Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 1

Sponsored Links

Marriage volume 1

For You Queen Bee🌹
“Relax!” Ya furta a hankali, har lokacin hankalinshi baki daya yana kan laptop. Yana aiki, kamar bai san yadda ta girgiza ba. “Ka ce me?” Ta tambaye shi, in sound tone. “How you endure like this ko? Lalacewar bata kai ki auri tsoho ba ko? To gaya min taya zaki biya ni kudina? Ko so kike mu ajiye zancen aure mu shimfida al’amarin ta wancan side ɗin.” Ya mata wani irin shegen kallon da sai cikinta ya bada wani irin sound na “kulu-kulu!” Ya wani d’age mata gira.
“Wallahi ba zan auri tsoho ba, ina laifin ka ɗauke ni aikin ciyar da kartin mazan da suke kewaye da kai. Tir ni ba yar iska ba ce da zan bada kaina wa tsoho irinka.” Tayi maganar in childish. Kallon yadda take mishi wani irin kallo tare da rufe kirjinta da hannu bibbiyu.
Dariya ne ya subuce mishi, madadin yayi dariyar sai ya tsinci kanshi da wani shegen smirks. “Ok ke yanzu ba auren ne matsalar ba ko? Tsoho me furfura irina ne baki so?”
“Haba Uncle Malik, ko Uncle Elbashir ka gayawa ba zai baka sufot ba, balle wani can a waje, kasan me za a kira ka?”
Zuba mata idanu yayi, tare da yin kwal-kwal da shi, kamar yaro karami.
“Arrrrrrsh ka daina irin wannan kalar tausayin kyau yake maka, ni kuma haushi kake ba ni.”
“Ok me kike so nayi?” Ya tambaye ta domin ya fahimce ta, so take ta shashsntar da zancen auren ne. “Kaga mu bar maganar nan, a fara biyan mutane kudin su!”
” Ba zai yiwu ba!” Ya faɗa kai tsaye, yana me tsura mata idanu. Wani murgud’a baki tayi tana faɗin. “Yo ko namar jikina aka yankan dai zata haura miliyan dari huɗu. ”
“Wayo zaki min?”
“Aahaaaaa!” Ta saka hannu a bakinta, tana faɗin. “Na shiga uku, an fasa aurena wani munafinki ne ya gaya maka zan maka wayo, Ni me biyayya ce idan kaso ma kayi yadda kaso da ni, amma maganar aure gaskiya ban shirya auren tsoho irinka ba!”
“Zainab!” For the first time da aka kira sunanta cikakken, tura baki tayi tana faɗin. “Ni bana son Zainab Zeenobia zaka ce.”
“Tabbas sunanki Zainab, kuma da shi zan kira ki, so ki biya ni kudina da na mutane baki daya, ko kuma na saka a yi ta farautar ki babu dare babu rana!”
“Barazana kake min?”
Ta tambaye shi a nutse, bayan ta mike daga inda take. Ta koma bayan kujeran, ta dan sunkuyar da kanta. “Ba dai barazana kake min ba, idan shi ne ma ka daina tunanin haka, domin ban san tsoro ko barazana ba, yana da kyau ka bi wata kofar ban da wannan!”
“Da zaki daina min magana, ta haka da kin taimakawa abubuwa dayawa!” Ya fada muryanshi tana cracking. Sam bata fahimci maganarshi ba, amma kuma bata fasa abinda take ba, domin wani irin kusanci ne da ya haifar mishi da wasu abubuwan da ya kasa jurewa. Hankad’ata yayi ya fadi can da baya, wanda sanadin faduwar, ya ja mata buga kanta da table din dinner.
Dafe kanta tayi tana kallonshi, ta kai minti goma a zaune, juyawa yayi ya ga yadda ta rike kanta jini na zuba a hancinta.
“Ya ilahi!” Wayar shi ya lalluba sai, kiran Elbashir yayi. “Ka shigo!” Ba iya shi ba hatta Shatima sai da ya shigo, kasa boye halin da ya shiga ne yasa shi nufarta. “Innalillahi, Baby!” D’ago kai tayi, ta kalle shi kafin ta fashe da kukan makirci. “Boy ika cewa ba da gayya na amshi kudin ba?” Gyada mata kai yayi sam ya manta a gaban Malik yake, don haka ta kuma cewa. “Kaga yadda ya min, kashe ni yake son za i yi akan kuɗinsa.” Juyawa yayi ya kalli Malik cikin fushi. “Yanzu kai Malik ko kunya baka ji ba, yar wannan yarinyar zaka nime kashewa akan kuɗinka? Me Baby ta maka?”
“Kudina zaku bani, kai Elbashir ka sakata gaba ka kaita asibiti! Kai kuma kazo nan ina son magana da kai!”
Yadda yayi maganar a nutse zai tabbatar maka, Malik Menk Jordan shi ne a gabansu. “Ok sir!” Suka ce mishi”Ke muje!” Inji Elbashir, “Boy kace ba ni zuwa!” Ta fada tana kwakulo hawayen wanda sam ba dabi’arta ba ne. Shi kuwa da tausayi ya kama shi, sai yake hango rashin Malik. “Ki bishi za a kaiki asibiti ne!” “Ni bani zuwa domin yace sai ya saka a min alluran mutuwa!”
“Ke wacce irin sakarya ne?” Elbashir ya daka mata tsawa, juyawa tayi a fusace ta rike necktie dinshi, kafin ya yi wani tunani ta buga shi da kasa, cire hular kanta tayi, ta gyara zaman daurin gashin kanta. “Ke!” Malik ya daka mata tsawa. Hasken da ya wuce ta idanunta babu shiri yasata nufar Malik da wani kofin Mug.
“A’a! Ke dakata.” Kafin su rufe baki, ta nufi Malik zata rosa mishi mug din nan. Wani irin dukar cinyarta yayi da bayan hannun shi. Ta koma ta zauna dabas a kasa. Kujeranshi shi ta guragu ta dauka, zata maka mishi, Shatima ya rikota. “A’a” hankade Shatima tai, ta nufi Malik. Wanda ta gama karantarta, kafin ta kai Mishi duka da karfe, ya kai kauce, ya kuma fisgota, ya dauke kunnenta da wani irin mari da yasa ta suma lokaci guda. “Bashir! Ka wuce da ita, Menk Jordan World cares.” “Ok Malik” “duk abin da ake ciki ka tabbatar ka sanar min!” “Tow Malik!” Sabata yayi s kafad’arshi, suka fita ko inda Shatima yake bai kalla ba ya ce mishi. “Mene ne alaƙarku?” “Ina son aurenta ne!” Ya gaya mishi gaskiya domin Malik ya kyaleta.

“Hmm! Kasan dai ta shiga takun saka da ni?” “Malik yarinya ce!” Shatima ya fada a hankali. “Ba yarinya ba ce, tasan me take yi, idan kuma yarinya ce zaka biya ni kudina ne?” “Amma Malik ba wani abu bane a cikin dukiyarka, idan ka yafe mata.”.”ban san wannan zancen ba, domin ta sayar da ranta. Ciniki muka yi na bata kudina. Ita da kanta da duk wani abun da ta mallaka yana hannuna ne, na ja maka layi akanta, kada na kuma ganinka da ita.”

“Malik” juyawa yayi ya kalli Shatima, “Shi kenan Malik an gama!” Yaji haushin Malik sosai, kai taya ma ba zai ji haushinsa ba, domin ya girma da jin haushinsa har yau gani yake nasarar da Malik ya samu shi ya cancanci haka, hassada da kyashin Malik yake ji, wanda idan ya boye sai yaji kamar zai mutu.
—–
Sun hadu da Malik, akan kudiri daya tun a gidan Yari suka haɗu. A lokacin da suka hadu bai tab’a zatan Malik zai zama wani abu ba, domin lokacin shi yake tsayawa Malik idan aka nime cutar da shi. Bai mantawa akwai wani mutum da ake kiran shi. Shaidan bai damu mutuncin ko kaɗan ga hada husuma sakawa yake ayi ta dokuwa a gidan Yarin, kuma Jami’an ganduroba basu isa yin kome ba.

Akwai wani abu daya da yake faruwa a cikin gidan, shi ne na yawaitar yan homo. Yan luwaɗi sun yi yawa a cikin gidan, wanda yasa ko yaya kake sai ka samu lover, wannan abin ya d’aga hankalin Malik,. Domin yasan dai wannan dabi’ar tana cikin manyan kaba’irai. Shi yasa yake cin duka a hannun wadanda da suka fi karfinshi idan sun nime shi da Lalata yaƙi.
Haka ma Shatima, mutane dayawa sun nime shi yaki, sai tafiyar su tazo daya, anan ne suka fahimci ai duk mutum daya yayi silar fadawarsu matsala guda, sannan kowa ya san cewa duk wanda ya zauna a gidan yarin, tow ba mutumin kirki ba ne. Haka yasa baki daya ake kallon duk wanda ya fito gidan yarin yana zaga bayan gida.

Wata rana ana ruwan sama, Shaidan ya turo a dauki Malik domin yafi son Malik. Ya ce duhun fatarshi yana daukar hankalinshi.. sai aka yi rashin dace, aka ɗauki Shatima. Malik yana dawowa aka gaya mishi an zo daukar shi amma sun dauki Shatima. Yasan kuma wanda aka kaiwa Shatima ba zai bar shi ba, cikin fushi da fusatar da yake tare da ita, kawai ya dauki wani katako me kusa, ya nufi can dakin shaidan, ya damu ya kwabe Shatima yana kokarin saka mishi abin, bai san lokacin da ya make kanshi da wannan katoko me kusar ba, sai ganin jini aka yi yana sartuwa a dakin, ya kuma cigaba da dukarshi dai da ya daina motsi, karshe jami’an tsaro suka dauke shi. Aka ji aka rufe shi. Koda aka kai Shaidan asibiti kwanan shi goma ya ce ga garin ku.
Wannan abun ya d’aga hankalin kowa, domin koda aka bude Malik, take ya zama sabon shugaban gidan Yarin. Sannan ya kafa doka babu gay a cikin gidan..
Wannan abin ya dame su sosai, har aka fitar da shi, matsala daya ya fuskanta, ba kome ba ne, Malik yana da tsananin bukata, matukar zai ga mace ta mishi magana, ko yaya ne tow yanzu zai bawa mace dama, babu ruwanshi.

Shi yasa a lokacin daukar fansa shi, yayi ta gudun mata, amma karshe samun laluran kafarshi tow mace ce, wanda ya haifar mishi da mutuwar kafaffunshi da duk wani masarautarshi. Haka yasa shi boye kanshi, don ko ture Zeeno da yayi, abin da ya faru da shi shekarun baya ya dawo mishi kanshi, mace tayi sanadiyar da ya tasa kafaffunshi, sannan itama don hauka a hatsarin ta mutu, Yarinyar da yaso kuma ta ci amanar yardan da tayi mishi, inda ta dauki Nuratu kanwarshi tow kuwa da bata fara aikata mummunar hukunci kanta ba, Bayan ya rabu da ita ya gane shi din sai a hankali ba zai iya zama babu mace ba, sai dai bayan hatsarin shi an sha kawo mishi yan mata karshe su suke fita duniya suna gayawa abokan harkallan shi nakasashe ne, shi yasa ya hakura da mata, ya kuma hana mata shiga hurimin shi, sai Lalla Salmah, itama bai fi su hadu a shekara sau biyar ba. Duk lokacin da suka hadu da ita sai ta kai mishi farmaki, duk da Nuratu ba ciki daya suka fito ba, itama ƙaddara ta haɗa su, har yake jin ya samu kanwa wacce zai yi kome akanta, ita ta fara ce mishi abin da yake aikatawa kuskure. Ya daina ya hakura daukar fansa yana iya zama alakakai, ba iya kai yake kyalewa ba, yana iya binka har karshen rayuwarka.
Shi yasa bayan rasuwarta yasa Sayyadah Qudussiyah ta kwashe yaran suka tafi can Demark. Ba zai iya kallon yaran ba, ya rasa kome amma baya Fatah ya kuma saka wani na kusa da shi a matsala.
★★★
Menk Jordan World Cares.
(MJWC)
Tunda aka kawota, suka shiga bibiyar ‘lamarin jinin da yake fita ta hancinta, abun da suka fara, shine aka mata scanner da X-ray, kamar Dr Wardah Nyako ta sani, ya kalli sauran likitocin ƙwaƙwalwa ta ce mishi.
“Akwai matsala a cikin kanta, kuyi zooming ɗinshi muga.” Haka aka yi zooming sai dai sun sha mamaki. “Bullet!!” Baki daya suka tsaya a kanta.
“”Miracle ” Dr Wardah Nyako ta furta tana kallon Zeeno. “Ku kira Sir Elbashir!”
Fita suka yi, can sai gasu tare da Nurse.
“Sir kasan yarinyar nan akwai bullet a brain dinta?” Ware idanu yayi yana faɗin. “How can be? Mutum ya rayu da harsashi a ƙwaƙwalwar shi?” “Wannan shi ne ake kiran shi, baiwa da al’ajabi.” Shiru yayi yana kallon Zeeno, wacce irin ƙaddara ce hada ta da Malik.
“Yanzu ya za ayi da ita, domin dai tsautsayi yasa ta fadi , Yallabai ya ce a kawota.” “Zamu jira mu ga tashinta sai mu ji yadda jinyar yake a jikinta.” “Zan fara sanarwa Malik abinda ya ce xan gaya muku.”
Gyada kai tayi tana kara mai da hankali akan Zeeno, fita Elbashir yayi ya shiga Mota. Kiran Malik yayi ya gaya mishi halin da ake ciki, “ku kyaleta a bata abun da ya dace, ku uzurawa rayuwarta, har sai ta kawo kanta. Ba zan lamunci renin hankali ba.!”
book 2 zai zo muku Whatsp da Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/10, 9:17 PM] Yan Mata:

Leave a Reply

Back to top button