Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 29-30

Sponsored Links

Page 🖤29••30🖤

 

Da dauki akalla daƙiƙu masu yawa tana jujjuyawa,amma kwata kwata bata kulada mutumin dake zaune akan gefe da itaba bisa kan kujerar roba fara,shima kaman ita ƙananan kayane a jikinsa,saidai nasa basu kamashi ba kaman ita.
Tunda tafito idonsa yake kanta ƙyam bai ɗaukeba,lokaci bayan lokaci yana ƙurbar lemon dayake hannunsa,wanda yana daga cikin waɗanda tasaka masa a fridge.
Gabaɗaya yarasa mai yake damunsa,idan yace badan ita yazo wajennan ba,ko kuma bata burgeshi to yayi ƙaryah,abubuwan datakeyi abin yaji takaicine kuma yaji haushi,musamman daya san ta taba yin masha’arta harda sakamako na yaro.
Amma kuma yarasa mai yasa ya gagara jin haushinta kaman yanda yake son yayi.
Ɗan murmushi yayi wanda hakan yasa ya ƙwaru da abinda yake shirin haɗiyewa,ganin tayi ƙoƙarin damewa akan ƙafafunta takasa kaiwa ƙasa,yanayin yanda ta cune fuska tayi haushine kaman an ƙwacewa yaro alewa yasashi yin dariyar.
Dara daran idanuwanta ta watsomasa,da alama bata kulada shi a wajen ba.
“Barka da safiya mrs workout,waike kullum kina cikin motsa jikine,da alama akwai aikin dakikayi wanda ya haɗa da hak?”
“Tambayata kake yanzun ko kuma bawa kanka amsa.
Ina mamakin mutum ya auri mace amma kuma bai san ita wacece ba,abin tausayin gareka kuma nina san waye kai sosai”
“Hmmm kinfi kowa sanin ta wanne irin aure kika shigo gidannan ai,banda haka inaga ko gari ɗaya bazamu taba haɗawa”
“Hhhhh mundaɗe da haɗa gari ai Mr CEO,koda ƙaddarar aure vata haɗamuba dama dole zakaji labarina koda ana gaba idan abin hakan yafaru”
Ɗan tafiyah tunani yayi na ɗan lokaci kafin ya taso daga kujerar dayake ya taho inda take tsaye.
“Wacece ke? Shin dama a garinnan kike,sannan mai kike shirin aikatawa? Shin kinzone domin ki saci zuciyata kicika muradinki?”
Ƙarisawa tayi kusada inda yake har suna jin numfashin juna,idanuwansu na saƙaƙe.
“Tambayoyinka sunsa naji kaman ƙwari na yawo akan fatata,kaman Mr CEO na company guda,kamata yayi ace bani zakayiwa wannan tambayar ba,saidai kawai kayi bincike ka gano gaskiya.
Uhm duk da nina faɗamaka cewar kayi bincike,amma zanso kada kasan koni wacece ko kuma mai nake shirin aikatawa a yanzu.
Komai na rayuwata sirrine Mr CEO,sannan a kowanne mataki dazaka hau na sanin koni wacece bazai maka amfani a yanzu ba saima ƙara maka Wasiwasi fiyeda wanda yake ciki a yanzu,domin kai ɗin kana cikin yanayin da ko marar zuciya a ƙirjinsa sai tausaya maka, kayi sa’a daka saka zuciyar dutsen dake cikin ƙirjina ɗan motsawa har takalli halin dakake ciki da kuma wanda zaka shiga.
Dan haka abinda nakeso kayi min ba a matsayin Wacce baka saniba zanyi maka maganar ba,sai a matsayin matarka wacce har yanzu bakayi mata kallo goma ba da shigowarta gidanka.
Shine ka jure zuciyarka kada kayi binciken koni wacece,sannan in wani abu danake yaci karo a wani waje dazan ganka kada kadamu dasanin mai nakeyi ko kuma yin bincike akai.
Nasan bazaka taba amincewa dani ba ammma…….”
“Na yarda dake”
“Me mai naji kace ka yarda dani?”
Bombee ta faɗa cikin kaɗuwa tana ja da baya,da dai duniya bata taba tunanin jin wannan maganar daga bakin mutumin da ta sani a lokaci ƙalilan.
“Bansan meyasa ba amma zuciyata ta amincewa da cewa bakida niyyar cutarwa a gareni,nima ina mamakin hakan amma haka nake ji.
Bansani ba ko kulawar dakikayi da rayuwata a kwanakinnan ne yasakani jin haka,amma koma menene kada ki daina yimin abinda kika fara,shin zaki iya cigaba hakan,idan zaki cigaba dayimin nikuma bazan taba damuwa da sanin koke wacece ba.
Saidan inason duk ranar dakika ji ra’ayin sanar dani sirrinki a shirye nake da saurarar menene.
Ɗaga masa kai Bombee tayi,saboda bakinta yagagara furta komai,bata taba tunanin haka zata sameshi da sauƙin kai ba,tayi tunanin mutum ne mai kuɗi mai jiji da kai,baidamu da abinda naƙasa dashi suke ba..
Lokacin data fara jan ra’ayinsa da gyara da kuma abinci,tayi zaton sai ta ɗau lokaci tanayi kafin ma yasan tanayi,sai gashi a sati guda har yana faɗamata jin daɗinsa akai,abin ƙarin mamakin ma wai ya yarda da ita.
Anya kuwa da irin wannan zuciyara gen Abdu manga zaisha wahalar ƙarbar kujerar nan,kokai saboda tsawon rayuwarsa bashida masu kulada yaya yake,shiyasa ta narkar da zuciyar sa a ƙurarraren lokaci.
Ɗan murmushi ya sakar mata alamar baiga abin mamaki ba.
“Da alama maganata tasakaki cikin bazata wanda nasan kina buƙatar nazari a kebance,amma kisani kada ki damu,komai dayake faruwa a duniyar nan yanada dalilinsa,in har na yarda da zabin mahaifiyata kuma nayi mata biyayya akai to na yarda dake,saboda nasan bazata kawo abinda zai cutar da rayuwata ba”
Yana gama faɗin hakan yasaka hannunsa a aljihu ya bar wajen.
Binsa tayi da kallo,har yanzu ta gagara fitowa daga mafarkin data shiga ɗaxu.
Gabaɗaya sai taji babu daɗi da abinda take shirin yi,wanda tasan dole sai ya shafeshi,amma kuma in ƙaddara ta nufo ka dole ka fuskanceta inkana so kayi nasara,koda kuwa zaka fuskanci ƙalubale gameda hakan.

“Toh munshigo anguwar da mutumin ya faɗamin anan estate ɗin take.
Ku dan zauna a mota barina tambayi mai shayin can tukunna”
Fita yusuf yayi daga taxi ɗin ya nufi masu shan shayin,yabar su innayi a motar sai zazzare ido take tana ƙarewa anguwar kallo.
Tun shigowarsu bataga mutane ba sai a wajen masu shayin,shima kuma ba wajene haka irinna cikin anguwa ba.
Sunan zaune ya dawo tareda tada motar.
Inda suka kwatanta masa yafi,har ya tsinci kansa a bakin shantamemen Estate ɗin..
Kallon innayi yayi tareda cewa.
“A yanda suke kwantantamin nanne wajen,amma kuma anya kuwa kina ganin nanne?”
Innayi bata amsa masa ba,sai fitowa datayi tana kallon get ɗin dake gabanta.
Shima yusuf biyota yayi ya tsaya wajen yana nazari.
“Hamma yusuf kana ganin zamu sameta anan wajen kuwa,duk da cewa ba abune dabazai iya faruwa ba samun addah Bombee anan wajen ,amma kuma abin da matuƙar ɗaure kai,gidan yayi girma ace tana cikinsa”
Kafin yusuf yabata amsa sukaji maganar wani mutum yafito daga gidan.
“Bayin Allah me kuke anan wajen,in motace ta baci muku kuyi hanzarin gyarawa ku matsa,domin dokace ba’a tsayawa a nan”
“Ba motar muce ta baci ba yallabai,wata muke nema a cikin gidannan mai suna Bombee,kasanta dan Allah?”
Nazari yatafi kafin yace.
“Ahah bansan ta ba,bamma tabajin sunanta ba a cikin gidannan.
Amma bari na duba datar sunayen ƴan gidan nagani,ku jirani ina zuwa.
Juyawa yayi ya koma,ya ɗan daɗe duk suna tsaye kafin ya dawo.
“Baiwar allah munduba gabaɗaya amma bamuga mai sunannan ba a ciki. Kiyi haƙuri kutafi ”
“Bawan Allah kasake dubawa dai,indai nanne JAAN Estate to na tabbatar tana ciki,dan bazata bada address ɗin karya ba”
“Wai me kike sone baiwar Allah,dui yadda nake binki saikin ƙureni tukunna,na faɗamiki babu wata mai irin wannan sunan anan,Kaff cikin ƴan aiki na duba bangani ba.
Haka kawai yanzu haka ƙarya kuke danku shigane”
“Kinga kiyi haƙuri innayi,inaga tunda yafaɗa ba’anan take ba wataƙila”
Har sun fara tafiyah tasake juyowa,shikamma securityn har ya fara tafiyah.
“Ahh yallabai naji kace sunayen ma’aikata ka duba koh?”
Tsayawa yayi bai juyoba,sai itace ta je inda yake ta gabansa.
“Yallabai addahta ba aiki taxoyiba,ta auri ɗan gidanne wata ɗaya daya wuce”
“Uhm daga Gembu kuke garin Hajiya maryam?”
“Ehh eh daga can muke,ni ƙanwarta ce kuma hakane sunanta na gaskiya maryam”
Cikeda zumuɗi innayi tafara bashi bayani wani nabin wani.
“Uhm duk da haka bazan barku kushiga ba,bari naɗau hotunanku na tura mata,idan tace tasanku saina barku ku shiga”
“To shikenan muna jiranka dan Allah”

A kwance take tayi biris tanajin Hilyaan tanayi mata magana,amma sai tayi kamar bacci takeyi,saboda a yanda take batajin son magana tunda ta tashi da safen.
Gaba ɗaya yanda zata tafiyar da rayuwar tata ne a ranta,jiyq bata kaiwa Jabeer abinci ba,tasani sarai yazo yaga babu abincin,haka kawai tunanin ya zaiji yasakata cikin wani yanayi na musamman.
Komai yasama take saka wannnan bawan Allah a ranta oho,ita ji take anya ma kuwa ita ce,kaman wanda aka sanja ta,tsoronta ɗaya kada zamanta cikin gidannan yasa tafara mantawa da ɗaukar fansar dake ranta.
Inaaa hakan bazai yiyuba bata fatan tabar mutuwar abokinnata ta tafi a banza.
“Anty maryam inata magana nasan kina jina ba bacci kike ba,daga motsa jiki yanzu sai bacci,ko zaman gidanne dukka yamaidaki haka”
Cikin kasala ta buɗe idonta a hankali tareda ɗorasu akan Hilyaan.
“Wai nikam Hilyaan yaushe muka fara wasa ne dake,duk zaman waje ɗayanne yakawo haka,tabbas na sanja kam tunda har ake ganin fuskar tsokanata,ke barin gidannan zamuyi,bazan zauna zuciyata ta sanja ra’ayi ba,dolene na ɗau fansa”
“Kiyi haƙuri anty maryam amma wanene yahanaki ɗaukar fansa?”
“Wani yanayi nakeji yana shiga raina wanda yake son fitarda Muradi na daukar fansa a raina,me kikega zanyi yanzu?”
“Uhmm mai yafaru haka,ko……..ko kinfara developing feeling ba Jabeer kai,shiyasa na haidar ke ƙoƙarin fita daga ranki,na tabbatar haidar ma zaiso hakan,ki bar ɗaukar fansar nan ki tafiyar da rayuwarki yanda kowacce mace takeyi”
Wani saurin tashi Bombee tayi daga kan kujera kaman zata haɗiye Hilyaan da Idon takaici.
“Me kike cewa Hilyaan? Nabar komai ya wuce sun kashe banza kenan,inaaa bazai taba yiyuwa ba,koda abinda kike faɗa gaskene bazan taba bari abinnan yatafi a banza ba”
Tana maganar tana nuna Hilyaan da yatsa,kaman itace ta kashe mata aboki.
Sai bayan tayi ya isheta kafin ta kulada faɗan ta takeyi marar dalili.
Ruwa ta tsiyanya mata a kofi ta bata,bayan ta kulada ta sarara tayin faɗan.
Ƙarbar ruwan tayi ta shanye tareda runtse ido,da alama kanta ciwo yake sosai.
Hannu tasa ta rufe kunnenta na wani lokaci kafin tayi collapse akan kujerar tana maida numfashi.
“Ɗazu kince akwai abinda kike son faɗamin,menene shi?”
“Uhm dama security ne suka ce wasu sunzo neman Bombee a bakin ƙofah,budurwa da kuma Makahuwa kurmiya,to nayi zaton ko su innayi ne shiyasa nazo faɗa miki.
Zabura Bombee tayi ta miƙe kaman ba itace ke magana a kasalance ba,zaro ido tayi tareda cewa.
“Kuma shine baki faɗamin tunda wuri ba,maza kicemasa ya shigo dasu siɗe dina yanzunnan”
“Okay to bari na faɗamasa”,karbar tablet ɗin hannnun Hilyaan tayi tasake ganin hotunansu,suiɗinne ba gizo take gani .
Ajiye tayi akan kujera tareda nufar waje inda motarta take,tun daga bakin ƙofah ta buɗeta taja sai bakin get ɗin.

Securty na jiran yaji ƙira daga wajen Bombee sai ganinta yayi da kanta,buɗe mata get ɗin yayi tafito inda su innayi ke tsaye.
Tun kafin ta buɗe motar ta fito ta ganeta,saidai wanda yake tsaye a gefenta be bata sanshi ba.
Kasancewar tajuya bayanta bataga isowar Bombee ba,saida yusuf ya fadamata tukunna.
“Am innayi inaga kaman yayar taki ce ta ƙariso”
Da sauri tajuyo tana karewa Bombee kallo,kaman wanda ta shekara bata haɗu da itaba,gaba daya mantawa tayi da basa shiri da yayartata,cikeda zumuɗi ta rungumeta kaman haɗe jikinsu waje daya.
Duk abin yayi mata banbarakwai amma bazata iya cewa baya ji daɗi ba,rabonda tayiwa kanwar tata haka tun tana ƴar ƙaramar yarinya,ita kaɗai tasan son datayiwa mata,sannan kuma tasan zafin abinda tayi mata na yaudara.
Saidai yanzu ganin yanda taketa garuruwa domin neman ta yasa tafara mantawa da abinda yafaru.
Kaman bazatayi magana ba ta furta.
“Innayi lafiyah na ganku anan,mai yafaru kuka baro gida,bayan kinsan hatsarin hakan”
Maimakon tabata amsa saita fashe da kuka,wanda ta daɗe tana tarashi.
“Kiyi haƙuri Addah kiyafemin abinda nayi miki ko……”
“Kinga nifah ba wannan na tambayeki ba,yanzu dai ina inna naji ance da ita kuka taho?”
“Ehh tana cikin motar yusuf,yawwa gashi ma ku gaisa,a gidansu muka zauna shikuma yana nema mana inda kike”
Kallonsa Bombee tasakeyi jin abinda yayiwa ahalinnata..
“To yanzu dai ku shigo ciki tukunna,ke shiga motata inyaso shi saiya biyomu ciki”
Hakan akayi yusuf yabi Bombee a baya har bakin side ɗinnasu.
Itada kanta tariƙe inna Danejo suka shiga ciki..
Sai bayan sunsha ruwa an maida labari kafin yusuf yatafi,bayan Bombee tayi masa godiya sosai,tareda cewar zataje har gida ta gaida Malm tijjani.
“Inna ya bakyacin abincin,ko kin ƙoshi kai?”
Tayi maganar cikeda tausayawa dakuma kulawa.
Ɗaga mata kai tayi bayan takama hannun Bombee ɗin ta rike,duk da bata gani ballanta na maida magana,amma yanayinta ya nuna yanda take son ƴar tata sosai.
Kama hannunta tayi suka tashi.
“To inna barina kaiki ɗakina ki huta kiyi wanka”
Za tayi tatsaya ta daina motsi jin maganar da Bombee tayi,a fuskarta ya nuna bataso maganar ba sam.
Alamu sun nuna bazata shiga ɗakin Bombee ba,duk da yanayin daya shiga amma dattako na fulaninnan yana nan babu inda yaje.
“Oh nagane,to muje can Sashen inda ɗakin Hilyaan yake,karki damu akwai wasu ɗakunan ai”
Duk abinda suke su Hilyaan da innayi suna kallonsu har suka ƙule.
Shuru an daɗe Bombee bata dawo ba,ganin suma rashin maganar ya ishesu yasa Hilyaan ta tashi tafara tattara kwanukan wajen zata wanke.
Tashi innayi tayi tafara tayata,duk da a cikinsu babu wanda yayi wani magana.
Sun gama kenan sukaga Bombee ta dawo tana riƙeda kai.
Zama tayi akan kujera bata ce komai ba.
Wajenta suka matso suna karantar yanayinta,sai bayan wani lokaci ta ɗago ta kalli innayin da kuma Hilyaan.
“Hilyaan yazanyi da wannan rayuwar ne? Nakasa jin tausayin inna a raina,nakasa jin soyayyarta a raina,nasan ina son ta amma banajin hakan,idan kuma na tursasa saina ji kaman akwai wani abu a bayan kaina dayake jana na daina.
Idan naƙi saurararsa kuma saina……..sai kaina yafara matsanancin ciwo,shigowar inna yanzu haka cikin gidannan,ji nake tamkar nikuma an jefani cikin ruwan zafi”
Tana maganar ne tana ciccijewa,babu wanda zai kalleta batareda yasan tana cikin mugun yanayi ba.
“shin daga ni har innata in zamuje da wanann tarin alhakin,naji kunya na muzanta kasancewata ƴa ga mushirika,bazan iyah sake buɗe baki na furta miki kiyi haƙuri ba Addah Bombee,saboda nasan ban cancanta kiyin min afuwa ba.
Ni yanzu zan tafi tunda na huta,dama na faɗawa inna idan nakawo ta zan tafi,tahakane kawai idan natafi zan samu sauƙi daga zunuban dana ɗauka”
Tana kuka take bayanin,kana ganinta zakasan nadama ce ƙarara a ranta.
Tashi zata tafi,har takai bakin ƙofah tajiyo muryar Bombee.
“A tunaninki dan kin shiga duniya shikenan sai hankalina ya kwanta na yafemiki,kinsan wanne irin nema nasaka ayimuku danaji labarin kuna garinnan,sannan kowacce rana saina saka an je andubo ya kuke?,kar shashancinki yasa ƙi ƙaramin abinda yafi wanda nake ciki,na daɗe da sanin kema kina cikin abin wasansu,koba ku taho ba dama inada niyyar turawa a kawoku,saidai bata yadda kuka taho zan sa a kawoku ba.
Inkin gama tsayuwar ki shiga ɗaki inna tayi bacci,na ajiyemiki kaya a kan gado,kiyi wanka kisaka na jikinki a shara.
Kafin nan da zuwa yamma zansan abinyi”
Sunkuyar dakai tayi jin maganar yayar tata,kenan har yanzu ta damu da ita kaman da,kawai halin da innarta tasakata ne yasata zama mai kaushin zuciya.
Hanyar inda taga Bombee ta nufah ɗazu tayi domin yin yadda tace ɗin.
“Anty Maryam lfy naga kina riƙe kai,zuwa kusada inna ne yajawo miki hakan?”
“Uhm shine,yanzu ykk ganin za’ayi,kuma banason na kaisu wani wajen daban,saboda gabaɗaya yanzu garinnan ban yarda dashi ba sam”
“Inaga mu ƙira khamees a san abinyi,to mai zai hana mu kama wani gidan inda zasu zauna,nima kinga saina zauna dasu,tunda Kince zan koma barrak na gano mai yake wakana”
“Ahah karki damu ,babu inda kowa zaije anan zaku zauna dukka”
“Hakan ba abune mai yiyuwa ba,ki kulada yanayin dakike ciki mana,idan kika cigaba da tursasawa kanki bakya ganin zasu iya cutar da haidar ko kuma Inna?”
“Sannan ki tsayah kiyi magana da Innayi kiji mai nene dalilinta ma na gudowar,inhar wani abu ake shirin yimusu,bakya ganin na jikinki zasu faɗamusu inda suke?”
“Eh hakan mai yasa banyi tunani nnan ba,shikenan zan faɗawa khamees yasamomin gida a wanda zaku zauna,zaki dunga shiga wajen aiki kina dawowa,innayi zata kulada inna nasan,to amma kuma inason ƙara wani plan ɗin.
Ina buƙatar wanda zai dunga ganemin abinda yake faruwa a gidan Gen abdu manga,har yanzu jikina ya daina bani shi kaɗai yakeyin komai,sannan duk neman danayi banga wani a waje wanda yake taimaka masa ba.
Ɗaurin gindin dayake dashi a shari’ah yasa na fara zargin akwai hannun matarsa akan komai,dan haka in buƙatar mai kawomin bayanan cikin gidansa.”
Ɗariya Hilyaan tayi tareda cewa
“Karki damu da wannan anty maryam,wacce ta dace da wannan aikin ta dawo,yau basai gobe ba zan shaida mata”
“Really ta dawo,ya ta samo wani bayanai gameda ahalinku kuwa?”
“Ahah tace wai wajen gidanmu ma a ƙone yake,da alama bayan munyi gudun ceton rai sun kashe iyayemu sun ƙone gidanmu”
“Am sorry Hilyaan”
“Babu komai anty maryam,nagode Allah dana haɗu dake,ba a iya shugabata nake kallon ki ba,harda yaya kuma ƴar uwa,Hakan kaman matakine na hawa wata rayuwar,na yarda da hakan”
“Shikenan ba komai,amma fah kinaga zata iyah,karfa mu sakata cikin hatsari”
“INAYAH(identical twin sister ta Hilyaan,su kaɗai suka tsira daga harin da aka kaimusu suda iyayensu a Chadi,a garin gudu har suka samu kansu a nigeria Lokacin suna ƴan shekara Sha uku
Inayah tana son wana mutum,sanja kama daga kuka zuwa dariyah,mutumiyar kirki zuwa ta banza.
Yayinda Hilyaan kuma take son zama jami’ar tsaro.
Da tafiya tayi nisa har aka kama inayah a wani Baɗɗa kama da tayi a gidan wani minister,Bombee ce ta taimakawa Hilyaan suka fitar da itah,dagananne ta fara shiryuwa har take abu irinna sauran mutane.
Banda wannan halayya tasu komai nasu iri ɗayane itada ƴar uwarta.),dama a hatsari take,yanzune ta ɗan fita,thanks to you ta shiryu da tadawo hanya”
Tam shikenan bari khamees yazo da yamma zamu tsara komai dashi.
“Nikuma anty maryam wanne aiki zanyimiki”
Maleekah tafaɗa tana ɗaga hannun daga bakin ƙofah,gaba ɗaya basu san tana wajen ba sai yanzu.
Ta tare suka kalli juna,wato taji abinda suke faɗa kenan.

 

 

____****🖤🖤****_____

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

Leave a Reply

Back to top button