Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 42

Sponsored Links

CHAPTER 42

Harya kai hannun da nufin damƙota sai kuma yayi saurin dunƙule hannun nasa saboda wani abu dayaji ya tsargar masa tsigar jikin sa.

“Lafiya?
Suka jiyo muryar Anty hajjia a bayan su wannan ya bawa Aisha daman kwasa da gudu bako tare da tabi takan tambayarta da Anty hajia keyi ba tayi waje.

Ikon Allah kaji wani shashanci kuma komai yake damun yarinyar nan oho ta faɗa tare da ƙoƙarin juyawa tasake jinjina wa a ranta komai ya tsoratata harhaka,idanta ne yasauka kan mutum dake tsaye kaman an dasashi tace kai kuma yaushe kazo nan kode kaine dama ka firgitamun ƴa?

Ɗaga mata kafaɗansa yayi yana cewa”ni kuma anty hajiya yo mai haɗina da ita.

Wacece ita?

Naga kyawawan yara da zam shigo tare da Abdul malik gaskiya sun burgeni sosai?

“Na tambayeka madadin kabani amsa sai ka bige da sake tambayata.

To itade wannan da kagani yanzu sunan ta Aisha waƴan can yara da kagani kannentane suɗin,ai yaran sun samu tarbiya sosai wallahi uwarsu mutuniyar kikece data kawaici idan kaji ance jajirtacciya to wannan ta amsa wannan sunan.

Ai Aisha da kake gani yarinyarce tsayayya abun duniya be taɓa tsone mata ido ba fatan da burinta kullum ta nemi nakanta da gumin ta aima tajima tana aiki ƙarkashin ma’aikatanja fannin ɗinki,wallahi ba yanda banyi da ita ta koma makaranta ba bayan dawowarta nan da zama amma cemun kawai tayi ita burinta be wuce ƙannenta suyi karatu ba.

Shiru kawai yayi yana sauraron ta sai data dire sannan yace”wai anty ina su ummu salma da malika ne?

A baɗini basu yayi niyar tambaya ba kawai de yatsinci bakinsa da furtawane duk kokawa dayake da zuciyarsa.

“Ai tuntuni suka fita,Faisal kuma tun safe be shigo nan ba yana can yana fama da aiki ya tasa computer gaba.

Nan ta hau bashi labarin yanda aka tarɓrsu jiya a gidan surukan nasa dasuka kai lefe,shide sai binta yake da e’e kawai a fakance yake wulwulga ido yaga ta inda zata ɓullo dan yanason sake sakata a ido haka kawai yaji yana mararin sake ganin ta.

“Anty ni zan wuce”to to to dawuri haka idan can company zaka ɗan ragewa ɗiyata hanya yau bata shirya ba malik yayi tafiyar sa ya barta.

Yatsune fuska yayi yana duba agogo daya ɗaura nai shegen tsada da kyau da kallo sai kuma ya miƙe tsaye batare da yace da ita komai ba,yana cewa”wai Anty wace yarinyace da Ammi ke magana a kanta da zan fito a gida.

“Aisha ce ko batayi maka ba,tako bashi amsa kanta tsaye dan koda wasa batayi tsammanin Aishan ta fito ba.

“What ya furta da karfi yana mai kafe Aisha da itama ƙirjinta yabada sautin dum to mai tayi kuma karde zargi datake musu yazama gaskiya kuma wace irin alaƙa ce tsakanin su ƴan gida da oga Ahmad.

Duk wannan magana a zuciyarta take yinsa yayinda jikinta ya ɗauki rawa karrr karrr karrr.

Maganan sane ya daki dodon kunneta da yake cewa”haba Anty gaskiya batamun ba kalleni fa kalli wannan yarinya da ba komai a cikinta sa tsiwa da rashin kunya kumama nide nake da buƙatar mace wacce ta amsa suna mace ƴar jami’a mai aji ina zankai wannan jaririyar yarinyan rainonta zanyi,ina ina gaskiya ku canja tunani banda wannan idan kuwa kun matsa saide na zauna da ita na WUCIN GADI wato de ina nufin AUREN WUCIN GADI,dan zata taimakamun kota fanin aikace aikacen gidana ne.

Can na hango Alhaji sunusi cikin gawani rumfa da alama wajene da aka keɓe dan shan iska wasu ƙatti ne majiya karfi dake tsastsaye zagaye dashi suna gadin sa,gefe ɗaya kuwa harkar business ɗinsa yake yana kallon komai dake gudana cikin systerm dinda ke gaban sa,kasan yanzu duniya ta cigaba kana zaune a wani kauyenku dako sunan sa zeyi wuyan fadi bakin wasu amma saikayi kasuwanci da wanda yake birnin sin ko dubai da England kuma kuna kallon junan ku kaitsai.

Yana cikin wannan sai wayan sa dake ajiye kusa dashi taɗau burari neman agaji daga maishi ganin mai kiran nasa nasa sashi cewa da wanda yake magana dashin”zan nemaka zuwa anjima”ok sir aka amsa masa daga can ɓangaren rufe systerm din yayi sannan ya ɗauki wayan da harta katsa yana shirin bin kiran aka sake kiran sa.

Saurin ɗauka yayi yana kara wayan kunne”hello aka faɗa a ɗaya ɓangaren kafin Alhaji sunusi ya amsa yaji ansake cewa”oga ansamu matsala fa

Miƙewa tsaye Alhaji sunusi yayi daga zaunen da yake dan shi a rayuwarsa ya tsani yaji an kira masa matsala”what Mashi mai kake cewa kode kunnuwa nane basuji da kyau ba.

Yafaɗa yana sauke wayan a kunnen sa da ɗansaka yatsa cikin kunnun yana kaɗawa,dasake maida wayan kunnen sa fatansa de be wuce yaji Mashi yace ba abunda yaji da farko bane.

“Eh oga dan wallahi wani sabon jami’ine yakame mana dukkan nin kayan da mukai order jirgin yana dawowa gaɓan teku kawai sai ganin mutane mukai daga sama da alama kuma mu suke jira kode nace sunsan komai gami damu…..wani irin ashar ya lailayo yaɓa wanda yasaka Mashi dole dakatawa daga yi masa bayani da yake.

Cikin kumfar baki yace”to mai amfaninku bazaku bude musu wuta bane?

“Haba oga ya kake cewa haka wani wuta zamu bude bayan mudin ma nace maka daga sama suka faɗo mana ba tare da munsan da su ba,kuma wayasan yawansu.

“Waye wannan mai son wasa da rayuwarsa ya shiga gonata?

Eh Mashi wannan karon a zafafe yayi maganan kuma da karfu tsaɓanin ɗazun har saida Mashi ya sauke wayan a kunnensa.

“Wanine wai sunan term din nasa operation sari ka nuke kuma su kansu su CP wannan yankin yace besan da wannan tsarin ba,dan da alama umurni suka samu daga sama amma yace ze bincika idan ya gane wanda ya jagoranci wannan aikin ze tuntuɓe mu,oga rayuwar mu tana cikin hatsari zamubar wannan yanki daren yau idan munsami mafaka zan kiraka.

Faɗin halin da Alh sunusi ya tsinci kansa wannan lokacin ɓata bakine,dan karshe cire hulan sa yayi ya shiga firfita da shi saboda tsaban rikicewa,kai karshema cire babban rigar yayi yashiga zarya cikin ɗan rumfarda yake tare da tunanin wani ɗan kasadan ne yashiga rayuwar sa lokaci gudan dan son tarwatsa shi.

WAYE WAYE WAYE?
yakare faɗi da karfi yana watsi da kayan teburin dake gaban sa.

“Easy sir ɗaya daga cikin guard ɗinsa yafaɗa.

“Nabi easy da gudu ba wando nace nabi easy da gudu ba wando ko baka jini bane”sorry oga ya faɗa kansa duƙe a ƙasa.

Kirane ya shiga wayan sa,saurin duba wayan yayi fatan sa CP mambila ne sai tsaɓani hakan ya gani Alh hamza ne ke kan layi ƙoƙarin daidaita nitsuwar sa yayi yan ɗaga kiran tare da salama.

“Riƙe sallaman ka Alh duba wayanka ina ganin bakasan abunda ke faruwa ba ko,to duba wayanka kagani kitt ya katse wayan ba tare da yabashi daman tambayan sa ba.

Hannu na rawa ya kunna datan wayan sa,abunda yagani saida yasa numfashin sa daukewa na wucin gadi,wati duk wani order da sukai ankame kuma ganan wani shegen jami’i yabawa ɗaga manyan kifi dake cikin kwando ko ince kwanduna yana bude cikin kififayen tare da ciro hodar iblisi wato koken yana ajiyewa ƴan jarida sunyi caa akansa da tambayayo.

Wanine yamai tambaya kaman haka”shin waƴan dake safaran miyagun ƙwayoyin da sanin hukuma?

“Kwarai kuwa dan bakin su ɗaya da wasu guɓatattatu cikin mu sune masu daure musu karƙashi suke tsula tsiyarsu lokaci yayi da zamu karya ƙasusuwar su sai mun sakakasu guduwa wanda yake da niyar gyara ya gyara dan akwai cuta acikin garin nan dama ƙasar tamu baki ɗaya dayake bukatar magani.

Daɓas Alh sunusi yakai zaune wani irin zufa na karyo masa.

*******
“Anty hajia me naji wannan yana cewa..au…au…auren wucin gadi dani kuma wayyo Allah wayyo Anna mairaici beyi ba a rayuwa,mai yasa Anna kika tafi kika barmu a lokacin da mukafi bukatarki.

Wannan duk yana daga cikin rashin gata da rashin galihu da bamu dashi,na shiga uku dan Allah Anna kidawo ki daukemu daga nan gashi ana shirin ha intar miki ni.

Tana fadin haka tariƙo hannun Anty hajia tashiga raira kuka cikin kukan take cewa dan Allah anty hajia ki ceci rayuwata karki bari son zuciya ya kaiki ga cutar da rayuwa na ki tuna nifa marainiyace ba abunda nasani na daɗin rayuwa face rayuwar talauci da gwagwarmayar rayuwa indan saboda muna zaune gidanki ne zaki yanke irin wannan hukunci kiyi wallahi yanzun nan zambar miki gidan ki da ƴan uwana dan tsiratar da rayuwata dama Anna ce tace nazo nan gidan da zama bayin kaina bane amma bazan tsaya inaji ina gani a mun auren dole ba,kisani kema fa uwace kin haifa idan ƴarki akawa haka ya zakiji aranki?

“Ki nutsu Aisha
Anty hajia ta fada tana kokarin sata a jiki ta rungumeta,da sauri ta janye jikinta daga gareta tace”ina ni ina sauran nutsuwa vayan inaji kaman rayuwata tazo karshe wani har yana ikirari auren wucin gadi dani kai ina.

Faisal daya doso main falon gidan dan samawa kansa abunda zai saka acikin sa yafita aiki yasoma jin hayaniya natashi da sautin kuka.

Dan haka da ɗan sassarfan sa ya karasa shiga ciki ja yayi ya tsaya ganin Ahmad dake shirin fita Aisha ta ciƙwaikuye masa riga ta baya tana kuka harda jan majina tana cewa wallahi ba inda zashi saiya saketa idan ma anɗaura idan ko ba daura ba dole sai yafaɗa da bakin sa bayayi su anty hajia su janye banzan magarnar tasa na auren wucin gadi.

“AUREN WUCIN GADI
Faisal ya maimaita kkalman ƙasan maƙoshi.

Leave a Reply

Back to top button