Kanwar Matata 5
*_KāANWAR MATATA_*
_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_
*ZAFAFA WRITERāS ASSOCIATION*
Page 5
A gigice Sarah ta dāago tare da dafe kuncinta tace, āFarouuuuq.ā sai da ta ja sunan cike da tausayi tana kallon fuskansa hawaye na shatata a idanunta. Bakin Farouq har rawa yake yi wajen fadāin, āKar ki kuskura ki kāara kiran sunana anan wajen idan ba haka ba karya ki zan yi billahil lazi. Wawuya shashasha mai fuska biyu. Ashe watsatsatsiya ce ke kamar sauran yāan uwanki. Kin cucuni Saratu da har kika saka ni na dāauki dakon sonki a cikin zuciyata har tsawon shekara. Allah ya isa tsakani na dake. Kuma ki sani, ko da ace daga ni sai ke muka rage a duniya, har sai dai na mutu babu aure. Banza budur-bazar.ā Kuka Sarah ta fashe dashi jin zafafan kalaman da Farouq ke fadāa mata. So take yi ta budāe baki tace wani abu, amma rawar da bakinta yake yi ya hana ta iya furta ko kalma dāaya. Ji tayi an watso mata papers a fuska. Bin papers dāin tayi da idanu, sai kuma ta kai hannu ta dake rawa ta dauki paper dāin ta budāe. Waro idanuwa tayi ganin papers dāin scanning dāinta ne har guda uku wanda tayi jiya. Bata iya cewa komai ba don ta san babu abunda zata fadāi wanda zai saka Farouq ya yarda da ita. Tsirtar da miyau Farouq yayi tare da kama hannu aunty Luba yace, āAunty mu wuce anan kada amai ya kama ni dan Allah. Don ganin fuskan yarinyar nan kawai yana saka ni tashin zuciya.ā Rintss idanu Sarah tayi tana jin bugun zuciyarta na kāaruwa tamkar yanda jirgin kāasa ke malala gudu akan titinsa. Bata iya tashi a wajen ba sai da ta kwashi mintuna kamun ta mikāe, shima sabida mutanan da suke wucewa suna zundāenta ne ya saka tayi kāarfin halin tashi ta tura kāofar gida ta shiga. Kai tsaye dāakin mahaifinsu ta wuce duk da maganar da Lami take mata a tsakar gida tana yiwa yaran Naāima wanka, amma bata kula ta ba. Tana shiga dakin ta zube a kāasa sai da guiwowinta suka bugu da kāasa, amma bata damu da zafin da taji ba. Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi tare da fadāin, āWallahi, tallahi, billahil azim Baba ban tabāa sanin wani dāa namiji a rayuwata ba. Baba namiji da na tabāa bawa kaina. Ban san ta yanda akayi ciki ya shiga jikina ba. Na shiga uku na lalace Baba. Shikenan nima ba zanyi aure ba?ā Sunkuyar da kai Baba yayi yana mai zubar da hawayen tausayin Sarah. Dakyar ya iya dāago kai ya kalleta tare da fadāin, āSaratu da badin manzon Allah SAW yayi hani da dāauke mace a burni a kaita kāauye ba, da nace ki tattara kayanki ki koma _Wamba_ kiyi auren ki acan. Amma kuma Saratu babu ta yanda za ayi ki samu ciki ba tare da dāa namiji ba. Kin tabbata baki tabāa zuwa wani waje ba an baki abun sha kin sha ba? Watakāila ta nan aka yaudare ki.ā Girgiza kai Sarah tayi tare da fadāin, āBaba ban tabāa zuwa party ba. Ko kāawaye bani da balle su gayyace ni.ā Shuru Baba yayi na kayan tsawon mintuna biyar sannan ya nisa tare da dāagowa ya kalleta yace, āJeki dāakin ki Saratu. Allah shi yasan abunda ke bāoye. Duk wanda yake kāokāarin cutar dake, in Sha Allah, Allah ba zai bashi dama ba. Kina gani da idanunki Saratu, kina ganin irin wulakāancin da mahaifiyarku da sauran yāan uwan ki suke min a cikin gidan nan. Kina tunanin ko ban budāe baki nayi masu baki ba, Allah ba zai tsine masu ba. Ni dai Sam ban yi saāar mace ba. Haka zan koma ga Allah da bakāin cikin Lami da yāayāanta. Sai da yāan uwana suka yi min gargadāi, amma kuma nayi kunnar uwar shegu dasu. Gashi yanzu ina girbe abunda na shuka.ā Baba ya kāarisa yana mai fashewa da kuka. Itama Saratu kukan ta fashe dashi tare da fadāin, āKayi hakāuri Baba. Dan Allah ka cigaba da hakāuri dasu kamar yanda ka saba.ā Bai dāago ba ya ce, āSaratu yāayāan ciki na suke duka na! Wallahi tallahi har mahaifina ya koma ga ubangiji, bai tabāa fadāi na fadāa ba balle har in dāaga in kallesa inyi masa kāunkāunai. Wannan jarabta ce kawai daga Allah!ā Shuru Saratu tayi tana mai jin kāuna sosai a cikin ranta. āNaāima yāayāanta uku babu aure, dan ma Allah yayi wa dāayan cikawa da yanzu yāayāanta hudāu duk babu uba. Nuratu biyu, Marfuāa nada dāaya, Hassana kuma tayi yāan biyu, ko wata uku baāayi ba da dāaya daga cikin yāan biyun ya koma. Wannan bakāin cikin kawai ya isa ya kashe ni Saratu. Gashi itama autar taku Ainaāu tana so ta fadāa cikin halakar da yāan uwanta suke ciki. Yanda idanunta suke a tsatstsaye, wallahi ni sai nake ganin ma kamar sai tace duk abunda yāan uwanta suke yi basu yi komai ba akan wanda zata yi ita.ā āAāa baba, adduāa zaka yi mata. In Sha Allah hakan ma ba zai faru ba. In Sha Allah Ainaāu baza tayi halin su Naāima ba.ā Girgiza kai Baba yayi tare da fadāin, āUhm! To Allah yasa. Amma da kamar wuya. Hatta shi kansa namijin da Allah ya bani tilo, sakarai ne. Tunda shima shaye-shaye babu wanda bai yi da kuma dāaukar kayan mutane. Jiya da daddare, ina jin lokacin da wannan yaron wa yake da suna?ā ā *_Naliliyo_*ā Fadāin Sarah. āYauwa eh shi! Ina jinsa yana karta adda a kāasa yana zage-zage. Kuma uwar na dāaure masa gindi. Ya Allah idan wani laifi nayi maka kake min wannan jarabawar, Allah na tuba ka yafe min dan tsarkin mulkinka.ā Da āAmeen.ā Sarah ta amsa tana mai jin tausayin kansu ita da mahaifin nata. āTashi kije Sarah. Kije kiyi ta adduāa. In Sha Allah, Allah zai kawo maki mafita. Ki kāaddara dama can Umaru ba mijinki bane. Idan kuma mijinki ne, wallahi duk wannan abun da ya faro, babu makawa sai anyi wannan auren.ā Share hawaye Saratu tayi tare da fadāin, āNagode Baba. Amma dan Allah idan ka yi min izini, zan koma asibiti domin ganin likita.ā Sai da ya gyara kāafarsa sannan yace, āSaratu ki bari gobe kyaje. Yanzu ki koma dāakinki ki huta.ā Mikāewa Saratu tayi tare da fadāin, āTo Baba, nagode Allah ya baka lafiya.ā Da Ameen ya amsa, ita kuma ta fice daga dāakin. Sanye yake cikin jeans dāin _Secret Circus_ da shirt na kamfanin _Saint Laurent_, sannan ya sanya takalmin _Stuart Weitzman_. Babu abunda ke tashi a jikinsa sai turaren _Imperial Majesty_, kallon kansa yayi a cikin kāaton madubin dake dāakinsa ya saki lallausar murmushi ganin irin kyawu da yayi. Juyawa yayi ya nufi wani katoton showglass wanda ba komai bane a ciki sai mahaukantan expensive sunglasses, wani waje ya danna sai ga glass dāin ya zuge, rabi yayi sama, rabi yayi kāasa. Sai da ya kāarewa glasses dāin idanu sannan ya kai hannu ya dāauko _Bulgari Flora_ wanda duk cikin sunglasses dāinsa yana matukāar kāaunar wannan. Madannin ya kuma dannawa glass dāin ya rufe sannan ya juya ya koma wajen madubi ya dāauki Microfiber cloth ya goge glasses dāin sannan ya saka a fuskansa. Yanda yayi matukāar yi masa kyau, zaka dāauka dan shi kawai aka yi glasses dāin. Sai da ya kāara kallon kansa from head to toes yaga heās perfectly dress sannan ya dāauki iPhone dāinsa a kan bed ya nufi kāofa ya murdāa ya fito. āBarka da fitowa ranka ya dadāeā Shi gaba dāaya tsorata yayi don bai tsammaci ganinta a kāofar dāakinsa ba. āLaure! Kai Inna lillahi waāinna ilaihir rajuāun. Wai ni Ibrahim ya zanyi dake ne wai dan Allah? Sau nawa zan fadāa maki ki daina zuwa kina tsayuwa a kāofar dāakina kamar wata security. Dan Allah, dan Allah Laure ki daina firgita ni. Ni wallahi babu abunda ke tada min hankali da tsoro kamar wadāannan kacakoren hakwaran naā¦.ā Tun kamun ya kai kāarshen zancen ta fashe da dariya wanda ya bayyanar da manya-manyan hakwaranta na sama guda hudāu da suka turo suka yi curko-curko a waje. Sam bata iya rufe bakinta ruf saboda hakwaran. āPrecious Lord in heaven! Laure bar nan wajen tun kamun na zubar da wadāannan kacakoren hakwaran wallahi.ā Ja da baya tayi tare da fadāin, āNi hwa tsaya kaji Ya Khalif (Khalil), Hajiya ce tace nazo nayi kiranka tana can parlor kai take jira. Kuma ni kayi mani wanin (warning) akan kar ba kuskura na kuma shigar maka dāaki kai tsaye. Kuma nayi kāokāarin danna wanna madannin amma na kasa. Kasan ni dāin ce kamar a dukāe aka haifo ni sabida rashin tsaho.ā Harara ya maka mata tare da fadāin, āTo naji bar nan wajen.ā Washa bakin ta kuma yi sai da ya matsa baya don da gaske shi hakoran nata tsoro suke bashi. Gaba tayi kadāan, sai kuma ta juyo tare da fadāin, āNace dan Allah yaya khalif ko zaka dāan sammun wannan turaren naka mai shegen kāamshi anan, ko baka cika min ba wallahi nagode.ā Ta kāarisa maganar tana mai ciro wata kāaramar kwalba irinta fiya-fiya a kāarkāashin zaninta. Yunkāurowa yayi kamar zai kai mata duka ta juya a guje ta nufi dogon corridor dāin da zai fitar da kai katoton parlorn gidan. Tsaki yayi sannan ya jawo kāofar dāakina nasa ya murza key tare da saka key dāin cikin aljihun wandonsa ya soma tafiya majestically har ya iso parlor. Tsaye yaga Laure da mopa a hannunta, maimakon tayi abunda za tayi, sai ta bāige da kallon katoton tv na bango dake manne a jikin bango. Wani film dāin India mai suna *_Sultan_* ake haskawa dāai-dāai inda yake gudu domin kamo jirgin leda. Babu abunda Laure kayi sai kyalkyalewa da dariya. Khalil na kāarisowa ya dāauki remote dake hannun kujera ta jefi Laure dashi a goshi, don Hajiya tayi kiran sunanta har sau hudāu amma film ya dāauke mata hankali. Kuma ita ta zubar da juice dāin da Hajiya ke sha sabida rawar kanta. Saurin susa goshin Laure tayi tare da fadāin, āLaa! Wallahi kuma naji kamshin turaren ka, wata zuciyar tana ce min kai ne ka kāariso, amma wanna gayen ya tafi da imani na. Dan Allah Hajiya zaki biya min kudāin jirgin inje indiya mu gaisa tare da dāaukar hoto dashi? Na san wallahi zai ji dadāi idan ya ganni. Na san har fim sai mun yi tare in fito a budurwarsa.ā Harararta Khalil yayi tare da fadāin, āTo dan gidan ku matsayin saka ki a cikin keji ana zuwa ana ganin ki ba zaki samu ba, shashasha kaiwa. Za kiyi abunda ke gabanki ko sai na isko ki nan wajen.ā Marairaicewa tayi tare da fadāin, āAllah sarki yaya khalif. To na rantse maka fadāin kāasar indiya samu mai kyawuna abune mai matukāar wuya. Ko kai dāinnan da kadāan ka fini kyawu.ā Zama yayi kuwa da Hajiya yana mai fadāin, āTabbas, babu shakka. Dama ai samun irin ki a indiya ai sai an tona. Don ko namun dajinsu sun fiki kyawun gani.ā Turo baki tayi tare da fadāin, āKina dai jin sa ko Hajiya!ā āKar ma ku soma saka ni cikin shirmen ku. Ke da Khalil dai kamar kuna ganin hanjin juna.ā Fadāin Hajiya dai-dai lokacin da Maryam matar wan Khalil tayi sallama ta shigo dāakin hannunta rikāe da wani kyakkwar kula. Dai-dai inda Hajiya take ta ajiye kulan tare da fadāin, āTom and Jerry! Kun soma fadāan naku ko.ā Kallon kukan da aunty Maryam ta ajiye a gaban Hajiya yayi sannan ya kalli aunty Maryam dāin tare da fadāin, āAi kin san Allah, sai na kori yarinyar daga gidan nan. Ni da gidanmu amma bani da sakewa. Babu ranar duniya da wannan yarinyar bata tsora tai da muggan hakwaran nan nata.ā murgudāa baki Laure tayi tare da fadāin, āHalittar Allah kake zagi. Idan ka isa halicci kiyashi anan wajen mu gani. Sai rowar tsiya, dāan turaren da mutum zai baka kadāan cikin kwalba amma ya kiya sabida rowar tsiya. Wallahi Hajiya dai kowa ya san ita dāin hannunta a budāe yake kamar kasuwar kwari ta Kanon mu. Ko ina kayo rows oho! Kuma Hajiya kice ya bani makulli in tai in gyara masa dāaki.ā _Mastika gum_ da yake matukāar kāaunar ya fiddo daga aljihunsa ya jefa a baki ya hau tauna a hankali yana lumshe idanu. Allah ya hadāa wani strong love tsakaninsa da chewing gum. Da yuwa kaga bakin Khalil babu gum a bakinsa. Kuma gaba dāaya chewing gum dāin da yake ci daga waje ake kawo masa. Yasan expensive gum da yawa. Yana biyan kudāin jirgi ya keta hazo kawai domin sayo chewing gum. Kullum cikin browsing yake domin ganin sabon chewing gum dāin da aka yi. Hajiya tayi-tayi har ta gaji akan yi masa fadāa ya daina ci amma Sam yakāi bari. Har hakāori an tabāa cire masa tsabar cin chewing gum amma hakan bai saka ya daina ci ba. āDan gidan ku ina yi maka magana shine ka dāauki dāan iskan abun nan da ba tsana ka jefa a baki kana tauna.ā Tsayawa da taunar yayi tare da fadāin, āDan Allah Hajiya ki daina saka damuwar uncle Ridwan a zuciyarki. Ya kamata ki saba da riginarsu yanzu. Wai shi so yake na auri Nina, ni kuma da in auri wacce wani namijin ya riga ni saninta, gwara na mutu babu aure. Na tsani mace mara kamun kai. Hajiya Nina fa bata san iya adadin mazan da ta kwanta dasu baā¦ā¦ā¦..ā
08128755583