Furar Danko Book 2Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Furar Danko Book 2 Page 54

Sponsored Links

 

‘…..!!

Related Articles

 

5️⃣4️⃣

 

…….Hankalin ƙanwarta da ke jiyosu a tashe ta dannama mahaifiyarsu kira. Tana ɗagawa ta sanya mata kuka da faɗin suzo dan gida babu lafiya. Ga mijin auntyn ta nan zai kasheta. Wannan kalmar ta kisa ta ɗaga hankalin mahaifiyar tasu, babu ɓata lokaci kuwa sai gasu sun iso. Iya ƙoƙari iyayenta sunyi Dan ganin ya kwantar da hankalinsa an sasanta komai amma yaƙi sauraresu. Ya kuma babbake ƙofa yana jiran ta fito. Dole mahaifinta yay kiran Baba Garko. Baba Garko yaso ƙin shiga maganar, sai da ya jiyo manya-manyan ashariya da munanan kalaman bakin ɗan nasa ta cikin waya sannan ya shiryo yazo. Karo na farko kenan da suka haɗu tun bayan badaƙalar auren Lulu. Da ƙyar aka fidda amaryarsa a gidan bayan yasha mari a hannun Baba Garko. Sam bakinsa bai mutu ba, faɗi yake sai ya kasheta idan bata bashi abinda ke wajenta ba. Itako tana rantsuwar bazata bada ba. Ana tsaka da wannan rikici itama Hajiya Turai ta fito ƴan aikinta janye da akwatuna. Bayan ta gaida Baba Garko cikin girmamawa yake tambayarta mike faruwa a gidan haka. Tana kuka ta sanar masa iya abinda ta sani, harda marin da itama yay mata. A cewarta tasan itama amaryar tasa babu abinda ta ɗauka masa, ya jefa abunsa wani wajene kawai ya huce a kansu, dan haka ita gida Sokoto zata wuce. Baba Garko bai hanata ba dan shi yama rasa abin cewa gaba ɗaya…..

*_★UK★_*

Watan Aunty Bilkisu ɗaya da sati uku cir aka sallameta da ga asibiti. A lokacin Lulu nada wata biyu da sati guda a UK. Doctor ɗin da ke tsaye akan lamarin aunty Bilkisu ce ta duba Lulu a ranar da tazo yin planing. Kamar wadda aka matsi bakinta a ranar sai take tsokanar AA dake ta tsale-tsallensa a ɗakin dan yanzu yayi ƙafa. Cikin ƴar dariya take cewa Lulu ta bata fine boy ɗin nan nata dan ita dai tana sonshi. Lulu tai murmushi kawai da faɗin cewa ta bata. Dariya ta sakeyi da cewar karfa daga baya tazo tace zata amshe, tunda taga ita matsoraciyace tana gudun samun wani cikin. Nan ma dai Lulu sai tai ɗan murmushi kawai ta basar gabanta ba faɗuwa dan Smart na a ɗakin sai dai waya yake yi. Likitar nan da neman magana ta sake cewa abinda ta saka mata bai dai bata matsala ko?. Da sauri Lulu takai dubanta inda Smart yake tsaye AA na jikinsa ya riƙe masa ƙafafu. Ido suka haɗa da shi, tai saurin janyewa zuciyarta na wani irin rawa, dan tunda ta yaye AA baida magana sama da ALLAH yasa ta samu ciki. Kanta ta dafe tana rumtse idanu, sai kuma ta ɗago ta kalla doctor ɗin da tuni ta maida hankali akan Nurse ɗin dake cirema aunty Bilkisu abu a jiki suna magana. Addu’a ta shiga yi a ranta ALLAH yasa kada parrot ɗin likitar nan ta sake magana. Yayinda take satar kallon Smart ta gefen ido. (ALLAH yasa mutumin nan bai ji ba) take ta ambata a zuciyarta. Lokacin da ya kammala wayar yana takowa inda suke jitake sayin takun nasa tamkar yana yinsa ne da bugun zuciyarta. Bai nuna mata yaji ba, duk da yanayinsa ya sauya. Dan ko kallonta baiyi ba ya ƙarasa gaban aunty Bilkisu rike da hannun AA. Tambayarta yake badai tajin komai ko. Ta tabbatar masa da Alhmdllh. Kansa ya jinjina cikin lumshe ido, tare da juyawa ga doctor yace yana son magana da ita. Cikin tashin hankali Lulu da ke kallonsu ta gefen ido ta ɗago gaba ɗayanta. Nan ɗin ma bai kalli inda take ba ya saɓi ɗansa a hannu sukabi bayan Doctor ɗin. Da sauri ta motsa zata bisu, aunty Bilkisu ta kirayi sunanta cikin katse mata hanzari. Dan ita sam bataji furucin Doctor ɗin ba lokacin hankalinta nakan Nurse. Dole Lulu ta dawo badan taso ba. Sai dai gaba ɗaya jitake komai ya tsaya mata cak, hatta iskar da take shaƙa da fesarwa bata gamsar da ita. Kusan mintina goma Smart ya dawo ɗakin, daga ƙofar ɗaki ya dakata yana faɗa musu su sameshi a waje. Aunty Bilkisu ce tayi ƙarfin halin amsa masa. Lulu kam jitai tamkar an ƙarasa zare mata jijiyoyin jikinta.
Sun samesa a inda yace ɗin, Nurses ɗin da sukaima aunty Bilkisu rakkiya biye da su. Suna tsaye har sai da suka shiga mota sannan suka juya ciki. Aunty Bilkisu ya kalla ta mirror yace ta saka belt, daga haka bai sake magana ba ya tada motar batare da yace itama Lulun ta saka ba. Hakan ya mata ciwo, dan in har zasu fita shi da kansa ma yake saka mata belt amma yau ko arziƙin ta saka ɗin ma bata da. Jiki a saɓule ta saka tana mai karanto sunayen ALLAH a ranta, zuciyarta fal tunanin mi yaje yayo a wajen doctor ɗin. Rashin amsa ya sata jan bakinta tai shiru. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan, ya ɗauki ɗansa yay shigewarsa. Sai itace ta taimakama aunty Bilkisu da Iya Tabawa data fito dan ita suka bari a gidan. Baya falo sai AA kawai da ya fara karakainar ɓarnar da yafi ƙwarewa a kai. Da’alama anan ya ajiyesa ya shige. Dole ta cigaba da daurewa suka zube a falon suma. Suna nan zaune ya fito cikin shirin fita, tayi mamaki dan tasan a irin wannan lokacin yana a gida baya fita ko ina. Tana son masa magana tana tsoron ya yaɓa mata mai zafi. Duk da dai bai taɓa kwatanta hakan a gaban wani ba. Aunty Bilkisu ya cema tasha magani ta kwanta, da ga haka ya ɗauki AA suka fice.
“Wai shi wannan mike damunsa? Naga tunda ya gama wayar nan ya wani canja gaba ɗaya kamar wanda ke’a cikin ɓacin rai?”. Aunty Bilkisu ce mai maganar tana kallon Lulu. Murmushin ƙarfin hali ta saki da faɗin, “Ƙila wani abu mara daɗi aka faɗa masa a wayar aunty, kin sanshi da zurfin ciki. Idan bashi yaso a sani ba ba faɗa zaiyi ba”.
“Aike naga ma da sauƙi Mawaddat. Amma a sanin da naima Hydar akan shiru-shiru banyi zaton zai iya sakewa da mace haka ba. Dan da idan yana abu saika ɗauka yana jin ƙyanƙyamin mutane ne ma. Ka faɗa masa magana ashirin ya baka amsar ɗaya sauran in zata kasheka ne ma ta kasheka babu ruwansa”.
Dariya zancen aunty Bilkisu ya bama Iya Tabawa. Lulu ma sai tai murmushin ƙarfin hali kawai….

Tsahon lokaci basu dawo gidan ba. Lulu ta kasa samun nutsuwa sau uku tana kiran wayarsa bai ɗaga ba. Sai da ta gama galabaita da rashin dawowar tasu sannan sai gasu. Iya Tabawa ce ta amshi AA da yay barci, shi kuma ya shige ciki abinsa bayan ya ajiye musu abinda ya shigo da shi ya shige da sauran ciki. Taja mintuna kafin ta tashi tabi bayansa, dan ita dai kam da wannan fisge-fisgen gara ayita ta ƙare kawai yamayi komi zai yi yafi mata sauƙi. Ta samu har ya shiga wanka, dan haka ta zauna bakin gado zaman jiran fitowar tasa. Zuwa can kuwa sai gashi ya fito da bathrobe a jiki yana faman goge kansa zuwa wuyansa da ƙaramin towel. Kallo ɗaya yay mata ya kauda kansa. Gaban mirror ya ƙarasa ya fara shafa mai, dan haka ta taso jiki a saɓule cikin dauriya tana faɗin, “Wai mike damunka ne? Gaba ɗaya ka canja ko wani abu ya faru? Idan abinda kaji doctor ta faɗa ne dan ALLAH ka saurare ni na maka bayanin da zaka fahimta”.
“Anyi wani abu ne?”.
Ya faɗa kamar a gatsine”.
Rasama mi zatace masa tayi. Sai kawai tai tsaye ta zuba masa ido. Suna samun saɓani, amma bata taɓa ganin ɓacin rai a tattare da shi irin yau ba. Dan saɓanin da suke samu ƙaramine a take su shirya kuma. Amma wannan duk ya ɗaureta da jijiyar wuyanta. Harya kammala shafa man ya miƙe zuwa wajen kayansu bata sake iya cewa komai ba. Babu jimawa ya fito sanye da pyjamas masu laushi, turare ya fesama jikinsa ya haye gado abinsa tamkar ma ya manta da ita a ɗakin.
Da ƙyar ta iya furta, “Coffee fa?”. Dan yana shansa sosai. Batare da ya kalleta ba yana jan duvet jikinsa ya ce, “Naƙoshi.”
Zuciyarta tuƙuƙi take mata, dan haka cikin rawar murya ta sake faɗin, “Dan ALLAH ka tashi muyi magana, dan nasan wlhy abinda likitar nan ta faɗa ne ya ɓata maka rai, tunda kafin hakan ai cikin farin ciki muka fita, kuma ko’a can ma babu wani canji a gareka sai da akai maganar. Ni gask…..”
A wani irin fusace ya ɗago yana kallonta. Tuni idanunsa sun kaɗa jazur. Cikin kaushin murya da ɓacin rai ya ce, “Mawaddat bana son damuwa. Kinji nace miki wani abu ne? Kin tambayeni na faɗa miki babu komai, to mikike son nace miki. Please bana son hayaniya ki barni nai barci na. Idan kuma ɗakin kike so na bar miki ki cigaba da damuna”. Daga haka ya juya yay kwanciyarsa da sake jan bargo ya rufa. Jikin Lulu rawa ya farayi dan ɓacin rai. So take itama ta masa masifar amma ta kasa, ta rasa miyyasa take jin shakkarsa a yanzu har bata iya maida masa murtanin magana balle yin wani yunƙuri. Gaba ɗaya cika mata ido yake da wani irin kwarjini, girmansa take gani mai girman gaske da bayan mahaifinta da Uncle Yousuf bata ganin wani ɗa namiji da shi a duniya. Bata son ganin ɓacin ransa a yanzu balle ace itace ta ɓata masa. Ko yaya taga yayi fushi hankalinta tashi yake yi har sai taga sun shirya….

_____★

Sam babu daɗi a tsakaninta da mijin nata ɗan tsakanin nan, zai zauna yay wasa da yaronsa suyi hira da Iya Tabawa da Aunty Bilkisu amma ita banda ita. Ya ƙaurace mata a shimfiɗa, abinci ma idon su Aunty Bilkisu ke sakashi ya ci. Amma idan daga ita sai shine sai yace ya ƙoshi. Suna a wannan halin ya wuce Coventry wasa. Tafiyar tasa ta bata damar zuwa asibiti ta nunama doctor ɓacin ranta akan abinda ya faru da tambayarta su dama basu da sirri ne tsakaninsu da patient nasu, haƙuri ita dai doctor ta bata dan batai zaton al’amarin zai zama a haka da girma ba. Sannan ta faɗa mata bata san mijinta bai sani ba ai.
Kwanansa uku ya dawo. A ranar ne ta gama shirya sai dai suyi duk wacce zasuyi. Dan ta haɗa kayanta tsaff akan zata koma Nigeria. Kamar yasan shirin nata bai shigo gidan ba wannan karon sai dare. A yanayin gajiyen da yake yasa bai zauna ba suka gaisa da su aunty Bilkisu sama-sama ya shige ciki……..✍️

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*

Zafafa

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*

Leave a Reply

Back to top button