.

Bude idanunta da yake tsiyayar da ruwan hawaye tayi tasauke a kansa tabbas Abban tane bazata taɓa manta wa dashi ba,koda shekara dawa suka ɗauka basa tare dashi batasan sanda ta fada jikinsa tasaki kuka ba cewa take”ina katafi kabarmu tsawon wannan lokaci dama kana raye Abba ashe kana a raye kabarmu mukai maraici Abba Anna tasha wahala akanmu ina kashiga sai kuka ita kuka shi kuka ta ƙankame shi sai risgar kuka suke gwanin tausayi suma kansu yaran nasa saida suka shiga matsan kwallan zallah tausayin su dakyar suka tsagaita da kukan Goga ne ya motso yakawo musu ruwa mai sanyi ba musu Daddy ishaq ya ansa yaɓalle marfin goran yamiƙama Aisha ganin ta kasa ansa sai shasshaka take yashiga share mata hawayen yana cewa”kinga yi shiru kuka ya ƙare yanzude sharuwa sai kibani labari ina Nafeesa?tana lafiya ko ina khadija ƴar baba?me nafeesa tahaifa yaro ko yarinya tahaifa duka waƴan anan tambaya ajere yayisu ga Aisha wani sabon kuka tafashe dashi tana sake faɗawa jikin sa tace”baba muma kanmu bamusan inda Anna take ba yanzu.

Dagata yayi daga jikinsa yana kallonta da idanunsa da suka kaɗa sukai ja kansa yashiga girgizawa da karfi jin kannasa yake kaman ze rabe gida biyu saboda sarawan da yake masa”a’a Aisha a’a karkice karkice narasa nafee haka yadawo kaman zautacce,zaman da yayi na ƙunci tsawon shekara takwas daya dauka yana ƙillace yadan taɓa lafiyar ƙwaƙwalwar sa abun yakan tashi masa lokaci zuwa lokaci kasancewa ya fuskanci zaman ƙunci da wahala wajen Alh sunusi ganin halin da yashiga yasake tsorata Aisha ƙanƙameshi tayi tashiga kiran”Abba dan Allah kadena abunda kakeyi din nan wallahi tsoro kake bani Anna bata mutuba tana gida tana jiranka dawowarka tsawon wannan lokacin”kin tabbata zaki kaini inda take”eh eh tace tana sake fashewa da sabon kuka shiko jin tace zata kaishi wajen nafeen sa yashiga washewa yana kallon yaran nasa yana cewa”ai dama na fadamu ku nafee zata zo gareni sai kuma yashiga dariya yana cigaba da cewa sunusi ka ƙwashe mun komai nawa ka rabani da kowa nawa ka kawoni tsakar daji ina rayuwa cikin dabbobi inda ba kowa sai kuma ya kalli Aisha dake kuka kaman ranta zefita yace waye ke…….allura da wani daga cikin yaran nasa yasa masa sai kuma ya ɓingire a wajen yafara bacci kallon su Aisha tayi fuska faca faca da hawaye tace”me yasami Abbana “kwantar da hankalin normal ze tashi yanzu

Leave a Reply

Back to top button