Furar Danko Book 2 Page 59
‘…..!!
5️⃣9️⃣
………Tana gama sakin videon da mintuna kaɗan Abdull na isowa asibitin shi da Asma’u. Da gudu tazo ta rungume Lulu cike da farin cikin ganinta. Basu wani ɓata lokaci ba suka shiga motar da Abdull ɗin ya tuƙo. Kai tsaye gidan da su Ammah ke zaune a yanzu kafin a kammala nasu da saura ƙiris suka nufa. Nan ɗin ma gida ne babba wadatacce da suke zaune babu takura. Duk zumuɗin ganin Ammahn da takeyi sai kuma ta ɓige da jin kunyarta. Ammah dake mata dariya ta rungumeta a jikinta tana mai farin cikin ganinta. Harga ALLAH ita tana jin Lulu a cikin ranta tamkar ƴar da ta haifa bawai suruka ba. Bata bari ta zauna ba sai da sukaje ta gaida Abba. Shima yayi farin cikin ganinta yana ta sanya mata albarka da mata ƙorafin rashin zuwa da AA bayan ya tambayeta jikin Dada. Duk da anan ɗin ma dai ya mata ƙorafin rashin faɗa musu da basuyi ba sai jiya suke sani. Haƙuri ta bama Abban da tabbatar masa suma basu sani ba sai da ga baya. Ta ɗan jima a wajen Abba suna hira sama-sama duk da ita duk a kunyace take kafin suka dawo ɗakin Ammah. Mama tayi ƙarfin halin zuwa mata sannu da zuwa kamar yanda taga aunty Amarya tayi. Bata nuna musu komai ba duk da dai taso taga idon Ummah, amma Asma’u ta sanar mata ai tana gidan yayanta ne sai an gama gini zata koma can da zama, sai dai Abba ya mata saki uku ma. Ko a jikin Lulu, sai ma zama data gyara tana shan kunun gyaɗa datace tana so Ammah da kanta ta dama mata. Dan a kallo ɗaya ta fahimci Lulu na ɗauke da ƙaramin ciki. Murnar kasancewa da su Ammah dan Maryam ma babu jimawa ta dawo daga makaranta ya mantar da ita wani batun Alh. Sulaiman. Sai dai tayi kiran Aunty Naja’atu ta tambayi ko Dada ta farka. Ta sanar mata bata farka ba ance sai bayan la’asar. Dan haka ta sake miƙe ƙafa har sai bayan la’asar ɗinne suka fito harda su Ammah da zasu je duba Dada. Sai a lokacin sukaji halin da garin Kanon ke a ciki. Abdull da Mubarak dake bibiyar komai suka shiga basu labari. Kwaɓarsu Ammah ta shiga ƙoƙarin fara yi wai saboda Lulu, amma sai sukaji lulun na ƴar dariya da faɗin, “Ammah barsu su bamu musha. Indai wannan ne baida maraba da wanda ban haɗa komai da shi ba a duniyar nan, dan inda akwai wanda ya tsanesa to nice farko kuwa.”
Shiru kowa ya kasa cewa komai a motar har suka iso asibitin dan furucin Lulun ya girgiza zukatansu…..
_________★
Ba jama’ar gari ba, hatta jami’an tsaron duk sun ɗauka Alh. Sulaiman ya kashe kansa ne. Hatta Smart da ke kallon komai ta can wani irin rumtse idanu yay da dunƙule hannaye ya kaima iska naushi da faɗin, “Ohhhh Shiittttt!!!!”.
Wahalalliyar ƙarar da Alh. Sulaiman ya sakice ta saka kowa ɗagowa da sauri. Dai-dai Alhaji Sulaiman na kaiwa ƙasa durƙushe akan gwiyawunsa bindigar hannunsa na faɗuwa ƙasa itama ya dafe hannun damarsa dana haggu dai-dai inda ƙwararrren maharbin jami’in ya sakar masa bullet. Kowa kallonsa ya maida akan jami’in, shiko ko’a jikinsa sai ma hura bakin bindigarsa da yay da baki ya turata cikin aljihun wandonsa yana ƙarasowa gaban Tsule. Wani irin fisgar hannuwan nasa duk biyu yay zuwa baya batare daya damu da jinin dake ɓulala a hannun Alh. Sulaiman ɗin da bullet ya ratsa ba balle jin tausayin maɗoɗowar azabar da yake yi ya saka masa handcuffs. Sai a lokacin mutane suka farga da ashe bai kashe kan nasa ba jam’in yay nasarar harbinsa a hannun bindigar ta faɗi.
Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama jiƙe Alh. Sulaiman. A haka aka taso ƙeyarsa zuwa wajen airport ɗin yayi wujiga-wujiga. Da ƴan uwansa ya fara tozali tsaye reras su huɗu mahaifinsu a tsakkiya cikon na biyar. Kallo ɗaya dayay musu bai sake marmarin ƙarawa ba saboda irin wutar bala’in da ya hanga a fuskokin nasu musamman ma autansu na maza dake wani irin huci kamar kumurcin maciji Uncle Taheer. A karo na farko yaji wasu irin hawaye sun sakko masa masu zafi da ɗaci. Babu zato babu tsammani yaji saukar wani irin gigitaccen mari maisa a gano ƙyallin kabari har saida ya durƙushe ƙasa. Bai gama dawowa a hayyacinsa ba aka sake sauke masa wani. Ba kowa bane da wannan aikin face auta da Uncle Amin. Har sai da sauran ƴan uwansa Uncle Muneer da Uncle Khamil suka rirriƙesu. A hankali Baba Garko ya ƙaraso gabansa hannunsa riƙe da ƙyaƙyƙyawar sandarsa ya zuba masa idanu na wasu sakkani. Sai kuma cikin ƙarfin hali ya saki murmushi mai ciwo. Cike da dattakon nan nasa yasa sandarsa ya ɗago haɓar Alh. Sulaiman da bai gama dawowa daga gigitar marin da yasha hannun ƙannesa na uku dana huɗu ba. Muryarsa da ɗaci sosai yace, “Sulaiman bazan maka baki ba. Sai dai ina baƙin ciki da takaicin saka maka suna mai daraja da kima irin wannan. Sannan ina jin raɗaɗin kasancewar ka jinina. Sai dai bazanma UBANGIJI butulci ba, domin ya bani huɗu gasu nan duk na ƙwarai, tare da biyu mata da basa raye duk da kaine kai sanadin mutuwar Sultana. Sulaiman kai ba mutum bane shaiɗani ne, dabbane tunda har zaka iya haikema ƙanwarka ƴar shekara tara kacal da lafiya bata isa ba. Kaiconka Sulaiman ka tabbatar asararre a wannan duniyar wlhy. Gashi nan kazo a banza zaka koma a wofi dan bana maka fatan shiriya harka koma ga ALLAH. Yau ina kuɗin daka tara ta hanyar haramun ɗin? Ina damar da kake ganin kanada ita ta lafiya da rayuwa da dukiya? Ka lalata dubban al’umma ta hanyar miyagun kwayoyi, kasa iyaye da yawa kuka! Kasa mataye da yawa kuka! Kasa mazaje da yawa kuka! Ina zaka da hakkin waɗan nan bayin ALLAH koda basu furta maka ALLAH ya isa ba. Kaiconka Sulaiman, wlhy bana fatan wani ya yafe maka akan wannan al’amarin koda mutum ɗaya ne. Kaje in dai duniya ce gaka nan a cikin tarkonta, ka gama wahala a cikinta kaje ka fiskanci hukuncin UBANGIJI kuma. Da ga yanzu na haramta maka sake amfani da sunana kona zuri’ata har bada”. Daga haka ya juya yana sharar hawaye. Yaransa dake bin Sulaiman da mummunan kallo suka take masa baya.
Wani irin durƙushewa Alh. Sulaiman yayi a wajen ya ɓarke da kuka. Dan kalaman makaifin nasu sunyi masifar shigarsa shiga mai tsanani da ƙarfi a cikin jini da ɓarko ta yanda baiyi zato ko tsammani ba. Da ƙyar jami’an tsaron suka iya ɗagashi aka jefa a cikin mota….
*_3 DAYS LATER_*
A yanzu kam babu wani latest topic dake yawo a media da gari sama dana Alh. Sulaiman. Hatta maganganun da Baba Garko ya faɗa masa da marin da ƙannensa sukai masa sai yawo suke a social media. Hakama ɓoyayyen Companyn sa na magunguna sai da aka gayyaci ƴan jaridu sannan akai masa filla-filla. Baba Garko da ƴan uwansa sunje har Companyn suma. Sosai hankalinsu ya sake tashi saboda ganin ɗunbin aika-aikar da jinin nasu ya jima yanayi batare da sun farga ba. Harda jarirai a wajen da ake gwada magani a jikinsu kafin a fitar, wasu sukan mutu wasu su kamu da ciwuka al’amarin zattashin hankali dai. Ƴaƴansa kam kuka har suna rasa hawaye. Dan biyu da ga ciki harda saki mazajensu sukai musu.
Duk yanda Baba Garko ke ƙoƙarin danne komai ya cigaba da zama ba komai ba hakan ya gagara. Dan kuwa dai sai da takaisa kwanciya a gadon asibiti. Yayinda aka samu ita kuma Dada ta maro. Sai dai bata iya dogon magana sai kuka da jama Sulaiman kalaman ALLAH ya isa da faɗin, “Nayi dana sani ni Hajarah, dama Mawaddat tasha faɗa min Sulaiman na lalata yaran masu aiki kuma nima na sani amma son zuciya da son ƴaƴa ya hanani ɗaukar makaki sai da akaima Sultana fyaɗe. Ashe na rigada na makara tun a wancan lokacin, ashe shine ya wulakanta min mutuncin yarinya ya halaka min ita. Yarinyar da ko cikakkiyar lafiya bata da shi. Kaicona ni Hajara kaicona da irin son zuciyata. Gashi nan takaini ta baroni a gaɓar da bazan iya komai ba na dawo da baya balle na gyara. Wane irin abin kunya ne wannan da tozarci. ALLAH ya tsine maka Sulaiman. ALLAH ya ƙuntata rayuwarka tun daga nan duniya. Wlhy bazan yafe maka ba. Inama ɓarin cikinka nayi ko mutuwa naima gaba ɗaya a lokacin haihuwarka. Dama kin cemin zanyi nadama mara amfani idan ban gyara ba, kin faɗamin banji ba Mawaddat,, ban saurareki ba, da ace na saurareki da banga wannan mummunar ranar ba a rayuwata. Inama na mutu kafin zuwan wannan ranar. ALLAH ya isa Sulaiman…..” ta sake fashewa da kuka. Lallashinta aketayi akan ta daina tsine masa da muguwar addu’ar nan. Amma ina Dada idonta a rufe yake. Babu abinda take hangowa sai Sultana kwance cikin jini, yarinyar da har aka kaita makwancinta jini bai daina fita a jikinta ba. Haka aka sakata a kabarinta likafaninta duk jini.
Lokacin da Lulu dake kwana a wajen Ammah yanzu ta shigo Dada ta riƙota jikinta tana kuka. Itama sai Lulun ta kama kuka. Da ƙyar Uncle Khamil ya janye Lulu da ga jikin Dada saboda aman jinin data fara. Dama Doctor ya sanar musu zuciyarta ta taɓu sosai sai abinda ALLAH yayi kawai. Hankalin kowa ya sake tashi, dan Baba Garko ma hanawa akai a faɗa masa……….✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*
Zafafa
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*