ILIMIN HADISI

ILIMIN HADISI A SAUKAKE KASHI NA GOMA

Sponsored Links

                           بسم الله الرحمن الرحيم

       (29)    MENENE HADISI MUKTALAFI?

Shine hadisin da suka zamo sun daidaita a wajen rubutu amma suka saba ta wajen lafazi.

             {29}   MENENE HUKUNCINSA?

   Hukuncinsa shine zai iya zama sahihi ko hasani ko kuma ra’ifi.

                                      مؤتلف متفق الخط فقط
                  وصد مختلف فاخش الغلط

             {30}   MENENE HADISI MUNKARI?

       Hadisin munkari shine hadisin da ra’ifi ne ya rawaito shi.

           {30}   MENENE HUKUNCINSA.?

    Hukuncinsa shine ba za yi aiki da shi ba kuma ba za a  karbe shi ba.

                                 والمنكر الفرد به راو غدا
                     تعديلهُ لا يحمل التفردا

       (31)   MENENE HADISI MUTRUKI?

     Shine hadisin da mallaman hadisi masu yawa suka ruwaitoshi daga ra’ifi.

             (31)  MENENE HUKUNCINSA?

    Hukuncinsa shine ya fi ra’ifi rauni.

                    متروكه ما واحدا به انفرد
         واحمعوا لضعفه فهو كرد

                (32)  MENENE HADISI MAURU’I?

      Shine hadisin karya da aka kirkira aka dangatashi ga Annabi ko zuwa sahabi ko tabi’i.

       (32)     MENENE   HUKUNCINSA ?

    Ruwaito shi ma haramun ne.

                                                وكذب المحتلق المصنوع
                       على النبي فالك الموصوع
                           

      . الحمد الله الصلاة والسلام على رسول الله صلى الله عليه وسلم.

                        

             {     WANENE   SAHABI? }

  Sahabi  shine wanda ya hadu da Annabi yana mai imani da shi ya mutu akan haka

Place                      ( MENENE HUKUNCINSU?)

To, shabai dukkaninsu Adalai ne manyansu da ya ransu, ko da ya halacci yakin da akayi  سيدنا Ali da سيدنا da Mu’awuya dalili kuwa shine Allah yace  MUHAMMADU MANZON ALLAH NE WANDA YAKE TARE DA SHI (wato sahabai) masu matsawa kafirai ne, masu tausayi a tsakanin su.? suratul fatahi aya 29: 

  Dalili na biyu Allah ya ce : 
     kun kasance kune fiyayyun Al’umma da aka fitar daga mutane. suratul Ali Imarana.  
     sannan kuma sai hadisin da bukhari ya rawaito wanda ya ke cewa; 
        fiyayyun mutane wadanda suke cikin lokacin da na ke. a raye wanda muke yi zamani da su sannan wa ‘yan da suke biye da su. 
   sannan hadisin da turmuzi  y a rawaito, wanda Abdullahi dan mugaffin ya ke cewa: 
     Annabi (S A W) yace ku tsoraci Allah cikin sahabbaina, kar ku rikesu  A wulakan ce bayan na bar duniya, domin duk wanda ya so su, to da son da yake min ya so su, Wanda yaki su saboda kin da yake mini ya kisu, wanda ya cutar da su ni ya cutur wanda ya cutar dani Allah ya yiwa wanda ya yiwa Allah, Allah zai kamashi. Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, da dayan ku zai da dutsen uhudu na zinare ace duka zinari ne, to ba zai riski ladan mudu daya ba da suka ciyar. 
        da kuma hadisin da jibiru yya rawaito in da Annabi (SAW) ya ke cewa : hakika Allah ya zabi sahabbai na a cikin mutane da Aljanu. In dai ba manzanni da Annabawa ba to waddannan da ayoyi da hadisai sun nuna cewa  A duniya ba wani mai daraja daya kai ta sahabbai in dai ba Annabi ba ne. 
            
      Allah abin da muka fada  dai dai Allah kaba mu ladan abin ko mokai kus kure Allah kaga farta tamana.       A YAU NE MUKA KAWO DARASI NA KARSHE A CIKIN  LITTAFIN  ILIMIN HADISI A SAUKAKE. 
                                                 وبالله التوفيق 
  ALLAH KASA MUNDACE. 
DAGA DALIBINKU 
  MUSA S ZAGE 
      KANO  
Mai Karatu Amma Ka kula Karatu Aje Wajen Mallami ya Fi Alheri da kuma fahimta wannan kawai haska ma Akayi . Allah ya datar da mu duniya da lahira.
     

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button