Furar Danko Book 2 Page 50
‘…..!!
5️⃣0️⃣
…….Haka dai ta yini a ɗaki tana ƙulla wasikar jakai, sai wanda yaga dama yake shigowa gaisheta da jiki. Kowa yana tsakar gida yana raƙashewarsa hankali kwance harda su DJ suka saka Dan taro akai fa na gani na faɗa a harabar gidan. Ga abinci da kuɗi ana bishasha kamar ba gobe. Babu wanda ya damu dawai cewar Dada nada hawan jini bari a sassauta. To kowa sha’aninsa yake kamar ya manta da ita a gidan, sai ƴayanta ne kan ɗan leƙata time to time. A ƙarshe dole sai da likita yazo dubata. Washe gari da Uncle Khamil zai wuce ya roƙi Baba Garko ya bari ya wuce da ita Abuja ta ɗan huta. Cayay shi babu ruwansa duk ma inda zata taje. Wannan kalma ta sake sanyaya musu jiki. Yayinda Dada ta ɓarke da kuka akan ita babu inda zataje, ba komai ta tuna ba sai wahalar da tasha a hannun matar Uncle Manner. Babu yanda basu lallaɓata ba tace wlhy babu inda zataje garama idan mutuwa ce ta ɗauketa a ɗakinta yafi mata. Dole suka barta suka wuce….
(Su Dadancy anji gwale-gwale )
_______★
Gaba ɗaya nutsuwa ta ƙauracema su Alh. Sulaiman. Dan sunbi duk matakan kawar da Alhaji Dikko al’amarin ya gagara. Duk wani babban ɗan siyasa da suke tare da shi a baya sun bisa amma kowa ya kife musu ciki akan case ɗin. Hakan ya sakasu fahimtar akwai wani babban ƙulli a ƙasa. Dan ko inda Alhaji Dikko ke ɓoye babu wanda ya sani a cikinsu har yanzu. Sun nema ganawa da gwamna amma hakan ya gagara, hasalima amsa ɗaya ake basu a koda yaushe shine yana Abuja. Tashin hankali na biyu a randa Alhaji Dikko ke cika kwanaki tara a hannun hukuma akai ram da babban yaron Hon. Nakowa. Da yamma sai ga labarin kama MM Atik Kumo shima. Kama MM Atik Kumo ya matuƙar ɗaukar hankalin jama’a fiye da na Alhaji Dikko saboda kowa yasan MM Atik Kumo dai ɗane ga tsohon gwamna M Atik Kumo, kuma ogane na gwamna maici a yanzu dan shine ma ya tallata shi ya kuma tsaida shi a takara. Wannan al’amari shiya ƙara maida hankalin mutane da yawa akan case ɗin, yayinda cecekuce ya ɓarke kasancewar kawunan jama’a na neman rabuwa. Wasu na ganin aikin gwamna na ƙyau, wasu na ganin al’amarin akwai lauje cikin naɗi dai. Sai dai yanda mahaifin MM Atik Kumo ya fito yay magana da nuna goyon bayansa akan aikin da gwamnan ya fara da kuma binsa da fatan alkairin kammalawa yasa zukata girgiza. Gwamna ya fara samun mafi rinjayen yabo ga mutane, suna ganin zuwa yanzu da gaske ake aiki za’ayi tuƙuru. Wasu kuma na ganin duk lumbu-lumbu ne kawai na ƴan siyasa musamman da ya kasance gab ake da yin zaɓe. Sai suke fassara abinda ke faruwar da kamar campaign ne kawai, komai na lafawa za’a saki duk wanda aka kaman.
To a baɗini zamu iya cewa kam harda hakan. Domin kuwa shugaban ƙasa shi abinda ke faruwa a Kanon yaja hankalinsa da ganin cewar in fa ya tallafa aka riƙe wannan makamin a ƙasar gaba ɗaya komawa kujerunsu babu fashi. Dan haka ya riƙe wuta shima tare da motsa sauran gwamnonin akan wannan aikinkin fa na kowa ne. Hankalin wasu a ciki ya tashi, kasancewar suma a cikinsu akwai ƴan safarar, wasu ma tsumu-tsumu suna cikin group ɗin na su Alh. Sulaiman ɗinne. Tuni suka fara kaima su Alh. Sulaiman labarin wannan fa al’amarin babba ne, dole akwai ta inda ake kunno wutar kuma dan shugaban ƙasa ma da kansa ya ɗauki lamarin da muhimmanci. Sun tabbatar da hakane kuwa a dalilin kame yaransu da aka cigaba dayi da customers ɗin su ƙananun diloli irin na anguwa da ƙauyuka. Gaba ɗaya duk sai suka sake susucewa da tunanin waye ke buɗe musu sirrika irin haka. A take fa aka fara zaman meeting meeting da bincike-bincike domin kamo bakin zaren. Duk wanda suke tunanin zasu iya buɗe musu aiki sun sakasu a faifai, Daddy shine na farko, dan haka suka zuba masa idanu. Sai dai me ta ko ina sun kasa gane komai, dan iya bibiyar Daddy da suka saka anayi babu wani motsi daga garesa a kansu. Hasalima wani business ya maidama hankali sosai. Al’amarin ya fara sakasu a ruɗani, suka cigaba da bibiyar duk wanda suke zargi amma basu gane komai ba. To dama hasashe ne kawai, domin sun tabbatar duk da wanda ke musu wannan illar ba ƙaramin sani yay musu ba. Sai kawai suka fara zargin junansu kuma. A randa sukai wani zaman da har ya jawo sa’insa a tsakaninsu suna barin wajen meeting ɗin aka cafke Hon. Baita. Al’amarin ya fara kaiwa intaha, dan lokacin da labari yazo ma Alh. Sulaiman harda cin tuntuɓe zai faɗi sai da yaronsa Malami ya tarosa. Hankali tashe ya shiga gida tamkar zai tashi sama. Yana shiga ciki kuma yaci karo da wani bala’in. To bala’i mana, dan ya samu kwali ne da aka nannaɗe da leda mai ƙyalƙyali kamar gift. Da farko bai maida hankalinsa akan abun ba sai da Hajiya Turai ke sanar masa ga saƙo nan ɗazun aka kawo wai a bashi. Kamar zai share sai kuma dai bayan ya gama bige-bigen wayoyinsa ya jawo abun ya hau farke ledar. Dan yanzu ya fahimci komai ma da zai iya zuwa musu ba abin yarda bane ba. Babu komai a ciki face envelopes guda biyu. Babba da ƙaramar. Babbar ya fara buɗewa, inda yaci karo da hotunansa har guda huɗu. Na farko shi da wasu mutanen kudu ne abokan huɗɗar kasuwancinsa suna tsakkiyar cinikayya, dan gabansu akwai cocaine har jaka uku a buɗe, sai jakkar kuɗi daloli a wata jakkar daban, a hannunsa na dama riƙe da ɗauri ɗaya na haggu riƙe da parcket na cocaine yana murmushin sa na basanci. Hoto na biyu tare yake da karuwarsa daga shi sai ƙaramin towel tana zaune a jikinsa itama da towel ɗin. Rawa jikinsa ya farayi, sai da ya wawwaiga falon ya sake tabbatar da shi kaɗaine dai sannan ya tafi hoto na uku. Tare da budurwar tasa ne dai suna shan cocaine a wani guri tamkar club. Da ƙarfi ya jimƙe hotunan cikin hannunsa illahirin jikinsa na wata irin tsuma, shin wanene da wannan aikin haka?. Zuciyarsa dake kumburowa take ayyana masa a hargitse. Tamkar wanda aka tsikara ya fisgi ƙaramar farar envelope ɗin itama ya buɗe. Takarda ce guntuwa a ciki mai ɗauke da gajeren rubutu, da words ɗin cikinta bazasu gaza 150 ba…
*_Da ace kasan ma’anar kalmar gidan rina da baka taɓoba, da ace kasan ma’anar fara takalo wasan da bazaka iya ƙara sawa ba da baka kalleni a matsayin birin wasanka ba. Abinda baka sani ba, ni idan na fara bana ajiyewa sai na kai ƙarshe. Haka nake kwanto nakeyi tamkar mage ta hango abin farautarta, saika gama sakankancewa dana ɓace sai na maka dirar mikiya. Wannan match ɗin sharar fage ne, na zahirin a tsakiyar filin da za’ayi yaƙin DUNIYA na uku zamu ƙarasa shi. Sai ka fara shirin saka sulken yaƙin, danni nawa sun jima a jikina. Ya rage naka neman bindiga, nokiliya, takubba, bomb, domin kare rayuwarka, dan kaima gab kake da bin sahun abokan naka zuwa jail……_*
*_AMM✍️_*
Wani irin gigitaccen ihu ya saki yana mai ɗaga Centre table ɗin falonsa ya wancalakar da shi gefe. “Wanene kai? Uban wanene kai? Dan uban wanene? Idan ka isa ka bayyana kanka mana. Nace ka bayyana kankaaaaa!!”.
Da alama dai Tsule ya fara zarewa bari nayi nan
___________★
A ɓangaren Umma wahala da azabar ciwo ya sata fara sambatu. Tana kwance a ɗaki hawan jini na neman kaita lahira. Bata iya fitowa ba’a iya shiga inda take. Cikin ƙarfin hali tazo ƙofar ɗaki daga ciki ta zube tana kuka da roƙon a kira mata malam na kan tudu ya warware wannan asiri, su taimaka mata dama sai da ya faɗa mata in har asirin bai kama wani acikin Smart ko matarsa ba zai iya dawowa kanta. Batayi zaton hakan zata kasance ba shiyyasa ta amince. Da farko babu wanda ya fahimci abinda take nufi, sai da ta cigaba da kururuwa da ihu mutan gidan suka fara maida hankali a kanta. Aunty Amarya ce tai kiran Ammah dake ɗaki tana waya da Lulu. Duk da Ammah ta jima da wannan zargin a ranta zantukan Umma sun kiɗimata, amma baiwar ALLAH haka tai kiran Abba tana roƙonsa ya dazo gida. Kamar zaiƙi sai kuma dai yace gashi nan dama ba nisa yayi da gidan ba. Koda yazo yaji shima abinda Ummahn ke faɗi sai ransa ya sake ɓaci, wajen yay niyyar bari da tabbatar musu da shi fa babu ruwansa su kira ƴaƴanta. Sai da Ammah taita roƙonsa da magiya yaran gidan na tayashi sannan dai ya haƙura ya dakata amma yay kiran Yayanta Jibirin. Zuwansa yasa suka fara mata tambaya, da ƙyar take amsawa da basu adireshin inda malam na kan tudu yake. Anan ma Abba ya bijire bazashi ba, da ƙyar aka taru a kansa daban haƙuri dai, sai dai yace ba ranar ba dan bazaiyi tafiya cikin jeji da yamma ba. Dole suka barsa sai a washe gari aka shirya tafiyar a motar Salim da ya yarda zaije da ƙyar, dan shima sai ƙunƙuni yake akan tafiyar, damma dai Abba ba kanwar lasa bane.
Su biyar sukai tafiyar, Abba, Salim, Kawu Jibirin da Kawu Idi shima ƙanin Ummah ɗinne, sai ƙanwar Hajiya Naqiba da suka taɓa zuwa wajen da ita, itama wai zata amsowa ƴar uwarta magani dan ƙafar Hajiya Naqiba ta rure tana jan ruwa ne. Sun sha wahala, yayinda motar Salim taci ubanta a hanyar jejin cikin sahara, da ga ƙarshe ma dole suka ajiyeta a wani waje suka cigaba da tafiya da ƙafa. Matuƙar mamaki ya kamasu da ganin inda wai su Ummah ke zuwa yin mugun abu, can wani ƙauyen Jigawa ne, bama cikin ƙauyen bane a bayan gari bokan yake sosai cikin tsakkiyar sahara a saman dutse (dan bama ce malami ba). Duk azabar zafi ranar wajen baya damunsa, dan ko bishiyoyin kirki babu saboda sahara. Da ƙyar suka iya hawa dutsin, Salim ya fasa hannu, cikin zafin azaba da ɓacin rai ya ce,…….✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
Zafafa
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*