Bakar Ayah Hausa NovelHausa Novels

Bakar Ayah 9

Sponsored Links

Page 🖤09🖤

 

Buɗe ido tayi ta kalleta a wani ɗaki mai rufin zana,saidai yanayin zanar wata kalace daban mai ƙarfi da kuma adon rawaya rawaya.
Abinda ya farune yafara tariyowa cikin ranta.
Kama daga fitowarta daga gida neman wacce zatayi mata maganin lubna,harma da kuma shigowarta wata duniya sabuwa da tayi.
Zabura tayi ta miƙe tareda ya mutsa fuska,jikinta yayi tsamin kaman anyi mata dukan tsiyah.
Tambaya tafarayi a cikin ranta,akan nan ɗin inane,batakai ga samun amsar tambayar ta ba,kokuma son tunowa yaushe ta shigo wajen ba,ta kalli labulen ɗakin ya motsa,da alama wani ne ke son shigowa a cikin ɗakin.
Zurawa baƙin ƙofara ido tayi,yayinda bayan kowanne daƙiƙa zuciyarta ke hawar da bugunta zuwa matakin sama.
Sauƙe ajiyar zuciya tayi tareda runtse ido ganin ba kowa bace ta shigo face Iyani.
Tana sanye da wasu irin kaya da bata taba ganinta da irinsu ba,hannunta kuma ɗauke da akwashi guda uku akan akan faifayi.
Murmushi tayi tareda ajiye abin hannunnata kana tace.
“Ina kwana Hajiya sannu da tashi,ya jikin?”
Batareda ta amsa gaisuwar ba tafara jefowa iyani tambayoyin data kasa bawa kanta amsarsu.
“Menene ya faru bayan barin mu jejinnan,sannan nan inane?”
“Uhmm Hajiya suma kikayi lokacin da toro ya sauƙemu,bayan munshigo garine na roƙeshi ya kawomu har ƙofar gidanmu,kasancewar ni ban iya tuƙi ba,shima kuma iliya a lokacin bazai iya tuƙi ba”
“Yanzun wane lokacinne,tun yaushe nake kwance?”
“Eh tun jiya da yamma,yanzu kuma karfe 9:45am na safiyah.
Yakamata kici abinci kiyi wanka sannan ki rama sallolinki,kafin kuma muyi maganar abinda ya kawomu”
Tana gama bata amsar ta buɗe kwanukan da suke gabanta,ɗayah tuwon Doyane,ɗayan kuma miyace mai kala kalar ja da kuma baƙi,wanda Hajiya zeenah bata taba ganin irinsa ba”
“Wannan kuma mai nene?
“Uhm ɗayane daga cikin irin abincin nan yankin,muna dayawan doya sosai,shiyasa yawanci abincinmu muke sarrafata dashi,baƙin cikin miyar kuma kifine da kuma busashshen inibi,kici akwai daɗi sosai.”
Daga haka tabar ɗakin domin bata damar samun cin abincin.
Kaman mai tsoron kada taci ta mutu haka ta tsoma hannunta a cikin miyar takai bakinta domin ta ɗanɗana.
Uhm babu laifi fuskarta ya nuna abincin yayi daɗi,babu bata lokaci tafara yankar tuwon doyar tana ci,har saida taji cikinta ya ɗauka tukunna.
A ranar basu samu damar fita zuwa gidan su Bombi ba,saboda har yanzu jikinsu bai dawo normal ba daga tafiyar da suka niƙo.
Iyanice ta kalli mahaifiyar su wacce take zaune tana bushe tsinkayen da suke cikin ganyen shayinta,maganar da iyani tayi ne yasakata tsayawa da abinda take takalleta.
“Inna ina labarin Bambi kuwa,wacce da addah ke bani labarinta?”
“Oh ɗiyarnan,ke kuma mai zakiyi da labarin bombi har kike tambaya,na daɗe banga mai son yaji sunanta ba ma ,ballantana kuma labarinta”
“Ayyah inna inaso na haɗu da itane,akwai abinda nakeso muyi magana da ita akai,gidansu zakiyi min kwatance?”
“Handi mee Iyani,ki haɗu da Bombee?,akan wanne babban dalili haka?”
“Lahh bafah abune babba sosai ba,dama Hajiya ce takeson yin magana da ita”
“Hajiyannaki dan batasanta bane hala,tun wuri ina yimuku kashedi ku fita a harkar wannan yarinyar,dan ita ɗin tauraruwa ce mai wutsiya,ganinta bashida alheri ko kaɗan,maza ma basuja da sunanta bare kuma ku da baƙine,bakusan komai a gameda garinnan ba da kewayensa”
Shuru iyani tayi tana kallon mahaifiyar tata,da alama bazata samu amsar da takeso ba a gareta sam.
Tashi tayi ta nufi ɗakin da Hajiya zeenah take,tun kafin tace wani abu Hajiya zeenah ta dakatar da ita tareda cewa.
“Naji duk abinda innarki tace iyani,tabbas daga yanda nakejin labarinta a bakin mutane,ita yarinya ce mai hatsarin gaske,saidai nayi tafiya mai nisa nazo garin da take,bazan iya tafiya haka hannu rabbana ba batareda na ganta ba,idan itace taƙi amincewa buƙatata to shine zan haƙura”
‘Jinjina taurin kai da kuma Ra’ayi irinna hajiya zeenah tayi,a zatonta jin labarin inna zaisa tace ta fasa,amma kuma ashe abin ba haka bane’
“To shikenan Hajiya zamu je gidanna su a gobe inshaaallah,koma menene sai muji mai zatace”

___ ____ ___

A bakin wajen wani mai shayi iliya ya tsayah ta motar,tareda fitowa ya nufi wajen da samarin ke zaune a waje.
Sallam yafara yimusu suka amsa,kafin ya tambayesu abinda yake nema.
“Bayin Allah idan bazaku damu ba dan Allah gidan su Bombi muke nema?”
Kowa zaro ido yayi yana kallonsa ,wani kanma daya kurbi shayi da biredi,bai san lokacin daya furzar dashi ba yana kallon iliyan.
“Kai amma kai baƙone a garinnan koh,rabon danaji ance gidan su bombi shekaru da dama,ai kawai kace mana gidan su Innayee,waye ma yasan gidannan danasu bombi,ko mutanen gidan bazasuso ka haɗata da gidansu ba,amma jirani nagama shan shayi na rakaka gidan,maƙwantanmu ne katanga ɗaya”
Yana gama faɗin hakan ya cigaba da cusa biredinsa,iliya yana tsaye yana jiransa har yagama kafin yazo suka nufi wajen motar.
“Kai kuma daga cewa zaka tambayo gidansu saika yi tafiyarka, kaman an aiki bawa garinsu,wannan kuma wanene a tareda kai,a shegen surutunka har kayi aboki a garinda baka sani ba koh?”
“Ahah hajiya wannan ɗin ɗan anguwarsu su bombinne,na jirashi yagama shan shayine,akan zai rakamu gidan”
Kallon ta fahimta tayi musu kafin da ɗauke kanta.
Zagayowa yayi ta zauna a wajen zaman banza ba gefen drivern kafin suka fara tafiyah.
Tunda suke tafiyah babu wanda yace uhm a cikinsu,sai iya saurayin dayake nunawa iliya inda zaibi,da haka har suka ƙariso ƙofar gidan su bombin.
Sallama yayi musu tareda cewa.
“To ga gidan da kuke nema kun ƙariso,Allah ya baku sa’a sannan ya fitarku matsala,ni nayi nan”
Baƙin ƙofar gidan suka ƙarisa tareda yin sallama,da har sun sare akan babu wanda zai fito,sai kuma sukaga wani dattijo fari sol mai ɗan tsayi kaɗan ya fito daga gidan.
Gaisawa sukayi hannu da hannu da iliya kafin yayi musu iso zuwa cikin gidan.
“Lale maraba daku,daga ina haka kuka zo”
“Eh to tafiya da nisa malam,ko zamu iya shiga mu zauna”
“Eh to mai zai hana”
Tun daga bakin zauren gidan yake ƙwalawa matar tasa ƙira.
“Yawuro ina kike so munyi baƙi daga waje mai nisa”
Farar dattijuwa ce tafito daga ɗakin,fuskarta cikeda fara’ah,kana ganinta kaga wayayyiyar mata.
“Lale marabanku da zuwa,sannunku da zuwa”
Cikin annashuwa da sakin fuska ta tare su,duk da kasancewar bata sansu ba.
Ruwa aka kawo musu mai sanyi tareda kindirmo,domin kowa yakallesu dama yaga wayayyun fulani masu cikeda ilimi,domin duk yankinsu su dama fulanine a wajen.
“Innayee maza kizo ki gaisheda baƙi mana,sau nawa nake faɗamiki banason wannan halin na kunyah sosai”
“Lahh mace ai ana sonta da kunya,musamman a wannan lokacin”
Hajiya ta faɗa itama cikin fara’ah.
“Eh to hakane,musamman ma kinga mu fulani hakan a cikin jininmu yake”
Suna cikin maganar ne farar yarinyar tafito daga ɗakin kanta a sunkuye,a gaban su Hajiya zeenah ta tsugunna tareda gaishesu ƙaramar murya mai sanyi,kayan Makaranta a jikinta,da alama islamiyyah zataje.
“Ina kwana Hajiya ya hanya”
“Lafiya kalau,makaranta za’aje kenan,to Allah ya taimaka”
Motsin mutum sukaji yana shirin fitowa daga wani ɗaki take kallon na Yawuron.
Wata matace tafito daga cikin ɗakin tana shashima bangon da take bi.
Duk da kana kallon yanyinta zaka hango tana cikin yanyin laluri,amma kuma fatarta fari sol,ga idonta kuma dara dara,saidai da alama basa aikinsu da kowanne ido yakeyi.
“Innayi innarki daneji ta fito,rakata banɗaki dannan buta a hannunta,da alama bayi zata zaga”
Tun kafin ta rufe baki innayin ta tashi tareda ƙarisawa wajen wacce aka ƙira da Danejin.
Duk abinda yake faruwa su Hajiya zeenah suna kallo,har innayi takai matar banɗaki ta dawo da ita ɗakinnata.
Sallama tayiwa su Hajiya zeenah da kuma innar tata,kafin ta tafi makaranta.
Malam Ahmadu yashigo gidan tun bayan da yayiwa su Hajiya zeenah iso ya fita.
“To Hajiya muna jinki mai yake tafe dake,domin bamu wayeki ba,gashi kince mana wajen mu kika zo”
“Eh hakane malam wajenku nazo,idan baxaku damu ba dama wajen ƴar ku nazo da magana muhimmiya,shin kozan iya ganinta?”
Murmushi Yawuro tayi,da alama hasashenta yazama gaskiya,neman iri hajiyan tazo nema a wajen su.
“Ai Hajiya kin riga kin ganta,saidai ko kuma maganar manyan yanzu daza’ayi”
“Ahah baki fahimceni ba,bombi nake nufi,akwai abinda nakeson tattaunawa da itah”
Tsitt wajen yayi kaman an ɗauke ruwa,yayinda murmushi da kuma fara’ar dayake fuskar mutane biyun ya bace nan take,babu abinda ya maye gurbi zai mamaki da kuma baƙinciki.
Baki buɗe suka tsaya suna kallon Hajiya zeenah,kafin daga baya mlm Ahmdu yasamu ƙwarin gwiwar cewar.
“Uhm Hajiya inaga kinyi batan gidane,amma ni ƴata guda ɗayace Khadeejatu(innayi),bayan ita kuma banni da wata”
“Amma mlm an ce mana nan……….”
“Ya isa haka hajiya,tun inaganin girman ki,kina ganin nawa ki daina kawomin wanann zancen,idan kuma kin dage dole saikin samo mai sunan da kika ambata,to ki tafi jeji can inda yadace da mai sunan,amma banan ba gidan mutunci”
Yana gama faɗin hakan yatashi yayi waje.
Itama yawuro kallonsu tayi tareda cewa.
“Dan allah kozaku iya tashi,ina son naɗe tabarmata da kuke zaune akai”
Cikeda mamaki Hajiya zeenah suka tashi suna kallon Yawuron da lokaci ɗaya ta sauya daga matar da ta tarbesu.

Toh fah yaya takene?…….

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

 

 

 

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

Leave a Reply

Back to top button