Auren Wucin Gadi 38
CHAPTER 38
Saurin riƙo hannun ta yayi be bari tafita da gudu kaman yanda ta bukata ba.
Ta faɗo jikin sa yayi saurin ya rungumeta kaman dama jiran haka yake kiciniyar ƙwantar kanta tasoma cike da taƙaicin taɓa mata jiki da yake da zallah masifa tace”dallah malam cikani.
Ta faɗi haka ciki da tsoro a muryarta”idan naƙi sakin naki fa mezaki iyayi?
Yayi maganar cikin ƙaramin murya kaman na mai raɗa a cikin kunnen ta,ƙirjinta ne yasoma wani irin bugawa da karfi jin sauti yake cikin jiki da ɓargon sa wanda haka shima ya haimar ma nashi zuciyan sauya bugun ta.
Wani karfine yazo mata bazata ta ture shi tama mai share fuskarta da hannuta na dama tabude baki da ƙyar tace dashi”Allah ya isa taɓamun jiki da kayi kwarto kawai,tana kare faɗin haka ta kwasa da gudu tayi waje.
Komawa yayi yazube saman wani kushun da aka tanada saboda hutawa yana mai jin haushin kansa.
Basma
Kasa tuƙi tayi sai raihana data miƙawa key din motan kuka take riris kaman karamar yarinya tasan iyayenta nada wani shiri akan aurenta da ahmad kuma sunkashe maƙudan ƙuɗade dan ganin burin su yacika,amma da alama ze kawo musu cikas dan yanda yake tsaye tsayin daka da alama duk aiki da akai masa be kamashi ba.
Idan ko hakane akwai aiki ja a gabanta ko tace a gabansu da iyayen nata dan ita Allah yana gani tanason Ahmad bilhakki da gaskiya zata iya koma menene dan ta samu ta mallaki zuciyar sa.
Amma ta ya?
Sannan wace alaƙace tsakanin sa da wannan ƙaskan tacciyar ƴar aikin?
“Ina da bukatar sanin wace alaƙace tsakanin ta da Ahmad?
“Bakida matsala cewar Salaha gobema zan saka a bincika mana amma kinsa aikin ɗan kunama sai yaji dumus a hannun sa.
Harara ta maka mata tana mai cewa”matsalata daku kenan bakusan zaman tare ba komai sai kuɗi mtssss takare maganan tana tsuka.
*****
Ya alhaj gafa sabuwar yarinya da nake faɗa maka nan zatayi aiki damu dan tana da ƙwazo sosai takuma iya takunta,dan dama tajima tana aikin saida syrup da tabar wiwi tana kuma da ɗaure gindin wasu daga cikin jami’ai musamman ta NDLE.
Duka wannan magana da mutumin yake idon ya Alhaj nakanta saide duk ƙwafƙwafin sa nason ganin ainihin fuskarta abun ya faskara saide shigar da tayi na baƙaƙen kaya sun matukar burge shi.
“Kina da sa’a ƴan mata a rayuwarki da kika haɗu dani kai tsaye.
Hmmm tace tana sakar masa da murmushi mai sauti ta amsa masa da cewa”dama can niɗin da sa’ata nake tafe saide zan iya cewa kaine kayi sa’an samuna matsayin wacce zatayi aiki daku.
Takuwa burgeshi dan kanta tsaye take maganarta ba tare da nuna tsoro ko shakkan sa dan ganin yanda yake zagaye da guggan ƴan daba ba.
“Wannan gwarin gwiwa taki da yanda kike maganarki kanki tsaye ya burgeni”hmmm haka nake dama ta bashi amsa tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun ta lokacin tafiya ta yayi ko zan iya tafiya.
“Baki da matsala ya amsa yana ƴar dariya da cewa yaushe zamu haɗu naga kaman kina sauri dan inada sharaɗuna kafin ki soma aiki damu.
“Zanso hakan dan nima inada nawa sharuɗun kafin na karɓi aiki dan nasaba cin gashin kaina ban saba zama karkashin ƙwarin bariki ba shi sa.
Dala dubu goma yamika mata yace”kyayi kuɗin mota kafin musake haduwa dake kafin sannan inason sanin sunanki da kuma address dinki?
Dan shiru tayi sai kuma ta sakar masa da
murmushi mai sauti kana tace”sunana NATASHA address kuma duk sanda ka bukaci ganina zan bayyana a wajen dan bana da address taƙa maimai ɗaya tana kare faɗin haka ta amshi kuɗin daga hannun sa ta daga masa ƴan yatsun hannun ta uku alamun bye.
Da ido ya Alhaj yayima wani dake kusa dashi alama da yabi bayanta.
Saide kash ta katse masa hanzari wajen cewa dashi”Alhaji ba sai ka wahal da kanka wajen sawa a bibiyeni ba idan kana da shakku a kaina kabar aikin kawai dama ni ba wani damuwa nayi da sainayi aiki karkashin wani ba.
“noo noo noo hajjaju Natasha bazamuyi haka dake ba yafaɗa cikin rawar jiki da ido yama yaran nasa alama da suja da baya.
A ransa kuwa mamakinta ne fal ransa ya akai ta gane yasa a bibiyeta idan kin sa wata baki san wata ba ya faɗi haka a ransa yana sakin murmushin mugunta.
Ɓangaren Natasha bayan barinta wajen cikin sauri ta faɗa motar da yazo ɗaukanta saida ta daidaita zamanta motan tabar harabar wajen ta cilla hancinta kwalta sannan ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya tana cire face mark ɗin fuskarta ta gurgar gefe tace”wai dakyar nasha gaskiya ya faisal bazan iya tunkarar waƴan mutanen kaitse haka ba.
Dariya faisal yayi harda buga sitarin motar yace”haba hajiya natasha kenan bazaki iya tsayuwa tsayin daka kijajirce dan ganin kin cika burin uncle ishak ba?
Idontane ya ciko da kwallah tunawa da wannan shine azzalumin da yasaka rayuwarsu shiga garari ya maishe su marayu karfi da yaji.
Yaya faisal nashirya koda zan rasa rayuwanane zanyi komai dan ganin wannan azzulumin da kuma ire iren su sun kau a doron duniya.
Fatan anyi sallah lafiya Allah ya amshi ibadun mu yasamu muna daga cikin salihan bayin sa Allah maimaita mana na baɗi Allah yasa muna daga cikin salihan bayin sa Amin