ASAN MUTUM AKAN SANA’AR SA ]AIKIN YUNBU A KASAR HAUSA .
AIKIN YUNBU
Ma su aikin yunbu su ne wanda a kafi sani da Magina Tikwane, Randuna, Tule, zuwa su Kwatanniya, da sauran abubuwa da su ka shafi
yanayin aikinsu.
Ma su wannan sana’a da farko su kan samo kasar Yunbu ko kuma jar kasa mai danko, ya danganta da irin kasar da za su yi amfani da ita.
Yayin da su ka sami kasar, su kan kwaßa su fidda lauyin abinda su ke so su yi Kaskone, Tanderune, ya danganta, da zaran su fidda surar abinda a ka gina sai a barsu su sha iska, sannan a zzuba su a wuta aita gasa su kamar ana nama har sai sun gasu sun hade jikin su, inda gashin yayi kyau, kuma an hadu da gwani, har wani kyalli suke kamar an shafa ma su man shanu.
Daga
Tsangayar da ta himmatu wajen
kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa
Daga naku
Isah musa mukutar