Cinikin Rai Book 2 Page 46
46- Kwana uku kenan da dawowarsu. Da yamma ta shirya ta nufi ɓangaren Ammyn duk da a cikin gidan suke amma ko wani gida da tazara a tsakanin juna. A dawowarsu da Malik, ita kanta tasan zuwa yanzu tayi jiki. Domin tana tafiya tana jin kamar jikinta ya mata nauyi. Kiba tayi shi tun wata biyu da suka wuce, izuwa yanzu kuwa kowa ya ganta yasan tayi kiba ba laifi, sai dai a yadda take jin nauyin jikinta. Cinyoyinta sun fi kome d’aga mata hankali. Lokacin da ta isa falorn Ammyn, zubewa tayi a kujera, tana haki. Kallon Mamaki suka bita da shi. “Mommy baki da lafiya ne?” Lumshe idanunta tayi, tana me girgiza musu kai, alamar A’a, dan tafiyar nan da tayi ya saukar mata kasala da gajiya me tarin yawan gaske. Don haka ta bige da barci. Ita da dazo hira dole aka kyaleta.
Kuma maganar gaskiya, Malik fitinanen mutum ne, duk yadda ta kai ga hakuri da shi, sai ya kureta. Idan yayi farkon dare zuwa tsakiyar dare sai ya kuma yi. Kafin asuba sai ya sake yi bayan asuba ma zai ce Bismillah. Shi da kanshi yau da safe yake gaya mata cewa. “Baby Girl, kina shan wani abu ne?” Girgiza kai tayi tana kwance. “Gaskiya akwai wani abu, domin naji new change’s!” Lumshe idanunta tayi, tana faɗin. “Babu kome kawai dai bana jin dadin jikina ne!”
Haka ya tafi yana zolayanta da cewa, ta gaya mishi yaushe zata dauki babynshi, murmushi tayi kawai, ta cigaba da barcinta. Haka tayi barci har aka kira sallah magariba, kafin ya shigo domin ya shiga gida ya samu tana barci. Ammyn kan hana kowa taba tayi, domin daga kallonta ta gano ciki ne danyen a jikinta. Shi yasa take yanayin gajiya da barci.
“Sannu Ammyn, ya Yaran ina mutumina?” “Ya fita gidansu Hibba!”
“Allah ya dawo da shi lafiya.” Ya faɗa yana kallon Zeeno. “Tayi sallah ma kuwa?” “A’a kasan a wannan tak’in ana dan musu uzuri ne, domin yanayin ba yadda take da ba ne, abinda zan faɗa shine kada a matsa mata, kasan har yanzu bata san ciwon kanta ba, yanzu take ashirin da biyu. Idan Allah ya bude idanu lafiya sai a koma kamar da!” Murmushi yayi yana faɗin. “Ita dai mai albarka, Allah ya sauketa lafiya!”
A hankali ya dauke ta, yana faɗin. “A gaida min su baki ɗaya.” Yadda ya ɗauke yana kallon fuskarta, sai yanzu ya lura da yanayinta da ya sauya. Da barci da take yawan yi idan sun gama kula da junansu.
Ayya ashe cikinshi ne, ko da safe sai da ya mata fadar rashin cin abinci. Ta ce miishi. “Baki na ne ba dad’i, da naci.” Shiru yayi yana faɗin . “Ke albarka ce a gare ni, ke Allah ya albarkace ki, !” Tun kafin ya isa kofar entery din main falorn dinsu, aka bude mishi kofar shi,. Yana shiga suka rufe kofar, yana murmushi har ya wuce da ita dakinnsu. Tunda ya shiga ya kwantar da ita, ya zauna, yana shafa kanta. Tun tana jin abin daga sama, har ta bude idanunta. Riko hannunshi tayi tana faɗin. “Barci bai ishe ni ba.”
“Lokacin sallah ya wuce!” Dakyar ta yunkurin tashi, ta koma tana sauke wani irin wahalallen numfashi. “Ko na d’aga ki ne?” “Hmm!” Ta mike dakyar, kallon yadda take kara barcine. “Ya hakuri ki tashi muje.” Murmushi tayi tana faɗin. “kai na kamar zai fashe. Na gaji wallahi!”
“Sannu kin ji” daga haka ta mike zuwa bandaki yana kallon bom-bom dinta, da suka kara cika bayan. “mazaunan ko?” Share shi tayi tayo alolanta, tana faɗin. “Don Allah Daadi taimaka min da abinci!”
“Ok Madam!” Daga haka ya wuce yana faɗin a ranshi. “Duk wanda ya ce ba zai zama bawan mace ba, yayi karya. Keivroto baki daya tsoron malik Menk Jordan ake, amma yarinyar nan saka ni aiki take.” Ya fada yana shiga kitchen yana murmushi. Hada ya hado abincin ya nufi dakin, ya same ta . Bata idar ba sai ya ajiye ya koma gefe yana jiranta ta gama.
A lokacin da ta idar da sallah, ta koma tana addu’a, shima kuma shafawa yayi yana kallonta. Da sauri ta nufi abincin kamar ta shekara bata ci ba, tana hadiye na bakinta, tana tura wani. Tausayi ta bashi, domin a yadda take ci kamar vata tab’a cin wani abu ba, dole ta karya maka zuciya. Wato haka uwa take fama da ciki, cikinsu Yan uku, ashe jinya ya boye laulayin.
Kafin ya dawo daga duniyar tunani, ta tashi da flat din. Kallonta yayi ya ce mata. “Are you okay?” Gyada kai tayi zufa na karyo mata. Mika mata ruwa yayi ta buɗe, ta sha sosai, sannan tayi gyatsa.
“Bari na kwanta kafin ayi isha!” Riko hannunta yayi yana faɗin. “A’a ki zauna, dai sai ya faɗa mikiko.” Gyada kai tayi ta zauna tare da ku jingina da jikin gadon, kamar jira take ta jingina sai jin ajiyar zuciya take saukewa, barci me nauyi yayi gaba da ita. Zuba mata idanu yayi yana jin wani abu yana ratsa ranshi, tare da jin kamar ya cire zuciyarshi ya bata, wani dadi yake ji, yana kara jin kaunarta yana cike wani kebataccen wurin da ya jima da wawakewa, shafa sajenshi yayi yana kallon agogon hannunshi, saura minti biyar a kira isha, don haka ya kyaleta.
Sai da aka kira sallah, sannan ya tashe ta, shi kuma ya tafi masallaci. Kafin ya dawo ta idar, a daddafe tayi sallah. Ta koma gadon ta kwanta.
Lokacin da ya dawo masallaci, ya samu tayi barci. Wanka ya shiga yayi sannan ya fito ya saka gajeren wando da singlet ya shiga bargon ya kwanta a bayanta.
*Asuba ta gari, Zeemalik*
*** A hankali laulayin cikin ya tasota a gaba, duk da bata amai amma kuma tana ji a jikinta. Domin bata cin abincin sai kwadayin masifa,
Shi kanshi Malik, tausaya mata yake duk da craving din bai bar shi ba, domin kome dare idan ta ji kwadayin ya taso mata, toh ba zaman lafiya sai ya nimo. Karewa da fitina ya kai fitina. Ranar cewa tayi ita lallai ya nimo mata farfesun ganda. A daren ya kira Ammyn ta tambaye ta a ina zai samu farfesun ganda? Shiru tayi kafin ta kira Hafsy, aikuwa aka samu a gidan, ta kuma kiran Malik ta gaya mishi gidan Elbashir zai tafi ya amso, ba tare da bata lokaci ba, yaje ya amso mata. Yana bata ta shaki kamshin ta ce mishi. “Gidan Hafcy ka amso min?” Ta ajiye kwanon. Bata kuma waiwaya ba, ta koma barcinta sai da safe, ya kira Wahida ta amsa musu.
Satinsu uku da dawowa, Nadrah ta kirata a waya, ta mata zagin tsamar miya. Allah yasa Malik din yana nan, kwace wayar yayi domin itama Zeeno ba tayar baya bace kuma ta ce idanunta idanun. Nadrah ta fara gudunta.
Kiran Elbashir yayi ta sa a mishi trace number, kafin wani lokaci an turo a inda suke, daukar motar shi yayi bai dauki kowa ba, ya tafi har gidan Shatima. Ba tare da an bashi izini ba, yar aiki na bude mishi kofar ya shiga, inda Shatima yake zaune sai zare idanu yaƙe. Zama yayi yana faɗin. “dama baka da lafiya ne?”
Shiru ya ratsa falon, kafin ya cigaba da cewa. “ka kira min Nadrah!”
“Ba zan kira maka ita ba, sai me?”
“Ba kome, amma kuma bana son daukar doka a hannu, tsakanina da kai babu kome sai alkhairi, sannan kana cin darajar Mariyah yasa nake dauke kai, daga abinda kuke min, idan da wani ne da tuni ya shafe tarihinku.
Ban san me yasa nake jin a raina na maka uzuri ba, amma nasan har ga Allah kuna cutar dani. Rigimar ta tsaya iya kanmu me yasa sai mun gayyato Yaranmu? Na Kyale ka ne yasa kake wannan tunanin da ba cigaba da farautar rayuwarka, ba mamaki dole ka kyale ni nazo da kafana, kada ka sake na fusata. Domin ba zan maka da kyau. Idan kuma muka sake haduwa. Abinda zai faru ba zai mana kyau ba. Khamis! Kada yarka ta kuma kiran matata, nasan halaccin da kai min, ba zan tab’a mantawa da kai ba, ba zan tab’a yada kai ba, domin ka min adalci da halacci, haka ba yana nufin idan kuka min abu na kyale ku ba. Don haka idan kuma haka ya sake faruwa, sai na baka mamaki!” Yana kai karshen maganar, Nadrah tana fitowa daga dakinta. Razana tayi ta sake wayarta. Takawa yayi har gabanta ya daka mata tsawar da sai da ta kusan faduwa, domin fitsari ta sake a jikinta. “Kada na sake jin ko text messages ki turawa Matata, kada na kuma ganin ko ji wani ya gankin kina me niman tab’a min matata, bari na gaya miki idan layin sadarwan suka ga sakonki. Abin da zai aikata babu me ji ko gani.”
Daga haka ya juya ya fice, kallon yarshi yayi da take kuka. “Ki hada mana kayanmu,mu bar garin nan.”
“Ni ba xan tafi ko ina ba, zan zauna sai naga bayan matarshi.”
“Ki shirya mu tafi, zai kashe ki ne! Tunda ya iya zuwa nan ba tare da yasa an wulakata mu ba, Malik ya shirya yakar mu har sai mun dawo muna rokon shi ya kashe mu. Tunda ya zo da kafarshi yana niman zaman lafiya ne, na bi Malik da sharri babu iyaka, gashi nan Allah ya mai damun abina, don haka kiyi hakuri mu bar garin nan ba zamu kuma dawowa ba. Yayi magana akan halaccin da na mishi wanda kafin nayi mishi, shine ya min har kwanan gobe ina cin halaccinshi. Ba zan iya juyawa alfarman da yayi min ba, gara nayi nesa da shi da haka zan kara samun nutsuwa, da tsira da rayuwata da mutuncina. Na hakura na nisancin rayuwar Malik.”
‘Jin haka yasa baki daya, tsoro ya kamata. A ranta kuwa baza ta tab’a barin garin nan ba, sai ta haɗawa Malik bala’i. Har zai wuce ya ce mata. “kada ki sake tunanin hanyar da zaki cutar da shi. Ke daya kika rage min, idan na sake na rasa ki ba zan yafewa kaina ba, domin ni na kai ki na baro”
Yadda yake mata magana yasa ta hakura da abinda take da niyya, domin kuwa bata taɓa kawowa mahaifinta zai risina ba. Don Malik yazo masa na, sai dai yayi yadda yake so.
—- A bangaren Malik kuwa, da yake gayawa Elbashir tsaki yayi ya ce masa. “Me yasa baka gaya min, na ci uban yarinyar ba. Sam daga Shatima har Lalla Salmah, basu san darajar haihuwa ba, shi yasa suke ganin yaran sun zame musu karfen kafa da zasu na cusa su cikin kowacce badakala.
Allah na tuba ko ina wasa da rayuwata, ba xan yarda Yarana cikin cinikin rai ba, domin ba zan iya kukan da bai da karshe, rayuwa irinsu masifa ce, domin ko sun rasa Yaran basu da kaico. Amma Allah ya kyauta.”
“Yawwa dan gari ka kyauta, ba gashi nan ka bi da Allah ya kyauta ba, ai babu wanda baya kuskure, na dai gaya masa ya jawa yar shi kunne, domin ba zan zuba mishi idanu yarshi tana jangwalo min liki a gidana ba.”
A haka ya kashe wannan rigimar,. Domin kuwa yasan Matarshi a wannan halin da take ciki na laulayi, baya fatan wani abu ya same shi.
Lokacin da ya koma cikin gidan, suke hira yaƙe tambayarta. “Idan kin haihuwa waye kike son a daukota?”
“Ummi Jalilah!” Ta faɗa tana kallonshi. “Hmmm! Ba wata ba?” “Ita dai, nake son zuwanta.”
“Zata mai dake karuwa ne ki fi karfin zariyar wandona.”
Kur ta mishi kafin ta ce mishi. “ba dan tab’a fin karfin zariyar wandonka ba, don haka Boy ka gane ita nake son ta min wanka, domin akwai gyara na musamman da take son ta min tun haihuwar su Hussaini.”
“Hmmm! Tow dai kada a yi abinda zai tsinke min shi, na shiga uku don ba yarda zan yi ba.”
“Sai na ajiye shi, a friji ina kallonshi lokaci zuwa lokaci tunda haka kake son jin magana.”
“Ko daya ba son jin magana nake ba, tausayin tabaryata nake ji, kada ta tsinke wurin cin dad’i.”
“Lallai kuwa, ni kuma turmin nawa ahaka zai zauna ba zai ji wahala ba.” Rike baki yayi yana faɗin. “na shiga 9, haka kike ashe kema?”
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/29, 10:36 PM] Yan Mata: