LAFIYA JARICE

{Koksan me ake nufi da Cholesterol ?}

Sponsored Links

 Cholesterol shine
 Wani irin sinadari ne da jikin dan adam ke amfani dashi domin gudanar da wasu ayyukan lafiya a cikin jinin mutum.
{Wasu daga cikin ayyukan cholesterol a cikin jini sune:}
1- Sauye-sauyen halittar dan adam yayin da yake balaga da kuma sarrafa sha’awar sa.
2- Dai-daita sukari a cikin jini
3- Kare mutum daga daukar wasu cututtuka ( kamar su infection, Fungals da kuma Virus).
4. Samarda VITAMIN Rukunin D (sinadari maisa kwarin Qashi da kuma kwarin hakora) da sauransu.
Cholesterol dai sinadari ne mai danko kamar kitse.
Idan yayi yawa a cikin jini yana likewa a hanyoyin jini dake daukar jini (artery) zuwa zuciyar dan adam.
Faruwar haka na iya haddasa toshewar fayif din hanyoyin jinin (wato plague/atherosclerosis a turance), da hakan ta faru sai Hanyoyin dake kawo jini zuwa zuciya su toshe (Coronary artery disease). Daga nan sai a samu
“heart attack” (zuciyar mutum ta samu Matsala ko mutum ya mutu).
Ko kuma Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran hanyoyin jini na sauran jikin mutum (heart failure).
{Sauran Cutukkan da Yake kawowa Sun hada da]
1. Hawan Jini 
2.Ciwon suga 
3. Paralyse ,( Mutuwar Bangaren jiki).
5- Obesity , (Nauyi ya mai wuce Kaida) .
6- Free Mature ejaculation (Raunin Al’aurar Namiji Yayin Saduwa).
{Abubuwan da ke saka wannan Cholestoral din Ya ya waita a jikin Mutum kuwa Sune;}
1. Yawan cin lipo Protein, kamar su:- Nama , Kwai ,
2. Kayan Gwangwani, (Can food), misali Kifin Gwangwani , lemon Gwangwani , naman Gwangwani, dasauransu.
3. Yawan cin Saturated fatty acid, kamar Su; Butter, chocolate ,yawan shan Madara.
4.Yawan cin Kayan (Poultry) kamar Kajin Gidan gona, kifin Gidan gona, da sauransu.
5. Cin kitse ( Fat) Babbar musiba ce dake Sabbaba Samuwar cholesterol a jikin Dan Adam.
5. kwanciya nan Take bayan Cin abinci, kafin Narkewar sa da 2hours Awa Biyu.
{Maganin dai-dai tuwar wannan Sinadiri na Cholesterol.}
1- Motsa jiki. Babbar Hanya ce ta yakar yawan Cholesterol .
2- Cin Ganye da yawa.
3- Shan Ruwan Dumi ,shi kadai, bayan an gama cin Abinci.
4- Saka Lemon Tsami a cikin abinci ko abin sha.
5- Amfani da waken Soya Beans.
6- A Samu Tafarnuwa kwaya 10, da lemon Tsami guda 5, da Ruwa madaidaici kamar Babbar Robar Swan ko Faro, a markade Su a Blanda a Hade, a rinka Shan Ruwan bayan cin Abincin Rana ko na Dare a kullum har Zuwa kwana 10.
7- Nisantar dukkan Kayan Maiko, ko daina Cin Kitsi baki daya.
Allah ya kare mu da lafiya da abinda lafiyar zata ci.  Allah yasa Musa ce duniya da lahira.
 Daga naku 
musa s zage

Leave a Reply

Back to top button