Furar Danko Book 2 Page 52
‘…..!!
5️⃣2️⃣
……Sosai Smart ya tsinta kansa cikin farin cikin ganin ƴar uwarsa, duk da tana kwance a gadon asibiti hakan bai hanasu yin hira ba. Anan ne take basu labarin halin da Ummah ke ciki a yanzu. Babu ɗigon tausayinta a zukatansu sai Smart kawai, duk da yana jin ɗacin rabashi da matarsa da tayi hakan bai hanashi jin tausayinta ba. Dan ko babu komai tunda ya taso kallon uwa yake mata, sannan jininsa ce ita tunda ƴar uwar Abba ce. Sun jima a asibitin, dan Smart ya gana da doctor sun tattauna, daya buƙaci yanda biyan kuɗi zai kasance sai ya samu Lulu ta biya komai har kuɗin aiki dana gaba ɗaya zaman da zatayi ma a asibitin. Kasa cewa komai yayi har suka dawo gida. Sai dai sun sauke Ahmad a masauki. A falo suka sake zubewa aka ɗaura hira, Iya Tabawa na basu labari suna kwasar dariya. Sun jima a wajen kiran wayar Smart da akayi ne ya sashi miƙewa ya shige bedroom, hakan ya bama Lulu damar bin bayansa bayan wani lokaci. Ta samesa har lokacin yana waya da Usman da ke bashi labarin irin halin ruɗanin da Alh. Sulaiman da abokan cin mushensa suke a ciki. Sai saƙon daya bada aka aika masa ɗin nan. Sosai Smart ke kwasar dariya har yana jin inama yana Nigeria yaga wannan ruɗani a fuskar Alh. Sulaiman. Sai dai babu komai yasan zai gani ta cikin direct camara ɗin da suka sanyama Alh. Sulaiman batare daya sani ba. Bayan sun gama wayar ne yake bama Lulu labari, itama dai dariyar tasha da jin inama tana 9ja ake wannan irin cakwakiya haka.
AA ya tambayeta ta ce ai ya koma kwana wajen Iya Tabawa. Da mamaki yace, “Abincinsa fa?”.
“Wane abinci kuma bayan wanda yake ci ya ƙoshi. Ai ni na yayesa”.
“Yaye a wata goma sha ɗaya? Wane irin rashin tausayine haka Baby luv”.
“Haba kai kam miye abin rashin tausayi anan. Nifa wlhy dama so nake ya taka kawai, yaron da dama ba wani ya damu da shan nonon bane ba.”
“Kin dai so yayesa saboda kina buƙatar wani babyn”.
“Kamar ya?”.
“Kamar yanda kika ji mana”.
Ganin kamar cikin ɗan zafi yay mata maganar ya sata jan bakinta tai shiru. Ita matsalarta da shi kenan saurin fushi. Abu kaɗan bazai fahimcesa ba sai ya hau kamar fulawar burodi, sai idan shi yaso shanyewa ya nuna kamar bai gani ba. Bata yarda ta sake magana ba. Shima sabgar gabansa ya cigaba da yi batare da ya kulata ba. Ganin abin nasa babbane ta fita ta bar masa ɗakin dan bata buƙatar wani ɓacin rai kuma a yanzu….
Bayan kwana biyu da dawowarsa akaima Aunty Bilkisu aiki. Duk halin da ake ciki jama’ar gida sun san komai. Dan haka kowa nata faman addu’ar nasara. Alhamdullah anci nasarar kuwa, dan anyi aiki har an kaita ɗakin hutu, basu sami ganinta a wannan ranar ba sai washe gari da safe. Sunji farin cikin samunta a cikin hayyacinta. A take kowa farin cikin sa ya gagara ɓoyuwa. Fatansu kuma yanzu ALLAH ya bata lafiya. Smart bai sake ma Lulu magana akan yaye AA ba, itama bata sake tayar masa da zancen ba har ya sake barin London ɗin a weekend daya zagayo. Sunje yin wasa, yayinda ita kuma take cigaba da zama tsaye akan al’amarin aunty Bilkisu daketa samun lafiya. Kullum sai sunyi waya dasu Ammah da kuma ƴan gidansu ta video call, musamman ma Ummita da ke tsaye akan al’amarin Nadiya dake a asibiti ita da Uncle Yousuf. Kwanan Smart uku ya dawo, yayinda Ahmad ke shirin komawa Nigeria. Taka tsantsan ta dingayi a ƴan kwanakin nan na ganin saɓani bai shiga tsakaninta da mijinta ba. Alhamdullah kuwa anci nasara, dan banda murzar juna babu abinda sukeyi sai zuwa asibiti wajen aunty Bilkisu da ɗan fita hutawa domin bama kansu farin ciki. Sosai kuma suna samu, dan yanda suka murje tsaff da su, ga tattalin juna da nuna kulawa kowa yasan hankalinsu ya kwanta. Sun kuma samu nutsuwa irin wadda duk wani mai aure ke buƙata a rayuwa. Sai ɗan saɓanin da ba za’a rasa ba na tsakanin harshe da haƙori dake zuwa yau da gobe. Duk yanda Lulu zatayi kuma takanyi na ganin abin baiyi nisa ba ta shawo kan abinta ya huce, shima kuma da yake bason ganinta a damuwa yake ki ɓacin rai ba baya barin abin yay nisa sam…..
*_NIGERIA_*
Alhamdullah an samu nasarar dawowar Ummah dai-dai, nakan dutse ya gama kunce ƙullin daya ƙulla su Salim suka miƙashi hannun ƴan sanda batare da sun saurari bayanin da yake musu akan bafa wai Ummah ta kuɓuta bane ba ɗari bisa ɗari, dolene sauran bala’oin data saka akai mata aiki akan Smart ɗaya bayan ɗaya zasu cigaba da dawo kanta. Sai ta shirya. Babu wanda ya sauraresa, sai yan jarida da suka kafa suka tsare har sai da suka samu cikakken bayani a bakinsa. A take fa al’amarin Umma ya shiga media da duniyar yanar gizo dana kafafen ƴaɗa labarai musamman irin na rediyo. Kafin kace mi mutane da yawa sunji kuma sun sani anata ALLAH wadai da al’amarin nata tare da mata irinta.
Ana wucewa da nakan dutse dole itama Ummahn aka kwasheta zuwa asibiti dan hawan jini ya mata biji-biji. A asibitin ma dai ƴan jarida basu barsu sun huta ba da jama’ar gari ƴan so da jin ƙwaƙwaƙwaf. Musamman ma da ya zam hotunan Ummah sun gama zagaye gari a suffar Dodo, saboda lokacin da nakan dutse ke ƙoƙarin warware asirin mutanen da suka samu shigowa musam yaran maƙwafta ɗauka suka dinga yi a wayoyi suna sakawa a shafukan su na sada zumunta. Dan danan fa sunan Ummah da Hajiya Naqiba yay amsa kuwwa a duniyar labarai da yanar gizo. Dan hatta Hajiya Naqiba basu bari ba sai da suka bibiyi al’amarinta.
(Su Umma an zama celeb…. sai ku tayata murna).
A washe garin da aka wuce da Umma asibiti Smart ya buƙaci su koma gidan daya kama musu domin fara gyara wanda suke a ciki. Kusan dama a shirye suke da hakan, dan haka babu ɓata lokaci suka tattara zuwa can ɗin nan kuma aka bajeshi aka fara aiki bisa tsayawar Coach da manyan yaran gidan duk da Salim ya nuna hassadarsa a fili. (Nonon Ummah ba wasa ba ai).
Suko su Mubarak farin ciki suke abinsu ganin za’a gyara musu gida. Sai addu’a da fatan alkairi suke jerama Smart. Mazansu da matansu haka suka dinga kiransa suna godiya. Duk da wasu sun gagara hakan musamman a mazan saboda baƙin ciki. Dan Mama ita kanta a wannan gaɓar Hassadarta ta gagara ɓuya. Sai da taga Abba na neman birkice mata ne fa ta kama kanta. Sai ƴaƴanta mata da suka nuna mata karfa ta tafka kuskure makamancin na Ummah. Dole ta kama kanta ta koma yaƙe da addu’a a fatar baki. Ƙasan zuciyarta kam kamar zata ƙone, a ganinsu dai ƴaƴansu ne sukafi cancanta da wannan arziƙin.
Ni dai nace, “Hummm”.
__________★
A ɓangaren su Alh. Sulaiman suna tsaka da kukan targaɗe sai ga karaya ta samu. Dan kuwa dai al’amarin Nadiya ma ya bayyana wa duniya. Inda ta tabbatar da cikin jikinta na su Hon. Nakowa ne dan su duka babu da wanda bata mu’amula. Ta kuma tabbatar da cewar su ɗin manyan diloli ne na miyagun kwayoyi, dan ko ita sune suka koya mata shaye-shaye. Ta kuma tabbatar da in har sunce ƙarya ne su fito duniya su musa zancenta ita kuma zata bada manyan hujjoji a kansu. Tace bayan itama akwai yara da yawa da suka lalatama rayuwa ta hanyoyin shaye-shaye da zinace-zinace. Wasu sun jima da rasa ransu, wasu iyayensu sun koresu a gida sun shiga duniya. Wasu kuwa a gidan iyayen nasu ake lalata musu rayuwa batare da iyayen ma sun sani ba. Acewarta Bama su kawai ba, akwai manyan ƙasar da dayawa sukai suna da nisa a irin waɗan nan al’amuran, su suyi ƴaƴansu suyi. Ba kunya Uba da ɗa za’a haɗu a club ko da ƴa anama juna kallon kallo. Akwai wanda ake kaima yara ƙanana gida suyi musu fyaɗe, wasu ma harda maza sukemawa. Ta tabbatar da idan zata tona asirin mutane da yawa akan wannan al’amarin tofa manyan nan da yawansu bazasu sha ba a bisa madafun ikon da suke kai. Dan haka a rufe rufau kawai. Wannan video ya girgiza al’umma da yawa. Yayinda ya bama wasu da ke fuskantar irin raɗaɗin da Nadiya ke a ciki fitowa suma suyi magana. Fiye da yanda ba’a zato al’amari ya sake rincaɓewa. Dan kuwa a ranar kame na hauka jami’an tsaro sukayi, kuma duk yaran su Alh. Sulaiman ɗinne da Nadiya ta dinga lissafowa a faifai. Inda kuma duk akayi dacen kamasu dumu-dumu da abinda ta lissafa ɗin kasancewar dama sai da aka shirya musu talala aka saki video ɗin.
Zuwa yanzu kam su Alh. Sulaiman sun tabbatar da akwai mai musu zagon ƙasar nan. Duk da shi zai iya bugar ƙirji akan babu ruwansa da wata yarinya a cikin garin kwano. Iskancinsa a wajen Nigeria yakeyi sai ko Lagos. Dan budurwarsa ɗaya ce tak a Nigeria kuma a Lagos take zaune. Asalinta ma ba ƴar 9ja ɗin bace shine ya kawota ya ajiye. Sai dai kalmar fyaɗe da akace akwai masu yima yara kam ya girgiza shi, dan abune da anan kam baida tacewa. Dan haka idanunsa suka fara rufewa ya dannama Daddy kira dan ya fara ji a ransa anya Daddyn baida wata rawa da yake takawa a al’amarin nan kuwa. Duk da a yanzu haka ana tsaka da masa bincike akan *_AMM_* ɗin nan da ya aiko masa da takarda da hotuna, har yanzu kuma ya kasa hasaso kowa, ba komai ya jawo haka ba kuma sai kansa dake a birkice…..
★★ Daddy na a gidansa hankali kwance dan kallon wasan su Smart ma yake tare da su twins. Da farko kamar bazai duba mai ma kiran nasa ba sai kuma dai ya ɗauki wayar. Yasha mamakin ganin Alh. Sulaiman Garko. Har ya maida wayar ya ajiye da nufin sharesa sai kuma dai ya ɗaga tare da miƙewa ya shige bedroom ɗinsa.
Cikin wata irin gigitacciyar tsawa Alh. Sulaiman ya ce, “Isma’il mai kake tunanin ka taka ne?!”.
Daddy ya saki murmushi mai sautin da har Alh. Sulaiman na jiyosa. Kansa tsaye babu alamar ɗar a tattare da shi ya amsa masa da faɗin,…….✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
Zafafa
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*