Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 59

Sponsored Links

CHAPTER 59

Fizge wayan hajia mariyah tayi daga hannunta tana kallonta cike da fushi tace”amma anyi shashashan yarinya wallahi bakiyi kuka a gidan ubanki ba sai ga gadin miji tunma kafin kishiga wannan idan kuma kin shiga ciki yakenan?

Faɗawa tayi jikin umman nata tace”dan Allah mummy kiyi wani abu wallahi ina sonsa zan iya yin komai saboda shi,bansan abunda yasa yatsani har haka ba wallahi mummy dan Allah koke zaki gwada kiransa a waya ki bashi hakuri yaxo ya fiddani kunya.

Kallon baki da hankali tamata sannan ta juya ga Alh dake hakimce tawatsa masa wani muguwar harara tace”wallahi Alh kabani mamaki har yaushe zaka biyeta ka zubar da ƙimanka ga wannan yaron mara kunya da besan mutuncin na gaba dashi ba,idan kai bega girmanka ba ai yasan girman uban da ya haifesa kai kuma kana da iko da uban nasa kira ɗaya zaka masa kafin nan nikuma yanzu zani wajen mai charbin ƙwai ba matarsa ba har uwar da ta tsuguna ta haifesa inaga sai yanance sunan ta bare wata mata tashi kishare hawayenki jeki kici gaba da shirinki zuwane kaman yayi kai kuma sai ka amshi wayan kakira uban nasa dolene ya turasa.

Daga haka tasa kai yafita daga falon tana magana da ƙawarta hajia shema a waya kan su haɗu a hanya dan zuwa gidan mai charbin ƙwai.

****
Aisha ƙudundune take cikin duvet tayi luf tana sauraron yanda kanta ke sara mata ji tayi anyaye mata lulluɓin saurin runtse idonta tayi dan duk a zatonta ta ɗauka anty malika ce da tun ɗazu ta dameta data tashi ta wanke bakinta koda tea ne tasamu tasha saide tsaɓanin tunaninta jin ƙamshin turaren sa”oya tashi yafaɗa mata muryar sa ba wasa ciki miƙewa tayi zaune dafe da kanta dake barazanar rabewa biyu.

Amshi nan miƙa mata kufin hannunsa yayi ɗan kauda kanta gefe tayi zaki karɓane ko sai namiki ɗaure yanzu yafaɗa da kakkausan murya,tura bakinta tayi tana ɗan mutsu mutsun kaman mai magana oh zagina kikeyi ko?

Sake tura bakin tayi batare data amsa masa ba,wayansa ne yayi kara hakan yasashi fita daga ɗakin bayan ya dire mata da kofin tea yana cewa minti goma nabaki ina jiranki kisame ni waje karki kuskura nasake shigowa nasamu baki shirya ba,daga haka yasaka kai yafita yana amsa kiran.

“Assalamu alaikum daddy barka da warhaka yafaɗa kaman yana kallon sa cike da ladabi.

Madadin daddy ya amsa masa sallamar sai cewa yayi”to sannu ishasshe nace sannu ishesshe tun daga nan ya fahinci inda daddyn nasa yadosa dan haka cike da zolaya yace”Alhaji wai lafiya kuwa irin wannan fusatan haka kasanfa ni yau nake ango dan yanzu haka ina shirin kai surukuwarka wajen ƙunshi gashi naga kaman….”dallah rufamun baki wanda besan inda yake masa ciwo ba,yanzu Ahmad saboda Allah ga inda akeson yima gata amma kaɓige da shashanci”wai Alhaji mai akace nayine?

“Yanzu kaman Alh sunusi yakira yana neman alfarman yau kaɗai kaje wajen taron yarinyar nan kona minti goma amma ka iya bude baki kace masa bazaka ba wai….katse mahaifin nasa yayi yana cewa”daddy dama saboda wannan kka fusata nifa na mijin mata biyune Alhaji yakare magana cike da zolaya.

Jin abunda yake fadin yasake tunzura Alhaji badamasi sai faɗa yake ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba karshe yarufe da cewa kashirya anjima karfe bakwai na dare kutafi kodasu khalid ne wannan umurni nake matsayina na mahaifinka idan ko kaki tafiya to wallahi ran uwarkane ze ɓaci dan nasan ita ke zugeka.

saka Amminsa ciki yasa shi yaruntse idonsa cike da ɓacin rai zuciyarsa na masa suya can yace”Alhaji tun tuni munyi da ita bazan halarci ko wani irin taronsu ba,kuma ta amince sannan kuɗina ko kwandala na bazeyi ciwon kai ba”ai idan naka beyi ciwon kai ba ni nawa sunyi dan duka party goma da sukayi nina ɗau nauyin bakwai daga ciki kama daga abunda zaci awajen da abun sha da biyan kudin hall da zasu gudanar da taron kai harma da makaɗa da za gaiyato duka”yanzu Alhaji a wannan marran dakuma halin da kake ciki shine….”dakata mun Ahmad yakatse sa cike da fushi wai kaine ka haifeni ko nine na haifeka?

“Kai ka haifeni ya amsa cikin sanyi murya.
“To inde ni na haifeka to kashirya zuwa ba ruwanka da halin da nake ciki abun kunyane gareni ace ɗana ze auri kaman ƴar Alhaji sunusi amma ina da kuɗin nakasa ɗaukan ɗawainiyar komai na barmasa,sannan ita wancan mata taka ban amince da tare warta nan kusa ba,duk da dama ni banwani dauki auren nan a aure ba dan nafi daukansa da auren wucin gadi kokuma auren jingina.

“Alhaji yanzu bakaji kunyan tattauna irin wannan da danka ba,kai da yaka mata kaimasa addu’an Allah yatayashi riƙo amma kake wani zance mara dadin ji da sauraro to wallahi kasa aranka cewa wannan da kakewa fatan auren jingina ko na wucin gadi in sha Allah itace wacce zakayi alfahari da ita gaba,dan wannan ƴar gwal ɗin taku da ubanta ba komai suke yiwa ba sai abun hannun ka ina kyautata zaton akwai abunda wannan mai ido a tsakar kan yakewa bazaka taɓa ganewa ko kayarda ba sai lokaci ya ƙure maka idanma bacci kake ka tashi wallahi ko wannan abunda yafaru dakai bana zargin kowa sai shi tabbas dasaka hannun sa ciki wallahi Allah ko kaffara bazanyi ba,sannan kuma bincike da ake shine ze kara tabbarwa da shidinne da sannu zaka gane bason Allah yake maka ba.

Tunda Ammi ta soma magana yayi saroro yana kallonta ko kiftawa bayayi saida ta dire sannan yasamu zarran cewa”amma ma’arufa bantaɓa sannin ƙiyayyarki da Alhaji sunusi yakai kimasa sharri ba sai yau yana fadin haka mikewa yayi yayi wucewarsa daki.

Hajiya mariyah da kawarta hajia shema ne gurfane gaban wani gajeren mutum mummuna da wagege baki hanci kaman ƙofan kasuwa..bude baki tayi da nufin tamasa bayanin abunda yakawota saurin dakatar da ita yayi da cewa”tun ma kafin kuzo anfaɗamun so kuke yaron nan yanuna musu wani ƙwaya dake gaban sa cike daruwa matso kugani matsowa sukai ai kuwa azabure suka ja baya ganin Ahmad tsaye jinjine jikin mota waya kange a kunnesa yace ko bashine ba.

Saurin amsa masa sukai cikin rawr murya da”wallahi shine”ai kinku mai saukine amma sai kunsamo mana sunan ita matar tasa da kuma ta mahaifiyarsa sai kuma bayan ita mahaifiyarta sa akwai wata ɗaya da ita ke juya uwar yaro bata iya tsalleke maganarta ba.

Ina zuwa tace sannan ta kira wayan mijinta yana dauka tace”Alh wai ya sunan mahaifiyar yaron nan ne dan malam yace sai an samo sunan su sannan aikin zeci,dan jim yayi kaman mai tunani sai can yace”marfu’at ne ina ji”kana tantamane?kode ka tabbata karfa asamu matsala Alh”hakanne ma ita kuma matar tasa kibari zan tambayo badamasi idan yaso ko a waya kyafada masa zuwa gobe”tom ta amsa tana kashe wayan.

Cike da kwarin gwiwa ta faɗawa malamin sunan sannan ta daura da cewa”sunan ita matar tasa zuwa gobe zankira ka ko ta waya idan yaso nasanar dakai”ba matsala yace.

Dan Allah malam aiki mai zafi nakeson ai mun akansu so nake wannan yaron yamace akan yarinyata sannan inason a dasa tsana mai tsanani tsakanin sa da iyayensa shikuma yazama bashi da maganan kowa saita basma duk abunda yasamu da wanda ya mallaka duka ya mallaka mata.

“Wannan shiyafi komai sauki amma kafin sannan duk yanda zakuyi kuyi dan ganin be tare da matarnan tasa sunyi taraiyar ba idan ko ya tare da ita duk aiki da mukai ze karye karshe komai ze koma kanku dan haka ku kiyaye kunisanta shi da duk inda kukasan yarinyar take idan baya ganinta baze taɓa tunawa da ita ba.

Kayan aiki muna bukatan hantan baƙar karya da huhun cinnaka sai maniyin sauro da sune za haɗa maganin.

“La’ila ha illallahu”yimun shiru yadaka mata wani gigitaccen tsawa dayasa duka dajin amsawa rai a mugun ɓace yacigaba da cewa kinsan da Allahn kika kawo kanki wurin mu”tuba nake ran malam yadaɗe ruɗewa nayi”ki kiyaye gaba dan duk wanda kika gani anan ya kauce hanyane ɓatacce kaɗai kanzo nan.

“Tuba muke baza kara ba suka faɗa kaman zasuyi masa sujuda.

“Yawuce yanzude ku chake kuɗin da zabada dan nemo muku kayan aikinku aikinmu kaman yankan wukane”munsani ran malam yadade amma dan Allah aimana sassauci kar atsuga mana kuɗi dayawa shekara da shekaru muna tare.

“Hakane yanzu de kuɗin kayan da nafaɗa dubu ɗari biyar zaki bada sannan zaki bada dubu ɗari da hamsin kuɗin kafin alkalamin aikinki idan aiki ya kammala saiki cikatomun da dubu hamsin.

Jiki na rawa ta ciro damin kuɗi cikin jakarta ƴan dubu dubu sabbi kar dasu ta ajiye masa daukan kuɗin yayi yana shinshinawa yana babbaƙewa da wani irin dariya mara daɗin sauraro saida ya tsagaita da dariyan sannan ya ɗaga hannun sa sama saiga wani ƙullin magana ya miƙa mata yace duk yanda zakiyi kiyi yau din nan ki tabbata kin bada anzuba masa a abinci ko abin shansu dan yau shine ranarki ɗan tsuku yana kan aiki shi kuma yaron ze zo taron da tawagarsa dan haka amshi nan hanzarta kar asamu matsala kuma duk yanda zakiyi kisa ƴarki ta tambayo sunan matar tasa kutashi kutafi,kufita da baya da baya kutaka a hankula karku taka mana yara suna wasa duk sun tsure baramma hajia shema da bata taɓa zuwa irin wannan wajen ba.

*****
Aisha tunda Ahmad ya fita a ɗakin zaune tayi bakin gadon dafe da kanta yafi minti talatin kafin yasake shigowa ɗakin yanda yabarta haka yashigo yasameta tunma kafin ya karasa shiga dakin yasoma tattare hannun rigarsa kaman mai shirin kaukawa da gefe idon take kallon yanda yake takowa da karfin sa fuskar nan tasa ba alamun rahama a tare da shi take taji cikin ta yasoma kugi kuuuuuuuuu wani kakkauran ƴawu ta haɗiye mukut miƙewa tayi da hanzarin ta dan shiga toilet tama kanta maɓoya saide tana miƙewa taku ɗaya biyu taji anyi sama da ita buɗe bakinta tayi da nufin fasa ihu kaman ko yasan abunda zatayi yayi saurin rufe mata baki da ɗaya hannun sa.

Leave a Reply

Back to top button