Yankan Karfe 1-2
*💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫*
~Written By~
*Hanyluv✍🏻*
_*Free page*_
Page 1 & 2
…… 06:30pm!! Tafe yake cike da murna a yar rugar tasu yana ta faman zuba sauri bakin shi ya kasa rufuwa saboda tsabar farin cikin da yake ciki, hannun shi riƙe da wata bakan leda, dan Magidancin mutum ne bafulatani ne fari tassss kaman wani balarabe, duk da idan ka qare masa kallo zaka gane yana cikin yanayi na rashi hatta tufafin jikin shi ma duk sun koɗe, beyi wani tafiya me nisa ba ya isa wani dan gidan ƙasa tare da tura yar lange²n kofar ya shiga da sallama, wata farar kyakkyawar mata ce zaune akan tabarma ta mike ƙafan ta, ta ɗan jingina da jikin bagon, tana dauke da tsohon ciki, kana ganin ta kasan shuwa ce saboda yaukin nata ya wuce na wannan mutumin, wani sassayyan murmushi ta sakin mashi tare da fara qoqarin miƙewa, da sauri ya qaraso tare da maida ta zauna shi ma ya zauna a kusa da ita hannun shi a cikin nata yana cewa
“ Haba Matar So na sha ce miki ki daina bawa kan ki wahala baki ga halin da kike ciki bane!” murmushi ta qara sakin mai wanda ya zama ɗabi’anta tace “Mai Martaba toh zan daina neman lada na ne! Ace Miji na guda ya dawo bazan tashi na tarbe shi ba” shafa gefen fkuskar ta yayi yace “wannan kyakkyawan murmushin naki kaɗai ya ishe ni Mata ta! Allah yayi miki albarka!!”
“Ameen Gorko am(Miji nah)” ta faɗa tana mai ɗaura hannun ta kan na shi..
“Daadah! Daadah!! Daadah na mun dawo!” wani dan kyakkyawan yaro da baze wuce shekara 7 ya shigo a guje yana faɗa, juyowa duk kansu suka yi suna murmushi da sauri Daadah ta buɗe mai hannayen ta alamar yazo ya rungume ta aikuwa da gudu ya qaraso tare da faɗawa jikin ta ya ƙanƙame ta,
“Gidadon Daadah wato ni ba a sanni ba Daadah kaɗai aka sani koh?” juyowa Gidado yayi tare turo baki yace “Abboh toh ba kai bane ka qi buɗe mun hannu Daadah na ce kawae ta buɗe mun nata,” murmushi Abboh yayi tare da buɗe mai hannu yace “ Toh a gafarce ni Gidado nah taho nan shi ma Abbohn ka yaji dumin ka,” washe baki Gidado yayi tare da zare jikin shi daga cikin na Daadah sannan ya faɗa jikin Abboh, sosae Abboh ya rungume shi yana shafa kanshi, sallama suka yi da zazzaƙar muryar su, amsawa su Daadah suka yi murmushi kwance a fuskar su, wasu kyawawan ƴammata ne suka shigo masu kama ɗaya sak, fara’a kwance a fuskar su, kana ganin su kaga tagwaye, kamanin su sak na Daadah, suna da manyan idanu da zara²n gashi, suna da cikar gashin gira, hancin su dogo ne lips din nan pink da shi, ta inda zaka bambamce su ɗaya na da dimple ɗayar kuma bata dashi, baza su gaza 18 years ba, ni dae babu abin da nake cewa se Masha Allah!
“Yan Albarka an taso!” Abboh ya faɗa yana sakin musu murmushi,
“Eh Abboh, sanunku da gida” suka faɗa a tare, nan suka ƙaraso tare da gaida iyayen nasu, suka tashi tare da shiga ɗakin su suka cire hijaban su sannan suka fito, miƙewa Abboh yayi sakamakon jin an fara kiran sallah,
yana qoqarin juyawa Daadah tace “Abbohn su nace wannan ledan fah na meye?” da sauri ya juyo tare da dafe goshin shi yace “Ohh kinga ganin ki ya mantar dani ledar da na shigo dashi, dama Babansu Rabe ne ya bada cefane yace na kawo musu, ɗanyar shinkafa ce da nama da dae sauran kayan cefane,” wani irin tsalle Gidado yayi yace
“Abboh shinkafa harda nama! Lallai yau zamu ci daɗi,” dukkan su dariya suka yi, shi kam Abboh wani irin tausayin iyalin nashi ne ya dirar mai “Allah sarki shinkafa tamkar nama take a gurin su dan se sallah suke ganin ta,” ya faɗa a ƙasan ran shi, girgiza kai yayi tare da riqo hannun Gidado sannan suka fice daga gidan su Daadah suka yi masu a dawo lapia, juyowa Daadah tayi tare da cewa “Ni’imah ku tashi kuyi sallah idan kun idar se azo a daura girki,” mara dimple din da aka kira da Ni’imah ta miƙe tare da cewa “Toh,” itama ɗayar tashi tayi, Masha Allah nace dana kalli dirin nasu dan wani irin jiki gare su da ake kira da coca cola, itama Daadah miƙewa tayi a hankali tare da ɗaukan buta ta nufi banɗaki,
Bayan sun idar suka fito tare da hura murhu suka fara kiciniyar ɗaura girkin, Abboh basu dawo ba har se da aka idar da Sallahr isha’i sannan ya riƙo hannun Gidado suka nufo gida, da sallama suka shigo a lokacin sun gama girkin tuni, sun shinfiɗa babban tabarma a tsakar gidan tare da jera abincin, su kuma suna gefe suna jiran dawowar su,
Shigowar su Gidado ya zame hannun shi daga jikin Abboh tare da qarasowa cikin gidan aguje, cike da murna ya zauna akan tabarmar yana bin kwanukan da kallo, murmushi kawae Daadah take yi ta sa hannun akan shi tana shafawa tana bin shi da kallo,
“Sannu da dawowa Abbohn su,”
“Yawwa Hajiya ta,” Abboh ya faɗa yana zama kusa da ita, suma ƴammatan suka yi mai sannu da dawowa ya amsa yana murmushi,
“Nimrah zuba ma Abbohn ku da ɗan auta na don naga alaman ba iya jira ze yi ba,” Daadah ta faɗa tana kallon mai dimple din nan, tashi Nimrah tayi tare da qarasowa ta buɗe abincin dake cikin langa, farar shinkafa ce yar hausa amma tayi kyaun dahuwa tayi wara², zubawa Abboh tayi sannan ta buɗe qaramar langar ta miyan ta zuba mai da nama sannan ta miqa mai,
“Yawwa sannu Mama nah,” Abboh ya faɗa yana murmushi itama murmushin tayi tare da juyawa ta zubawa Gidado da ya ƙagu sannan ta zubawa Daadah itama ta zuba musu nasu sannan ta kwashe ragowar ta kai ɗaki ta ibo ruwa ta kawo ta ajiye, ta dakko kofi ta diba kai wa Abboh ta diban ma Daadah sannan ta ajiye ragowa a gefen su, zama suka yi suna cin abincin,
Bayan sun gama Nimrah ta kwashe komai ta wanke sannan ta dawo ta zauna suka dasa fira, dama hakan ya kasance daga cikin dabi’un Abboh koh da yaushe idan yana gida ya kan zauna suyo ta fira shi da iyalanshi…..
Se 9:00pm Abboh yace kowa yaje ya kwanta, su Nimrah suka wuce ɗakin su dake ɗauke da shamulalliyar katifa se wata fatattakiyar leda da bata gams rufe ɗankin ba, se kayan su dake cikin ganamasgo, suma su Daadah suka wuce nasu ɗakin su da Gidado duk dae iri ɗaya ne da ragwaɓaɓɓiyar kwaba nasu yafi nasu Nimrahn..
Washegari tun asuba da suka tashi basu koma ba saboda makarantar asuban da suke zuwa koyarwa, haka suka riƙe hannun Gidado suka tafi….
___________________________
Wata farar Mata ce zaune cikin wani hamshakin parlor cikin shiga ta alfarma ginin duplex, wani hadadden lace ne a jikin ta light blue da touches din milk colour, daga ganin ta baza ta haura 50yrs ba, kyakkyawa ce ajin farko don duk da ɗan shekarun ta baze hana ka gani kyawun ta ba, babbar iPhone ce a hannun ta tana latsawa tana shan slice fruits🍎🍌🍉🍒🥭🍓 din da aka ajiye mata gaban ta cikin kwanciyar hankali,
“Assalamu Alaikum!” Akayi sallama da wata sassanyar murya, dagowa matar nan tayi tana kallon bin me yin sallamar da kallo, wani dogon kyakykyawan guy ne fari tass, kyanshi har ya ninka na matar nan, dan shi da ka ganshi zaka ɗauka wani balarabe ne, yana da jikin maza, yana da kwantacciyar suma baka wuluk, fuskan shi saje ne kwance liif, hanci shi dogo ne, lips din nan pink zarrrr, idanun shi manya² me eyelashes zara², kananan kaya ne a cikin shi, a hankali yake tafiya, cikin qasaita ya qaroso parlorn tare da zama kusa da ita yana sakin mata murmushi itama murmushin ta sakin mai,
“Saheel ina kaje haka this early without telling me?” Matar ta fada tana dan hade rai, murmushi yayi tare da riqo hannun ta ya fara motsa baki kaman baya son yin magana yace “Mami naje gidan su Khaleel ne gaishe da Hajiya Mama she has been sick for long but am sorry if i did wrong🧏” ya fada yana holding ears👂din shi, murmushi tayi ta sa hannun ta tare da janye hannun na sa daga kan kunnan shi,
“Bari nasa Lanti ta shirya maka breakfast🥞 don nasan you haven’t take it!” ta faɗa ta na ƙoƙarin tashi da sauri ya riƙe tare da cewa “No Mami Hajiya Mama ta sa an haɗa mana, am okay!”
“are you sure?” ta tambaye shi, lumshe ido yayi tare da buɗewa alamar eh, komawa tayi ta zauna, matsowa yayi tare da qara riƙe hannun ta alaman yana so yayi magana me muhimmanci, jinjina kai tayi alamar tana sauraran shi, tsawon 5min ya yi shiru sannan a hankali ya fara magana,
“Mami bana so ki ɗauki maganan da zanyi da zafi, kin san dae ina sonki sosai kuma bana son abun da ze ɓata miki rai koh sannan Umarnin ki duk abunda kika sani i always do, right?” ɗaga kai tayi alamar eh, ya jinjina kai sannan ya cigaba,
“fyn! Kuma kinga Daddy shima a matsayin shi na mahaifina ya kamata ace koh sau ɗaya ne shima nabi Umarnin shi, Mami I have to go back UK! I have to fulfill his dream! Mami kin san Daddy bashi da burin da ya wuce yaga Companyn nan ya bunƙasa ta yadda talaka ma ze ji daɗi! Kuma kinga dukkan mu zamu samu lad…”
“Dakata mun!!” ta fizge hannun ta daga na shi tare da miƙewa cikin ɓacin rai ta cigaba
“yanzu bayan ka nuna mun ka fi son Daddyn ka a kaina harda wasu bazayen talakawa zaka nuna sunfi maka Ni!! Lallai Saheel ka bani mamaki! Ban taɓa tunanin soyayyar da nake nuna maka zaka ɗauke shi a matsayin cutarwa ga!! Toh shikenan Saheel ga hanya nan Allah ya kiyaye hanya!!,” tana gama faɗin haka ta wuce upstairs fuuuu, fuska a marairaice yake kallon ta har ta ɓace ma ganin shi, kanshi ya dafe tare da runtse idanun shi cike da tashin hankali, shi a yanzu kwata² yanzu kanshi ya kulle be san abun yi ba kuma, tashi yayi a hankali ya bi bayan ta,
Knocking yayi a door din shiru ba respond, ƙara yi yayi nan ma shiru, dama yasan baza ta amsa ba, tura ƙofar yayi ya shiga, dakin yanda kasan na matar shugaban kasa milk and golden ne komai na ciki, ɗauke da sallama a bakin shi ya shigo bedroom din, tana zaune bakin gadonta, kawar da kai tayi ta cigaba da latsa wayar ta, lumshe lumsassun idanun shi yayi ya buɗe tare da ƙarasowa ya zauna gefen ta a hankali ya buɗe baki,,
“Mami if my statement hurt you I’m so sorry🙏🏻” banza tayi da shi, tashi yayi tare da durƙusawa a gaban ta fuska a marairaice ya riƙo hannun ta,
“Mami dan girma Allah kiyi haƙuri idan abun da na faɗa miki ya ɓata miki rai, wallahi banyi maganan nan da wani nufi ba, kuma ni nasan baza ki taɓa cutar dani ba saboda babu wanda ya kai uwa son ɗanta, koh Daddy be fi ki ba a waje na balle kuma wasu can, kawae dae shima Daddy ina so na gujewa ɓacin ran shi ne!” tashi tayi tare da fizge hannun ta a fusace tace………..
😍😍😍😍Yawan masoyan littafin YANKAN ƘARFE yawan posting✍🏻✍🏻🥂😎
*@Hanyluv*✍🏻
*07044454719*📲☎️