TUMFAFIYA 54
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
 ,,,,,,,,,,
5️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
 DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
 MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
 AMIN,,,,,,,
Sannu a hankali wani irin shakuwa da sabo yake shiga
 tsakanin mu wanda hakan ya kara kwantar min da hankali a gidan matsalata dayane
 zuwa biyu shine irin matsalan dake tsakanina da uwar Ahmed da kannen sa har ma
 dai ita karamar tafi shiga min ido sosai.
  Don dayan ba zance
 ga wani matsalan daya taba hadani da ita ba saidai kawai ba sakin fuskane itama
 daga wajen ta kamar yadda uwar da yar uwan keyi min.
   Sai tsohuwar gidan
 ce mai sake min fuska don ina zaune zanganta a parrt dina ta shigo mu danyi
 hira ta kuma ta ban hakkuri na daure da yanayin dana tsunci kaina a ciki wata
 rana sai labari.
    Nakanyi mata godiya idan ina da abu na dan
 bata ko nayi dafuwa in saka mata da dan yawa duk da nasan bata iya cinyewa ita
 daya .
   Don su din na kula
 da sunyi fushi kan zancen abincin da master yace a daina sakawa dasu din gashi
 koni din bako yaushe yake bari inyi girki ba a part din mu din.
  Saidai idan zai dawo
 ya sayo dan wani abu mu danci harda ma yan cikin gida wanan sallon kuma yasa
 mahaifiyar shi saka ido ga hakan da yakeyi din .
  Tana fada ranan a
 gabana cewa wanan ai salon kashe mata dane aka dauko wai ace mace ba zata girka
 abinci suci ba sai an fita an sayo abin kwalan a kasuwa taci.
   Da Dije taji fadan
 yayi yawane ta fito tana fadin kai kai Rashida baki biyo halina ba wallahi baki
 da godiyan ubangijo ko kadan dake watace sai ki godewa Allah daya hada danki da
 yarinyar nan a yanzu.
   Koda yake ba abin
 mamaki bane don kinyi hakan a yanzu don baki san irin wahalan da muka fito a
 cikiba a baya har zuwa ranan da Allah ya hada dan naki da yarinyar nan abubuwa
 suka fara bude mashi.
   Fadin hakan da
 tsohuwar tayi sai naji maman ta saka kuka tana fadin Dije ko baki min gori ba
 nasan na tafi na barku a cikin wahala shekara da shekaru nima kuma hakan ai ba
 laifina bane tunda aure nabi.
    A,  toh ni dai na fada in kina cire ido ga yaran
 nan ki cire don arzikin su yazo data idan kinyiwa dan ki sawal, walin tsiya
 kuma ya rabu da yarinyar nan wanan kuma kinwa kanki don dai ki sani.
   Shine kwana biyu
 naji shiru ta daina shiga harkan mu tama dauko fita in tabar gidan tun safe sai
 yamma zata dawo.
   Da yan kushin
 abubuwan irin su rake yalo karas lemu mangoro ayyah da sauran su a nan zasu
 baje saman tabarma da yaranta suci sai wata rana wata rana akan debo min akawo
 min dan kadan.
   Saidai Allah bai
 sako min kwadayin irin kayan nan ba wata rana in karba in aje idan ya shigo shi
 zaici wata ran kuma ba zan karba nace a mayar nagode.
    Sai su cinye
 abinsu ko wanda ake kawo min din ma ita yar babban yar nata Aishan ce kecewa a
 diba min sai karamar ta yatsune baki tace abinda baida yawa zatace wai sai an
 dibamin shi.
 Haka dai zasuyi ta
 fada a tsakanin su har ta kawo min ruwa kuma koda sanina koba da sanina ba haka
 zasu shigo su bude fridge su dauka susha saidai wanan bai dameni ba kamar yadda
 sukanyiwa fridge kamar da gaiya zakaji an rufe shi da karmi har sai mutum yaji
 shi har cikin ranshi .
   Irin hakan wata
 rana ya faru yana gidan Asmau tazo ta dauki ruwa ta buga marfin saida duk muka
 zabura lokaci guda.
   Ya mike yana fadin
 meye hakan da kyar na iya dago kai na bashi amsa da frige ne aka buga wata kila
 wanine ya dauki ruwa a ciki.
   Ya juya ya fita a
 hasale ya samu yarinyar Asmaun daice ma lokacin yayi mata tas saiga uwar ta
 fito tana fadin don ruwan da nace ta dauko min din shine zaka zo kana kokarin
 fadawa mutane maganan banza.
   Ke karbi ashirin ki
 karbo ruwan ki mayar masu don Allah kuma daga yau kada wanda naga ya koma shiga
 sashesu da sunan dauko wani abu.
    Innan mu bafa
 fadan an dauki ruwa yakeyi ba yadda asmau ke buga masu marfin fridge dine yayan
 mu ke magana a kan shi.
   Wani tsawa ta dakawa
 yar nata da saida ta kadu lokaci guda ta koma ta rakube a bayan Dije tana ci
 gaba da sauraron uwartasu dake sake magana.
   Inna nifa ba ruwa
 nace meyasa ta dauko ba yadda take rufewa yarinyar nan fridge ne bai mun ba don
 Allah ai mata magana ta bari.
    Yana fadin hakan ya juya ya tafi ya dawo
 dakin yana cicika kafin muji muryan Asmau tana sallama tare da fadin ga ruwanan
 ance in kawo.
    Ya mike ya fito da
 sauri yabi bayanta yana kiran tazo ta dauke ruwan ko ya saba mata abin taron
 kurciya dukansu sai ya kwasa ya bita da gudu ita kuma ta koma bayan uwar dake
 hasale ta boye tana leken shi a inda yake tsaye yana wa uwar kallon mamaki.
    Dake fada tana
 fadin don ruwa kawai zaka taso min ya a gaba zaka doketa ina dai don ruwan kake
 wanan hasalan gashi kuma na sayo na mayar maka da abinka.
   Mama don me nake
 sayen ruwan ba don asha bane nake sayowa ni magana nake mata cewa ta dinga kula
 mata da kaya kada a bata matashi.
   To ai shina nace
 mun daina tabawa ruwan kuma dana dauka nasha gashi nan mun biya koba shike nan
 ba ta fada tana mai wani irin kallo na tsana.
    Kai Amadi maza
 koma ka zauna in fita zakayi kuma tai zuwa inda zaka ke kuma in dai radhin
 kunya abin yine ki   biyewa uwarki gara
 ita takamanta a yanzu na haihuwan shi da tayine keko fa ?
   Ina shi din daine
 gatan ku garin nan don in kun iya ko abinci sai ku daina cin wanda yake sayowa
 kunaci din karewan dai ke nan ke yar banza ko mutum daya kun gani gidan nan da
 sunan dangin uban ku halan ?
   Zaki biyewa uwarku
 da bata san ciwon kanta ba kunawa yaro iya shige iri iri idan yai magana uwarku
 ta tare maku tundai ke Asmaun nan ba ma,un arziki kike ba wallahi don duk wani
 iskanci da iya shige kece ummul,abasin shi a gidan nan yanzu.
    Ko shekaran jiya
 in kula dake da kika gama wanki yarinyar nan tana shigowa kika dauki ruwan
 wankin nan kika watsa mata da kadan a jikinta in ba Allah ya gyara ba.
   Ido waje yace kin
 gani ba kingani ba Dije ni idan zasu takurawa yarinyar nan ne gaskiya saidai
 nabar gidan nan mu koma haya da ita don ba zan dauki hakan ba a rayuwata tunda
 yan uwanta ni basu raina min ba don me ni nawa zasu dunga wullakanta min ita ?
    Jeka ai abin
 baikai na barin gida ba yar banza maganin shegiya mara kunya zanyi gidan nan
 tun kan aika ga hakan asirin mu ya tonu idan ka bar gidan nan yanzu da dan Amo
 ya gwajesu yaran banza kawai.
   Ya juya ya tafi har
 ya shigo part din kuma yasa kai ya fita zuwa wajen dabbobinsu a nan Aisha din
 kanwarshi ta bishi tana fadin.
  Yayan mu kaiyi
 hakkuri nima ynzu na gane gaskiya abinda akai wa amarya ba a kyautawa ko ranan
 ni nishigarwa maganan da Dije ka hwadi dazun da niyi magana innan mu ta dawo
 Asmau ta kwashi karya da gaskiya ta hwada mata.
  Kije ai ba komai duk
 abinda mutum yayi don kaine don kuma baku san irin gidan da zaku hwada ba ai ga
 amre don Allah yayan mu kayi hakkuri damu da innan mu.
    Ya duka yana gyara
 wurin dabbobin yana fadin ki tahiyar ki ai komai ya wuce garan nikan bandai
 yadda a rainawa matana da wayo don na aurota gidanga shin hakan laifina ?
  To in abin yayi min
 yawa daukan mata zanyi mubar garin in koma gidan ubana mu zauna don su can basu
 gudun mu duk wanan abin na kula cewa dani innan ku ke adawa kiyayyana ne ya
 shafi Zahra yanzu itama.
  Yarinyar tayi shiru
 na dan lokaci kafin ta furta don Allah kayi hakkuri ta juya ta tafi dama ya
 fadi hakan ne don yasan sako ya bata zai isa kunnen mahaifiyar nasu.
    Yasan kuma ba zasu
 taba yarda dacewa ya koma gun mahaifin nasa ba a yanzu don irin yadda suka
 kulla shi a ransu irin yadda suke ganin yayi banza dasu a baya sai yanzu da
 yaro ya fara tasowa zaice zai koma garai.
    Tana shiga ta samu
 suna maganan tsakanin Djje da innar tasu nan ta samu wuri ta zauna tana
 sauraren su kafin a kawo inda ta tsoma baki tana fadin.
   Ai yayan yace
 tahiyatai zaiyi gidan ubanai wane uban ne ubanai uwar ta tambaya a hasale tana
 kallon yar nata.
   Lokaci daya suke
 kara tambayan junan su da cewa wane uba kuma to ai yanzu kin gani kinji
 hukuncin da dan naki ke kokarin yankewa zuciyarshi yanzu akan halin da kika
 dauko mashi a yanzu.
    Sai in bani raye hakan
 zai faru mutymin da yai tahiya tai bai ko taba tunawa da muwa ba a duniya sai
 shi da rashin zuciya ya daukeshi ya kaishi inda yake .
   Yan uwanai sunka
 taho nan da barazana waisu ga dangi wagganshi ko yasan inda yake yanzu maganar
 banza da wofi kawai.
   Ki dai natsu kada
 wani abu yaja maki bacin rai daga baya wanda ba maganin hakan a gareki yanzun
 dai kekin ka rage da shawaran da zai fusheki inba haka ba kina kallo danki ya
 gujeki saboda halinki na banza.
  Shiru tayi har
 tsohuwar tagama ta naji tayi shiru tana nazarin zancen tafiya gidan ubanshi da
 kanwar nasa ta fada masu lokacin.
   Ina kwance ina
 karatun handout a hannuna don abin ya dan shige min duhu shi kuma baida lokacin
 zama ya koya min karatu yanzu sosai.
    Sallama nake ji a
 kofa yasa na aje takardan na mike zuwa falon din don ganin wace ke min sallaman
 Tani ce mai aikin ummah bansan lokacin dana sako fara,a a fuskana ba lokaci
 guda ina fadin.
   Tani kece da yamman
 nan ta karaso ciki tana fadin wallahi uwar dakina yau dai nace barin lekoki
 muji lafiyan ki kwana biyu shiru koda yake hjy tace min ai kuna gaisa.
    Tani ai nayi fushi
 rabon ki da gidan nan har na manta na dauka kema ke manta dani ai yanzu takai
 zaune inda taga alaman nake nufin ta zauna don ganin na cire filon dake wajen .
  Uwardakina aure kan
 ya karbe ki kinga yadda kika koma kinyi kiba hasken ki ya karu ai kan zaijewa
 hjy dake cikin damuwa akanki da wanan labarin mai dadi wallahi.
   Kin kyauta da kika
 rufawa kanki da mahaifiyar ki asiri inyi hakan ne garuku dan a cutawa rayuwan
 ku kekan alheri wanan aure ya zama maki yanzu.
   Ba irin auren yan
 uwanki ba da yanzu ya komawa iyayyen ciki kullun ana gida tare da uwa shiyasa
 nake fadawa hjy cewa hakan yafi maku in anyi da sunan kuntata maku yanzu ya
 zama alheri a wajem ku.
   Don ga zahiri na
 gani nikan walle hjy zataji dadin labarin nan nawa dama damuwanta shine ba
 komai kike iyaci ba a rayuwanki.
    Banda matsalan
 abinci ko abunsha don gaskiya ina samu iya karfin shi Tani ba laifi yana iya
 kokarinshi dani alaman jin dadin hakan dana fada ya baiyana a fuskanta dkn
 bakin danaga ta kara washewa lokaci daya tana fadin.
    Haka akeso ka
 godewa Allah da mai maka idan har yana maka ko da kadan ne watarana idan ya
 samu zai maka wanda yafi hakan ai.
    Ki kara hakkuri
 sosai sama da wanda kikeyi din yanzu insha Allahu zuciyana tana bani cewa kinyi
 dace da miji nagari wanda kowa keson samun irinsa nan gaba.
    Don nasan baki
 sani ba duk jumma,a yanzu zaije gidan ku ya kwashi kannen ki yaje masalaci dasu
 idan zasu dawo kuma ya hadosu da tarkacen makulashe ya dawo dasu.
    Haka duk ranan
 talata yakan zo ya gaida mahaifiyar ki har yayi kokarin masu alheri hjy taso
 hana hakan amma nayi mata magana ta daina kinga kuwa ko hakan abin alfaharine
 gareta yanzu.
   Aiko kinga bai taba
 nuna min yana zuwa gidan mu ba fa koda wasa bai nuna min hakan ba yakan dai
 kira waya ya bani mu gaisa idan yana gida wanan kawai nasani ni.
    Na fada maki hakan
 ne don ki kara rike mijin ki da zuciya daya kamar yadda shima ya rikeki har
 cikin ranshi.
    Muka dan taba hira
 wanda taso ta fada min halin da Aisha da Rukkaiya ke ciki a gidajen auren su
 nayi saurin tarewa da fadin Allah ya kyauta yasa su gane gaskiya su rikesu
 amana ta amsa da Amin.
   Da zata tafi na
 hado mata clean da sabulun wanka da yan tarkace harda soyayyen nama tana ta
 godiya muka fito na rakata ta gaidasu Dije munyi sa,a inna ta dawo har ita suka
 gaisa tana ta kallon ledan dana rikowa Tani din tana son tantace abinda ke
 cikin ledan lokacin.
   Bayan na dawo daga
 rakiyanta din zan koma part din mu naji muryan Dije tana kirana da yaki nan
 amarya nazo take fadin.
  Nace matar nan ya
 kuke da itane wai na dan sake murmushi ina fadin mai aikin muce ita keyiwa
 mamata aiki ai.
   Bana fada maki
 basuda alaka ba dama wanan yar garita sosai yar unguwan tudun wadace ai
 shinagani haka kawai mace ta mayar da kanta baya taje tanawa wata katuwa aiki
 kamarta.
   Uwar Ahmed ta fada
 hakan yasa na dan daga kai na kalli gefen da take take naji raina ya baci har
 yanayina ya canza taci gaba da fasin baki fini ba don kwadai kina kwance da
 yayan ki ni ina maki wahala.
  Muryan Dije naji
 tana bata amsa da fadin yafi mata alheri don hakan yafi mata yawon tallan gida
 gida wai kayan mata ana daukan ta yar iska mara kamun kai .
   Inno tallan nawa
 shine na kika kira da iskanci ta fada cikin tashin hankali sai tsohuwar tace
 aikin nemam na kai da rufin asiri ma an zageshi mai zai hana masu yawon talla
 kica kica suna gogaiya da maza ba a zagesu ba.
   Nan ta soma cewa ni
 dai waga sana,an bari nai nikai gara inyi zama hakan tunda ya zama illa garan
 yanzu kuma .
   Nidai na wuce da
 mamakin su a raina ina mai jin zafin irin yadda uwar mijin nawa takan jefeni da
 kalamai haka masu zafi kai tsaye.
  Ban taba fadawa
 Ahmed ba saidai idan shi yaji ko yagani idan yana gari ya dauki matakin hakan
 don yakan dan debi kwanaki yana school zaria inda yake hada masters din shi
 yanzu.
  Yayin da ni kuma
 nake nan gusau ina hada nawa digree din wanda a lissafina saura shekara daya da
 yan watani na hada karatun nawa lokacin.
    Tani kuwa ta koma
 da labari mai dadi wurin ummah wanda hakan yasa ummah farin ciki tayiwa Allah
 godiya don ko tani bata raga komai da taji ko tagani ba a ziyaran data kai min
 din harma da kari.
  Ba abinda yaiwa
 ummah dadi a cikin labarin sai jin da tayi nayi kyau daki sosai a bakin mutane
 ga kuma karatuna yana tafiya daidai haka kuma ina zaune lafiya da kowa a gidan.
    Dama damuwanta ke
 nan dani idan ta tuna cewa bana son yawan mu,amula da mutane sosai a rayuwana
 gashi kuma Allah ya jefani gidan yawa yanzu.
    Satin shi biyu a can
 zaria din ya dawo ya dubamu ya samemu lafiya saidai ya samu wai kayan abincin
 su ya kare dole ranan ya fada kasuwa yayo masu sayayya ya kawo masu dan ledan
 semo da kubewa danye ya riko muna jin karan ledan yasa uwar kyala idonta akan
 roban tana son sanin meya dauko a ciki a zaton ta wani abin dadine ya sayo min.
    Aisha ki dauki
 ledan nan ki kaiwa Zahra ta tuka muna shi don naga nata ya kare ya fada don
 kawar da wani zargi a zuciyar mahaifiyar nasa lokacin.
    Da sauri yarinyar
 ta dauko ledan zuwa part dina ta sameni a dan kitchen dina na dora ruwa don
 ranan nasan yana gari zan girka muna abincin dare ke nan ranan.
   Don in baya nan
 saidai nasha tea ko complain in kwanta ban damu da girka komai ba tunda ni
 kadaine kuma abincin bai dameni ba ni .
    Amarya yayan mu
 yace in kawo maki ki girka ta fada tana miko min ledan dake hannunta din na
 juyo ina kallon ledan kafin nace me kuma ya kawo yanzu har na dora ruwan zafi
 zan zuba shimkafa a wuta ?
   A gaban ta na bude
 komai ta gani tace na bata kubewan taje ta gyara min sai hakan yai min dadi
 sosai don dama shine abu mai wuya ga aikin nake gani gashi kuma ta taimaka min
 da gyaran shi.
   Don haka na hada na
 wanke da kyau na miko mata tare da abinda zata gurje min shi ta tafi wurin su
 dashi ni kuma naci gaba da aikina.
  Duk daba saurin
 aikin nake dashi ba amma ina kwantar da hankalina na girkashi da kyau yayi dadi
 saida saurin aikin da bandashi kawai ne matsalana.
    Sai gani nayi
 Aishan ta dawo min da kubewan data fara gurza ranta kuma bace tana fadin anty
 kiyi hakkuri ban kai ga gamawa ba innan tace in dora girkin mu.
   Na mika hannu na
 karba ina fadin aiba komai ko hakanma nagode ai saura kadan ki gama min ba zan
 dade ba zan gyara shi yanzu.
  Tace bari dai in
 tsaya nan in karasa maki kafin na koma ita innan mu bansan abinda ke damunta ba
 haka wallahi dan wanan zatace din me na karbo maki aiki in tayaki bayan ga namu
 nan har na dora tukawa kawai zanyi yanzu ida
 na gama.
    Muna magana tana
 gurza da sauri tana kallon hanyan shigowa part din namu saura kwara uku ta kare
 nina juya ina kokarin yin talgi mukaji muryan mahaifiyar nasu a bayan mu tana
 fadin.
   Kekan anyi mara
 wayau  da rashin sanin ciwon kai na
 rasama me zan kiraki dashi naji sanyi yanzu kece don rashin sanin ciwon kai
 zaki dawo nan kina kamawa wata aiki kin bar na uwarki can yana konewa ?
   Kiyi hakkuri mama
 don Allah na fada daga inda nake tsaye nasha jinin jikina don banson wani abu
 ya hadani da matar nan ko kadan don ban hango kaunata ba a zuciyar ta.
   Don Allah ki rufa
 min baki idan ba lalaci ba wanan dan girkin ne za ace sai an kama makishi ko me
 ko idan kin dafa damu zakuci ?
   Naga yar nata ta
 kallota da sauri tace ke kuma munafuka kallon me kike min don na fadi gaskiya
 tasan ba zata iya kula dashi ba tayi auren ko an fada mata yar aikina haifa
 matane tunda sun saba kwanciya ana girka masu suna ci ko ?
    Ke Aisha fito ki
 koma cikin gida ki daina zuwa kama mata aiki tunda tana iyawa inma bata iyawa
 ai gani saiki fada min abinda zan kama maki kiyi ba sai anje ga haka ba.
     Daga dan tsakar
 wurin mu ya tsaya yanawa kanwar tashi magana a fakaice ta aje abin kubewan ta
 juya ta fita sai naji uwar tayi kwaba tana binshi da kallo ta juya ta tafi.
   Jikinane yayi sanyi
 saiga hawaye na silalo min a fuskana ya karaso ciki bayan fitan ta yana fadin
 kema princess meyasa zaki basu aiki bayan kinsan halin inna ?
   Dago kai nayi da
 niyar in fada mai yadda zancen yake sai na kasa sai hawayen dake bin fuskana ya
 dauki roban ya daga yaga saura kwara uku a ciki wanda bata goge ba yace aima ta
 gama ashe akwai wani abinda zan kama makine dashi ?
  Na girgiza kai na
 samu na bude baki da kyar nace komai na hada sai wanan din ya rage min dama
 kuma Aisha din ta gyara min shi ai.
    Ya danyi shiru
 yana kallon yanayina kafin ya juya zuwa ciki ya koma ya kwanta yana duban
 laptop din shi da yanzu yake aiki a cikinsa har na gama girki ana gab da
 magariba na wuce shi na fada bandaki nayi wanka tare da dauro alwala.








