Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 28

Sponsored Links

 

28- “Me kike ci kika zama ƙatuwa haka?” Ya tambayeta, yana kallon yadda ta zauna a wurin kamar kayan wanki. Tura baki tayi tana fadin.”Ba wani katancin da nayi kawai baka gani ne!” Sosa goshinsa yayi yana faɗin. “Kuma gaskiya ne,bana gani sosai. Amma, cire min wannan abin na ganki da kyau!” Kallonshi tayi sannan ta ja mayafi ta rufe kirjinta. “Da nace maka ina son baby tafiya kayi baka kula ni ba” dafe goshinsa yayi yana faɗin. “Na manta ne, amma kuma ina son naga yadda zan iya baki wani Babyn babu matsala!” A ranshi yana see mamakin wannan haukar na Zeeno ga ciki a jikinki kina niman wani cikin, salon da yana nan, suna rigima da junansu.
A hankali ya kura mata idanu, shiru yayi idanunshi yana ɗaukar saken fatarta. Har ga Allah Zeeno bata gane mijinta take haukar son Kasancewa da shi ba, shi yasa take damuwa ya mata wani cikin, kurawa kirjinta idanu yayi yana faɗin. “Good girl! Gaskiya na yarda kina son Baby! Zan saka Adnan ya saya miki ticket zaku tawo dasu Ammyn kinji.”
Gyada kai tayi tana faɗin. “Hmm! Ni dai yau nake so?” “Kin ga in sha Allah jibi!” Kamar tayi kuka ta ce mishi. “Tow shi kenan!” Ta faɗa tana yada kai. “Sorry kinji!”
“Tow!”
Kashe wayar tayi, tare da sakawa a fly mode, sannan ta wuce ban daki. Ruwa ta sakarwa kanta, sai da tayi wanka ko zata ji sauƙin ganinshi da tayi. Zama tayi a bakin gadon kamar wacce ta rasa kome nata.
***
Keivroto
Zaune yake yana kallon hotunan da ya dauka, suna wayar. Hotunan ta ne. Juyi yake a kan kujerar office dinshi, yi mishi kyau matuƙa amma yana gudun kada ta zo a samu matsala, wayar shi ya dauka yayi baya da kai yana kiran Adnan. “Kayi musu booking jirgin asuba!”
“An gama yallabai!”
A hankali yake kara zooming hoton yana murmushi, yar siririya tayi kiba! Ya faɗa a ranshi, yana kara jin kaunarta.
Al’amarin rigima da bude file din kisan iyayensu aka bude, bincike ake yi kamar akwai wani abu da ya alakanta haka da gwamnatin kasar na da. Haka yasa Malik ya kuma bude wuta, sai an yi.
Haka yasa ake farmarka shi, duk da baya son wani abu da zai shafe ta, amma yadda take nuna tana bukatar ganinshi yasa shi. Sawa a mata booking. Kiran Elbashir yayi yana faɗin. “Zainab zasu shigo da Ammyn Abbas. A bawa airport tsaro sama da baya.” “Malik a hakura da zuwanta, Hafsy ma tana karkashin kulawarmu balle Zainaba da kasan shegen taurin kanta kamar na karamin jaki;”
Wani irin dariya Malik ya saka yana faɗin. “Bashir Matata ce take da taurin kai, kamar a jinjirin jaki?”
“Malik waye bai san halin taurin kanta? Sannan Ammyn da Abbas su zauna, kafin kome ya lafa. Ita tsuntsuwar soyayya sai ta zo.”
“Yawwa Yallabai Bashir!” Kashe wayar yayi yana dariya, kiran Adnan yayi ya gaya mishi ya cire sunan Ammy da Abbas, ya turo Zeeno. “Tow yallabai!” Ya kashe wayar.
Shigowar wani sako, yasa shi dubawa. “Kamar yadda na rasa Y’ata wallahi sai na saka ka rasa kome Malik, hakkin mutuwar Maidah yana rataye a wuyarka”
Kiran layin yayi, yana faɗin.
“Lalla Salmah! Kashe Nuratu da kaita wurin Khuldu Jahid Khan da Shu’iba, turo Jalilah ta hana ni auren Zainab, ko kawo Maidah ta saka min gida on hell ko? Duk basu isa hujjar da zai saka ki gane kawaici da kunyar da na miki ba? Kizo Keivroto babu me tab’a ki.”
Ya faɗa yana murmushi, sannan ya koma kujerarshi yana murmushi.”mutanen da ba yarda dasu, sune masu shirin su yake ni akan gaskiyaida na san nike da ita!”
Kiranshi aka yi, ya ɗauka. “Maciyi amana, fasiki makashi sai na tabbatar da rabaka da kowa sannan kayi mutuwar da gawar kare sai ta fika daraja!”
“Khamis Shatima! Tow dai Allah ya baka sa’a zance ba”
“Kai Malik karshen ka yazo!”
“Allah ya sa muyi kyakkyawar karshen!” Ya fada yana dariya, domin da haka ya dace da shi.
***
Demark.
Da wuri ta shirya, domin Adnan ya gayawa Ammyn an soke tafiyarsu, dama tasan Keivroto babu lafiya, don haka ta saka Zeeno a gaba da faɗa. “kin san halin da ake ciki a inda zaki je kuwa? Shima da yake namiji da gaske yake kokuwa da rayuwarshi balle ke, da yanzu ba da ba ne, ba zaki iya kare kanki ba, balle wani da baki san da zaman shi ba”
“Kai Ammyn tow ni yaushe zan girma? Nayi kewar Keivroto ne fa, nake son zuwa na ga mutane su ganni!”
“Zainab mijinki kike kewa, a wannan yanayin da kin hakura ya gama magance matsalar gabanshi zai zo gare ki ”
“Ammyn!!” Ta kira sunanta kamar zata yi kuka.
“Don Allah ki daina faɗar haka kada ki hanani zuwa don Allah.”
Ta fada idanunta yana kawo ruwa, “Maman Abbas, kyaleta mu da muke bukatar zuwanta, yau ta ce zata da kafarta Allah ya tsere ya kuma kai su lafiya. ”
“Shi kenan Inna, wai dama saboda yanayin ta ne, amma Allah ya kiyaye hanya ba”
Gyada kai tayi, tana zama kusa da Inna. “Gaskiya matar nan ba zan so ki mutu da wuri ba.” “Saboda rayuwata a hannunki take ba, don kaniyarki.”
Dariya Zeeno tayi tana me wucewa dakinta, da idanu suka bita. “Zan ga ranar da Yarinyar nan zata yi hankali. Abu a jikinka baka gane ba sai yaushe zaka gane!”
“Yarintar fa! Idan ba yarinta ba, me zak saka haka? A yanzu cikin ya fara kwari dakyar take zama dakyar take tashi amma haka bai saka ta fahimci yanayin da take ciki ba.” Inji Sayyada Quddisiya.
Murmushi suka yi, daga tafiyar Malik zuwa yanzu wata uku kenan, lokacin da cikin ya damu matsala yana wata wata uku ba don ya damu matsala ba, cikin watansa shida da wasu kwanaki kenan, yanzu kuma ya koma baya, ko don abin da ya faru ne cikin ya saka mata kiba kamar an hurata, sannan duk wani wurin sharholiya na jikinta ya kara girma da cika.

Ita tana ganin kamar kiba tayi, bayan cikin ne yasa haka.
A hankali ta gama kwashe kayanta, sannn ya koma ta kwanta. Shiru a yan kwanakin nan, sai ta ji cikinta kamar ana yawo ko ana motsi, ita ta gaji da yiwa nurse bayani tana cewa lafiyarta lau. Wancan karon da Dr Helin tazo ta gaya mata cewa tayi normal ai wani lokacin organ na cikin mutum yana haka. Shi yasa ta share bata kuma magana ba, amma gaskiya har yanzu abin yana mata wannan yawon.
Dake a duniya bata da wanda take saukewa mitarta, a zauna lafiya sai Malik don haka ta kira shi kamar zata yi kuka ta ce mishi. “Mayorrrrrrr!” Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce mata. “ina jinki babyna!”
“Mayorrrr! Wani abu yana motsi a cikina?”
“Ikon Allah kuma Helin ta duba?”
“Ina ta duba ni, kullum sai su ce organ dina ke motsi.”
“Ok idan kin zo sai na kai ki wurin Dr Saddika ta duba baki”
Aikuwa ya biye mata suka sake zama sakarkaru, dama can sakarya ce bata sani ba, amma zuwa yanzu Malik ya kara girmama sakarcinta da shirmenta.

Ya kuma biye mata tana kara, sakalce mishi. Ba zuwan Zeenobia ba ne, bai zama dole ta iya daukar wasu al’amarin. Don haka har suka isa airport tana waya da shi, sai da suka kusan tashi ta kashe wayar ta saka a fly mode.

—–
Tunda suka ce mishi ta taso, ya tattara suka koma airport. Domin ya san zata sauka da safe ne, don haka ya tare a airport ɗin, zuwa yanzu an mishi txt na barazanar za a kashe ta. Ita da abin cikinta. Da ya hanata zuwa zata ga kamar bai sonta ne, amma yanzu da ya barta ta tawo yasan koda wasa ba zata sake yarda ta cusa kanta a hatsari haka ba. Aiki kawai ake ana leke leke. Yana zaune idanunshi a kan kofar da matafiya suke fitowa. Dan kishingida yayi, barci ya dauke shi.
“Mayor!” D’ago kanshi yayi ya kalli yadda ta jike cikin jini har yana d’iga. Nuna mishi hanyar da ta fito tayi, Elbashir ya hango kwance cikin jini! “Har mutane nawa zasu mutu domin ka!”
A firgice ya farka, Elbashir ya gani zaune a gefenshi. Mikewa yayi ya kallon kofar da shi kanshi Elbashir din, wayar shi ya ciro tare da kiran Commander na sojojin kasar, akan a turo musu sojoji.
Sannan ya kashe wayar, ko minti ashirin ba ayi ba, suka iso. Fuskar shi a hade ya ce musu. “Ku tafi da shi!” “Malik me nayi ?” “Ku tafi da shi kawai”
“Malik gaya min meye nai maka!”
“Ku bashi abinci, ya ci ya koshi. Sannan a rufe shi a idan zai huta yana fama da cutar hauka ce, idan ya ga mata masu ciki farmakarsu yaƙe. ”
“Malik!” Ya kira sunanshi kamar zai tashi sama, haka sojojin suka tisa keyarshi. Tare da barin airport ɗin, ajiyar zuciya Malik ya sauke. “Ba zan yarda ka mutu domin ni ba!”
Yana ganin yadda aka tusa shi cikin motar, sannan Commander Keivroto ya kira shi. “Me yasa ka saka aka kama shi. ”
“Bana son na saka rayuwar mutanen da suke kusa da ni a matsala ne. Shi yasa don Allah a kula da shi, zan kula da nan ɗin.”
“In sha Allah!”
Daga haka ya cigaba da kula da zuwan Zeeno, wurin karfe biyu na rana, jirginsu ya sauka. Idanunshi yana kan fitowar mutane, idanunshi ne, ya sauka a kan Zainaban shi, tana tafiya a hankali, tare da yatsuna fuska sakamako gajiyar da tayi, kafaffunta sun kumbura, da sassarfa ya isa wurin kafin ta iso, bude mata hannu yayi ta shiga ta. Tana sauke ajiyar zuciya. Kar’ar harbin da ya cika wurin yasa aka musu zobe, tare da kare Malik da ita, ware idanu tayi kamar zata fashe da kuka. “Me haka yake nufi?”
“Rayuwar da nake ne yanzu, muje!” Wayar shi tayi kara, dauka yayi yana rike ta. “Ka duba wuyar matarka, ba fa kai kaɗai ka iya wannan wasar ba!”

Duba wuyarta yayi yaga jini na zuba. “Shatima! Kada ka sake ka tab’a min mata da yarona. Domin yanzu haka Nadrah tana Cyprus tare da kanwar mahaifiyarta, tana cikin hotel din da aka kama ta, sannan tana sanye da bikini skyblue. Sai kanwar mahaifiyarta tana sanye da bakaken kaya, tana cikin swimming pool, kayi kokarin dakatar da ita daukar ruwan da yake gefenta, ko kuma a kira ka domin binciken taya aka yi yarka da kanwar mahaifiyarta suke tu’amali da miyagun kwayoyi!.”
. Ya kashe wayar, tana kallonshi. Har suka fita. “Me haka yake nufi?”
“Ba matsalarki ba ne, muje gida.” Radadin da take ji ne ysa ta shafa wuyarta, “Jini!” Ta fada a firgice, tana rike wurin. Daukar hanky dinshi yayi ya goge mata, yana cewa.
“Kasan halin da ake cikin ka sani na zo?” Zuba mata idanu, kafin ya ce mata. “Tow ya zanyi?” Bata san lokacin da jikinta ya fara rawa ba. “Ke!” Ya daka mata tsawa. “Ki kula da kanki, cikin jikinki kike son mu rasa shi?” Ware idanu tayi, tana rike hannunsa. “Ciki ne a jikina!”
“Shi yasa nace ki bari kome ya lafa, sai ki zo kin ga gashi nan, zaki saka mu cikin tashin hankali. Ban damu na mutu ba, amma please ki kula da cikin kinji!”
Ya faɗa yana sumbatar goshinta, kwantar da kanta tayi tana sake ajiyar zuciya. “Me yake faruwa ne?”
“Wani dan karamin rigima ne yake faruwa, idan na magance zan miki bayani!”
Kwantar da kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya, wani irin bala’in tsoron kada wani abu ya tab’a babynsu. Har suka isa gidanshi me cike da sojoji da yan sanda.
“Sannu kinji!”
“Yawwa! Ina Uncle Elbashir!”
“Sawa nayi aka garkame min shi, domin kada wani abu ya same shi!”
Zillo da cikinta yayi ta rike hannunshi. “What?” “Wani abu ya juya a cikina”
Rungume ta yayi yana dariya, “Babyn mu ne yake murnan ya hadu da Daadinshi” kwantar da kai tayi, tana tuna bayanin matukar ta fahimci tana dauke da cikin Malik zata rabu da shi. Kallonshi take,
“Me ye?”
“Ka hakura da abinda yake faruwa, mu tafi wani wuri mu rayu! Ko na tafi da Babyna!”
“Me yasa baki son zaman lafiya?”
“Taya zan zauna a nan kayi sanadin rasa cikin jikina? Idan har da gaske kana son mu, ka bar kome kazo muje mu bar wannan duniyar da abin yake cikinshi, mu yi tarbiyyar Yaronmu!”
“Anan aka fara, anan zan karkare shi ban miki wannan soyayyar da zaki juya ni!”
“Malik ka bar wannan rayuwar mu tafi wani wuri!”
“Babu inda zani dama kin zo ne, kin zo ki d’aga min hankali ne?”
“Ba zaka zo ba kenan?”
“Kema kin san baki yi wannan isar ba.”
Ganin da gaske ba zai yarda ya hau ra’ayinta ba, yasa ta Fara faɗa.
“Zan zauna da kai, daga lokacin da wani abu ya faru wallahi zan aikata abinda zai wargaza ikonka!” Ta wuce bata kuma magana ba. Sako Shatima ya turo mishi.
*Da alamu Zainab bata san kai ka kashe mata iyaye ba, wannan shine numberta.*
Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/23, 1:53 PM] Yan Mata:

 

Leave a Reply

Back to top button