Bakar Ayah 1
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
*Assalamu alaikum*
Godiya ga Allah maɗaukakin sarki daya kawomu wannan rana na fara sabon littafi.
Dama an ce rana bata ƙaryah saidai uwar ɗiya taji kunyah. Barkanmu da wannan rana mai albarka,dafatan An wayi gari cikin ƙoshin lafiya.
*GARGAƊI*
Ban yadda wani ko wata ya kwafamin littafi ba ta kowacce siga,sannan akwai halayya da ɗabi’u a cikin wannan littafin wanda basu dace ba,dafatan za’a ɗaukesu a matsayin darasi mai isarda saƙo.
Sannan abu na ƙarshe ayimin afuwa idan wani yaci karo da abinda yayi daidai dashi,banyi niyyar yin hakan ba sam.
Nagode sosai ayi karatu lafiya……
Page 🖤01🖤
……….”zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi”
Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici.
“Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!”
Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane.
“”Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24”
“Toh ranki ya daɗe”
Ta faɗa tareda zubawa dagudu. Bayan barinta wajen sake maida hankalinta tayi kan hafsa,wadda take ta nishi amma babu alama haihuwar tana kusa,gashi kuma jininta ya hau sosai babu dama suyi mata cs.
Girgiza kanta tayi cikeda tausayawa,dan duk wanda yakalleta a wannan halin yasan ba ƙaramar wahala take sha ba sosai.
“Sannu kinji,bari yazo ya duba koda akwai matsala,dan ni gaskiya bamu taba ganin irin wannan ba tunda muke anan asibitin,komai ƙalau amma kan yaron yaƙi motsi tunda yafara fitowa?”
“Nurse to ki sake yimin allurar naƙudar mana,inaga yanxun a dace wataƙil”
“Ahah kiyi hakuri,a iya daga jiya da daddare zuwa yanzu mun yi miki allura kusan biyar,bazayyi ki sake ɗaukanta ba yanxu,tana da haɗari sosai.
Baridai doctor yaxo muji mai zaice,inshaaallah zaki haihu lafiyah,kada ki damu,Allah yana tareda ke”
Karfafa mata gwiwa ta cigaba dayi akan lamarin,duk ita kanta ta sare da irin wannan case ɗin.
Waje ta leƙa suka haɗa ido da HAJIYAH ZEENAH,wanda tun ɗazu take zirga zirga a wajen.
“Ya ake ciki nurse,ta haihu ne?”
Jijjiaga sister suwaiba tayi,shekararta ashirin kenan tana karbar haihuwa,amma wannan kam yacaza mata kai matuƙa,.
“Har yanzu dai hajiya lamarin jiya i yau,ni har na fara tsorita ma da abin,gashi tana naƙuda amma kuma babu haihuwa babu alamunta”
“Kai innalillah,ni banma san mai zanyi ba,ga IYAH SAYYADA ma,saida akayi da gaske kafin ta hakura da zuwa asibitinnan,nasan tana can ta ɗagawa kowa hankalinsa,sannan gata itama yarinyar tana shan wuyah sosai……to maizai hana ayimata cs,shi mijin baya ƙasar,amma kuma ƙaninsa yana nan ai sai ya saka hannun”
“Shima hakan bazayyi yiyu ba Hajiya,domin jininta yana at risk,a kowanne irin lokaci zai iya zama matsala”
Suna cikin maganar ne likitan ya iso wajen da coat a jikinsa,da alama zuwansa kenan.
“Ya akayi sister suwaiba,naji ance kina nemana a ɗakin haihuwa,wane abune haka daya gagareki?”
“Uhm sir babbar matsalace sosai,yarinyar kwana uku kenan tana naƙuda,gashi tana last stage,amma kuma jinjirin ya gagara fitowa,idan muka saka hannu kuma saiya koma da baya,sannan da alama kaman yaron bashida rai”
“Oh to a shirya shiga operation mana,bazayyi yu a barshi a cikinta har yanzu ba ai”
“Uhm uhm sir jinin yana over tension fah,operation bazayyiyu ba shima”
“So do you like us to watch her die(so kike mu zuba mata ido ta mutu) dolene muyi wani abun,maza muje na ganta yanzunnan.
Naji kince mrs.JABEER .A.JAAN ce koh”
“Eh hakane doctor,yana shirin tahowa yanzunnan”
Juyawa yayi yana duba file ɗin ta suka haɗa ido ta hajiya Zeena,waccce gabaɗaya damuwa a tattara akan fuskarta.
“Barka dai ranki ya daɗe”
“Yawwa barka doctor,ya kamata kuyi wani abun,idan ta kama fita da ita ne ma sai a shirya yanzunnan ta private jet”
Karki damu hajiya,zamu yi iyah koƙarimmu akan matsalar.
Daga haka suka shige site ɗin da Hafsan take kwance.
Wayar tace tayi ƙara,hakan yasa ta koma inda su LAYLAH matar ƙanin mijinta (facalah)suke a zaune.
“Hello ina jinka ABDULMALEEK ya ake ciki?”
“Hmmm ummah ina hanyar zuwa asibitin,kuma tare mukeda Iyah Sayyada,tace wai dole saitazo taga jikinta,na kawota ko muyita wani wajen?”
Jan ajiyar zuciya Hajiya zeenah tayi kafin tace.
“Shikenan babu komai ka kawotan,idan ka kaita wani wajen ma,kasan bazata haƙura ba”
Sauƙe wayar tayi tana kallon Lylah wacce take danne danne a wayah.
“Lylah Iyah Sayyada tana zuwa,yakamata ki ɗora alamar tausayi akan fuskarki,inba so kike kuyi ba”
Tabe baki Lylah tayi tareda cewa.
“Nina gaji da zaman wajennan wlh,kawai akan wata zata haihu a ce saikazo ka zauna,da muka zauna ɗin uwar me muka tsinana a wajennan ne,in matsalar wanine a sakoka,idan taka ce kuwa kai kake magance abinka”
“Toh yanxun wannan habaicin dani kike kokuma da mijinki dayace kizo? Bar ganin ina cikin jimami ki sami dama akaina,kinfi kowa sanin halina banida daɗi,batun zama kuma babu wanda ya riƙeki ki tashi ki bar wajen,daɗin ta ma kema naki ahalin ba ƙalau suke zaune ba,shanyayyen ɗanki ma ya isheki”
“Ehhh naki shanyayyene,amma dai surukata ai bata kashe kishiyoyinta koh,matsala kan ai tana gindinki,surukarki tazame miki alaƙaƙai,kowa shaidane ita ta kashe kishiyarta,wannan ma kar ace komai,dan biri yayi kama da mutum”…………..”
“Lahhhh ha ila ni Sayyada Tatin,yanzu mai zan gani,maizan gani haka,ƴar jikartawa tana ciki rai a hannun Allah,ku kuma kuna nan kuna saida hali…….ke Zeenatu,wato surukarki batada lafiya ma amma bazaki daina ɗiban rashin arziƙi ba koh……”
“Amma iyah Sayyada itah fah ta fara,kuma…….”
“Dallah rufemin baki ni,saina kunyi abu nayi magana kununamin ku ƴan zamanin nasara ne,kalleku tula tula daku,ƴaƴanku na ƙasar masu jan kunne suna holewa,nikuma ƴar jikata ƙwaya ɗaya ta ni kaɗai take da,an kasa yimata gatan magani,sai paracetamal ake bunka mata dan rashin imani”
Dukkan su jugum sukayi suna jinta,ta riƙe ƴar ƙafar data ke mata ciwo tana ta zuba kaman ƴaƴan kanya,idonnnan sai fici fici nashi takeyi,kaman na ƙwarƙwata.
“Habba Sayyada kiyi shuru mana,wai bakya ganin yanda kika tara mutane sai kallonki suke ne,ni wlh dana sani dana barki kin cigaba da kukannaki ban kawoki ba”
“ABDULMALEEK ya faɗa yana zuya fuska”
Duka ta kai masa a gadon baya tareda cewa.
“Gyauton uwarka data ke tsayennan Audulolo,a gidan ubanwa nayi kukan,ko sharri zakamin dan ka rainani?”
Daga haka bai sake cewa komai ba ya koma gefe yana kallonsu,ta kama uwarsa ta matar baffansa sai tsefesu take a dandazon mutane.
“Mai me Kakah ma yagani ma a wannan matar ya aura har ta haifi ubanka oho,mtsww ba dama ka fita da ita saita zubarmaka da ajikinka a gaban abokanka”
Gyaran muryah likitin yayi hannunsa duk jini,ga gumi akan fuskarsa.
Sakin baki sayyada-tatin tayi tana kallon jinin dayake hannunsa,
“Kai…..ɗan saurayi,yanzu wannan jinin danake gani a hannunta na hafsatuna neh,mai kayi mata kaji mata ciwo haka?”
Saurin cire safar hannunnasa yayi tareda ɗorata akan tiren da nurse ɗin take binsa dashi
“Ahh iyah ba haka bane,jinin haihuwa ne kawai”
Ɗora idonsa yayi akan Hajiya zeena,tareda yimata Alamar yanason magana da itah.
“Am Iya bari muyi magana da Hajiya yanzu nan”
“Mai zaka faɗamata,faɗaminnan ni kakarta,duk nan wajen nafi kowa ƙaunar ta da son ta rayu”
“To Iyah a halin yanxu gaskiya,bamu sam mai zamuyi ba,dan wani abin mamaki ma,ta daina magana saidai bin mutane da ido,sannan gabobin jikinta munaji suna karyewa kass kass a duk sanda ta ɗan motsa,da alama kuma bata cikin hayyacinta…..”
“Yimin shuru haka baƙin jakada,ya isheka haka,wayyooo hafsatuna shikenan,sun haɗu sun cinyemin ita,saida nace bazan bashi ita ba matarsa mayyace,amma suka ƙeƙasa ƙasa su a dole wai yana sonta,kuma tana da hankali.
Gashi nan sun kaita wannan la’ananniyar matar tasa tacinyemin itah,bazan taba yafemuku ba wayoo ni Tateen ƴar mai Gaskiya”
Share hawayenta take da gefen gyalenta,tana kuka amma bakinta ya gagara yin shuru.
Buge likitan tayi tareda cewa.
“Dallah matsa na wuce naje na ganta,marasa imani kawai”
Turus tayi a bakin gadon,ganin yanda jikinta ya koma kaman babu gabobi,ta kwance take da tulelen ciki kaman gawa,dan yanxu kamma babu damar nishin da tayi ɗaxun.
Faɗuwa Sayyada-tateen tayi tana burburwa a kasan tile ɗin ɗakin,kaman sabuwar ƴar bori.
Sai ƙiran sunan LUBAN take da su hajiya zeena da Lylah tana tsine musu.
Abdulmaleek neh ya shigo ɗakin tareda dafa kafaɗunta,suma su Hajiya zeenah shigowa sukayi suna kallon yanda kamannin hafsan suka sanja daga yanda suke.
Madeenah ce da Maleekah ƴayan hajiya Zeena mata(ƙannen Jabeer babban yayansu,sai kuma Abdulmaleek &Abdulkareem su ƴan biyune,sun gama karatunsu wannan shekarar,ABDULMALEEK engneer ne,Abdulkareem kuma doctor ne na ƙwaƙwalwa,yana housemanship a india.
Sai mai binsu Madeenah,tana 300 level a University of abuja,ita kuma Maleeka a 100 level,suna zuwa su dawo).
“Allah sarki zainabuna ma(Mahaifiyar Hafsa,kuma kanwar baban su ABDULMALEEK),haka ta mutu a haihuwa,aka haifamin ita,sai gashi itama suna so ta tafi ta barni a lokacin haihuwar”
Likitanne yashigo da sauri shida nurse din suka fara shiryata zuwa ɗakin tiyata,
“Kiyi haƙuri hajiya,zamu shiga da ita tiyata,saboda mun gano abin cikinta bai mutu ba har yanzu,saidai amma kiyi haƙuri,dan iya ba lallai takai labari ba,amma duk da haka muna buƙatar addu’arku”
Dagata sukayi tareda ɗorata akan wani sabon gadon kaman gawa,suka nufi ɗakin tiyatar,suna barin wajen Sayyada-tateen ta ƙara gudun kukanta,kaman wata ƙaramar yarinya.
“Shima jabeerun sai naci bantan ubansa,dan tsabar ran yarinyar nan bai dameshi ba,shine ya ɗaga kafa daga dawowarsa shekaran jiya har ya koma yau da sassafe koh hmmmm,bamai zugashi ai sai wannan mayyar kuɗin,a son kuɗi zakiyi komai”
Ta faɗa tana nuna Hajiya zeena,wacce ta ɗauke kanta tana tabe baki,dan inda sabo sun saba ma……..
Kwana uku baya……….
🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03
*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna
______________****_______________