Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 23

Sponsored Links

 

 

 

Da kuka wiwi na fado part din ban tsaya ba sai a jikin ummah
dake zaune a cikin yanayin damuwa da takaicin hali irin na da namiji da bamu da
yadda zamuyi dasu a rayuwa sai zaman hakku

ri.

   Kalah ummah batace
min ba asalima kamar bata san inayi ba a lokaci sai can naji muryan ta tana
fadin tun farko na fada maki kibi komai a hankali gidan nan don nima hakkurin
nakeyi nakai ga samun ku a yanzu.

   Ban san me hjy
maimuna ta fadawa Abban ku ba har ya hau haka da zafi kan wanan maganan don ba
zanyi tunanen cewa hjy karima bace ta zugashi tunda a gaba data fuskanci rashin
gaskiya a cikin maganan suka rikice dasu a wurin .

   Jiya kuma hjy
maimuna a dakin Alh ta kwana bansan ya sukayi ba sai yau danaje gaisheshi yake
min maganan wai tunda yaron nan kike so a turo shi yazo naso fahintar dashi
gaskiya ya hauni da fadan hakan.

    Don haka komai ma
ya faru nasan itace ta kullashi don taga ta wargaje min farin cikina a gidan
nan dama kuma a cikin hakan muke da ita kullun.

    Salamu alaikum aka
fada hjy karimace ke sallama daga kofan ta shigo itama ranta a bace yake
lokacin da gani sin kwasa da Abba din kan zancen nawa ke nan.

   Au kuka kika tsaya
yi kan wanan zancen ke ina kina son yaron dai ba shike nan ba saiki turoshi din
kamar yadda ya fada ya bincikeshi don naga an zugashi sosai ya zugu kan zancen.

   Za a hana budurwa
yin saurayine ko macece zata kira maza zuwa gareta ni wanan maganan banga ya
kai wani abin tsayawa a tayar da jijiyon wuya ba hakan nan.

   Amma saina fahinci
zancen da akwai lauje cikin nadi tun farko so kawai ake aga an kuntatawa wani a
wanan zancen sam Alh baiyi tunane ba ta yaya mace zata fada ma zance ka tsaya
ka haushi haka ka zauna wai shine gaskiya.

    A gaskiya hjy
salma kinyi kokarin zama a haka cikin mutanen nan wallahi ni sam ba zan dauki
wanan irin rainin wayau ba tunda bana wa yayanta hakan nan ni don me wasu
mutanen basa tunanen mutuwansu ne wai ?

   Na fahinci komai a gidan
nan yanzu don haka mu zuba dani da matan nan zata gane cewa karyan iskaci
takeyi a baya yanzu ke zarah ki turo yaron wa Alh muji me zai masa.

   Shike nan kuwa ai
wuya baya kashe bawa idan kayi hakkuri sai ya zamo maka alheri wata rana idan
anyi hakanne don a tozarta mu na roki Allah ya mayar muna dashi alheri a
rayuwan mu ummah ta fada.

   Insha Allah sai
kunyi alfahari da hakan ban son ki nuna sarewa ko gazawa kan wanan zancen a
yanzu ki daure din ga duk hukkuncin da zai yankewa yarnan a yanzu ki bita da
addua da sadaka hakan ya zama mata alheri a rayuwan ta.

   Ina a jikin ummah
gurfane na lafe ina jin abinda suke fadi a gaskiya ba zance ban son Ahmed ba da
sunan so ba kuma zance bana son shi ba don halinshi dana sani a yanzu na
jajircewa rayuwan shi.

   Haka kuma har in
hakan ne meyasa ake son kashe mu da ran mune mu da mahaifiyar mune idan hakane
gara nabarwa mama gidan na huta da wanan ukuban da suke nuna min ita da diyanta
zaifi min sauki hakan ma.

    A ranan ina kuka
na kira Ahmed a cikin tashin hankali na fada mai neman shi da Abba din keyi
tunda umurni Abbah ya bani kan yin hakan don haka ya zama dole in kirashi in
fada mai hakan.

  Shima a rude yake
tambayana kome ya faru Abba din ke son ganin shi haka don yasan ba zancen
soyayya a tsakanin sai mutunci da girmamawa.

   Ban iya mashi
bayanin komai ba don banda karfin halin iya magana a lokacin don haka na kashe
wayata kawai shima ya shiga tashin hankali irin wanda na shiga din a lokacin.

   Don haka da yamma
karfe hudu ya fitowa sallah ya shirya ya fito zuwa gidan namu ba tare daya
fadawa kowa inda zashi ba don baisan dalilin dayasa Abba din yake neman shi ba.

   A iya tunanen da
zaiyi kan shawara guda ta yanke zancen shi shine kuma Abba zai mai iyaka dani
kan ya rabu mai da diyanshine.

   Yanzu in an mai
kashedi a kaina anya zai iya daukan hakan a yanzu kuwa yadda ya saba da
yarinyar tana daukan shi da mutumci takar dan uwanta najini neshi a gareta
yanzu don zarah ta zame mai wani bangare na rayuwan shi yanzu.

  Da wanan ire iren
tunanen ya kawo har kofan get din gidan namu ya sauka ga mashin ya biya dan
achaba kudin ya tafi shi kuma ya kalli gidan yana addua a zuciyarshi da neman
kariya daga wurin ubangiji.

   Maigadi yaiwa
magana don ya bude mashi get din gidan saida maigadin ya kalleshi da kyau duk
da yasan shi yana zuwa suna gaisawa kuma yana dan maj ihisani daidai karfin shi
kuma maigadin najin dadin hakan.

   Yaron arziki kaida
kanka kake son ganin Alh yau anya bakayi karanbani ba kuwa ganin Alh fa sai
manya ko manyan sai ka amsa sunan ka .

   Kai Ahmed din ya
daga ya kalli gidan namu cikin second yadawo da kallonshi ga maigadin yana
fadin yasan da zuwana don shi yace nazo yau din a daidai wanan lokacin.

 To to to aishike nan
bari na tashi naje nai maka iso dashi din tunda yasan da zuwanka din ai dama na
dauka ko zuwan kankane kayi da sai in baka shawara kawai ka hakura da ganin
nasa ka koma inda ka fito zaifi ma sauki.

   Ya mike kata kata
ya nufi kofan falon Abba din dake dan saye hakan ya nuna ba wanda zai shigo a
lokacin gidan saishi da iyalinshi ko wasu shakikai nasa na jikin shi.

  Wucewan maigadin
yasa Ahmed din kara tsarguwan kanshi duban jikin shi yayi yaga duk da yayi
shiri irin wanda bai taba yin irinsa ba a jikin shi amma sai yaji ya raina
kanshi a hakan.

   Bai dade ba
maigadin ya dawo da sauri yana fadin yace kashigo daga ciki yasan da zuwan ka
din haka yasa ya dufari inda yaga maigadin yaje duk dabai gama tabbatar dako
nan ne hanyar shiga cikin gidan ba yadai sakai ya shiga da sallama a bakin shi
.

    Sanyi da kamshine
sukai mashi maraba da zuwa lokaci guda har saida ya dan lumshe idanun shi kadan
don irin abinda yaji bai taba jin irinshi ba a rayuwa.

    Sallama yayi cikin
muryanshi mai taushi da izza da gadara bai shigo ba saida aka amsa daga ciki
tare da bashi izinin shiga falon shiga ciki ta hanyar fadin bissimillah shigo
mana ciki .

   Yana dan dukar da
kai yasa kafa ya shigo falon tare da dan gurfanawa can daga nisa yana fadin ina
wuni Abbah shima Abban kai ya dago yana kallon dan matashin saurayin daya
baiyana a gaban shi.

   Sau daya Ahmed din ya dago kai ya kalli Abba
din kwarjinin Abban din yasashi saurin dukar da kanshi kasa da sauri ya fara
gaida dattijon dake gaban nashi watau Abbah .

   Dan shirune ya biyo
bayan hakan tsakanin su bayan gaisuwa kafin Abba ya kawar da shirun da fadin
yaya sunan kane yaro Abba ya fada yana kallonshi ?

   Ahmed nake ya fada
sunan mahaifinka fa Sama,ila ya bada amsa kafin ya kara noke kanshi kasa kamar
kunkuru.

  Meye hadin ka da
yata Abba ya tambayeshi tare da tsureshi da ido yana son jin amsan da zai bashi
a lokacin lafin yasan hukuncin yankewa .

    Shiru Ahmed din
yayi kafin Abba yace dashi bakaji band meye hadinka sa yata zarah ne ?.

    Abba wallahi ba
komai tsakanina da ita sai alheri mun hadune a makaranta da ita ranan da wani
matsala ya faru da ita kowa ya kewayeta yana kallon halinda take ciki na neman
taimako.

   Naga rashin dacewan
hakan tunda mace ce shine na taimaketa har ta dan farfado daga yanayin da take
ciki din na fitan hankalinta.

   Tun wanan ranan ne
hakan yasa muka shaku da juna muke zumunci da ita nake kuma taimaka mata wurin
karatu don ina gaba dasu da shekara biyu a school din.

  Ka tabbatar wanan ne
kawai atsakanin ku  shi kawai na sani
tsakanin mu Ahmed ya fada yana kara soke kanshi kasa.

   Abban yayi gyaran
murya yace ji nan nayi binke nagane cewa duk makarantan nan dakai zarah ke
mu,amula fiye da kowa sai kuma kawayen karatun ta mata da maza da kuke zama
tare kuyi karatu dasu duk an binciko min hakan.

   A yau din nan nasa
aka bincika min komai game daka saidai na samu feedback maikyau game da halayeb
ka abu dayane ya daure min kai sai zancen mahaifin ka da akace ya barka tun
kana shan nono bai kara waiwayo ka ba har yau din nan ?

    How do you see
kaida baka tare da mahaifinka zakazo wanan irin gidan neman auren yata in baka
alhalin kaima kanka baka san mahaifinka ba ?

   Ahmed ya lankwashe
yan yatsun hannunshi cikin juna a ladabce ya dago kai ya kalli Abba din ya kara
dukarda kanshi kasa yace.

   Abba saukin abindai
bincike ya nunama cewa nidin ba shege bane mahaifina kuma da matsalace tsakanin
shi da mahaifiyata da bata bishi zuwa kasansu ba yasashi fushin haka har ya
wofitar dani na tashi mara galihu hakan baisa na watsar da tarbiyan da akeson
samu ga ko wani daba .

   Zancen Zarah kuma
ban taba tsayawa da zarah da sunan soyayya ba ko wani abu makamancin hakan a
tsakanin mu ba don ko nasan nidin ba dan kowa bane ban kuma kai matsayin da
zance zai nemi diya irin zarah ba.

    Don hakane alakan
mu ya tsaya a iya mutumci kawai a tsakanin mu ba kuma sai don banson zarah din
ba don sanin haka a gareni kawai da nayi.

    Kallonshi su Abba
suka karayi da kyau shida dan uwanshi dake zaune falon a lokacin kafin yayan
Abba din yace dashi sana,an me kakeyi a yanzu kuma meka karanta a karatun ka ?

   Wanan ma duk bai
taso ba a yanzu ai Abba ya fada a dan fusace sai yayan nasa yace ka barshi muji
tukuna ai ya kalli Ahmed din don son jin me zai fada masu.

   Yace kimiya na
karanta sana,a kuma saye da saye da sayarwa nakeyi ina shiga kauye ina sawo
hatsi in kawo birni in sayar da sauran yan buga bugan zamani da akeyi.

   Tsaya nan ma hakan
ya isa mun gamsu da baya nan ka baba sale ya fada yana gyara zaman shi Abbane
ya dago yace.

   Kai banda abinka da
wanan sana,an zaka rike min yata sana,an da ko kudin sabulunta a wata bai kai
ba balle zancen sauran bukatan ta na rayuwa.

   Kai Ahmed din ya
dago ya kalli Abba din dake magana ya sake dukarda kanshi kasa don zuciyar shi
dake tausan shi saboda su mahaifan  zarah
din ne a lokacin.

   Da badon hakan ba
yau da suka tayar mai da mikin dake damun zuciyar shi a kullun yana tausan
kanshi da hakan yana jajircewa don gudun irin hakan gareshi na tozartawa.

    Muryan Abbane daya
kira sunan shi ya katseshi Abban ke fadin Ahmed daga yau din nan ina son ka
nisanci yata zarah a ko ina don yanzu dai nasan kasan cewa zarah ba sa,arka
bace ita.

   Karatune kuma
kagama kai yanzu din haka banson jin wani mu,amula kuma kota mutunci ya sake
shiga tsakaninka da ita nan gaba zaka iya tafiya yanzu.

    Kuma kada naji
ance ka sake kawo wani abu nan gidan da sunan alheri niko yaushe ina tsaye kan
Iyalina ga komai don haka ka nisancesu .

    Ga wanan dubu
hamsin ne ka kara a jarin ka ka kiyaye don ka zauna lafiya Abban ya fada yana
kawar da kanshi gefe cikkn takaici.

   Kai Ahmed ya
girgiza tare da fadin a,a Abba ka bar kudin ka nagode aikai mahaifine a gareni
ko yanzu ka fadakar dani ga abndana manta cewa nidin mai raunine bai kamata na
dinga kai kaina inda Allah bai kaini ba.

   Ya mike ya tsugunna
tare da fadin zan koma nagode kwairai ga hakan yana fadin  haka ya mike ya fice daga falon suka bishi da
kallo kowa da abinda yake sakawa a zuciyan shi lokacin.

   Baba Salihu ne yace
yaron yaron kirkine alama ya nuna hakan gareshi cewa zaiyi mutumci sosai
wallahi saidai dan matsalan nan da aka samu kawai shine cikas din.

    Kirkin shi bai
dameni ba ya rabu min da yata kawai shi nake so a yanzu itama zanyi warning din
ta da kakausan murya kan hakan idan ba hakaba ranta zai baci dani sosai a gidan
nan kaji na fada maka.

   Banso ka da hakan
ba ana cizawa a hura don bamu san me Allah zaiyi nan gaba ba gara ka bita da
addua kawai shine mafita nake gani.

   Shiru Abban yayi
don takaici ya hashi yin magana sai can yace ita kuma shashan daya Aisha wai
yaron nan dan kawar uwarta dake Lagos ta lakewa gashi sunja min zubar da mutuncina.

   Yau nayiwa uwarshi
waya take fada min wai yaron bai yarda da hakan ba yace a barshi ya nemo
matarshi idan ya tashi kaga ke nan dama a tsakanin uwayen nasu ne sukeson hadin
shi kuma yaki.

   Ai kaji matsalan
shiyasa nace ko wanan din kabisu sannu don alama ya nuna cewa suna son junan su
saida sun kasa gane hakan suka tsaya a mutunci .

    Nan dai sukaita
tataunawa kan yayan nasu har tsawon wani lokaci kafin Abba din suyi sallama da
abokin haihuwan nasa yatafi shi kuma ya fara ganawa da mutanen shi yan maula.

   Ahmed ko da kyar
yaga ya isa gida dakin shi ya shige ya kwanta don bacin rai don ko Djje bata
sanda dawowan shi gidan ba lokacin.

   Ba abinda ke masa
yawo a rai sai irin maganganun da Abba ya fada mai masu zafi daba wanda ya taba
fada mai su a duniya sai yau saidai baiga laifin iyayyen nawa ba don shima
yasa  yakai kanshi inda Allah bai kaishi
ba lokacin.

   Wayan shi yai kara
ya dauko yana dubawa sunan zarah mayana ya gani a screen din wayan yaji kamar
ya share wayan kada ya dauko don shara din Abban daya kidanya mashi.

   Saidai kuma ya kai
hannu da zumar dauka wayan ya katse baikai ga dauka ba haka yasa ya juya ya
barta  da haskenta na kira kafin can ya
sake jin kiran ya koma shigowa again.

   Wanan karon bai
bari kiran ya katse ba ya daga yana fadin Zarah ya akayine daga bangarena nace
bakazo gun Abba din bane halan naji banji komai ba.

   Dan murmushi yayi
kafin yace nazo mana me kike son ji halan nace abinda yasa yake neman ka din
mana brother don bansan me aka fada mashi ba akan mu.

   Yace nazo tayi min warning akan kada in kara
tsayawa dake ko yaji an gamu tare duk abinda ya biyo baya nina ja yace min.

   Haba dai nasan Abba
ba zai taba fadin hakan ba ai yace yako fada wallahi don iyakan gaskiyata ke
nan na fada maki kinsan ban magana biyu ni ai.

   Yanzu Abba din ya
fadama hakan don Allah yace kwarai kuwa don Abba yau yai min tuni ga abinda
nina manta a rayuwana duk da ba soyayya mukeyi ba naji dadin maganan wani gefe
kuma naji zafi.

    Don Abba ya fada
min jarin hannuna ko sabulun wankanki ba zai saya ba don haka ya yanke duk wani
alaka tsakanina dake daga yau kuma ya kafa shedan hakan ga dan uwanshi da muka
zauna tare mu uku a falo  naku.

    Kashe wayan nawa
nayi domn kada yaji sautin kukan da yazo min a lokacin saidai abinda ban sani
ba ya riga da yaji ko hakan yasa yai ta kiran layin nawa ban dauka ba.

   Don kukan dana rufe
kaina  a daki ni kadai a ciki inayi
lokacin ina maijin zafin abinda Abba din ya fadawa Ahmed don ma bai fada min
duka ba ke nan iya wanan din daya fada min ke nan.

   Twelve misscal nasa
na daga waya na gani bayan sallah isha,i danayi na dauko wayan ina duba kiran
inda na samu sakonshi cewa don Allah in kirashi idan naga sakon shi.

   Ban kiba na danna
kiran rayin shi ya shiga ya daga ya dauka yana fadin yanzun kin sauko ke nan ko
kada wanan maganan ya bata maki rai don Allah.

    Ni nasan ke din ko
Abba bai fada ba keba sa,ata bace zarah don haka muyi hakkuri mu guji abinda
zai iya kai ya komo daga hakan.

   Dama ashe ba sona
kakeyi da gaskiya ba nafada a cikin wani murya ina sake kuka lokaci guda naci
gaba da fadin ni tunda ummah tayi muna adduan daidaituwa a tsakanin mu naji
zuciyana ya kwanta da hakan.

   Zarah dama kema
kina sona ashe kamar yadda nima nake son ki ashe bansan da son juna mukeyi ba
sai yau da Abba din yake furta kalman raba tsakanin mu dake.

Leave a Reply

Back to top button