TASKAR TARIHIN HAUSAWA DA AL'ADUNSU

{ASALI HAUSA DA GINUWAR DAIDAITACIYAR HAUSA DA KA’IDOJINTA}.KASHI NA FARKO BY MZS.

Sponsored Links

ASALI DA GINUWAR DAIDAITACIYAR HAUSA DA KA’IDOJINTA
Daga Malumfashi Ibrahim 
Tarihin rubutu da karatu irin na boko a kasar Hausa da muka sani ya biyo matakai-matakai a tsawon tarihi, wanda daga nan ne aka samar da 
ka’idojin rubutun da kuma samar da Daidaitacciyar Hausa.
 Tun daga farko dai abin da ya dace mu fahimta shi ne tun kafin zuwan Turawa an rubuce Hausa cikin wasu haruffan da ba na Turawa ba; 
akwai dai masu hasashen an rubuce Hausa cikin Girkanci, daga baya kuma aka sake rubuce ta cikin Larabci da Ajami. Da yake ba wani rubutun Hausa da muka gani a kasa na Girkanci har zuwa yau, za mu iya cewa an fara daidaita rubutun Hausa ne da Ajami, wato da haruffan Larabci. Wannan dadaddiyar hanya ita ce Turawan Mishau suka iske, suka gyara, suka bi domin kokarin daidaita rubutun Hausa a cikin Romanci ko Latinanci a cikin littattafansu da suka samar.
 
 Ke nan za mu iya cewa an soma yin rubutun Hausa ne da kuma daidaita shi a cikin Ajami, zuwan Boko ya kara masa muhibba da martaba a tsakanin 
masana, saboda haka muna iya cewa daga abin da Ajami ya tanadar ne aka samar da tsarin rubutun Bokon Hausa. 
 Ka’idojin farko na rubutun Boko da aka samu a rubuce su ne wadanda R. H.
 Robinson ya gabatar a 
1848 karkashin kungiyar CMS, inda bayan samar da bakaken Hausa da wasullansu an fito da batun haruffan nan da ke da lankwasa, wato d da k da b wadanda aka dinga yi masu digo a karkashi domin a bambanta da wadanda ba su da lankwasa. 
 Bayan Robinson sai kuma Raberan Schon wanda 
ya rayu tsakanin 1803-1889, ya yi rubuce-rubuce
da dama da suka hada da: 
Vocabulary of the Hausa Language (1843) Dictionary of the Hausa Language (1876) 
Grammar of the Hausa Language (1862) 
Magana Hausa (1885) 
Duk da cewa Schon bai ziyarci kasar Hausa kai tsaye ba, amma ta hulda da wadanda suka ziyarta da kuma ‘yan kasa da ya hadu da su a cikin rayuwarsa ya sa ya shiga cikin aikin raya da rubuta Hausa domin na baya. Shi ma ya tabbatar da kusan dukkan bakake da wasullan Hausa da Robinson ya samar, wadanda kuma har yau ana amfani da su, sai dai babbar matsalar da yafuskanta ita ce ta haruffa masu lankwasa da ya bari kamar yadda Robinson ya samar da su, don ya rasa yadda zai yi 
da su.
  Haka kuma ya ci karo da matsalar hamza,
wato haruffa irin su: 
/Tsami/, wanda ya rubuta kamar haka, /Sami/ 
/’Ya’ya/ da ya rubuta kamar haka /Yaya/ 
/Waje/ ya rubuta kamar haka, /Waze/ Wani da ya yi wa rubutun Hausa 
bauta shi ma shi 
ne Charles H. Robinson (1861-1925), shi ma 
manazarcin harshe ne kuma dan Mishau, ya iya 
Larabci sosai, ya kuma nakalci Ajami gwargwado. 
Ya yi rubuce-rubuce da dama da suka hada da: 
Specimen of Hausa Literature (1896) Hausa Grammar (1897) 
Dictionary of the Hausa Language (1899) 
Tun farkon nazarinsa ya san da haruffa masu lankwasa, saboda hakaya bar su da digo a karkashin haruffan d da b da k.
 Sai dai shi ma ya samu matsala wajen raba da kuma hada kalmomi ta yadda da yawa suka ba shi ruwa.
 Alal misali yana rubuta wasu jimloli kamar haka: 
/Akakama/ a maimakon /Aka kama/ 
/Anayaki/ a maimakon /Ana yaki/ 
Wani dan Mishau da ya taka rawar gani wajen rubuta da daidaita Hausa shi ne Hans Vischer Dan Hausa (1876-1945). 
Da farko aikin Mishau ya fara, 
daga baya kuma ya shiga aikin mulkin mallaka, inda ya zauna a kasar Hausa, ya nakalci Hausar da al’adun Hausawa har aka dinga kiran sa Dan Hausa 
saboda sajewar da ya yi. 
 Shi ne ya samar da makarantar Boko ta gwamnati ta farko a kasar Hausa, ya kuma kasance jami’i mai kula da sha’anin Ilimi a kasar Hausa. Shi ne ya fito da ka’idonjin rubutun Hausa na farko a shekarar 1912, wato 
Rules for Hausa Spelling, inda ya tabbatar da bakake da wasullan Hausa da muke gain yanzu, ya 
kuma nemi ya gyara matsalar haruffa masu lankwasa, inda a maimakon 
yadda ake rubuta su a da a karkashin haruffan d da b da k sai ya maido a 
sama da alamar hamza, domin a gan su a fili a kuma fade cikin sauri wajen karatu. Ga yadda ya tsara su da sauran wasu daga cikin dokokin da ya samar.
/’b/ /’d/ /’k/ /Mache/ a maimakon /Mace/ 
/’Ya/ a madadin /Y/ 
/Rigas Sarki/ a maimakon /Rigas Sarki/ 
/Sayam Masa/ a madadin /Sayar Masa/ 
/Farri/ a matsayin /Fari/ 
/Fatta/ a madadin /Fata/ /Sayesaye/ a madadin /Saye-saye/ 
Wanda ya biyo layi shi ne Raberan G.P Bargery 
(1876-1960), shi ma kamar sauran da ya biyo 
bayansu ya bauta wa Mishau, a cikin haka ya 
inganta rubutun Hausa da ka’idojinsa. Babbar gudunmuwar da ya bayar ita ce ta samar da kamus na Hausa-English 
Dictionary and English–Hausa 
Vocabulary. 
 A cikin wannangagarumin aiki da ya yi a shekarar 1934, ya ci gaba ne daga inda Hans Vischer ya tsaya, ta amincewa da haruffa masu 
lankwasa, sai dai shi ma ya rubuta su a saman haruffa da hamza, kamar yadda Vischer ya yi. 
 Sai dai ya sake canza wasu haruffa masu aure ko tagwaye, irin su /Ch/ ta koma /C/, wato ya rubuta / Caca/ a maimakon /Chacha/, ya soke amfani da nannagen haruffa a cikin kalmomi wato irin su /sh/ ko /ts/ a tsakanin kalma ya mayar da su zuwa /s/ 
ko /t/ alal misali, /shashshaka/ ake rubutawa a da, shi kuma ya rubuta 
kamar haka, /shasshaka/ ko 
kuma /tsatstsafa/ ya mayar da ita kamar haka, /
tsattsafa/. 
 Haka kuma shi ne ya fara bayani a fili
bambanci tsakanin ka’idojin rubutun Hausa na Karin Harshe da Daidaitacciyar Hausa, inda yake bambanta su a cikin aikinsa, misali: /Sayar da shi/, a maimakon /Sayad 
da shi/ wanda Katsinanci ne. 
/Rigar Sarki/, a maimakon /Rigas Sarki/ wanda 
Katsinanci ne. 
Bargery ne kuma ya fara tabbatar da samuwar karin sauti a cikin rubutun Hausa, yana sanya alamar – a karkashin kowane harafi mai dauke da 
karin sauti na kasa, na sama saboda yawan fitar sa ‘a cikin harshen bai ba shi wata alama ba. Haka 
yana nuna yadda ake rubuta dogo da gajeren wasali. 
Daga Bargery sai dalibinsa R. C. Abraham (1890-1963), ma’aikacin 
gwamnatin mulkin mallaka ne wanda ya taba zama ADO a Kano. 
Yabauta wa Hausa gwargwadon iyawarsa, inda ya rubuta littattafai da suka hada da Principles of 
Hausa a 1934 da A Modern Grammar of Spoken Hausa a 1941 da Dictionary of the Hausa Language a 1949 da kuma The Language of Hausa People a 1959. Kodayake aikin Abraham ya kasance na zamani, duk da haka daga abin da Bargery da 
Gwamnatin Arewa ta shirya ne ya gina nasa.
 Sai dai ya kasance mai kawo nasa canjin shi ma domin shi ne ya fara rubuta haruffan Hausa masu lankwasa kamar yadda suke a 
halin yanzu, wato a shekarar 
1938. 
 Haka kuma ya bambanta tsakanin haruffan / n/ biyu, wato ra-gare da ra-kade, misali a hanci da tankade. Ya kuma nuna inda karin sauti ke fita da 
tsawon wasali, inda yake sa wannan alamar – a saman dogon wasali da kuma – a kasan harafi mai karin sauti na kasa, kamar yadda Bargery yayi.
     Daga naku.         
                   musa s zage.     
Daga
 Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.
     Sai muhadu a kashi na biyu

Leave a Reply

Back to top button