Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 67

Sponsored Links

CHAPTER 67

Dole ne kisan meke tsakanin sa da ita ko itace yarinyar da akace uwar sa ta aura masa.

Saurin ɗagowa basma tayi tana kallon mummyn ta jin abunda tace ɗin”Aure kuma mummy?waye uwarsa tamasa auren?ta tambaya taba kafe hajia mariyah da ido,ganin mummyn tata taƙi tanƙata yasa ta cigaba da magana tana fadin bade kina nufin kice Ahmad nada wata matan bayan ni da ake shirin mana aure,kai ina ina tace tana girgiza kai abunda bezai taɓa yuwaba kenan Ahmad bashi da wata matan bayan ni inma auren akai masa to saide AUREN WUCIN GADI naɗan wani lokaci ƙanƙani da zaran nashiga gidan ita kuma zanyi checking nata out taƙare maganan tana huci tamike zata tafi.

Hajia bilki tayi saurin dakatar da ita tana cewa”ina kuma zaki ai sai kitsaya kiji dalilin kiran da mukai miki ko?batama juyo ba balle susa ran zata saurare su tace”kuna iya faɗawa mummyna koma mainene amma ni banajin zan iya sauraronku a halin da nake dan raina a ɓace yake daga haka tasa kai ta fita daga falon salaha namara mata baya,salaha ce tayi ƙasa da murya bayan sun fita daga falon tace””gaskiya basma be dace kice dasu hajia haka ba,duk abunda zasu faɗa miki ina ganin abunda ze amfane kine amma gaskiya amsa dakika basu be dace ba kwata kwata naso ace kintsaya kiji da wacce suka zo nasan sabida nema miki mafita suke zaunen”look salaha ki ƙyaleni kina kara batamin raine da wananan maganganun naki yama za’ayi mutumin da nakeso yake shirin zama mijina ace bikin mu dashi saura kwana uku amma ranan tsaka yazo da wata kucaka yaɓatamun party.

Yanzu kuma azo anamun faɗa kaman basuga halin da nake ciki ba,na dauka kirana sukai su lallasheni wallahi da nasan kirana sukai dan sumun faɗa wallahi baxan je ba.

“Wai meke faruwane sai wani cika kike kina batsewa?”kide bari ramla ba dole tariƙa cika tana batsewan ba tayi tacika mana baki karshe de….bata kaiga kareshewa ba basma ta daka mata tsawa duka ƴan matan da ke wajen dariya suka kwashe dashi suna shewa hakan da sukai yasake tun zura basma ta hau zage zage salaha na bata hakuri karshe kawai sai ta fashe da kukan baƙi ciki.

Alhaji sunusi da Alhaji bala tare suka nufi inda Makwa yakwatan ta musu,suna ta aiyana irin azaba da zasu gana mata saide tun kafin sukarasa gun Alh bala kasancewar sa matsoraci duk magana da Alh sunusi ke masa kawai amsa masa yake da eh ko a’a amma hankalin sa kacokan yana kan hanya tun daga nesa ya hango wata mota daban ba wanda su Makwa suka zo da ita ba,”tsaya yace da driven cikin rawar jiki kafin driven ya ida tsayawan yace yi maza kajuya mubar wajen da sauri yi maza yi maxa kajuya haka yarinƙa uzzurawa driven har saida yajuya kallon sa Alh sunusi yayi damuwa kwance saman fuskar sa yace”lafiyan ka bala?irin wannan ruɗewa haka sai kace wanda yayi arangama da zaki ko damusa”ansamu matsalane Alh wancen motar ba tasu bace kuma wanda yake tsaye kusa da motan baya daga cikin su banma taɓa ganin sa ba.

Take zufa yashiga tsastsafo ma Alh sunusi dan shi kansa yanzu yafara tsorata da alamarin sa dan komai nasa lalacewa yake duk abunda yasa hannu ciki yanzu zasamu matsala ko daga gareshi hakan yake faruwa ko daga wanninsa shide har yanzu yakasa ganewa dolene daren yau a zauna meeting koda a maƙabartane duk da wasunsu basason tattaunawan maƙabartan amma yazama muso dole duka wannan magana yanayin sa a zuciyan .

*********
Aisha zaune tayi tasaka Abbanta gaba sai kallon sa take ko kiftawa batasonyi”Aisha taji ankira ta ɗagowa tayi ta kalli mai kiran nata wanda yama Abban ta allura ɗazune yamiƙo mata ledan dake hannun sa karɓa tayi ta ajiye bata bude ba,shima zaman yayi kusa da ita shiru sukai dukkan su kaman na minti biyu zuwa uku sai can mutumin yakatse shirun yana fadin”karkiji komai nan da karfe sha biyu zakiga ya tashi normal,gyaɗa masa kanta tayi cike da damuwa kaman bazatayi magana ba sai kuma tace”tun yaushe yake fama da irin hakan?kaidin likitane kokuwa….sai kuma tayi shiru ganin yanda yake kallon ta sai yamata ƙwarjini….”ko likitan bogi ko?shima yafada yana murmushi riƙe bakin tayi da hannu tace”nide bance ba”faɗaɗa fuskar sa yayi yana cewa”eh bakice ba amma nasan zakice din ne ai,murmushi tayi ganin yanda yasake da ita kaman dama can yasanta”sunana isma’il hashim kuma na karanci likitanci na gama karatuna garin neman aiki wani attajiri yana ganin takadduna ba kunya ba tsoron Allah yace”wannan takardun da ɗansa na’im suka cancanta badani ba,jin abunda suke tattaunwa akai yasani daukan kayana nabar waje to kinsan halinda kasar mu yake nazalunci shuwagaban ninmu su komai ƙanƙantar shugabanci da kabasu sai sunci amanan ƙasar data al’ummanta to wallahi ina faɗa miki hargida aka biyoni cikin dare aka tafi dani,nima kuma dama kaman nasan za’arina tunda naji wannan Alhajin yana kiran million 20 ze bayar nasan za ayi haka dan haka da dare nabawa ƙawanta takardun wajen yayana,ni kuma akai garkuwa dani sai naba da takarduna harfa gidan mu saida sukabi dare sukaje ba inda basu dubaba amma basu samu ba,hakan yasake tun zura Alhajin shine yamun barazana da kisa idan naki bada takardun ba nau’i na azaba da basu ganamun ba Aisha niko nace wallahi ko kasheni zeyi ba zan bayar ba kawai dan anga iyayena su ba kowan kowa bane sannan bamuda idon sani a gomnati shine sukaci gaba da tsareni harma Allah yahaɗani da mahaifinki ….”tab lallai kaga tasku jiwani karfin hali kai da wahalan karatu su da shan ramo cewa Aisha sai kuma tace amma lokacin da ka haɗu da Abbana a wani irin yanayi kagansa?shiru yayi kaman ba zece kamai ba sai kuma yace”gaskiya Aisha nasame shi cikin mawuyacin hali da a kullum da akwai wani likita da ake turowa yana nasa allura ashe alluran na birkita masa ƙwakwalwa yake zuwa yamasa kullum baya cikin hayyacin sa,saide wani ikon Allah duk lokacin sallah idan yayi yakan tashi yayi sallah cikin nutsuwa,abun yana bani mamaki kuma ba wanda zan tambaya balle nasamu amsa,da kwai wani mutum dake zuwa wajen sa duk ranan alhamis dadare ze zauna ya aske masa kansa sannan ze yanka masa farace sai ya tafi da gashin dakuma farcen cikin wata jar ƙwalle akwai xuwan da yayi naji yana cewa”Ishaq kai wani irin hatsabibin mutum ne duk asirin da nake maka yau tsawin shekara shida amma haryau baya tasiri akanka allura da nasaka anayi makama banga alamum yana aiki a jikin ba gashi ƙungiya tace bata bukatar jininka yanzu saina ahalinka idan ansamu sai da jininsu sannan asirinmu zeyi tasiri kanka,ga kai kuma sabida tsabar wayo bansa wace duniya kakai iyalan naka ba.

tun daga nan nafara bibiyar duk lamuran sa karshe alluran da ake masa na danne likitan naƙwace bayan namasa dan banzan duka nace sai nayi masa na daureshi a ɗakin da muke shine fa dayaga ba sarki sai Allah yabini hakuri na barshi yakuma yimun alkawarin ba ze sake yimasa ba amma ze rinƙa zuwa yana masa wanda zerinƙa sakashi bacci ƙwaƙwalwarsa tasamu hutu yakuma kawomin magunguna ina bashi yana sha ban yarda dashi ba,saida na anshi wayan sa nashiga browser nayi searching sunan magani da alluran a ta google nagani sannan na yarda nabarshi da yace dani idan yace baxeyi ba wayan nan mutanen nan sawa zasuyi a kasheshi kuma yarda gaskiyane sa dan basu da imani bazance ba zasuyi ba zasuyi komai ma dan biyan bukatan su sannan duk sanda yakawo alluran ni nake masa magunguna kuma idan yashi yin sallah nakan bashi bayan nasa ya ɗanci abinci kinji handa akai ɗago kanda zeyi kawai sai yaga Aisha hawaye faca faca a fuskarta na tausawa Abbanta hakuri zakiyi Aisha kima gode Allah dayasa suka barshi da ransa.

Share hawayen ta tashigayi tace”mun gode sosai da taimakon da kai ma Abbanmu Allah yabiyaka da mafificin alher”amin ƙanwata yanxu de bude kici abincin karya huce”tom kawai tace sai kuma ta waiga ta kalli su Goga dake zaune suna lido a waya tayi ƙasa da murya tace”sukuma wayancan fa?ɗagowa yayi sukayi ido biyu da goga yana murmushi yace”sune waƴan da suka ƙuɓutar damu nan din da muke zaune ma gidan sune sannan su din sunsan sirrin komai na Alhajin da yakama Abbanki hatta sirrin gidan Alhajin idan akwai wanda basu sani ba to ɗai ɗaine”kun haɗa kai kuna gulma ko?”gulma kuma suka faɗa atare sai goga yace”eh in ba gulma kuke ba to me kuke kun hada kai tode kuyi a hankali kar ɗayanku ya ciji kunnen ɗan uwan sa ehem karkuce ban faɗa muka ba,dariya sukai dukan su banda Aisha data ɗan murmusa.

Ahmad kaman wani zautacce haka yakoma sanda yazo gidan Anty hajiya yaga halin da take ciki kaman yayi kuka yaɗauki lefin duka yadaurawa kansa cewa yake kiyafeni Anty hajia duka nina jawomuku shiga wannan halin da kuke ciki da nasan haka ze faru da bange da ita ba”kai ma ganganci kai Ahmad kai da uwayenka duka baku daukeni abakin komai ba har aure zasu maka kuma saboda rashin hankali irin naka kadauke ta kaje da ita wajen sha’anin bikin ƴar Alhaji sunusi kayi tsammanin kaci banza ai wannan wasane sai kuma ya kwashe da dariya yace wannan auren ai na wucin gadine kaman yanda kukayi shi a gantale haka ze kare a gantalen dukkansu sakin baki sukai suna kallon sa harda Ammi dake rungume da Malika suna kuka.

“Alhaji amma kanka ɗaya kai wai mai yasaka baka da tunani shin baka ganin halin da ƙanwata keci ne?harkake irin wannan magana to bari kaji inde Alhaji sunusi ne kai kanka ba barin ka yayi ba dan ƙaidinsa yawa garesa yamafi mata karkayi zato ko tsammanin katsira daga kaidin sane,kaima a’a baka tsiraba munanan wataran zamu ganku a rana kai da shin,kai da anyi magana idan tashafe sa karinka tada hankalin kana tada jijiyar wuya karka manta idan ma kamance ni bara na tunatar da kai shine wanda yajefaka halin da kake ciki yanzu amma duk da haka baka hankalta ba da zaran kaji an ambaci sunan sa jikin ka har rawa yake aure kuma da kullum kake kiran auren wucin gadi to bara kaji saide wanda kake shirin yimasa shine na wucin gadi amma wanda kake kira mu uwayansa mun masa kai ma kanka saikayi alfahari da ita dan sai yayi karƙo saboda nariga da nasawa abun albarka kuma albarkata saitayi ta bibiyarsu.

“Ma’arufa ni kike gayawa magana haka saboda kawai nafaɗi gaskiya,Ammi zatayi magana Ahmad yayi saurin cewa dan ALLAH Ammi kudena haka mana idan shi be damu da halin da Anty hajia ke ciki ba ke ai ƙanwarkice kuma be kamata ki biye masa kuna musayan nƴawu anan mutane na ganin ku ba.

Leave a Reply

Back to top button