Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 8

Sponsored Links

Chapter 8

Wannan littafi na kuɗine ga masu bukata su tuntuɓeni ta wannan Number kai tsaye 07038486776

Wucemu yayi batare da ya kalli kowa cikin mu ba,sauke nannausan ajiyar zuciya nayi har yarintar da muke tare sai data tuntsure da dariya tana cewa”amma wallahi muguwar matsoraciyace ke murmushi nayi nace”kede bari ai tsoroma rahamace”tab bade irin taki dakike kasa ɓoyeta ba kinga duk sanda mutane suka fahinci tsoranki afili tofa kinzama abun wasan su dan haka lalle lalle ki koyawa kanki jarumta koda kinji tsoro ya shigeki to kiyi ƙoƙarin ɓoye tsoronki daga karshe sunana laila kefa?”nikuma Aisha naji daɗin haduwata dake kuma insha Allah daga yanzuma zan koyawa kaina jarumta dariya mukai sannan muka tsaida abun hawa kan sai gobe.

Ina cikin napep Allah Allah nake nakai gida na ɗan huta araina kuma ina ta addu’an Allah yasade yau muna da ɗan abunda zamuci a gida dan yunwa nakeji kaman ƴaƴan hanjina zasu zagwanye.

Alhaji sunusi dake zaune cikin wani katsaitaccan falo tare da wasu manyan Alhazawa ya kalle su ɗaya bayan ɗaya yatsaida kallon sa kan ɗaya daga cikin su yace”Alhaji mahdi kasan wannan tafiya dole ayita tunda yanzu anfito da wata fasahar kaman yanda kuke gani yanzu a cikin allon majigin nan nan duka suka maida hankalinsu kan allon daya hasko musu.

Kunde gani a zahiri magunguna ne masu lasisi amma a baɗininta kuma hudar ibilisce kowane capsule kana buɗewa kayane a ciki kuma zamu rinƙa turawa dukkan nin inda mukeso acikin africa dama kasashen ƙatare amma kafin nan kasan muna bukatar bullet?

Dukkan su kallon rashin fahinta suka masa sai Alhaji lawali ne yayi karfin halin tambayan sa”oga wani irin bullet kuma mukeda bukata?

Dariya yayi irin ta bosawa sannan ya gimtse fuska yace”makami wannan tafiya dole sai da mata yara ƴan shilla zamu ɗauke su aiki suna mana tallan magunguna mukuma ta ƙasan ƙasa zamuna wannan bussiness ɗin idan anyi order sai mu basu sukai tasha subawa driver sukai kai kuma Alhaji badamasi sai ka ƙara bincike dakuma baza basiran ka dan ganin ka inganta magungunan wajenka tare da sarrafa su yanda yadace.

Sannan mukuma namu zakana durawa a mazubin capsule sai ayi pakin ɗinsu cikin ƙwalba mai tsabta amma kuma dole sai ansamo ma aikata masu amana dakuma sirrin.

“Wannan ba damuwa bace ba cewar Alhaji badamasi mahaifi ga Ahmad sannan shiɗin masanine ta hanyan kiwon lafiya Allah yabashi ilimin sarrafa magungunan gargajiya tun tuni yanzu kuma da komai yakoma zamanance suna sarrafa magungunasu tare da gwaje gwaje wajen inganta magungunan wajen nasa yayi fice sosai saboda ingancin magungunan sa shine yanzu waƴan nan manyan suke son suyi amfani dashi wajen cimma nasu manufan.

Basma ta kalli mummynta dake riƙe da waya a hannu yanzu suka gama magana da kawarta hajia balkisu take sanar mata yanda sukai da Aishan jiya.

“Mummy nifa na rasa gane me yarinyar nan take takama dashi wai me tatakane da har zakice kinaso tazo tamiki aiki zataƙi itada naji hajia balkisu nacewa saboda talauci watarana sai suyi kwana biyu batare da sun hura wuta a gidan nasu ba.

Eh haka nan nima naji hajia balkisu nacewa saide kawai abunda nake tunani suɗin ba irin sauran talakawan nan bane masu yawon maula ba dan ni kaina sama da shekara goma kenan da sanin mahaifiyar Aishan tunma aisha na ƙarama amma tun can ita ɗin mai neman na kantane bata yarda wani yabata ba,cewar hajia mariya.

Amma kibarni da su nasan yanda zanje gidan na kalallamesu da baki”mummy basma takirata tana zaro ido”gyaɗa mata kai tayi tace ai tsugunnawa wada ba gajiyawa bace asiyasance zan jawota zuwa masarautarmu sannan nayi wasan kurah da rayuwarta ita ɗin banza itaɗin wofi mai akai Nafi balle wata Aisha can takare maganan suna sakin shewa tare da tafawa kaman wasu ƙawaye.

A gajiye na sauka a napep ɗin bakin layin mu na ratayo jakata ina tafiya cikin nutsuwata da ta gama zamemun jiki wasu na ganin kaman yanga nake amma ni nasan ba yanga bace ba haka Allah yayini.

Ina ɗiyar talaka mara galihu ina ni ina wata yanga kullum muna fafutukar neman abunda zamu ci,tunda na doso lungunmu naji gabana na tsananta buguwa ganin lungun namu cike da mutane yanda nakejin gabana na harbawa har yana ɗagamun riga take wani tsoro ya shigeni Allah yasa ba Anna bace wani abun yasameta.

Shine kawai abunda yake tafiya araina ratsa mutanen da suke tsastsaye nayi zuwa cikin gida ganin kowa kallona yake dana wuce ba mai iya yimun magana zuciya tagama saddakar mun cewa la shakka Anna ce.

Sai de me ina dosan cikin gida kalma da natsinkayo ya nasani faɗawa a matukar fusace Anna nagani duƙe tana sharan hawaye raina idan yayi dubu to duka ya ɓaci bansan sanda nayi kan mai maganan ba.

“Ilu nakira sunan sa kai tsaye cikin ƙaraji”ilu kuma?ya maimaita dan bantaɓa kiran sa da sunan kai tsaye ba sai yau kuma anzo limit dinda bazan iya hakura ba,dan mutum duk girman sa idan yace ze taɓamun Anna ta to wallahi sai inda karfina yakare.

Koba sunan kaba ne hakan?na tambayeshi kai tsaye na ɗaura da cewa karuwanci yawon dandi dakake ta hargowa kana ɗaga murya da tara ƴan kallo kana wani faɗin hakan ai shima iyawane idan wani ya isa yayi idan besha ɗankaren duka ba.

Ko cema akai haurawa katanga gidan matan aurene,yayi matukar harzuƙa kaman ze kaimun duka haka ya hayayyaƙomun yafara zagezagen borin kunya.

Dan halin sa kenan kowa a nan anguwar yasani ganin zagin nasa bana karewa bane nace”to dan Allah idan kagama kafita mana daga gida dan wallahi ko maza sun kare ba abinda Anna zatayi da ƙazami irin ka idan tallata kanka kazo to albarka bazamu taya ba shashasha wanda besan mutuncin kansa ba.

Haka ake zuwa gidan mutane kai tsaye dan kawai muna haya a gidan ka,nagade kowa anan anguwar yasani idan ba munafinci ba aiko waƴanda suke kiran kansu maza wallahi sai mun biya kuɗi suke bada nasu daga baya kawai dan an shirya cimana mutunci shine shine….”ya isa Aisha cewa Anna tana dakatar dani tuni ƴan kallon suka suka watse dan ɗaga murya nake ina magana kowama yaji kai kuma nafada ina nuna malam ilu da ɗan yatsa nace kasaurari kira daga mai anguwa saboda karya doka dakayi kashiga mana gida sannan katasa mata da ƴaƴanta da maganan banza…..salati kawai malam ilu yasa tun karfinsa.

 

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button