Hausa NovelsYankan Karfe Hausa Novel

Yankan Karfe 5-6

Sponsored Links

*💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫*

 

 

 

 

 

 

~Written By~

 

 

 

 

 

*Hanyluv✍🏻*

 

 

 

 

 

 

 

*Free page*

 

 

 

 

 

 

*Page 5 & 6*

 

 

 

 

Kwance yake a mamakeken gadon shi cikin lumtsumamman bargon shi yana bacci cikin kwanciyar hankali, ɗakin nashi ya haɗu iya haɗuwa, white and nude colour ne komai na ɗakin, firgigitt! ya farka da salati a bakin shi duk AC da ke aikin a ɗaki ta amma shi zufa yake yi, dafe kanshi yayi da hannayenshi ya tunano mummunan mafarkin da yayi, wae yana tsaye a kusa da babban rami me ɗauke da micizai dasu kunamu dadae abubuwan ban tsoro, Mami tazo tana kiran sunanshi tana murmushi, juyowa yayi tare da buɗe mata hannu ta ƙaraso tana mai fara’a tare da tare da rungume shi, can kawae kuma se ta zare jikin ta tare da juyo dashi bakin ramin tana faɗa mai wasu maganganu da be gane ba kawae se ji yayi tasa hannu tare da hangitsa shi cikin wannan rami sannan ta juya, tana murmushi tayi tafiyar ta shi kuma Allah yasa be faɗa ba ya riƙe wani ice dake bakin ramin, can kawae se ga wata babbar mata ta miƙo mai hannu ya kama ta zaro shi daga cikin ramin sannan ta ja hannun shi suka fara tafiya cikin wani lambu amma ya gagara ganin fuskar ta har ya farka daga mafarkin, ajiyen zuciya ya sauke tare da zuro ƙafafun ƙasa ya zura takalmin da yake yawo dashi na ɗaki, ɗaga kai yayi tare da kallon tamfatsetsen clock🕑 ɗin dake manne a jikin bango, 2:00pm ya gani, tashi yayi tare da fitowa haɗeɗɗen parlorn shi, anyi decoration ɗin shi da white and light blue, kitchen ya wuce shima dae ya haɗu iya haɗuwa, gaban makeken fridge ya ƙarasa tare da buɗewa ya ciro table water ya ƙarasa ya ciro glass cup🥛 ya tsiyaya tare da kafawa a bakin shi, se da ya shanye ruwan tass sannan ya cire tare da ficewa ya daga kitchen ɗin, koh da ya koma bedroom be zauna ba ya wuce bathroom ya ɗauro alwala sannan ya fito tare da zura jallabiyar shi ya shimfiɗa dadduma sannan ya tashar da sallah, haka ya raya wannan daren da nafilfiloli, be koma bacci ba har aka kira Sallahr asbah, ya fito tare da wucewa masallacin jikin gidan.

6:30am ya fito daga masallacin tare nufo tamfatsetsen gate din su, turawa yayi tare da turo kanshi, da sauri me gadin da ke gefe ya zube yana gaishe shi, amsawa yayi ba yabo ba fallasa sanna ya nufi part din shi, bayan ya shiga be tsaya koh ina ba se a bedroom ɗinshi, cire jallabiyar dake jikin shi yayi sannan ya nufi bathroom, tsawon 30mn ya ɗauka sanna ya fito ɗaure da towel a ƙugunshi, yana goge kanshi da ɗan ƙarami, kana ganin shi ka ga ingarman na miji, kirjin shi lallausan baƙin gashi ne kwance she sheƙi yake yi, santala²n ƙafafun shi ma gashin ne kwance, ƙarasawa gaban dressing mirror yayi wanda ya ke nan kaman na mata, perfumes ne kala² da mayika,

Ajiye towel din da ke hannun shi yayi a gefe tare da sa hannun shi ya dakko lotion me kyau, ya fara shafe lallausan fatan shi, bayan ya gama ya feshe jikinshi da turararruka sannan ya ƙarasa gaban closet tare da danna wani ɗan abu a gefe a take kuwa ta bude, duk kayan nashi a jere yanda kasan wata yar karamar shop a UK🇬🇧, manya kaya gefen su daban ƙananan kaya ma gefe su daban haka ma suits, hannu shi ya miƙa tare da zaro milk long sleeve shirt da brown jeans, wata yar door dake gefe ya tura tare da shigewa, wani haɗeɗɗen waje ne inda gefe aka shirya mai difference kind of shoes👞🥾👟🩴 dayan side din kuma P- caps ne da hulunan manyan kaya ,daga gefen kuma hand watch ne kuma kala2, ɗayan ɓangaren kuma ƙaton mirror ne da frames🖼 da akayi decoration dasu da flowers daga gefe, shiryawa yayi tsaf sanann ya fito daga dakin yana daura agogo, ya shirya cikin kayan nan da ya ɗakko sannan ya ɗaura P-cap brown, ni dae Masha Allah kawai nake faɗa tsabar kyan da yayi, ƙarasawa gaban dressing mirror yayi ya ƙara feshe kan shi da turararruka, sannan ya ɗauki wayan shi ƙirar IPhone📱ya fice daga bedroom ɗin nashi.

Wasu fararen Emmata ne zaune a parlorn kamarsu daya da Mami, babbar zata yi 23 years dayar kuma baza ta gaza 18 years ba, ƙananan kaya ne a jikin su wayanda koh rufe jikin su basu gama yi ba gashi koh wacce taci kitson attachment, waya ce a hannun su se danne2 suke yi, Lanti na ta faman shirya mamakeken dinning table da kala2n abubuwan breakfast🍳🍜🍲☕️🍯, door bell ya danna suna zaune babu wanda ya motsa balle suyi kokarin zuwa su bude kofan, yatsine fuska yayi tare da kara danna door bell din a karo na uku Lanti dake cikin kitchen ta jiyo kaman karar door bell ta fito da sauri tare da nufan kofan, dago shanyayyun idanun shi yayi jin alamun an bude kofan, da sauri Lanti ta rusuna tana gaishe shi, alam yayi mata da ta mike sannan tare da gaishe ta ya wuce, ita dae a koh da yaushe tana mamaki sam shi ba irin sauran yaran Hajiya bane, shi sam ba ya wulakanta talaka,

Fuska a hade ya shigo parlorn,sam babu alamun wasa, a zumbur suka mike koh waccen su baki na rawa,

“Y.. Ya Saheel in.. ina kwana!” Fuska ba annuri ba tare da ya amsa su ba yace “Bu ku ji karar door bell bane?” Shiru su kayi se wuri2 suke da ido, tsawar da ya daka musu ce ta firgita,

“Ba daku nake magana ba!!!” Jiki na rawa Babbar tace “Ya Saheel wallahi ni ban ji ba se dae Siyamah..” da sauri karamar ma ta cafe,

“Ya Saheel wallahi nima banji ba kuma ai ka ga Lanti tana nan dama aikin ta kena..!”

“Will you shut your mouth!!!” Tsawar da ya buga mata se da ta kusa sakin futsari a tsaye,

”Ita Lantin sa’ar ku ce! dan kawae tana aiki se kuma aka ce mu ku baiwar ku ce ita?” jiki na rawa suke girgiza mai kai, kallo ya ƙare musu daga sama har ƙasa murya a cinkushe yace ”How many times do i warned you to stop wearing this kind of dress? Ba ku jin magana koh?”

“Ya Saheel dan girman Allah kayi haquri wallahi baza mu ƙara ba,”

“shi kuma wannan ɗan iskan kitson fah? Ban hana ku yin shi ba?”

“Wallahi ka hana mu,”

“Toh meyasa ku ka ƙara yi?” shiru suka yi se wuri² suke, jinjina kai yayi yace “Ohh Alright! Saboda kun isa ne koh?” da sauri suka girgiza kai babban baki na rawa tace “yanzu nan zamu tsefe,” shiru yayi na some minutes murya a murɗe yace “this will be the last time da zan ƙara warning ɗin ku akan komai! The next time you repeat!! common get out from here!!” da sauri suka ɗauki wayoyinsu su jiki na rawa suka wuce stairs har da ɗan gudun su, Lanti na kitchen tana jiyo su murmushi tayi tace“Allah dae yayi maka Albarka Saheel, kai dae sam baka da irin halin Maman ka da sauran ƴan uwan ka, halin ka sak na Alhaji!”

A corridor suka kusa cin karo da Mami hannun ta cikin na ƴar autar ta Anam kyakkyawar yarinya tana cikar suma baƙa ƙirin, irin yaran nan ne masu ƙiba, baza ta wuce 7 years ba,

“Ku kuma lapian ku qalau kaman an wani jeho ku,” ta faɗa tana binsu da kallo, ƙaramar ce ta shagwaɓe fuska tace “Mami wallahi har ban so Ya Saheel ya dawo gidan nan, kina gani daga zuwan shi har ya har ze ishe mutane da faɗa..” da sauri Mami ta kai hannu zata bige bakin ta ta kauce, hararar ta Mami tayi tace “Khairiyyah baki da kunya koh? tunda gidan ki ne ba se ki hana shi dawowa ba! Kuma ae dole yayi muku faɗa kuka yi abun da ba daidai bane!” ɗayar ce ta cafe “Toh Mami yanzu fisabilillahi se ace baza mu dressing haka ba a cikin gidan mu,”

“Ba a ce kar kuyi dressing haka ba amma ku dunga rufe jikin ku idan zaku sauka downstairs, haba Nadiyyah ke kina ma babba ke da ya kamata ki dunga nuna ma kannen ki hanya amma se ki dunga biye musu kuna abun da ba shi ne ba, se ku wuce ku canja kayan ai!” wucewa ɗakin su suka yi suna tura baki, girgiza kai Mami tayi sannan ta ja hannun Anam suka wuce downstairs, zaune ta same shi a kan 3 sitter yana danna wayan shi,

“Son ashe ka shigo!” Mami ta faɗa tana zama kusa dashi,

“Eh Mami Good Morning!” ya faɗa fuskan shi ɗauke da fara’a yana miƙawa Anam hannu, aikuwa da sauri ta ƙarasa wajan shi tana shigewa jikin shi, murmushi Mami tayi sannan ta amsa, nan Anam ta fara zuba mai surutu shi kuma yana ta biye mata, sosai yana son Anam saboda ita sam ba irin su Khairiyyah bace, ga yarinyar da shiga rai,

“Kaga Son taso muje kayi breakfast kar Anam ta tareka da surutun nan nata,” Mami ta ƙarashe faɗa tana miƙewa tare da nufan dinning area, murmushi yayi tare da kama hannun Anam suka nufi dinning arean.

___________________________

 

“Nimrah! Nimrah!”

“Na’am Daadah!” Nimrah ta faɗa tana fitowa daga ɗakin su tare da ƙarasowa inda Daadah take,

“Daadah gani,” cikin sanyin murya Daadah tace “Ga kudin nan kije gidan Laure ki siyo mana mai da kayan miya,”

“Toh Daadah ” ya faɗa tana amsan kuɗin, ɗaki ta shiga ta zura hijab ɗin ta sannan ta fito tare da wucewa aiken da Daadah tayi mata,

Tafe take tana rera yar waƙar ta ta fillanci cike da nishadi,ji tayi ansha gaban ta, ɗago dara²n idanun masu ɗauke da dogayen eyelashes tayi tare da daurawa akanshi, wani ɗan saurayi ne, bakin shi baƙiƙƙirin alamun shi ɗan shaye² ne, kuma daga ganin shi gagararre ne,

washe mata baki yayi yace“Masoyiyah barka da wannan lokaci”

“Mtwssss!” ta yi tsaki tare da bi ta gefen shi ta cigaba da tafiyan ta, da sauriya ya ƙara biyo bayan ta yana mata magana, banza tayi da shi,

“Haba Masoyiyah se magana nake yi miki kinyi banza dani, kiyi mun magana koh na ji sanyi a raina mana,” ya faɗa yana ƙara shan gabanta, a ƙufule ta ɗago,

“Wae kai wanna irin maye ne! Sau nawa zane faɗa maka ka fita a sabga na! Ba ka da zuciya ne?” jinjina kai yayi yace “Ina da zuciya mana amma ta son ki, kin ga duk wannan rashin son da kike nuna mun gwanda ki ajiye shi a gefe koh ba komai ni ɗan uwanki ne kuma auren zumunci za ayi mana, kar ki damu da duk tsanar da Inna (Gwaggo) take nuna mi ki in dae na aure ki dole ki ta so ki!” se da ta ƙare mai kallo sama da ƙasa sanna ta sannan ta juyar da kai tare da tufar da yawu sannan ta dawo da kallon ta kanshi ta fara magana cike da ƙyama…………….

 

 

 

Dan Allah a firgita ni da ruwan comments😍😍😍😍😰

 

*@Hanyluv✍🏻*
*07944454719📲☎️*

Leave a Reply

Back to top button