SANA'O'IN
{ASAN MUTUM AKAN SANA’AR} WAN-ZANCI .BY MSZ
Sponsored Links
° WAN-ZAN CI °
Wanzanci na da ga cikin sana’oin mu na hausawa wanda suke da tsohon usili, sana’ar wanzanci, kowa na iya yin in har idan zai tsaya ya koya, amma yawanci masu yin ta yanzu magada sun fi yawa, akwai sirri mai ƙarfi da babban al’amari ga ma su yinta, kuma su kan shahara a kan sana’ar ta su, ban da aski da yin kaho d acire beli, dayin kwalliya ko yin shashshawa ga mai sha’awa ko yan gado, su kan taimaka da bada magun- guna na gargajiya abisa lakaninsa, kuma da yardar Ubagiji akan dace.
Wanzamai suna da kyan aiki Wanda suka hada da Aska da Kaho. A. cikin Asaken akwai ta bakin karfe da farin karfe da jan karfe.
Ko wacce Askar da Wanzamai sukan yi niki da ita, sukan lakaba mata suna da sukan kira ta shi. Misli, akwai Hinde, Aska ce da’ake yinta da bakin karfe wadda ake yin kaciya da ita., sai kuna Banasariya, wadda ake yinta da farin karfe don yin aski, sai kuma Bintila wadda akeyi da bakin karfe, amfi amafani da ita wajen shashshawa ko tsagar kabo, akwai Kugiya ko Koshiya abin cire Beli,
sai Dutse abin washin wuka da kuma Kaho wanda ake zukar jini da shi in an tsaga da Aska. Sai Uwa-Uba Zabira, wadda wata Jaka ce da take dauke da duk kayayyakin da aka lissafa a sama.
Anan zamu diga sai a taremu a shiri na gaba inda zamu ka wu muka wata sana’ar da take ta Hausawa.
Daga