ILIMIN HADISI A SAUKAKE KASHI NA TARA
بسم الله الرحمن الرحيم
(25) MENENE HADISI MA’ALULI?
Shine hadisin da mahaddacin dubban hadisai ya gano cewa akwai illa abar suka a cikin hadisin da aka shigar da wani lafazi na wani wanda ba lafazin Annabi ba ne.
(25) MENENE HUKUNCINSA?
Hukuncinsa shi ne ra’ifi ne.
وما بعلةعموض أو خفا
معلل عند هم قدعرفا
(26) MENENE HADISI MURDARIBA?
Shine hadisin da aka rawaito shi abisa fuskoki daba- dabam daga mai ruwaya daya.
(26) MENENE HUKUNCINSA?
Hukuncinsa ra’ifi ne ba dan komai ba sai sabo da rashin haduwar masu ruwayarsa.
وذو إجتلاف سند أو متن
مصطرب عند أهيلاألفن
(27) MENENE HADISI MUDRAJI?
Shine hadisin da aka shigar da wata magana bata Annabi ba.
(27) MENENE HUKUNCINSA?
Hukuncinsa shine zai iya zama sahihi ko hasani ko ra’ifi.
ومدرحات فى الحديث ما أتت
من بعص الفاظ الرواة إتصلت
(28) MENENE HADISI MUTTAFIKI MUFARRAKI?
Sune hadisai biyu da lafazin su da rubutunsu suka daidaita amma suka canza wajen ma’ana.
(28) MENENE HUKUNCINSA?
yana iya zama sahihi ko hasani ko kuma ra’ifi.
متفق لفظا وخطا متفق
. وصده فيما ذكرنا المفترف
daga dalibinku
musa s zage
Mai Karatu Amma Ka kula Karatu Aje Wajen Mallami ya Fi Alheri da kuma fahimta wannan kawai haska ma Akayi . Allah ya datar da mu duniya da lahira.