Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 30

Sponsored Links

Nihad ta fito daga wanka bayan ta gama shafe shafenta ta zauna tana tunanin abinda xata sa yau ta kwanta don dama kayan baccin biyu ne kawai ya rage mata kuma duk ta sa su bata wanke ba, ita tunda take ma ta ta6a wanki a rayuwarta banda pant da bra, Husnah tayi mika tana kallonta tace “Ke kuma tunanin me kike haka?” Nihad ta kalleta a sanyaye tace “Toh kayan baccin nawa duka duka biyu ya rage fa a gidan nan gashi nan kuma duk na sanyesu ba a wanke ba” Husnah ta mike zaune tace “Toh ke garin yaya kika zo da kayan bacci kala biyu kawai?” Nihad tace “Ko ba can kauyensu na rabar ba, da tsummokara fa mutanen kauyen ke yawo wallahi” Dariya Husnah tayi tace “Toh kawai ki saka undies dinki sai ki saka hijabi ki kwanta” Nihad tace “Kin ta6a ganin na kwanta haka?” Husnah tace “Yanzu ma dai ina kayan wanki naki yake?” Nihad ta nuna mata inda ta ajiye su har da hijab kala biyu, Husnah ta mike tace “Nasan ko tsutsa xa su yi a nan ba wanke su xa kiyi ba bari in wanke maki su in samu ladanki” Daga haka ta kwashi kayan ta shige bandaki, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta kawai ta saka don dama akwai sanyi sanyi garin alamar hadari, tana ta zaune tana game da wayar Husnah, sai ga Husnah ta fito rike da bucket tace “Can waje zan je in shanyasu ko?” Nihad tace “Ehh ta baya xa ki ga wajen da xakiyi shanyan” Daga sama har kasa Nihad ke kallonta don wani skimpy night wear ne a jikinta, gashi ko bra bata saka ba, Mikewa Nihad tayi tace “Bari kawai in shanya” Husnah tace “Ka ji ki, Aa wllh gwara in cike ladana, da me ya hanaki wankewa balle ki shanya, kawai ni bari in je inyi shanyana” Daga haka ta nufi kofa, Nihad ta kwashe gwangwanin maltina da suka sha da bottle wata ta bi bayanta, Yana zaune parlor hannunsa rike da remote, ga ledan abincin nasa har sannan bai ta6a ba, Husnah sai satan kallon ledan take har sai da ta buge da kujera ta kusa faduwa, da ido ya bi ta, ta nufi kofa da sauri, Nihad dake kallonta har ta fita ita kuma tayi hanyar kitchen taje tayi disposing thrash din hannunta a dustbin sannan ta fito parlo, ta koma kamar xata shiga daki sai kuma ta tsaya bayan 2 seater dake side din tana kallonsa, shi dai idonsa na kan tv, ta yanda xata fara masa tambayar da Umma tace tayi masa kawai take tunani, Ganin bata da alamar barin wajen can dai ya daga kansa ya kalleta yace “Lafiya?” ta jefa masa wani kallo tace “To banda ina son inyi maka tambaya ance maka xan tsaya nan ne” Ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Wa za ki yi ma tambaya?” A takaice tace “Kai” Yace “Ohk, ni za ki yi ma tambaya kenan” Hararansa ta dinga yi wato har wani feeling kanshi yake zata masa tambaya, ya kafeta da ido yace “Yi tambayar ki” Babu yabo babu fallasa tace “Dama baka gaya min sunan gwaggwonka ba a can garin, har da babanka ma duk baka gaya min sunansa ba” Ita kanta tasan she sounds stupid, sai kuma ta fara sosa kai, kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace “Tun a garin baki tambayeni ba sai yanxu da daddare?” A takaice tace “Ehh saboda sai yanxu na tuna” Yana gyada kai yace “Ohk!! To wa ya aikoki ki tambayeni sunan su?” Ta wara ido kamar munafuka tace “Aa fa, ba wanda ya aikoni yace in tambayeka nice kawai na tambayeka ina son sani” Yana kallon kwayar idonta yace “NIHAD” ta kara buda ido a ɗan rikice tace “Na’am” Yace “Sunanta kenan” Lokaci daya ta hade rai tace “Ban gane Nihad ba, sunanta ne sunana?” Yace “Ehh” Ta dinga masa wani mugun kallo, can tace “Toh don baka da kunya sai ka wani kira sunana gatsau wai Nihad, sunan nawa ka raina haka? waye ma ya gaya maka sunana? Aminu me gadi ko???” Khalil bai kuma ce mata komai ba ya bude ledan dake ajiye gabansa ya ciro drink din, dai dai nan Husnah ta shigo parlon ganin lemon a hannunsa wani farin ciki ya mamayeta tana kallon Nihad tace “Ke an fara yayyafi fa, kije ki rufe windows ko” Khalil ya ajiye kwalin lemun hannunsa ya mike ya shiga kitchen xai dauko glass cup, wajen lemon Nihad ta nufa da gudu, Husnah da ke kokarin shiga daki tana ta murmushi ita kadai kamar ance ta juya taga Nihad ta kinkimo lemun ta taho da gudu xata shige daki, cike da zafin nama Husnah ta fixge lemon daga hannunta tace “Meye haka sai kace mayunwaciya Nihad, bai siyo ya baki ba sbda rashin hankali kin wani dauko masa abinda kika fi karfi, me xa ki yi da abin hannunsa, bayan kudin ma kinsan na wanene ya ke ci, a’a wllh kin bani mamaki” Bata jira cewar Nihad ba ta koma da sauri sauri ta ajiye masa lemon ta bar wajen sai gashi ya fito kitchen, tuni Husnah ta figi hannun Nihad ta shige daki da ita ta kulle kofar tace “Wallahi kin bani kunya, me xa kiyi da lemonsa ke da ko ni kika ce in kawo maki carton din lemon can tsaf xan siyo in kawo maki, balle Umma ma kina gaya mata xata bayar a kawo maki har gida? Me ya kai ki? Ke fa har yanxu yarinta na damunki wllh, banda yarinta meye kike abu haka babu class, yanzu na gano dalilin da yasa yayi mugun raina ki” Nihad dai bata ce komai ba, Husnah ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dai dai nan aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya, Husnah ta zaro ido tace “Lahh ga ruwan ya sauko, ki kulle windows din dakunan ni kuma bari inje in kulle na parlor” Daga haka ta fice da sauri zuwa parlor, Nihad ta bi ta da kallo sai kuma ta bi bayanta, farin ciki bai kara lullube Husnah ba sai da tagansa rike da lemon a glass yana sha, ta kasa daina murmushi ta tafi ta kulle windown parlon ta shiga ma kitchen ma ta kulle sannan ta fito tana kallonsa tace “Sai da safe” Bata damu da ta ji ya amsa ba ta nufi daki tana jijjige inda ya kamata a jikinta, Tana kallon Nihad dake bakin kofa tace “Wai duk kika ga na fito sai ki biyoni” Nihad tace “Aa ni kitchen xan tafi ne” Husnah bata ce mata komai ba ta shige daki, Nihad ta shiga kitchen ita kanta tasan babu abinda xata yi a kitchen din bayan ta gama zagaye zagayenta ta fito ta nufi dakinta, da ido khalil ya bi ta har ta shiga dakin, makulli ta saka ta zare makullin, Husnah dake kwance tana danna waya tace “Kamar da wasa fa sai ga ruwa ko ba komai garin yayi sanyi naturally ayi bacci me dadi” Nihad dai bata ce komai n a ta hau saman gado daga daya side din ta jawo pillon ta jefa makulli a ciki Husnah dai na ta kallonta da gefen ido, Husnah ta mike zaune tana kallonta tace “I want to take malt but gaskiya baxan iya shanye daya ba, idan na rage maki xa ki sha ai ko?” Nihad ta girgiza kai tace “Aa na koshi” a hankali Husnah tace “Toh shikenan, bari in bari kawai kar ayi asaran sa” Nihad tace “Ki sha ki rage ki ajiye mana” Husnah tace “Aa ni kinsan bana son almubazzaranci ke kuma dama kin iya walakanta abinci, da dai kuna da fridge ne sai in je in ajiye sauran amma idan aka bar shi haka ai lalacewa xai yi, ba fa wai da yawa xan rage ba ni nasan gejin cika na, kadan zan rage wllh” Nihad tace “Wa yace maki malt na lalacewa??” Husnah tace “Ke dai tunda baxa ki sha sauran ba shikenan sai in hakura in kwanta da craving dina” Nihad tace “Ni wallahi ban ta6a jin inda malt ya lalace ba sai a bakin ki, ki sha kawai ki rage yayi ta lalacewan mana” Husnah bata kuma cewa komai ba ta kwanta, bayan kusan 10 mins ta mike zaune tana kallon agogo dake nuna karfe goma da rabi ta jawo malt daya kawai ta bude ta fara sha, kallon Nihad tayi ganin kamar ta fara bacci ta tasheta, Nihad ta bude ido a hankali Husnah tace “Wai kin daina alwala ne idan xaki kwanta?” Nihad na lullumshe ido tace “Zan yi” Husnah tace “Aa tashi kije kiyi gaskiya kafin bacci me nauyi ya dauke ki” Sai da ta tashi Nihad kusan sau uku sannan Nihad ta tashi da kyar duk da tunda ta xo gidan nan bata ta6a alwala idan xata kwanta ba amma dabi’arta ce yin hakan tun bayan da taje tayi wani hutu wajen Aunty Jamila na sati uku, Aunty Jamila bata ta6a barin ta kwanta bata yi alwala ba, kuma bayan ta dawo gida kawai training din ya zama jikinta, in dai xata kwanta sai tayi alwala wani lkcn Umma tayi ta mata fada idan taga tayi tace so take sanyi ya shiga jikinta, Nihad na shiga bandakin Husnah ta jawo jakarta da sauri ta bude wani abun maye ta zuba kusan quarter a cikin ɗan malt din ta rage sannan tayi saurin mayar da shi cikin jaka ta ajiye jakar, har ta dauko pillown Nihad xata cire makulli sai kuma ta fasa ta mayar da sauri, Nihad ta fito daga bandakin bayan tayi alwalan ta nufi inda xata kwanta Husnah tace “Don girman Allah ki shanye guntun malt din nan saura kadan, ta6a ki ji” Nihad ta girgiza kai tace “Aa baxan sha ba kawai ki ajiye” Husnah ta dinga kallonta sai kuma tace “Ohhh sai yanxu ma na gane, wai kyankyami yasa baki son ki sha kamar warce ta zuba na bakinta a ciki?” Nihad ta kalleta tace “Ni nace maki haka?” Husnah tace “Aa haka ne mana, banda haka meye don na sha malt na rage maki ki ki shi Nihad?” Nihad tace “Ke dai kin san yanda xa ki bi ki juya magana, ni na gaya maki haka? Ko daxu da kika dau ruwana kika sha gani kika yi na zubar?” Husnah ta mika mata gwangwanin tace “Ni dai gashi babu yawa ki sha don bana son Allah ya kamani da walakanci da abinci” Nihad tace “Wai ba daxu kika ga na dau malt na sha ba salon inyi ta tashi cikin dare fitsari” Tsaki Nihad ta ja ta amshi gwangwanin hannun Husnah ta kwankwade lokaci daya ta ajiye gwangwanin, Husnah sai kallonta take tayi wani Murmushi, Nihad ta kalleta, da sauri Husnah ta dauke kai ta lulluba da duvet tana cewa “Ki kashe mana wutan sai da safe” Nihad na yamutse fuska tace “It has a different taste” Husnah tace “Aa hajiya sai dai bakinki ne” Nihad na kallonta tace “Amma tsakaninki da Allah babu abinda kika zuba a malt din nan Husnah, ni na sha gaya maki bana son irin abubuwan nan kuna forcing dina sai na sha, dama shi yasa kika dage sai na sha?” Dariya kawai Husnah tayi tace “Oho dai, ko ba komai yau xaki yi bacci me dadi brain dinki yayi relax, habaa” Daga haka Husnah ta shige duvet, Nihad ta dinga mata wani irin kallo, can ta ja tsaki ta yi kwanciyarta, she wish ta gano abinda Husnah xata mata kenan da baxata sha malt din ba ko me xai faru, ko minti goma ba ayi ba Nihad ta bingire da wani nannauyan bacci, Husnah ta juya tana kallonta tana Murmushi, har sannan kuma ruwa ake kamar da bakin kwarya. Sha daya dai dai Husnah ta cire duvet din jikinta, ta sauka daga kan gadon, ta zaga ta inda Nihad take bacci kamar warce tayi tseren awa biyu, janye pillon kanta tayi ta ciro makullin ciki sannan ta ajiye pillown nan gefenta ta bude jakarta tayi shafe shafen da xata yi sannan ta nufi kofa, bude kofar tayi a hankali ta fita, taga duk an kashe wutan gidan, tana lalubawa ta nufi dakinsa, murda kofar dakin tayi slowly ta bude, she saw him kneeling a kusa da gadonsa ya daura kansa saman gadon wearing just his trousers, ta shigo dakin da sauri ta kulle kofar da makulli tace “Subhanallahi, me ya faru? Lafiyarka kuwa?” Lkci daya ya dago da fierce eyes yana kallonta, tayi kasa da murya ta karasa kusa da shi ta durkusa gabansa tana kallon broad chest dinsa tace “Ko dai baka da lafiya ne?” Bata jira me zai ce ba don she was more than Randy a moment din, ta kai hannu chest dinsa, lkci daya cikin dubara tayi loosening din igiyar rigarta, rungumesa tayi gam murya can kasa tace “Ka gaya min me ya sameka….” rufe idonsa yayi sai kuma ya bude da sauri, da duk karfinsa yayi karfin halin hankadata gefe har sai da ta fadi, sai kuma ya mike cikin husky voice dinsa yace “Me ya kawo ki dakin nan?” Daga sama har kasa take kallonsa, dariya ma ya bata, a wannan yanayin da take kallonsa daga sama har kasa har yake da karfin halin tambayarta me ya kawota dakinsa, wani er dariyar bariki tayi, tasan yau TBD straight up, cike da kissa ta cire rigar jikinta ta jefar nan gefensa tana masa wani shu’umin kallo da lumsassun idanuwa, kauda kai yayi cikin zafin nama ya nufi belt dinsa dake saman jaka bata ankaraba sai jin saukan belt tayi a jikinta, gigicewa tayi saboda azaba, ya dinga zabga mata belt din iya karfinsa, ihu take tana jin kamar ranta ake zarewa sbda azaban belt, ta dinga neman yanda xata kubuta daga hannunsa ta ihu a gigice, duk inda ta yi haka ya dinga bin ta yana sauke mata belt din duk inda ya samu a jikinta, a wannan daren Husnah ta ga jalala, kawai ta sa ma ranta karshen rayuwarta ne ya zo, tun tana rokonsa da muryarta har muryar nata ya daina fitowa, dukanta yake iya karfinsa da belt kamar an aikosa, ga shi ta garkame kofar dakin balle ta fita, har bandaki ta shiga ya bi ta yana duka daga karshe ta fito da rarrafe, dukan da yake mata ya sa shi jin saukin axaban da yake ji a lkcn, sai da ya gaji don kansa bayan yaga yayi mata lilis sannan ya jefar da belt din after 30mins kenan, nan ya bude kofar dakin yana sauke numfashi, tsabar yanda ta jibgu ga kofa a bude amma ta kasa motsawa daga inda take balle ta fita, ya nufota ya kalla mata wani wawan mari har sau biyu a fuska ya dau shegiyar rigar baccinta ya hada da ita yana janta ya fito da ita parlor yayi wani hajijiya da ita sannan ya cillar da ita da rigar ya koma dakinsa, gudun kar ya sake dawowa ya sa ta karfin halim rarrafawa da kyar ta nufi kitchen, gaba daya jikinta shatin belt ne rudu rudu ga bakinta sai zuban jini yake, idonta daya kuwa ya kulle, tana shiga kitchen din hannunta na rawa da strength dinta na karshe ta saka makulli kafin ta fada kasa rigijib. Tun Khalil na daurewa yana cijewa, daga nan ya koma can, daga can ya mirgina ya koma nan kamar me labor har dai yaji he is going to harm himself, he couldn’t bear it anymore, Mikewa yayi kamar wanda aka tsikara ya fice daga dakin, tsaye yayi corridor ya hade kansa da bango corridon, yana ta tsaye a haka for almost 5 mins sai kuma ya kalli kofar dakin Nihad, murda kofar yayi amma bai bude ba, can ya runtse ido ya sa kafa ya tura kofar staggering inside the room, ya manna hannunsa jikin switch din dakin yana sauke numfashi, standing there for another 2 mins kafin ya kunna wutan dakin a hankali, tana saman gado ta dukunkune can saman jikinta da hijab daga kasan waist dinta har ƙafafuwanta kuma babu wani obstacle sai na lingerie dinta and she is sleeping heavily, hade kai yayi da bango ya rufe ido yana sauke breathing dinsa a hankali, can ya bude idanuwansa da suka yi jajir, ya kashe wutan dakin ya nufi kan gadon, gefenta ya fada yayi rub da ciki, perceiving her scent all over, da yayi attempting kai hannunsa jikinta sai wasu abubuwa suka dinga fado masa a xuciya, and all of a sudden ya janye hannunsa ya zamo kasa a hankalii ya daura kansa gefen gadon, yana ta durkushe a hakan har kusan karfe biyun dare, zuwa sannan yayyafi kawai ake ruwan ya tsagaita… Da kyar Nihad ta bude idonta ta dalilin fitsari da take ji, ana ta kiraye kirayen sallahn asuba ta sauko daga saman gadon tana layi xata bandaki, gaba daya jikinta is so weak, tutunbe ta ji ta ci da mutum a kasa lkci daya kuma ta fada kansa, wani ihu ta fasa a mugun tsorace tana tattabasa amma lkci daya hankalinta ya ɗan kwanta jin kamshin turarensa, zamewa tayi ta sauka daga jikinsa ta zauna gefe tana kallonsa cikin duhun don jikinsa taji xafi kamar me, nan da nan mugun baccin da ke idonta ya washe gaba daya, da sauri ta mike ta tafi ta kunna switch din dakin, kwance ta gansa nan kasan tiles ko riga babu a jikinsa, ya bude jajayen idonsa, ta dawo ta duka gabansa tana kallonsa, bata san sanda tace “Baka da lafiya ne?” Bai ce mata komai ba yayi karfin halin mikewa zaune, ta koma baya bata kara ce masa komai ba, Mikewa tsaye yayi taga yana layi kamar wanda ya sha ya bugu, ta tashi tsaye da sauri kafin tace komai yayi baya zai fadi, xaro ido tayi ta jawosa ita a dole xata tarosa, amma ya rinjayeta sai ga su a kasa, ta zaro ido cike da azaba tace “Wayyo bayana” Cike da karfin hali ya dagata ya fada gefenta can underneath his breathe ba tare da yasan ya fada ba yace “Sorry” daga haka ya kulle idonsa, ta mike zaune tana kallonsa sosai jikinsa yayi zafi, bubbuga gado ta shiga yi da sauri tana cewa “Husnah, Husnah ki tashi” Amma jin shiru ta daga kai taga wayam babu Husnah a dakin, mikewa tayi da sauri ta fita parlor nan ma ta dudduba bata ga Husnah ba, kamar xata yi kuka tace “Toh ina ta tafi?” Sai kuma ta marairaice tace “Toh ni ya zan yi yanzu?” Juyowa tayi da sauri ta dawo dakin ta durkusa gabansa tana kallonsa, sai kuma tace “Toh Abba xan kira da wayarka?” Ya bude jajayen idonsa da sauri yace “Aa” Tashi tayi ta kara fita parlor dai dai nan taji kamar ana bude kofar kitchen, tsorata tayi tayi hanyar daki da sauri tana lekan kofar kitchen din, sai ga Husnah baki ya kumbura suntummm lebbenta ya koma kamar na rakumi, ga fuskarta yayi jajir kamar nama, jini kuma ya kwanta a idonta daya, dayan idon kuwa ya manne, kayan baccinta ne a jikinta, Nihad ta dafe kirji a tsorace tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Husnah what happened” Husnah na dingishi da kyar tace “Aljanun dare” Nihad ta jingina da bango a mugun tsorace tana zaro ido tace “Aljanun dare kuma?” Husnah ta gyada kai da kyar tace “Akwaisu a gidan nan wllh, Dauko min jakata da hijabi na” Nihad da hankalinta yayi mugun tashi tace “Ganinsu kika yi?” Husnah na sauke numfashi tace “Nace ki dauko min jakata da hijabi” Nihad taki motsawa daga inda take saboda tsoro, Husnah tayi zaman dirshan a kasa ta rasa inda xata sa ranta ta ji dadi, gaba daya shatin belt din jikinta yayi jajir gasu rudu rudu, Nihad dake ta kallonta a mugun tsorace tace “Husnah kalli jikinki fa” A fusace Husnah tace “Ki dauko min jakata da hijabi nace” Nihad ta juya ta koma daki da sauri bata ga Khalil kwance inda ta bar sa ba, cikin second biyar ta fixgo hijabi, jaka da wayar Husnah ta fito da gudu daga dakin, Husnah na ganinta ta mike ko ina na jikinta na rawa ta amshe jakarta da hijab da waya, bayan ta saka hijab din ta nufi kofa da sauri, Nihad ta fashe da kuka tace “Tafiya za kiyi ki barni Husnah?” Ko tsayawa Husnah bata yi ba balle ta juyo ta saurari Nihad tuni ta bude kofar parlon ta fice da sauri ta saka takalminta luckily taga lock kawai aka sa ma gate din babu key ta bude ta fice daga gidan. Nihad ta koma dakin Khalil da gudu ta kulle kofar, kan darduma ta gansa sallan ma ya kasa tashi tsaye, ta durkusa nan kusa da gado tana kallonsa kana ganin idonta kasan ta tsorata sosai, har ya idar taga ya fada kan darduman ya kwanta ya kulle ido, ita dai tana ta zaune maganar Husnah na mata yawo a kai, can ta mike a hankali ta nufi bandakinsa, a bude ta bar kofar, bayan ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito da sauri… Tana idar da sallah ta juya tana kallonsa, tashi tayi ta koma inda yake ta duka hucin zafi take ji a jikinsa, ta dinga kallonsa, a hankali ya bude idanuwansa jin ta a gefensa, ta 6ata fuska tace “Toh kuma kace kar in kira Abba” Wayarsa da ta hango gefen gado ta kai hannu ta dauka, yayi karfin halin kwace wayar a hannunta ya lumshe ido, tagumi tayi tana kallonsa, a hankali tace “Toh ni ya zan yi?” Tana ta zaune gefensa har gari ya waye gaba daya, tun da ya amshe wayarsa a hannunta bai sake bude idonsa ba, duk da baccin da take ji amma bata yi ba tana gefensa a zaune, lkci daya taga ya yunkura ya mike zaune, ta zaro ido ta koma baya tace “Amai zaka yi” Ya sunkuyar da kansa bayan few minutes ya koma ya kwanta ya kulle ido, a hankali ta kai hannu forehead dinsa taji har sannan da xafi, ya bude ido yana kallonta, tace “Toh safiya yayi yanzu ka bani wayar in kira Abbana” murya can kasa taji yace “Dauko takarda da biro” Tace “Takarda da biro kuma??” Jin bai ce komai ba ta mike har ta nufi kofa sai ga ta ta dawo da gudu ta tsugunna kusa da shi kamar xata yi kuka tace “Wallahi Husnah tace min akwai Aljanun dare a gidan nan, duk sun mata duka bakinta ya canxa yayi wani iri”

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, kiyi subscription ki karanta cikin salama er uwa!!!!

Ur evidence via👇🏻

07087865788✍🏻

 

 

Assalamu alaikum manyan mata!!

For your Egyptian Abaya’s, mad gowns, laces and handbags and all sort of jewelries… Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰

Message via👇🏻
https://wa.me/c/2349090591769

To view our catalogue🥰

Leave a Reply

Back to top button