Bakar Ayah Book 2 Page 53-54
Page 🖤 53••54🖤
Tun kafin asuba bombee ta tashi,saida ta tabbatar ta gyara Jabeer kafin tashiga banɗaki ta ɗauro alwala.
Nafilfili tayi kafin lokacin da alfijir zai keto,yanzu tana iya yin ibadunta yanda takeso batareda ciwon kai ba,saidai fah halin rashin haƙuri da ƙin ɗaukar raini takula su sun zama a jininta suke.
Tana nan zaune akan sallayah har haske yafara shigowa ta windown ɗakin,tashi tayi ta nufi bakin gadon ta zauna,kaman ko yaushe haka yake a yanda take barshi kullum batareda ya motsaba.
Tsira masa ido tayi ƙyam ko ƙyaftawa batayi,ita kaɗai tasan tunanin datakeyi a cikin zuciyarta,burin a yanzu shine samun lafiyar mijinnata,komai ma idan zaizo daga bayane.
Zamewa tayi ta ɗora kanta akan ƙirjinsa,a haka bacci yasake ɗauketa tana saurare bugun zuciyarsa wanda sai lura take jiyowa a hankali,shikaɗai ne kullum hope ɗinta datake dashi na cewar zai tashi wata rana..
Hayaniyar dataji a ɗakinne yasaka ta farkawa,Hajiyah Zeenah ce da kuma su maleekah,wanda ganin inda ta kwanta yasaka su sosa ƙeya.
Ko a jikinta ta tashi ta nufi banɗaki,sai bayan ta kintsa kana tafito.
Ƙasa ƙasa ta gaisheda Hajiyah Zeenah yayinda itama a takaice ta amsa tareda tambayarta ya mai jikin.
Suna nan zaune suma su inna Danejo suka shigo,saidai wannan karon akwai sabin fuska guda biyu,wato ummaruje da kuma Malam Ahmadu.
Duk da bombee tasan da zuwannasa amma ganinnasa bayan tsawon lokaci saida yabata mamaki..
“Baba”
“Na’am bombee ta ykk ya jikin mijinnaki,naji duk labarin abinda ya faru a wajen innarki da daddare,sannu kinji”
Bombee bata bari ya ƙarisa ba ta faɗa jikinsa,so take tayi kuka amma kuma yanzu ba lokacin kuka bane,dan haka kawai tayi shuru luf a jikinsa,innayi ce itama tazo ta baya ta rungumesu,ita kam tayi ɗan kukanta.
Ƙaramin hannu bombee taji ta bayanta ya rungumeta,dariya tayi tareda juyawa ta ɗagoshi jikinta,ɗan ta farincikinta nata na kanta,wato haidar.
Daga shi tayi sama yana ƙyalƙyala dariyah,banda mamma ba abinda yake faɗa.
“Um boy hadda kai aka zo asibiti?”
Ajiye shi tayi ƙasa tana ƙoƙarin boye farincinkinta na ganin ahalinnata saboda halin da ake ciki.
Abdulmaleek ne wanda ya tsugunna tareda kamo hannun haidar wanda bombee ta ajiyeshi a lokacin.
Kallon hannayensa yake da alama akwai abinda yagani daya tuna masa abu,saidai kuma shigowar Hilyan sai ya katse masa hankali daga kan yaron.
Kallonta yake yana kallon abdulkareem ma wanda shima ita yake kallo kafin ya kalli hilyan ɗin.
A tsawon wannan watannin gabaɗaya da dagula musu lissafi,a rana ɗaya saisu haɗu da ita lokaci guda, a wurare daban da kaya daban,amma kuma idan su suna tare guda ɗaya suke gani,kuma duk saita kallesu tayi musu murmushi.
Sun kasa gane wanne siddabaru takeyi a tsakaninsu.
Kiftawa abdulkareem ido Abdulmaleek yayi kafin yayiwa hilyan alama da ido kan tazo.
Ba musu tabi bayansa zuwa corridorn dayake ɗan nesa da inda ɗakin Jabeer yake.
Suna nan tsaye baicemata komai ba,itama batayi magana ba har abdulkareem ya iso wajen.
“Uhm shin kinsan wannan”
Ƴar dariya hilyan tayi tana kallon Abdulmaleek ɗin,mai yasameshi kuma yake tambayarta wanene ɗan uwansa.
“Aisha magana nake miki kin sanshi?”
“Na sanshi Dr. Abdulkareem ne ɗan uwanka mana”
“Okay to bayanni kina haɗuwa dashi?”
“What akan me zan haɗu dashi,kaima har yanzu ban amince da abinda yake tsakaninmu ba tukunna,saboda bakasan komai akaina ba, nikuma bazan iya faɗamaka ba”
“To amma duk sanda nake tareda ke muna magana sai yacemin shima yana tareda ke”
“Nikuma ohh…..minti ɗaya ina zuwa yanzunnan”
Barin wajen tayi da sauri,can anjima saigata ta janyo hannun Inayah sun taho,tundaga nesa da Inayah tagane mai yake faruwa tafara sunne kai,dan da alama ita take haɗa komai kenan.
“Kayi mistake inaga bani kake nufiba Dr abdulkareem,da alama ƴar uwata kake gani.
Kayi haƙuri ba sunana aisha ba Abdulmaleek.
Sunana Hilyan ita kuma wannan Inayah,mu yan biyune kuma marayu gaba da baya,bamusan kowa anan ba sai anty maryam wacce take tamkar jigonmu,iya wannan zan iya faɗamuku gamedamu mu zamu tafi”
Hannun tahaɗa tana roƙon su afuwa,amma Inayah ko a jikinta,saidai kana gani kasan akwai abinda take boyewa.
“Kince masa sunanki aisha,to amma nima cewa tacemin sunan ta aisha,kuma itace take tareda Ɗan uwana,inna ƙirashi kuma sai yace daga inda yake yana kallonki a wajen matar babban yaya,wani lokacin har hotonki yake turomin daya ɗauka a lokacin. Mu munyi tunanin mace ɗayace takeyin siddabaru”
Juyawa hilyan tayi cikin bacin rai ta kalli Inayah wacce take buya a bayanta.
“Inayah mai kika aikata faɗamin”
“Ohh ni babu abinda na aikata,kawai ranar ne naje shopping anty maryam ta aikeni sai ya ganni,najuya zan tafi sai yace min……..’Am kaman aisha koh wacce take zaune a gidanmu’
Nikuma dana gano ke yake nufi da alama kince sunanki Aisha,sai nace eh itace.
Wannan ne fah kawai”
“To meyasa bazakice bake bace toh?”
“To miye dannace nice ɗin,kema naga ba sunaki Aisha ba ko?”
Murmushi su Abdulmaleek suka tsaya sunayiwa adorable twin ɗin dake sa’insa a gabansu,sun shagala da kallonsu har basaso su daina faɗan.
Abdulkareem ne yayi gyaran murya tareda cewa.
“Yanzudai ke hilyan bakece mai ɗaukar zafi ba nine koh,to na yafe abinda tayimin,dan da alama naga abinda tayin ya sakata nishaɗi sosai,saidai fah bazan yafe dukka ba har sai kin bani dama munyi magana tukunna”
Cuno baki Inayah tayi tareda ɗaga kai.
“Uhm nima anyimin ƙaryar sunan Aisha,dan haka abani damar yin maganar kafin nayafe”
Abdulmaleek shima yafaɗa yana kallon hilyan ta gefen ido,wacce duk kunya takamata sai matse hannun Inayah take dayake cikinnata.
“Ke dallah sakemin hannun zaki karyani,duk salon soyayyar ne haka”
Ta faɗamata daidai kunnenta,amma Abdulmaleek yaji ta duk da tafaɗa a hankali.
“Looovvee is in the air”
Dukka tareda suka juya suna kallon maleekah wacce takeyimusu tafi.
“Sannan kuma ga wani labari dana ji yanzu a gida danaje ɗakko abincin da aka manta.
Baban haneef shida anty Lailah suna nan sun saka iyah a gaba wai saita amince da Abban haneef ya karbi kujerar yah Jabeer,tunda bazai tashi ba”
Dukkansu a tareda suka zaro ido gameda labarin da sukajin.
“Hmmm nima danaji abinda ake faɗa ɗin nayi matuƙar mamaki,kumada alama iyah ta yarda da abinda suke faɗa,a kowanne lokaci zakuji an ƙira family meeting.
Bayan sati biyu dayin aikin Jabeer aka ƙira family meeting domin tattaunawa akan waye zai riƙe Companyn na ɗan wani lokaci.
Duk da cewar babu wanda zaiso Alhj Abdullahi ya karbi Companyn,amma kuma kowa yasan shine yakamata ya hau.
Alhj aliyune ya fara magana tareda cewar.
“To Komai da ake ganin ya faru muƙaddarine daga allah wanda ba’a saka masa rana,Jabeer har yanzu yana kwance a gadon asibiti,sannan kuma likitoci sun tabbatar dacewa koda ya tashi toba lallai ne ya koma yanda yake ba a da.
Dan haka na yanke shawarar zan miƙa kujerar Companyn a hannun…….”
“A dakata haka Abba”
Muryar bombee ce wacce shigowarta kenan ɗakin meeting ɗin.
“A ƙai’dar tsari na riƙon Company,wanda yakeda mafi kason share shine zai karbi shugabancin sa,duk da cewar shine na biyu a kaso na biyu a yawa…..
Alhj Abdullahi bashida lasisin hawa kujerar wannan Company,saboda bincike ya nuna ya daɗe da siyarda da share sa a hannun wasu dasuke son karbar kujerar nan,duk tsawon lokacin da takardun jabu yake aiki”
Kowa kallon bombee yake da mamaki wacce take nuna takardun Alhj Abdullahi a hannunta.
Cigaba tayi da cewar.
“Shugaban Company yana kwance halin jinya,mataimakin sa kuma bashida share ko ɗaya a hannunsa,shin za’a miƙa kujerane ga na waje.
Zuwa yanzu wannan yafara kallon wannan,ciki kuwa harda manyan mutane biyar da aka gayyato wanda sukeda kaso mai yawa suma a cikin Companyn.
Magana suka farayi ƙasa kasa akan kowa nason karbar ragamar Companyn,wasu a cikinsu har sun fara murna da labarin da bombee ta kawo,domin hakan shine babbar damarsu.
Wata harara Lailah taje makawa bombee,yayinda mutanen gidan suke ganin sakarci na abinda bombee tayi.
Faɗa yafara kaurewa a tsakanin mutanen,kowa yana iƙirarin shiya cancanta da wannan kujera,har yazamo hayaniya tafara yawa.
Buga table ɗin bombee tayi,saida kowa yayi shuru kafin tayi gyaran murya.
“Wannan kujerar da kuke magana akan ta ta mijina ce,ƙannensa dukka suna da aikin yinsu,ƙanin mahaifinsa kuma bashida takardun riƙe Company a yanzu. Sannan shi wanda ake ƙoƙarin karbar kujerar sa ai bai mutu ba da ransa.
Dan haka ni matarsa Maryam Ahmad,nayi alƙawarin zan riƙe wannan kujera na tafiyar da ita yanda ya kamata,batareda na bari ta fada hannun wanda bai dace,har zuwa lokacin da mijina zai samu lafiya ya karbi abinsa.
Uhm na manta ma ban faɗamuku ba,barona asibiti a yanzu ya farfaɗo daga doguwar sumar daya shiga.
Saidai likitoci sun tabbatar da cewar komawar sa normal sai a hankali.
Dan haka na ɗaura ɗamarar karemasa matsayinsa da kuma kuladashi,har zuwa lokacin dazai iya aikinsa dakansa.
Abba idan ka amince dabani kujerarsa na kulada ita kasaka hannu akan wannan takardar,nizan koma Wajensa a yanzu”
Tana gama maganar ta tsugunna a wajen da Alhj Aliyu yake zaune ta miƙa masa takardar.
Hannu yasaka ya karbi takardar yana murmushi.
Tashi tayi zata tafi taji yayi magana.
“Keda kike buƙatar saka hannuna meyasa kuma zaki tafi?”
“Abba ba dole sai yanzu zaka saka hannun ba,miƙa ragamar aikin ɗanka a hannuna kana buƙatar yin dogon tunani,zan jira har sai sanda ka amince kafin kasaka hannun”
Jijjiga kai yayi tareda faɗaɗa murmushin sa kana yayi sign a wajen da ake buƙata,mika mata takardar yayi tareda cewar.
“Na yarda dake ɗari bisa ɗari da dukiyarsa da kuma kulada shi,maleekah tana bani labarin duk abinda kike masa,babu abinda zancemiki sai Allah yayi miki albarka kuma yabawa mijinki lafiya kinji”
Kallon dattijon take cikeda shauƙin jin girmansa a idonta.
“Nagode Abba,ina mai tabbatar maka bazakayi nadamar miƙamin amanar dukiyar ɗanka ba”
“Ina fatan hakan”
Tashi tayi ta tsaya,lokaci guda ta sauya yanayin fuskar tata.
“Defuty CEO and directors,ina buƙatar kasancewarku a office 7:00 am na safe,akwai abinda za’a tattauna”
Tana gama faɗin hakan tayi waje da sauri,bata daɗe da fita ba sukaji tashin motarta.
A bakin ɗakin taci karo da doctorn zai shiga.
“Mr Jabeer kin dawo,ɗazu nashiga bakya nan sai nurse kawai na gani”
“Uhm wani urgent abune ya taso,ɗazu kacemin ya tashi amma ni banga wani cigaba ba sosai”
“Bazaki gani a haka ba dama,amma yanzu baya numfashi da inji da kansa yakeyi”
Nurse ɗin da bombee ta buƙata a bata ta suna zaune a gefe guda.
“Sister Haleema shin akwai wani abu da kuka gani gameda shi?”
“Ahah babu komai doctor,saidai kaman yatsansa ya motsa,naga ya motsa daga yanda yake”
Ƙarisawa wajen bombee tayi da sauri tana nazarin abinda suka faɗa.
Kafin wani lokaci ƙanƙani kowa labarin farfaɗowar Jabeer yabaza yan uwa,saidai har yanzu baya motsi sosai,abinma sai yafi bada damuwa fiyeda da.
Da daddare bombee kwana tayi tana nazari gameda aikin da Jabeer yake,in bata gane abuba ta ƙira khaleel ta faɗamasa,dan da farko shi ta cewa ya karbi Companyn amma firr yaƙi ya manna mata.
To yanzunma dai kusan komai shizayyi,tunda ita ga kulada Jabeer.
Kaman koyaushe datayi asuba bata koma ba,zama tayi a bakin gadon tana ƙare masa kallo,alamar motsawa taga idonsa yanayi.
Fitila da ɗakko da sauri ta haska,tabbas hakane ba idonta bane yake mata gizo,fatar idonsa ne suke motsi.
“Mashallah nasan dama zaka tashi bazaka cigaba da barmu muna jira ba koh,ka tashi ka nuna musu,wanda burinsu shine faɗuwarka”
Maganganu tacigaba dayi amma ba amsa.
”Anty Maryam yah khaleel wai yana ƙiran wayarki,shin dagaskene 7:00 za’ayi meeting ɗin?”
Madeenah ce ta tambayeta cikin muryar bacci,ita da maleekah yau a nan suka kwana,tunda ita bombee tana bukatar zuwa aiki.
“Ohh wayar tawa inaga tana silent,kice masa eh yasanardasu nima yanzu zam shirya”
Tana gama faɗin hakan ta shiga banɗaki.
Bayan ta shirya kafin ta tafi saida su maleekah suka sha kashedi,kan ko motsi ɗaya suka gani suƙirata su faɗamata.
Abin harsai da yabasu dariya,itakuwa babu ruwanta.
Bakwai daidai tayi parking a ƙofar Companyn,ga wani baƙin glass data tare fuskarta dashi,wata tafiya take ta kasaita,duk da safiya ce amma kowa ya fito,don kowa yaci abinda aka faɗa na zuwan sabuwar CEO Mr Jabeer,wato Bombee.
Secretary yace tazo da sauri ta karbi jakarta zuwa cikin office ɗin.
A hawa na sha shida yake final floor yake,dan haka saida ta elevator,office ɗin ta nuna mata.
Saida ta ƙarewa ƙofar kallo kafin tashiga.
Mashallah wajene a tsare yasha kayan Alfarma irin na zamani.
Office ɗin Secretary ta wuce ta nufi na shigaban wato na CEO.
Akan table ɗin Ta ajiye mata jakar tareda komawa gefe ta tsayah.
Ƙaremata kallo bombee tayi bayan ta zauna a kujerar tans juyawa.
“Miye sunanki”
“Sunana Fadeela ranki ya daɗe”
“Tun yaushe kike aiki anan”
“Shakera uku kenan,amma nakusa dainawa zanyi aure nan da 6 month inshaallah,amma ƙanina ya cika gurbin aikin zai cigaba da aiki da ogah”
“Good Allah ya taimaka,menene schedule ɗina na yau?”
“Ranki ya daɗe basuda wani yawa,iya gabatar dakene ga directors dakuma Share holders,saikuma sign dazakiyi a takardun sabbin ma’aikatan da aka ɗauka”
“Ohk muje ki kaini meeting room ɗin,takardun dasuke buƙatar sign kuma in zan iya yinsu a gida to ki saka min su a mota kawai,dan ba zama zanyi ba”
“Ba matsala ranki ya daɗe”
Lokacin data shiga ga iya share holder ta gabatar dakan,sukam sauran dama sun ganta.
Daga nan tabar sauran aikin a hannun khaleel ta koma asibiti.
Tun a wajen fitowarta daga mota maleekah ta tareta tana dariya.
“Anty maryam albishirinki”
“Ahah ba goroba barina je nagani da idona,bazan iya bari naji mai zakice ba”
Dana dariya tabi bayanta da gudu har tuntube take.
Turus tayi a bakin ɗakin ganin likitoci a ƙalla uku zaunar dashi sukayi idonsa yana kallon ƙofah,saidai kana kallon idon kasan babu abinda yake gani dashi.
Wasu ƙarafa aka saka suka tareshi,saidai yana motsa hannunsa da kuma ƙafafunsa.
“Doctor yatashi kenan”
Bombee tafaɗa cikin zumuɗi
“Eh ya farka amma kuma har yanzu majority na jikinsa baya respond,hakan yana buƙatar ɗan lokaci,za’a dunga ɗagashi anan kwantarshi,idan hakan ya cigaba zamu baku wheelchair a dunga sakashi a kai”
Bayan kwana uku da farfaɗowarsa an samu cigaba sosai,dan wunin ranar yau bombee yi tayi tana kewayawa dashi cikin asibitin a wheelchair,dan yanzu har buɗe baki yake yana ƙarbar abinsha marar nauyi idan aka kai kusan bakinsa.
Sannan in aka kai haske kusan idonsa yakan ƙoƙarin saida kwayar idonsa akai.
Ganin hakan da akayi ne yasa Alhj Aliyu da kansa yanemi a dawo dashi gida,suma likotocin basu wani damuba,saboda zaman sa cikin mutane zai ƙara saurin samun sauƙinsa sosai.
Tsawon kusan wata guda Jabeer yayi a asibiti kafin aka dawo dashi gida,har sannan Jawaheer da Jaleelah basu fita daga sashensu ba,lubnah kuwa run a ranar daya fita itama tabar gidan.
Gabaɗaya babu wanda yakulada halinda suke ciki,saboda hankalin kowa yana kan jinyar Jabeer ɗin.
Su suke tafa abincinsu suci,kana kuma su gyara gidan tsaff,Hajiyah rabi tun tana zuwa akan Jawaheer tazo su tafi harta daina,yanzu sun fara tunanin ko rashin lafiyar mijinnasune ta taba su.
Sanda aka dawo da Jabeer gida,Hajiyah Zeenah taso akaishi shashenta,amma alhj Aliyu ya nuna mata ƙin amincewarsa,tareda yi mata magana akan tabar matarsa ta kulada shi,dan yanzu kowa yasan abinda Hajiyah Zeenah tayi wajen auro bombee ,shiyasa hatta ƴaƴan ta idan tace ga yanda za’ayi sai kowa yayi shuru kawai.
“Yanzu shikenan duk shirin yatashi a banza kuma haka zamu zuba ido?
Ka duba wannan Jabeer ɗin munyi zaton bazai tashi ba,saigashi kullum lafiya yake samu,kaman duk bakin duniya aka haɗu ana masa fatan tashi”
“Hmm kedai bari ni narasa ma mai zanyi,babu abinda yafi ɗagamin hankali kaman rashin takarduna,da yannzu fah na zama nine shugaba,koda zai dashi daga baya kenan,amma yanzu kiga yanda rishe ya juye da mujiya.
Waccar yarinyar yaishe ma to tasan banida takardu,ko itama wani aikin takeyi a boye?”
“Da alama,ko itace ma tasace takardunnaka ba. Takamar data fito tanayi duk dan Jabeer yana rayene ai,da ya mutu ai kowa yasan kaine mai gadon takardunsa ko kana da naka koda kuma bakada shi,tunda bashida magaji har yanxu.
Kuma dama haka akayi da alhj Aliyu ɗin,inba Jabeer kaine mai karba kujera idan Jabeer bashida magaji.”
“Uhm kuma kinsa nafara wani tunani”
“Irin wanda nakeyi koh?”
“Wanne kikeyi ke”
“Na kawar da Jabeer daga doron ƙasa,ai haka mukayiwa Aliyu ma ka manta,saida yarasa ƙafarsa kafin ka samu matsayin dakake kai a yanzu”
“Eh hakane amma yakike ganin zamuyi da Hajiya rabi wacce mukeson haɗa hannu da ita.
Kimsan dai bazata bari a kashe surukinta ba,musamman datake son ƴar ta haifi ɗa gidannan”
“Abu mai sauƙi saimu sanar da ita cewar Jabeer bazai haihu ba,kuma inka zama shugaban Companyn zaka bawa ɗan ta mataimakinka”
“Eh wannan shawara tayi,an gaisheki mamar haneef,nasarar mu takusa zuwa”
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________