Ramadan Kareem

ABUBUWAN DA MAI AZUMI ZAI KEBANTA DASU YAYIN GUDANAR DA IBADARSA TA AZUMI

Sponsored Links

ABUBUWAN DA MAI AZUMI ZAI KEBANTA DASU YAYIN GUDANAR DA IBADARSA TA AZUMI

Da farko mai ibadar azumi zai kebata da wadan nan abubuwa kamar haka. 

•karya

•giba

•zagi

•kallo

•ha’inci

•zancen banza kallon hoton batsa ko hoton Banza

•kallon films na batsa. 


» KARYA» karya wata abace da ANNABI (S.A.W) yai mana kashedi a kanta har yake ce damu ” Ayoyin munafiki guda ukune» na farko idan yai zance yai ‘ karya ‘ to kaga anan abinda yazo farko shine. karya sai kuma indan yai alkawari ya saba idan an amince masa yayi ha’inci .

»GIBA» giba wata abace daga cikin muggan kaba’ir ma’ana giba shine cin naman dan uwanka musulmi ta hanyar yidashi a lokacin daka fuskanci bayan an sai karin ka aibatashi kana fadin muggan halinsa ( yana dashi ko bai dashi ) wannan abu shine giba a takaice. 

»ZAGI» zagi wani abune da dan adam keyi a lokacin da wata husuma ko rigima ta taso a Tsakanin junansu Sai dai kuma mu al’umma musulmi ANNABI (S.A.W) ya hanemu da wannan ba dabi’a kamar yadda yake fada yake cewa “Zagin mutum musulmi fasikancine ” dan haka kai mai ibadar azumi bai kamace kaba ka dauki wannan zunubi (zagi) kace zaka rinkayinsa a lokacin da kake gudanarda ibadar ka.

»KALLO» kallo shima wani abune damai azumi zai kiyaye shi a yayin da.

Yake gudanarda da ibadarsa sai ya maida kallonsa ga kallon takarda.

Al’quran mai girma


»HA’i’NCI» ha’inci abune mai girman gaske idan ba mutum yayi da gaskeba wajen kawar da kansa daga Abin duniya mai ibadar azumi baya halatta yai tarayya dashi a cikin gudanarda ibadarsa (ha-nci)

»ZANCEN BANZA» zancen banza bai dace gamai azumi ba yarin ga yin saba a lokacin da yake gudanarda ibadarsa domin yin zancen banza zai kawo nakasa ga azumin ka. 

»KALLON HOTON BATSA» kallon hoton batsa abune babba idan mai azumi yai yarayya dashi a lokacin da yake gudanar da ita wato azuminsa

»KALLON FILMS NA BATSA» kalu balene ga mai azumi yarinka kallon film na Batsa a lokacin da yaKe Gudanar da ibadarsa a haramunne Da fatan za’ai aiki dashi ina murna da zuwan wannan watan mai albarka.

Yaa Allah kasa muna cikin wadanda Allah ubangiji sai Enta a cikin wannan watan na azumin mai Albarka.

Allah ka amsa addu’o’in mu

Allah kasa muna cikin yan tattun bayinka.

Amin 

Leave a Reply

Back to top button