Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 59

Sponsored Links

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/23, 11:49 AM] +234 816 310 0038: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5️⃣9️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Kusan lokaci daya muka mike zaune muna kallon juna wani ihun
ta sake sakewa wanda yafi na farkon da sauri ya sauka saman gadon yana fadin
innace fa .

   Yana kokarin
laluban riganshi dake gefe a falo ya karasa sakawa lokacin nida ya bari a ciki
tsorone ya kamani nima riga na dauka nasaka nabi bayan shi zuwa waje da sauri.

   Tun daga nisa na
hango inna tana faman nuna wajen da hannu tare da fadin gata nan tazo min a
wani halitta zata zane ni ku taimakeni tana faman nuna wajen kofansu da
hannunta.

    Ahmed ne ya karasa
wajen yana fadin ku jaye nan ya rike hannun uwar shima a kidime yake lokacin ya
fara fadin inna ba kowa wurin nan fa don Allah ki natsu ki daina hakan darene
yanzu.

    Saiga inna na
sambatu tana fadin to to zan bari amma ku rokan min ita don Allah ta rabu dani
tunda ban mata komai ba.

   Inna ba kowa fa
wajen nan killa mafalki kikayi haka kike ganin kamar mutum ne a wurin wallahi
ba mafalki bane itace ta tayar dani daga barci tana fadin in tashi ciwon da
nayi kadan ne bai isheni ba tunda banda tausayi .

   Ina jin hakan a
cikin tsoro don ina ganin kamar abinda take gani din muma zamu ganshine lokacin
nace to inna ki bar fadi kiyi ta addua a bakinki shine makarin bawa.

   To naji zanyi tace
dani kamar wata yarinya karama Aisha za a samu garwashin wuta yanzu gidan nan
Ahmed din ya fada yana kallon kanwar tashi.

    A,a yaya yau bamu
hasa wuta ba a nan na karba da fadin saidai a jona Bonner idan zaiyi tunda
akwai wuta yace a dauko a gwada mu gani.

     Saidai na kaaa
motsawa zuwa dauko abin a dakina sai can ya juyo yana fadin ina abin baki dauko
ba nace wa zai rakani part din mu din
kuje da Aisha mana idan kina jin tsorone.

    Tare muka tafi na
dauko mashi muka jona a dakin sai ya zagaya baya zuwa can ya dawo dauke da
bawan tumfafiya a hannunshi irin wanda ke bushewa a jikin iccen ya dan barbasa
a cikin abin.

    Dakin ya dauki
hayakin maganin daya turara mata din lokaci guda Asmau banda kuka ita da Aisha
babu abinda takeyi lokacina.

   Ita kuma inna din
sai wuri wuri takeyi da idanuwanta kamar me ganin wani abin tsoro a lokacin
gabanta ya rike mata kai yana addua .

   Muna tsaye cirko
cirko muna kallonsu zuwa can mukaji kamar motsin tafiya a wajen gidan muka
kalli juna da Aisha kowa na signal da idanu a tsorace .

   Ya kara mika hannu
ya kara zuba hayakin a wuta kowa dake dakin yaji tsoki kamar a fusace an nufi
baya inda dabbobin gidan suke hanyar makewayin su.

   Sai ga inna din ta
mike shambal a jikin dan nata sai kuma wani barci mai nauyi ya dauketa lokaci
guda haka  bai hanashi karanto mata
adduan da yake karanta mata ba lokacin.

   Ku dan kama min ita
mu kaita a shimfidanta ya fada nida Aisha muka kama kafafuwanta zuwa saman
katifan da take kwana a sama.

    Aka kwantar da ita
saman katifan tana barci sai lokacin muka dan zauna gefen katifan su Aisha din
muna mai kurawa inna din dake kwance idanu.

   Ganin ta samu barci
sosai a lokacin yasashi dago kai ya nisa yana fadin fadin Djje ina ganin inna
gamo tayi tunda har maganin nan yai mata amfani yanzu don bayan iccen tumfafiya
na debo na turara mata.

   A dan firgice Dije
din tace dashi gamo kuma na dauka zafin ciwon ne haka yace bashi bane saidai
idan dama haraswan da gudawan nada nasaba da hakan ne.

   Kowa dakin yayi
shiru karfe uku saura yacewa kowa ya kwanta tunda ta samu barci abari aga
abinda Allah zaiyi zuwa safen kuma.

  Mu zamu kwana da ita
ke nan Aisha tayi saurin tambayan yayan nata a dan rude lokaci guda tana
kallonshi.

   Kai ya girgiza
cikon takaici yace to menene tunda abin ya lafa a yanzu yana da wuya ta tashi
ai kuma ciki wanan daren.

   Saidai mu kwana da
Dije hakan zai danfi muna sauki da a barmu da ita a nan haka yace dama aida
Dije din zaku kwana a nan dakin.

   Ba zance tunda muka
dawo dakin ba ya kara runtsawa har zuwa safe don  ko masallaci da yatafi ban tsanmani ya tsaya
yin addu,a ba ya dawo gida ranan kai tsaye part din su ya nufa yana duba
mahaifiyan nasa wace a dan lokaci guda kamaninta gaba daya ya sauya a yanzu.

    Abin duniya baya
boyowa kafin ace haka labarin ciwon inna ya karade gari musanman unguwar namu
nan mutane suka fara shige da fice a gidan namu wurin gaida ita tare da ba
idonsu abinci su samu na karaswa gaba wurin bada labari.

    Sai da Ahmed ya
fahinci hakan ya dauketa a dakin nasu ya dawo da ita part din mu koda mutane
sun shigo sai ace dasu ai sun tafi wurin magani bata nan don abin ya zama mata
kamar tabin hankali.

  Don saita fara
kokarin cewa zata bada labarin yadda matar tazo mata tace ke dai bari kawai ina
kwanche sai ji nayi an tayar dani ina bude ido naga wata bakar mace da tunda
nake duniya ban taba ganin mutum mai bakinta ba sai ranan.

    Kaiwai tace min
tunda baki da tausayi da jin kai zanyi maganin ki gobe baki kara ganin wani
rayuwa na ciwo kiki tausaya masa kinyi karshen yin hakan a kaina.

  Jin irin maganganun
mahaifiyar nasa da in yana kusa sai ya kwaba mata yasashi shiga wani hali don
bashi kadai ba koni dake tare dasu yanzu hannu a gaba yake da ita.

   Ganin ba shiri ko
banza a tsakanin mu yasa nake kara kama kaina da ita yanzu don sai inga kamar
tana hararata idan na gilma a inda take zaune.

   A rana na biyu da
faruwan hakan na dauki waya da safe na kira ummah ina fada mata abinda ke
faruwa a gidan namu ta tausayawa inna sosai har tayi min fadan ban fada mata da
wuri ba ai ba a haka.

   Sam bansa zatazo
gidan ba don ta kira Ahmed din tayi mai jajen abindake faruwa tare da fatan
samun lafiya gareta.

  Washe gari sai gasu
a gidan namu shine karon farko da har ummah din tazo gidan namu tunda nayi aure
a gidan sai wanan zuwan.

   Duk yadda ake bata
labarin talaucin gidan sam ummah bata ga hakan ba indai muna zaune lafiya hakan
ba komai bane a wurinta don ko yawan maganan da mama kan sake mata a gida
sharewa takeyi bata amsa mata.

  Don su ko yaushe
suna gida tare da mama su kwasa zuwa unguwa ko wani wajen ba zakace sunyi aure
ba a lokacin.

   Mama kance rashin
jin dadi ko rashin samun waje da walwala yasa ban fitowa nima aiko yaushe din
don ina kunyar agani lokacin.

   Ga Aisha da tsohon
ciki a jikinta haihuwa ko yau ko gobe itama Rukaiya din nada ciki saidai baikai
na Aisha din tsufa ba.

   Kamar a mafalki
naji sallaman su ummah din duk da naje gida sau biyu da aurena amma hakan bai
hanani bin jikin ummah ba ina murnan ganin su.

   Haba ki natsu mana
mahmah gaida mara lafiya mukazo fa ummah ta fada min da dan rada sai jin hakan
yasana natsu na kaisu direct dakin da inna din take ciki.

   Ina shiga bata
farga da baki a bayana ba tace yarinyar nan bansan me kika daukeni ba tun dazun
nake jiran abinci shiriritan ki yasa baki gama ba da uwarkice a wanan halin
aiba zaki barta da yunwa ba.

   Sallaman su ummahne
ya katseta ta fara binsu da idanu tana kallon su har suka karaso cikin dakin
suna gaida ita lokacin ne Aisha tace Lah ummah kune tafe ashe inna ga
mahaifiyar matar yayan mu nan tazo gaidake.

   Sannuku da zuwa
ashe kuma kun samu labarin abinda ya sameni din kunzo kedai bari ina tsaka da
barcina saiga matar nan ta shigo min ta tayar dani wai kasheni zatayi.

   Koda yake sunce wai
nabar fadi kingansu nan wai mutane zasu dauka na tabune a hakan don na fadi
gaskiya.

   Tana fara fadin
hakan Aisha ta mike ta fita nima nabi bayanta muka barta dasu tana basu labari
kamar yadda takeyi idan wani ya shigo gaida ita din.

   Hawaye na samu
Aisha nayi tana fadin yanzu matar yaya wanan abinda inna keyi haka za a saka
ido abu sai gaba takeyi kafin na bata amsa Ahmed ya shigo fuskan shi a kan mu
yana fadin .

  Ummah ce tazo da
kanta ashe kin fada matane yana don jiyama ta kirani tana min ya mai jikin ya
fada yana kallona .

  Nace eh jiya na fada
masu inna ba lafiya kada taji daga baya taimin fadan hakan yace hakane yana
kokarin wucewa zuwa dakin .

   Gatacan ta fara
zuba masu ai Aisha ta fada a dan kuntace sai ya nufi dakin da sauri yana
sallama nan ya samesu suka fara gaisawa bayan sun gama gaisuwanne ummah tace
wanan abin sai kun dage da addua sosai a kanshi don kamar bana asibiti bane
kawai ?

  Eh ummah yanzuma
daga can nake na amso rubutu da za a bata tasha da hayaki don sunce ba shiganta
sukayi ba sun dai shafatane kawai don ta tabasu suma sukace.

   Ai abin ke nan
tunda muba ganin su mukeyi ba sai sunyi hakkuri rashin sanine ya kawo hakan
Tani mai aikin ummah ta fada tana kallon inna din dake wuri wuri da idanu tana
sauraren su.

  Kafin tace in na
sani aiba zan tabasu ba ko in takasu har wanan bakar macen na barazan daukan
raina lokaci guda haka.

   Basu jima ba suka
fito na zata zasuje dakine sai naga ba haka ba don suna fitowa suka fara muna
sallama muka rakasu har kofa suka tafi don haka bamu samu maganan komai ba da
ita a lokacin.

   A wurin Aisha yaji
abinda ya faru shigan mu dakin itin fadan da inna ke min a lokacin gaban
mahaifiyata sai ranshi ya baci da hakan har yake fadawa Dije abinda ya kawowa
inna din ciwon ta lokacin.

  Yace irin wanan
halin ne yajawa inna matsala har ta tabo jinnu suke wahalal da ita a yanzu don
malam yace ta nuna rashin imani a garesu ne.

   Ai kaji irinta
lokaci daya yarinyar nan ta canza halaiyarta dana santa dasu a baya wanan yawon
ciranin bai kara Rashida da komai ba wallahi shiko ba abinda ya tsaya mashi a
rai sai tunanen yadda inna din ta nunawa uwargarke a ranan.

  Sai wanan abin ya
tsaya mashi sosai a rai daya je basu abinci ya duka yana gyara mata wuri yana
fadin uwargarke nasan inna ta bata maki rai kin kuma rama amma don ni da yan
uwana ki barta hakan kamar da wasa yai maganan gami da kurciya lokacin tunda
yaji ance dabbobi suna jin maganan mutane..

   Abu kamar wasa
saiga ina ta mike wasai washegari kamar ba ita ba lafiya ya samu tana ta faman
kwasan barci kamar tasha maganin barci yana mata amfani a jiki.

   Alh ban fahinci
wanan sabon halaiyar daka tsiro dasu a yanzu ba matar ta fada cikin kunan rai a
cikin harshen fulatanci.

   Yana a yadda yake
zaune zakace badashi take wanan maganan ba lokacin yadda baiko motsa ba ganin
hakan ya kara bata haushe ta tako zuwa gaban shi ta tsaya tana kara maimaita
abinda ta fada da farko.

  Sai lokacin ya dago
ya kalleta da tun kan ya bude baki yai magana ta hango zallah tsana da masifa a
indon shi abinda bata taba hangowa ba ke nan a zaman su.

  Don tana da tabbacin
cewa duk yadda ta juyashiba nan yake tsayawa ba mussu gareta amma a yan
kwanakin nan abubuwa sai kara bata mamaki yakeyi na sabon halaiyan shi.

   A ranan sai ya koma
mata dangasken shi data sani ba Alh ta ba da take juyawa gabantane ya yanke ta
fadi sosai tasan akwai matsala babba dake shirin faruwa da rayuwanta nan gaba.

  Ke ki fita daga
dakin nan tunkan rayuwan ki yakai ga baci ya fada cikin kakausan harshe gareta
dole tanaji tana gani ta juya zuwa part din ta cike da fargaba a zuciyanta.

   Kallo  takaici ya bita dashi har lokacin data rufo
kofan ya sauke idon shi ga kallon rakiyan dayai mata din na takaici.

    A yanzu yake
nadama da dana sanin tare da tambayan kanshi na hada iri da wa yan nan mutane
marasa kirki a yadda yasan su a baya a yanzu ga zuria sun shiga tsakanin su
dasu haka.

   Ashine tambayan da
yake yawan yiwa kansa lokaci lokaci a yan kwanakin nan gashi ya kula duk wani
dan uwa nasa na jini a yanzu bai tare dasu sai yan tsiraru haka daga cikinsu
din duk halin hjy Yabi ya koresu gareshi.

   Kai ya mayar baya
saman makarin kujera yana mai sauke ajiyan zuciya a hankali ya dan runtse
idanunshi a hankali yayin dayake dan kada kafanshi a hankali.

  A haka barcin ya dan
daukeshi yana wanan tunanen ya kwana biyu da wanan mafalkin sai gashi yayi a
dan barcin daya daukeshi din lokacin.

   Yaron nan daine mai
kama da yasir dinshi duk da bayan shi yake yawan gani lokaci lokaci amma
kamaninshi da danshi yasir yana da yawa ko a hakan da bayan shi yake gani
kawai.

  Zubur ya dan zabura
yana waige waige a falon ta ina zaiga wanan matashin daya shigo mai yanzu yana
maganan akan hakkin shi wani haki nasa zai basane haka wai ?

   Hannu ya yakai a
fuska ya shafo kafin ya tsayar da hannun zuwa goshin shi yana dan murza kadan
kadan tare da tunane a zuciyan shi.

  Inda tunanen nasa ya
tsaya cak ga abokanshi na kurciya dake gida zaune a yanzun cikin halin irin na
rufin asirin bawa duk da yaci ace ya taimakesu a yanzu amma ya kasa hakan a
garesu.

    A hankali ya bude
ido kafin ya mayar ya rufesu a hankali yana mai jin wani irin zafi a ziciyanshi
don ya kasa gane dalilun haka a gareshi bayan yasan irin gudunmawa da suka
bashi a rayuwansu a baya suna yara dashi.

   Yanzu meye abinyi
ya tambayi kanshi a take zuciyarshi ta bashi amsa a wurin da ya nemi dan Jauro donshi
gaba daya cikin su yafisu natsuwa da sanyin hali ga sanin ya kamata.

  Bai karasa tunanen
shiba yaji jauro din yana masa sallama a cikin waya jin haka yasa ya katse
tunanen shi ya amsa masa sallaman shima.

   Ikon Allah yau dan
gaskene da kansa haka ya kirani ko batan layi kayine ya fadamai cikin zolaya
dan murmushim manya ya sake tare da fadin ba bata nayi ba kaidin dai na kira
muyi zumunci.

   Murmushin ya mayar
mashi shima tare da fadin aikuwa nagode gamuma tare da jabbo yanzu haka a kofan
gidanshi jauro ya fada .

   Wani iri yaji a
ranshi kafin yace dasu kai haba dai kuce ni kadai kuka ware dama ina Alamu
yanzu yabar nan zuwa asibiti shima duban yakumbomsu da aka kwantar jiya.

   Idonshi arufe yace
jam balafiyane haka har asibiti yace eh wallahi kasan tsufa da yan ciwarwatan
zamanin nan na yanzu da ba a rasaba.

    Badai kuna lafiya
da iyalin naka ba nan duka ko kuna kasan wajenne yanzu don baku zama a cikin
kasan nan sosai ku ?

   A,a muna nan duk
lafiya suke to madallah Allah abin godiya nagode nagode Allah ya bar zumunci
amin tunda ka tuna damu har munji lafiyanka a yau.

   Don ko jiyan nan
saida Alamu yai maganan ka nace tunda mukaji shiru lafiya kuke don shiru ke
nuna lafiyan mutum.

   Tau lafiyan dai
amma ba lau ba don wani abu ke damuna ya kuma daure min kai sosai a yanzu jauro
shine naga ba wanda ya kamata in nema yaban shawara illa kai  sai gashima kana kusa da Jabbo ashe.

   Jam jam dangaske
meye wanan abin wanda yai zafi haka ya daurema kai kuwa ku manyan kasa daku sai
yai masa murmushi irin nasu.

    Wayance ta dauke
ya barsu suna faman fadin hello hello don sunzaci cewa shiru yai masu yana
jinsu sai daga baya suka gane cewa wayance ta katse ashe.

    Shigowan
yarinyarshi yasa ya kashe wayan yana saurarenta don zancen data zo mai dashi
lokacin wanda tambayanshi takeyi Dad mekayiwa mommy take kuka ?

   Don yaran tashin
falone kai tsaye suke zance da iyayyen nasu saboda gata daso dayai masu yawa a
rayuwa sun tashi basu da kwabo ko kadan.

 Balle su san basuyi
daidai ba gashi uwar kamar itace uba a gidan duk komai na rayuwan gidan itace
ke gudanar dashi .

  Don hakane sukafi
ganin kimarta da uban nasu sosai yanzunma data samu uwar a daki ta gama waya da
yarta ta tambayeta meya sameta shine tace daddysune.

   Bata tsaya jin
meyafaru ba kawai ta juya ta fita zuwa wurin daddyn nasu ta tambayi ba,asi taji
abinda yaiwa mommy din nasu.

  Itama kamar uwar ya
barta da mamajinshi ranan don ya koma mata tankar wani zaki agabanta yadda ya
daka mata tsawan da saidata kadu ta koma tana mashi kallon mamaki lokaci guda.

   Don cewa da tayi
dashi bayan ta fado mai falon a hasale yana zaune yana waya lokacin da abokan
nasa.

   Tace dashi da daddy
mekaiwa mommy mu na samu tana kuka akan ka kuma ban saba ganin hakan gareta ba
sai yau ?

   Ya dago kai cikin
mamaki tare da kashe wayan yace you are very stupid Ni,ima you are more than
stupid da zakizo kina min wanan tambayan haka ba respect a tare dake ?

    Yadsa yake maganan
yasa ta kaduwa don gaba daya ya canzawa sanin ta a ranan ya koma irin mahaifin
da take gani a cikin film ko a wasu gidajen .

   Kofa ya nuna mata
da yatsa alaman ta fita mashi daga falon tayi saurin juyawa zata bar falon yace
dakata daga yau karki sake shigo min falo haka kai tsaye babu sallama
understand ?

  Ta gyada mashi kai
alaman taji ta juya ta fita zuwa part din uwan nasu hankalinta tashe tana
tafiya kamar tababa a lokacin.

Leave a Reply

Back to top button