Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 7

Sponsored Links

 

 

A hankali nake jin muryanshi dake dawo dani cikin hankalina
da har nasan inda nake a lokacin yana fadin this unfair ace komai sai kin dauka
a waya haka kuna yadawa duniya.

    Riban me zaka samu
a cikin yin hakan yanzu da kake daukanta din a haka ciwone fa ya kuma san kofan
kowa anan da ace kanwance ko wata taka zaka iya yada vedio ta a haka ?

    Maishi yaso yaja
dashi naji yace dashi kajinan wallahi duk wanan vedio din yayi link nasanka na
kuma sheda fuskan ka sai mun makaka kotu.

    Jin hakan yasa
maishi fadin kan wanan din gashi kaga a gaban ka na gogeshi ban iya wahala yace
ka iya tunda baka da tauhidi kun dauki dabi,un yahudawa kun dorawa kanku don
gulma.

    Ciwon kai din
shine abinda zaka tsaya kana dauka makin kai mata addua akan hakan kowa nan
yasan yadda ciwon kai mai tsanani yake ai.

   Ganin yadda yake
fada da yadda ya tsaya ya kula dani sai yawanci suka dauka ai yasanin ne muna
da wani alaka dashi dama sai gasu suna watsewa daga wurin daya bayan daya aka
barmu dagani sai shi a wurin.

    Watace tazo wuce
naji tace a, a Ahmad kana ganuwa kuwa kwana biyu kabar lekomu shago banji mai
yace mata ba sai tayi dariya kawai zata wuce takallo inda nake zaune a cikin
mota naji tace dashi OK ka hadu da ita ashe ?

   Sai a lokacin ya
juyo inda nake din ya dan kalleni farine sol dashi saidai wahala ya boye hakan
na gane hakane kawai don farin bai dishe duka ba gareshi yace wake nan yana
kallona.

   Tace yarinyar ranan
data saya ma abinci ta baka canji ai wanan dince itace gata tana nunoni daga
inda nake zaune a cikin motan nawa ina maida numfashin wahala.

    Bani ruwa daya ya
fada don ta dauko katon din ruwane saidai an fara taba ledan an diba yana
kokarin ciro kudi a cikin aljihunshi ta miko mai tare da fadin barshi kawai
lokacin daya mika mata tsohuwar dari biyun datasha takura cikin aljihunshi.

   Kai ya girgiza mata
yana fadin ki karba kema ba naki bane ai tace bani nace ka barshi ba zan jefa
mata kudin ciki ai kadai barmu ke nan yanzu gashi madam ta fara nadaman rashinka
wurin mu ko jiya saida tayi maganan ka.

    Nabar wurin ku
kenan har abada bana son harka da wullakanci gara naje na nemi wani sana,a
zaifi min da cin fuskan madam kullun a kanmu.

   Kakafa ta
tambayeshi tana nan lafiya ya bata amsa yana balle marfin ruwan daya karba a
hannun ta tare da cuna mata matattan dari biyu lokaci guda da karban goran
ruwan ya nufoni yana fadin.

    Dan sauke kafanki
ki wanke fuskanki zai kara lafa maki In sha Allahu wai dama ashe kasantane haba
nayi mamaki ranan nan data mika min kudi da abinci in baka ai ?

    Veronica please
excuse us bata da lafiyane ta kalloni tana fadin ayyah sannu ko Allah ya sauka
Ahmed sai gani na biyu ke nan ko duk lokacin ina jin abinda suke fada saidai
surutun yarinyar yana shiga min har kasan raina a lokacin don natsuwa kawai
nake son samu.

   Miko hannu nayi da
niyar ya ban sai yace miko hannu na zuba maki ki wanke fuskanki dashi kara miko
mai hannu nayi tare da kwatancen zansha.

   No ba zaki sha ruwa
yanzu ba wanke fuskanki kawai zaki samu relief kadan ko a zuba maki a kafanki
zaifi kice zakisha.

  Na sake kada mashi
kai alaman naji da kyat na sauko da kafana kasa ina gyara gyalen dana dora a
kaina lokacin don Allah ya taimakeni na yafa gyalen da kyau yana rufe min
jikina.

    Haka bujen dake
jikina ya sauka min har kasa dadin saka suturan kwarai a jiki ke nan don baka
san me zai faru da kai ba tunda rayuwan mu ba a hannun mu yake ba.

   Taro hannun ki ya
fada a cikin sound din command a gareni na tara ya zuba min ruwan tare da fadin
wanke fuskanki dashi nayi yadda yace din sai ya zuba min a kafa lokaci guda na
sauke ajiyan zuciya a wurin.

    Shi kuma yana
fadin sannu yanzu ya kikejin kanki ya lafa ko har yanzu yana sarawa ya lafa na
fada a kasalance har lokacin kuma akwai wasu da suka zubawa abinda mukeyi ido
daga nisa suna magana saidai sunki suzo su taimaka minne su don kowa na gudun
shiga wahala yanzu.

    A wahalce na dago
kai tare da fadin na gode dan uwa bai amsa min ba sai cewan da yayi zaki iya
zuwa gida da kanki kai na kada alaman eh ok shiga motan mu gani ya fada yana
tsureni da idanu.

  Ganin yadda na koma
ciki ina kokarin tayar da motan yasa shi fadin fito ki koma baya ki kwanta har
kan ya dan sakeki don tuki a gareki yanzu gangancine.

    Yadda yake ban
umurni zaki rantse shidin dan uwanane na jini ba lkkacin muka hadu dashi ba don
yadda yake nuna min kulawa sosai da damuwa.

    Fita nayi idanuwa
a kaina ya bude bayan motan na shiga ya rufe ya dawo yayi tsaye a gefe  window din motan yana mazurai da idanu ga
masu kallon mu lokacin.

   Yan mintina kadan
ya duko yana fadin zaki gane gida kuwa a haka dana lalaba nakaiki gida yanzu
kai na dan gyada masa dama key na jikin motan bawai sosai ya iya mota ba koshi
lokacin da yayi wankin mota da yana secondary a lokacin ya koya bawai ya wani
gwane bane da tukin.

   Haka ya lalaba ina
nuna mashi hanya saida muka kusa shiga layin mu na dan jawo jakkana da kyat
wayana na lalabo a ciki na dannawa ummah kira ringing uku ta dauka.

    Nace ummah banda
lafiya gani nan wani zai kawoni gida yanzu salati ta saka tana mikewa tsaye
wurin mama ta nufa ta fada mata abinda ke faruwa.

   Saidai tana kai
kofan shiga part din taji muryan mama da yar uwanta suna zagin ta haka yasa ta
juyo bata shiga ba ta nufo waje lokacin har Tani mai aikin ummah ta fita wajen.

   Zuwan ummah yayi
daidai da isowan mu gidan an bude get din gida muna shigowa lokacin suka nufo
inda motan ya tsaya sannu da kokari suke mashi ya fito yana gaidasu.

    Nan Tani ta bude
bayan motan ta fito dani a hankali lokacin shi yanawa ummah bayanin halinda ya
sameni ciki hankalin umma ya tashi sosai lokaci guda ga zancen data sama nata
anayi dakin mama ga kuma wanan matsalana a yanzu.

    Nan tayi mai
godiya suka kamani bayan ummah tace don Allah ya jira ai masa sako yace shi don
Allah ya taimakeni ai badon wani abu ba.

     Bawan Allah mun
gode don Allah ka taimaka muna da wanan maganin da kace shi ka shaka mata ta
dawo daidai din kaga sai a dinga mata amfani dashi Tani ku shiga ki dauko leda
ko kuma barin shigo dai ummah ta fada.

   Ta biyo bayan mu
duk da yace bai karban kudi haka bai hana ummah bayar da dubu biyar akai mashi
ba da leda amma yaki karban kudin ya dai raba maganin biyu yayi alkwarin zai
karo aimun amfani dashi.

  Ikon Allah ashe har
yanzu akwai irin yaran nan karamin yaro haka da halin manya ummah ta fada ta
maida kallonta gareni kuma kafin ta nisa don abubuwan sun daure mata kai a
lokaci guda haka gashi kuma bata ko karbi lamban matashin ba har ya tafi.

   Tsuki taja sai tani
ke fadin hjy wani abin ne wallahi ya kamata ace mun amshi layin yaron nan amma
rudewa yasa mun barshi ya tafi bamu karba ba.

   Hjy ni ai har gidan
su yayi min kwantace na kuma gane layin nasu kai amma kin kyauta min Tani don
in maganin yana da kyau ai dole mu nema mu aje a wurin mu don bacin rana irin
haka.

    Barci nayi sosai
ranan saidai ina tashi naji wasai ba wanan ciwon kan ko gani dishi dishi gashi
na koma ina jina normal dani kamar ba abinda ya faru dani.

   Saidai da idan na
tuna da abinda ya faru dani sai naji nauyi da kunyar hakan amma idan kuma
natuno da abinda wanan matashin ya fada sai naji somehow amma aiba kowane yasan
haka ba na fada ni daya a daki ina jan tsoki

    Itako ummah
kantane ya kara daurewa sosai da lamarin mama don data fito har kofa  ummah suke yarta tana sallama  ummah din saiki rantse babu wani abinda ya
taba hadasu ko suke shiryawa a kasa daya shafi kisantaka irin na matan da basu
da hakkuri da tawakkali ga ubangiji.

  Shin ko sun dade
suna mata wanan bata gano bane sai yanzu da ubangiji ya haska mata har taji da
kunnuwanta ba wani ya fada mata ba amma sai gashi taji  komai a saukake.

   Har da shigowa
dakin suna gaida maamah da jiki sukai Allah ya sauwaka kamar da gaske sun damu
bayan fitan su ta lekasu sai gashi suna dariya
kamar wasu yara dasu irin nuna sam basu damu ba su.

   Ranan haka ummah ta
kwana cikin damuwa da tashin hankali har gari ya waye tun kan tayi sallah saida
ta leka dakina ta tasheni da barci na tashi nayi sallah.

   Sam ummah bata zata
zan samu zuwa makaranta ba a ranan sai gashi na fito da shirina ina sallaman
ummah din bata yarda na fita gida ba saida ta tabbatar da cewa na karya kafin
na fita.

    Dkn Tani bata riga
da ta iso ba a lokacin don haka ummah ta hada min shayi da ruwan flask din dake
dakinta ruwan tea din kawai nasha ban hada da komai ba nasha na fita.

    Tani don damuwan
data kwana dashi bata zo gidan mu ba direct data fito sai ta wuce gidan wanan
matashin   don ta karbo maganin tayi sa,a
ta sameshi ya fito zai tafi school.

   Saida ta tuna mai
ko ita wacece tare da fada mai sakon hjy yasa ya dubi lokaci yace su shiga daga
ciki tabi bayan shi zuwa cikin gidan tana bin ko ina na gidan da kallon mamakin
iri rayuwan talaucin da bayin Allah nan keyi a cikin gidan nasu.

   Ke nan duk yadda
kake ganin kanka kafi wani don wani na can bai kaika ba don nasa irin talaucin
sudake cikin gida har da siminti a tsakar gidan tana ganin talaucinta ga wa
yanan su dan dakunane kamar madafi suke rayuwa a ciki.

   Nan yaiwa Dije dan
bayani a gurguje ya barta da Tani su karasa maganan tunda shima itace ta karbo
mashi don haka ita tasan yadda zasuyi bashi ba.

      Nan ne hira ya
barke a tsakanin su har take labartawa Dije komai har kudin dayaki karba hannun
ummah din duk a cikin dadin hira Tani taba dije labarin komai.

    Tare sukaje aka
karbo malam Tanimu yayi masu bayanin komai yadda za,ayi amfani dashi har dana
tsarin jiki da sauransu duk ya bada ta bashi dubu daya ya amsa yana ta godiya.

    Hakan yasata
makara da zuwa aiki koda tazo ta samu ummah tayi nisa ga aikin hada breakfast
ummah taso tayi fada sai ga leda ta fito dashi tana fadin aida zancen ku na
kwana a raina hjy.

   Shiyasa na makara
ga wanan na karbo dana uwar dakina wanka zakiyi har yaran kuyi hayaki
wanan  kuma yace kusha tun da asuba na
neman sa,an makiyane da makarun su.

   Kallonta ummah keyi
kamar da tuhuma a zuciyar ta sai Tani din tace hjy ko baki aikeni ba ni mai zuwa
na karbo maki wanan din don koba ki fada ba mai hankali yasan zaman da akeyi a
wanan gida.

   Ba wani abin muni
na karbo maki ba kariyane da tsari ance ko kana da kyau kara da wanka don ni
gaskiya ciwon nan da uwar dakina keyi kwanan nan da ayar tambaya a cikinsa.

    Ciwo bai tashi sai
lokacin da yarinya zata je daukan darasi kan abinda zai amfaneta a rayuwa kinga
wanan alaman wani sherine dake faruwa a wani kulli dake faruwa a wani wurin.

    Kome ke faruwa da
ita da sanin Allah nasan ina iya addua na kan zuri,ata koda yaushe ina neman
kariya gun ubangijina da ya tsare mu kan abinda bamu sani ba mai cutarwa zuwa
garemu.

    Kwarai kuwa hjy
nidin shedace kan hakan nasan baki wasa wurin ibadan ki don shine ma har yau ba
a ci galaba a gareki ba amma kuma ki sani.

  Yaran nan zaki duba
idan ana harin ka ba a sameka ba  za a
iya samun yaran ka ko wani abin ka shine dadin kiwon dabba da kikaga mutanen
kauye sunayi.

   Sun san ma,anan
hakan shiyasa ba kauye bai rabuwa da kiwo koda ta kazace kuwa don sai ya fadawa
dabban naka don ansan naka dinne.

    Kiga ko dole a
tallafawa rayuwan yaran nan don maganan gaskiya hjy maimuna bata kaunan yaran
nan ta yadda har bata iya boye hakan a gaban kowa saboda kishin ki daya
shafesu.

    Nisawa ummah tayi
kafin ta kai kallonta ga kullin maganin da Tani din ta karbo mata tace bawai
ban sanda hakan bane na dade da sanin akwai kiyayya har ya shafi yarana saidai
bana son na raja,a gun irin wa yan nan abubuwan ne har ya bata maka imanin ka.

    Amma na gode in
sha Allahu zan gwada zanyi muna amfani dashi da yardan Allah musanman kan ita
maamah din don wanan matsalan nata ya fara damuna gaskiya.

  Ciwo haka daga sama
Allah na tuba ni wanan matsalan haka ta ina zan soma taron shi hjy haka na faruwa
kana zaune da yaron lafiya da rana tsaka ya sauya ma .

  In sha Allahu maamah
tafi karfin duk wani shedani da shedanci ki dai dage kiyi masu amfani da wanan
maganin koba komai ba a san inda kizo ke saka ba ai shiyasa akewa yara tsari da
adduoi a yanzu sosai.

 

Leave a Reply

Back to top button