LAFIYA JARICE

KO KASAN AMFANI CUCUMBER A JIKIN DAN ADAM.

Sponsored Links

 AMFANIN CUCUMBER A JIKIN DAN ADAM TARE DA YADDA AKE LEMON  CUCUMBER 

written

   by

Maijidda Bello

       and 

 Hauwa’u Mohammed

   Jama’a da dama suna daukar CUCUMBER a matsatmyin wani sindari dake karawa abinci dadi ko samar da nishadi da jin dadi yayin cin abinci da shi,wanda kuma zahiri amfanin sa ya wuce haka nesa ba kusa.

 Inda a yau insha Allah zamau kawo amfani guda 7 da CUCUMBER yake da shi a  jikin bil adam.(dan Adam) .

                AMFANIN CUCUMBER 

1-Yana gyara fata

2-Yana rage kiba

3-Yana yakar cancer

4-Yana kara lafiyar gani(ido)

5-yana tsaftace nunfashi(yana magance warin baki yayin magana

6-Yana control na low blood pressure

7-Yana hana zubar jini ga masu haila,da masu basur mai zubar da jini.

            YADDA ZA’ A SARRAFA SHI.

     Da farko zaka samu CUCUMBER mai kyau kamar guda daya madaidaici sai ka yanke hancin sa ka wanke sosai ba sai ka cire bawon ba sai ka yayyanka kanana sanan kayi blending din shi da ruwa kamar kofi day madaidaici sannan kasha da safe bayam.

Tsawon sati 2.

       YADDA AKE LEMON CUCUMBER 

        LEMUN ZOBO DA CUCUMBER

                        KAYAN HADI:

 

1-ZOBO

2- CUCUMBER

3-LEMUN TSAMI

4-SUGAR

4- CITTA DA KIMBA

5- FILABO

                 YADDA ZA KI/KA HADA:

ki/ka dafa zobon ki tareda citta da kinba ki jefa lemon tsami cikin dahuwar zobo guda 3 Dan sunfi dadin matsawa ruwa yafito idan aka dafa, saiki yanka cucumber ki manya guda 5 kiyi blending ki tace, wurin tacewa zaki matsa lemun tsamin, karki cika ruwa. Saiki tace zobo shima ki hadeshi da cucumber da kika tace, kisa sugar da filabo sai ki juya harsai sugar ya narke kisa a fridge yayi sanyi.

Za mu cigaba da Kawo muku yadda kalulin style na jusy da sauransu.

                   Domin karin bayani  

Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 

Leave a Reply

Back to top button