Bakar Ayah 10
Page 🖤10🖤
Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani.
Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu.
“Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba”
“Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?”
“Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba’a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai.
Amma daman batun ku tsaya cikin gari kuna nemanta bazaku taba samunta ba,wanda suka sani ma bazaku kaiku ba,saboda gudun abinda ke iya zuwa ya dawo.”
Karisawa wajen motar sukayi inda saurayin yake tsaye,Hajiya ce ta kalleshi cikin maganar serious tace,
“To shikenan naji zan biyaka idan ka fadamin inda take,amma kafin sannan inason nasan ita wacece daga abinda ka sani,saboda daga yanda naga iyayenta fuskarsu sauyawa tayi lokaci guda,dan na ambaci sunanta,menene dalilin hakan.
Tunda kace maƙwantansu ne kai,to bashakka kasan wani abu dangane da rayuwarta”
“Zaro ido yayi kafin yayi murmushi,dan da alama bayyi zaton zata nemi sanin tarihin bombi ba,amma kuma koma wanene yaga abinda ya faru,dole zai zargi wani abun”
“Tabbas hakane nasan bombi ciki da bai,kuma inaga bayan mutanen gidansu babu wanda yasan ta kamanni,kasancewar ni ɗan ɗakin mahaifiyarta ne ina yaro,saidai amma saikin biyani,sannan kuma saikin min alƙawari babu wanda zai san na faɗamiki wanann labarin,saboda kar in kinji labarin ta ki fasa neman ganinta”
“Namaka alƙwarin babu wanda zaiji,sannan kuma zan biyaka kamar yadda ka buƙata,kawai burina shine ka faɗamin gaskiya”
“Inshaaallah zan faɗamiki gaskiya,amma kafin sanann mu shiga daga motarku,gudun mutane kar su ganmu,dan idon mikiya ne da ita,tana da mutane a wurare da dama a ko’ina.
Ina tsoron kar na samu matsala”
Amincewa sukayi da zancen saurayin,koba komai hakan yafi da tsayuwarsu a wajen.
Barin ƙofar gidan sukayi,tareda kama hanyar da yace su bi.
“Da farko kafin mu fara sunana Umar,ana ƙirana da MARUJE,labarin daya faru shekara ashirin da biyu baya,ya fara ne……………..
_______*****________
Ayyiriri ayyiriri,Malm Ahmadu ya iyo amaryah a hayin Fulanin yanki, masu ƙura,itace ta farkon mace wacce aka aura da Garesu.
To ikon Allah,shikuma mai takaishi auren ƴarsu,ana fa cewa iri irinsu mayune,shine yaje ya ɗakkowa kansa irinsu,ƙyan ɗan macijine fah dasu wayannan mutanen,lallai Inna laari taga takanta,saita san irin zaman dazatayi da ita. Su fah maza kana zaman zamanka sai su ɗakko maka alaƙa ƙai,daga kawai ta shekara uku babu rabo shine har ya manta soyayyar da sukayi dandali ya auro mata fulanin ƙaurah”
“Hmm kema dai kya faɗa,muma ina gashinan masu haihuwar ma anyi mana kishiyar daga shekara biyu da aure,maza ai sai a barsu”
“Larai ta faɗa tana nuna Innar muruje da baki,wacce take alwalar Azahar”
Duk abinda suke tana jinsu,amma ko ci kanku bata ce musu ba,saima shigewa ɗaki da tayi.
Dare yana kawo kai guɗa ta cike anguwar tasu da kuma raye rayen fulani sama sama,wai hakan ma ba’ayi wani bidiri da al’adu ba,kasancewar iyayen yarinyar basason auren.
Malm ahmadu ne yadage akan sai ya aureta,lokacin daya ganta takai nono gonarsu talle,dayake yana kuɗi a lokacin sosai,duk anguwar babu wanda yakaishi girman Gonar Ganyen shayi,gashi yanada hanya sosai a kamfanonukan da suke siye da siyarwa dasu.
Tun daga bakin ƙofar shigowar tasu LAARI ta fito da fara’arta ta tarbi Amaryartasu. Al’amarin daya bawa aminanta ma mamaki,ba iya su dangin amaryarba,dan kafin shigowarsu babu irin abinda su Larai da danginta basuce ba akan abokiyar zamannnata ba,amma tayi shuru tai biriss da abinda suke cewa,sai daga shigowar amaryar ta bawa kowa mamaki.
Duk da hakan ba abine dama da bazai iya faruwa ba,kasancewarta mace mai shuru shuru kuma marar hayaniya,sannan kuma ta yarda mijinta,tunda tasan badan yana ƙinta yayi mata kishiyar ba.
Har ƙofar ɗakinta ta rakata tareda buɗe mata kai.
“Sunan Laari,nice Abokiyar zaman ki dakika shigo gidannan kika tarass,ina fatan zaki ɗaukeni kema abokiyar zama,sannan kuma zaki bani hadin kai mu samar da zaman lafiyah,Allah yasaka albarka da zaman lafiya a zamantakewar mu”
“Ɗan murmushi Daneji(an samo sunan ne daga Alamar “fari” a harshen fillanci,Ainihin sunan ta shine Fatima,taci sunan mahaifiyar baffansu. To kasancewarta fara sosai ko a gidansu yasa ake ƙiranta da Daneji).
“Inshaaallah zaki sameni mai binki sauda ƙafa Addah laari,nagode da ƙaunarki gareni,bansan da wane kalmomi zan yaba miki ba”
“Bakomai ki nuna min a ta fuskar halayyarki ma ya isa”
Daga haka Inna laari takoma turakarta wajen mutanenta,tabar Daneji da Nata ƴan uwan a sabon gidannata.
Sai bayan kwana biyu da kawowa amarya kafin ƴan biki kowa ya watse,aka bar amarya daga ita sai halinta.
A zaune take ta tafi tunanin yanda rayuwarta a sabon wajen zai kasance,musamman da tasam cewa yan uwanta na daff ta yin ƙaura zuwa arewancin nijeria,dan dama su ba mazauna bane,abinda iyayenta suke tsoro kenan dama ita kanta,shine su barta a wajen da basuda tabbacin dawowa.
Saidai komai yayi rintsi maganin sa Allah,haka iyayennata suka koyar da ita,dogaro da Allah a kowanne lokaci,duk da kasancewarsu masu tashi basuyi boko ba,amma karatun addini kam ko na garin bazasu nuna musu ba.
Saurin share guntun hawayen daya gangaro mata tayi,jin motsin mutum ya shigo ɗakin.
Inna laari ce ɗauke da ƙwaryar abinci a hannunta.
Ƙarisawa tayi inda Daneji ke zaune a hankali tareda dafa hannunta.
“Nasan kuka kikeyi,saidai bazan hanaki ba, ko kuma naga laifinki,domin kowa yasan abin sai anjure tukunna a saba. Dan haka kema kiyi ƙoƙarin daurewar kuma ki saki jikinki,komai zai wuce kaman bai faruba inshaaallah.
Da haka cikin sigar lallashi da jan hira Laari tayi nasarar saka murmushi a fuskar danejin.
Har suka fito tsakar gidan suna aiki tare,yar hira suke kaɗan kaɗan,yawancinta kuma Laari ce keyi,sai ta tambayeta ne tace,uhm ko uhmuhm.
Haka zamannasu ya fara gudana,cikin zaman lafiya da kuma mutunta juna,abin ba ƙaramin faranta ran malm Ahamdu yayi ba,ganin matannsa sun rungumi junansu suna zaune lafiya.
Inna laari ce keyin Abinci,ita kuma Daneji tayi wanke wanke da kuma shara,sannan ta gyara mata kayan abinci.
Bayan sati da kawo Danejine su Larai suka shigo ganin amaryah.
Tundaga zaure ta rankwaɗa Sallam,dan dama itace a gaba sai kuma Shatu tana binta a baya,ta riƙe hannun ɗanta Muruje,wanda ko sati bayyi ba da yaye.
“Salamu alaikum masu gidannan,gamu munzo ganin baƙuwa ta ganmu mu ganta,ta kuma ganemu”
Inna laari ce ta amsa mata wacce take cikin ɗakin girki tana hura wuta.
“To sannunku da shigowa,sai yai kuka zo ganin amaryar?”
“Iyyi to ya zamuyi,munyi ƙoƙari ma,ita ina bata nememu ba,sai mune muka zo ganinta”
“Hayen wuri kukayi ai,dama tana shirin zuwa muku”
Duk zancen tsakanin larai da Inna laari akeyi,shatu kan da daneji basuce komai ba. Sai bayan an gama gaisawane suka shiga ɗakin Amaryar.
“Ahhh babu laifi kam ɗaki yayi kyau,zamuga shin za’a kawo kazantar ɗaki,ko kuma dai duk sammakal ne”
Larai ta faɗa tana fitstsina ido tareda dukan ɗan ƙaramin kunkuminta.
Shatu ce ta kallin Daneji itama ta kalleta,amma larai ko a jikinta,saima surutu da ta cigaba dayi,da kuma ganin ƙwakwaf.
Itada kanta da abin ya isheta tabar ɗakin,tareda nufar ɗakin Inna laari,a bakin ƙofa ta tsayah kafin tashige ta kalli shatu.
“To ni barina yi ɗakin yawuron gidan,ta inda muke muyi namu yakin,wanda ko an fadama mutum bazai ganeba,saura kuma a zunguri hancina idan anga na kauda ido”
Itadai shatu bata ce mata komai,saima maida kanta da tayi kan Daneji wacce take zaune a bakin gadonta.
“Hmm kiyi haƙuri fah amarya,yanayin zamanne sai haƙuri,bazaka iya sanja mutum ba,saidai dole kasha maganin zama dashi.
Sannan abinda zan faɗamiki kiyi taka tsantsan sosai,karki saki jiki ki bada yardarki dabaɗaya,za’ayi miki abinda bakya tsammani.
Murmushi Daneji tayi,da alama bata ɗau maganar shatun da gaske ba,saima kauda zancen da tayi ƙoƙarin yi.
“Ayyah Addah shatu babu komai dai,Inshaaallah babu wata matsalar……..kai ɗan saurayi ya sunanka?”
Ganin duk yadda take ƙoƙarin nusar da Daneji bata damuba,saima dauke zancen da take shirin yi,yasa itama Shatu tabar zancen tareda cewa.
“Ohh wannan sunan Umar,amma yara sun saka masa Muruje,kiji wani suna kaman na Warjayi”
Ƴar dariyah Daneji tayi,da alama sunan da kuma yaran sun bata dariya,haka ta zage tana ta tsokanarsa shikuma yana yi mata ƙiwuyah.
“Inasonsa ki bani shi innar muruje”
“Hhhhh baban sa zai dawo gidannan kenan,in kikayi haƙuri kema zaki haifi naki kaman yaune,saidai zai dunga zuwa miki yawon yamma”
Larai ce a zaune ta baje ƙafa kan kujerar Laari zance yayi zance,wanda yawancinsa duk na Adashen da suke ne a anguwa.
“Uhmm daikuma naga yarinya tasake abinta tayi mursul,ga kulawar miji ga kuma ta kishiya,abin har ya taru yayi mata yawa”
“Ke larai,banda abinki dama ai jajir take lokacin data zo ma”
“Ohh to inaga idona ne yagani badaidai ba,nikam da badan nasanki ba,sai nace yarinyyar can asirin tayi miki,dan inajin labarin duk abinda kike mata a wajen malm,insun zauna malam ahmadu na bashi labari. Yayi tayimin tujara kenan wai ni naƙi a zauna lafiya.”
“To kema ki riƙeta ku zauna lafiya mana larai,ni banga laifin shatu ba……”
“Ahah ahah nina gani inke baki ganiba,idan dole haka kawai banason ta saina ce inayi,gwanda tasan bani sonta,ta tsare tata rayuwar nima nayi tawa,innace zamuyi zaman da kuke da itama nayi ƙarya bazan iya ba”
“Kiji gulma irin ta maxa,wato mlm ne yake bashi labari?”
“Tabb yau kika sani,gulma ai ta daɗe da tarewa wajen maza,idan sun zauna a wannan majalisar,basa lazumi ko salati,sai aukin cin tsire da gulma,shiyasa kiga cikinsu tula tula kaman ƙore,kai sun barka da ɗumame da kuma cikon cefane”
Larai ta ƙarisa fada tana tashi tareda nufar ƙofa.
“To mu munyi nan,sai kun shigo,dan Allah kicewa magajiya zanyi ɗaukar wannan watan na adashen,auren ƴar yayata ya taso”
“To shikenan zan faɗa mata”
Daidai fitowarta daga ɗakin,itama shatu ta fito daga ɗakin Daneji,sallama sukayi musu suka fita.
…………”uhhhhhh uhhhhhh” ……….”laari Daneji fah amai take kwarawa tun daren jiyah,lafiya kuwa????………….
🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03
*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna
______________****_______________