Hausa NovelsSakayyah Book 2 Complete

Sakayyah Book 2 Page 9

Sponsored Links

 

                             By

Related Articles

            *GARKUWAR
FULANI**SAKAYYAH book 2… page 9*

 

          Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*

 

 

Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin
gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin.
Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya,
melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba,
domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi
al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin
wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma
saduwa, da dai sauran abubudann ban
lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman
kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari
kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin
kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi
bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta
lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwatanta
Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk
tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki
nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA
BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke
miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a
wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna
GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji
sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta
gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai
kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic
infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara,
Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar
komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin
infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar
infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin
set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na
shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in
akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita
tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki,
idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman
ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku
kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa
ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan
kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU
GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276
sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki,
gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi
daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu.
Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai
kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

Shiru Hajja Nana tayi kafin ahankali ta ɗago ta kallesu ɗaya
bayan ɗaya  tace.

“Shikenan ni babu abinda zance acikin wannan al’amari zira
ido da kunne nawa duk abinda yaje ya dawo Khausar ita tajawa kanta”.

Ƙwaffa tayi kana ta cigaba da cewa.

“Tunda kuma iyayenta kuce kun amince, to ni dai babu abinda
zance bare inyi baƙin jini”.

Kallon Baffa Jimeta daya sunkuyar da kai ƙasa tayi taɓe baki
tayi kana tace.

“Yo ni me zai da meni tunda uban daya haifi Aliyu bai damuba
yanuna ayi mata yanda take so ai shikenan, tunda bata illar tsintacciyar mage
bata mage ba, ɗan da ba’asan Asalinsa ba ba’a san tushensa ba duk abinda ya
faru ita tajawa kanta”.

 

Anutse Lamiɗo ya ɗago kansa ya kalli Hajja Nana cikin sauri
yace.

“Insha Allahu ma babu abinda zai faru sai Al’khairi”.

Abba kuwa karɓan maganar yayi ta hanyar cewa.

“Insha Allah Moddibo zai riƙe ta da amana da gaskiya da
Izinin Ubangiji Khausar ba zata tozarta ba yanda Khausar ta amince tayi niyyar
cikawa Jameelu na wasiyyar sa”.

Ahankali Khausar dake can cikin ɗaki ta lumshe Idanunta
zuciyarta na bugawa da Masifaffen ƙarfi.

Cikin sanyin murya Abba ya cigaba da cewa.

“Insha Allahu Ubangiji bazai tozarta taba Allah zai cika
mata burikanta na rayuwa insha Allah zata kasance cikin kwanciyar hankali da
nutsuwa”.

 

Kallonsa Hajja Nana tayi kana ta jinjina kai tace.

“Haka kake gani kk? Hmm ta yaro kyau take bata ƙarko, kai
yanzu Alh Bashir tunda kuke kasan asalin yaron ne?”.

Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa ƙasa batare da yace Uffan
ba.

Ƙwaffa tayi kana tace.

“Hmm ka buɗe baki kai tsaye kace baka sani ba shine magana”.

Kallonta ta mayar kan Malam Arɗo tace.

“Malam kai da suke aiki a ƙarƙashin ka kasan Asalinsa?,
kasan waye Ubansa? Kasan inane Ƙasar da suka fito kasan inane Jaharsu? kasan
menene tushensa? Waye ubansa waye Uwarsa?”.

Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe kana ya kalleta Anutse
yace.

“Ai a al’amarin Aure wannan duka ba magana bane”.

Kai ta girgiza cikin tsira masa ido tace.

“Yanzu ina magana da Malam Liman zai miƙe yace min Allah
yace Annabi yace amma ai Aure abin bincike ne ko”.

Cikin sanyin murya Lamiɗo yace.

“Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri wannan tone-tonen basu da
Amfani”.

Baki ta taɓe tare da Kallonsa kana tace.

“Eh basu da amfani Ni tunda dai aka samu antsira ba ɗan
Mayun bane zata aura, aishikenan sai inzira mata ido ni naɗan ji sauƙi ma akan
abin”.

Kallon ƙannenta tayi kana tace.

“Yo ai gaskiya ne na fada da kuka wani tsareni da ido, kuma
dole idan gaskiya ta taso a faɗeta da ace ta auri ɗan mayu jikan Mayu ai gwara ɗan
shegen tunda taji ta gani tana so ta bone dai tayiwa ƴaƴanta da ahalinta”.

 

Kai Baffa Liman ya girgiza tare da sunkuyar da kansa ƙasa
cike da takaici Hajja Nana ta cigaba da cewa.

“Tunda ta yiwa kanta tabo ita tasani amma Ni dai babu ba
kina babu hannu na babu ƙafana na suje can su ƙarata sanda ƴaƴanta zasu ce ina
dangin Ubansu ta nemi abin faɗa musu”.

 Ahankali Mommy da
Lamiɗo suka sunkuyar da kansu ƙasa Khausar kuwa hannunta riƙe da kofin madaran
da bata shaba bata ajiye ba ɗumin na ratsa tafin hannunta ta tsirawa waje ɗaya
ido ba ƙeftawa.

 

Ajiyar zuciya Malam Liman ya sauƙe tare da girgiza kai kana
cike da ladabi da nutsuwa yace.

“Dan Allah Addah Nana ya za’ayi ana kitse gaba kina warware
baya dan Allah wasu furucin ki riƙa sanin abinda zaki riƙa faɗa saboda Manzon
Allah (SAW)

_Falyaƙun Khairan Auliyastumu”_.

 

Baki ta taɓe kana tace.

“Naji naji Liman aini zuwa yanzu ko ƙwaƙwalwar kifi ne dani
yaci ace in haddace Hadisai sama da dubu tunda duk motsin da nayi sai kace min
ga abinda Allah da Manzonsa suka faɗa”.

Sunkuyar da kai Malam Liman yayi cikin taɓe baki ta cigaba
da cewa.

“Ni dai na faɗa ba bakina ba hannu na babu ƙafana kuje duk
abinda kuka ga ya dace kuyi. Kai kuma”.

Ta nuna Baffa Jimeta da kansa ke ƙasa kana tace.

“Tunda kaine madadin Uba agareta kace kaji ka gani ko?
Sannan kaima”. Ta nuna Lamiɗo daya ɗago kansa cikin haɗe girar sama da na kasa
tace.

“Kai kuma kaine wakili kuma Uba data tashi agabansa kai kace
kaji ka gani ai shikenan na cire bakina aciki amma dan Usmanu na baya raye
bazan bari jinjinsa ya cuta ba”.

 

Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauke kana yace.

“Insha Allahu ma ba zata cutuba da izinin Ubangiji zai riƙe
ta da Amana”.

Baki ta taɓe cike da takaici ta juya cikin ɗaki.

Takalli Khausar da har zuwa lokacin hannunta ke riƙe da
kofin madaran Harara ta watsa mata kana tace.

“Ke kam kinyi asara gaki mace har Mace Bafulatana tsayayyar
mace Kyakkyawa zubin zamani ƙirar masu tsada amma ace wai ke zaki buɗe baki
kice kina son Namiji”.

Cikin sauri Khausar ta ɗago kai ta kalleta.

Harara Hajja Nana ta watsa mata kana tace.

“Ki ɗauke wannan tsayayyun idanun naki akaina Ke zakice kina
sonsa wanda baisan dake bama sannan baice yana sonki ba bai damu dake ba wai
kice kina sonsa shi zaki Aura”.

Fuska Khausar ta ɓata kana ta kawar da kanta gefe tare da
murguɗa mata baki  da Ido Mommy tayi mata
alamar kar tayi magana.

Tsuke bakinta tayi tare da kawar da kanta gefe, jin lokacin
sallar La’asar yayi yasa duk mazan suka miƙe suka tafi masallaci.

 

Bayan sun daeone suna isa afarfajiyar gida suka zauna Anutse
Abba ya gyara zamansa tare da fuskantar su da kyau kana yace.

“Toh Alhamdulillah yanzu dai Kamar mun samawa tufkar hanci
amma kuma dai Babban abu da yake tafe damu acikin al’amarin”.

Ya sauke ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.

“Ayi ƙoƙari ayi abin cikin ƙanƙanin lokaci in Allah ya yarda
ya lamunce mana komai abune mai sauƙi agaremu inhar kuma kun shirya”.

Jinjina kai Baffa Jimeta yayi kana yace.

“Bakomai in dai wannan ne mu ba matsala awajenmu tunda abin
yazo na wasiyya kuma dama a wasiyyar sa ya roƙa ayi cikin gaggawa sannan ya faɗa
ya kara cewa yaron nan yana ɓuƙatar aure”.

Jinjina kai Abba da Malam Arɗo sukayi alokaci ɗaya.

Cike da kamala Baffa Jimeta ya cigaba da cewa.

“Tunda har ya fadi haka to yakamata ayi ƙoƙari ayi abinda ya
kamata ni awajena Insha Allah ba matsala tunda dama zan kwana biyu saboda zan
samu inji da tsohuwar kasan fatanmu da Adduarmu Allah yasa mu rabu dasu
lafiya”.

Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.

“Hakane ƙwarai fatanmu da addu’ar mu rabasu da lafiya domin
shi yafi al’khairi”.

Murmushi Baffa Jimeta yayi kana yace.

“Toh shine nake so in Zauna da ita Ni nan awajena duk abinda
ake buƙata wanda uba zaiyiwa ɗiyarsa Insha Allah bazai gagara ba komai Ashirye
muke Insha Allah”.

 

Cikin sauri Lamiɗo ya Girgiza kai kana yace.

“A’a Alh Muhammadu ai wannan hurumi nane don Allah dan
Annabi kada kuyi min haka Khausar ɗiyace awajena tun tana wata uku nake tare da
ita bata da bambanci da ɗiyan cikina inaji tamkar Ni na haifeta”.

 

Kallonsa Baffa Jimeta yayi cike da kamala yace.

“Anya Lamiɗo za ayi haka kuwa abar maka ɗawainiya?”.

Kai Lamiɗo ya Girgiza cike da dattako yace.

“Haba dai wace irin ɗawainiya kuma?,Meye aciki ai babu wani ɗawainiya
acikin al’amarin nan”.

Numfashi Abba ya fesar kana ya fuskance su da kyau yace.

“Ni duka wannan aikin ma na ɓangaren Khausar da Moddibo
zanso abarmin domin burin Jameeluna ne ni kungama yimin komai da kuka lamince
zaku wanzar da wasiyyar sa bayan rayuwarsa”.

Jinjina kai sukayi kana ya cigaba da cewa.

“kungama yimin komai babu abinda zan iya yi muku tukuici
dashi sai dai kubarni inyi dukkan abinda ya dace na fannin Auren nan”.

Murmushi Malam Arɗo yayi kana yace.

“Masha Allah wannan Auren yazo da al’barka Ubangiji Allah
yasanya al’khairi”.

Zama Malam Liman ya gyara tare da faɗin.

“Muma kanmu duk al’amarin Khausar hakkinmu ne mu sauƙe”.

 

Cikin sanyin murya Abba ya kallesu kana yace.

“Ni dai dan Allah na nemi alfarma abarmin wannan aikin
nayi”.

Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe kana yace.

“To ai ba laifi duk zamuyi buƙatun ƴa mace suna da yawa”.

Jinjina kai Lamiɗo yayi kana yace.

“Ni dai nafi so abarmin komai na fannin Khausar”.

Dariya Malam Arɗo yayi idanunsa akan su yace.

“Lallai dai kam wannan ai sai dai ɗakuna uku za aware mata
irin wannan lissafin.

Kai Abba ya gyaɗa kana yace.

“Insha Allah wannan duk bazai gagara ba da ɗakuna da kuma
duk abinda za’a buƙata zanyi”.

Numfashi Baffa Jimeta ya fesar kana yace.

“Allah ya temaka nima insha Allah nan da mako ɗaya zan
koma”.

 

Jinjina kai Abba yayi kana ya gyara zamansa cike da farin
ciki yace.

“Ai shi kansa Aliyu ma yanzu haka yana can ƙasar Marocco
yana kulamin da ayyukan Company na to Auren ma bazata muke son yi masa”.

Murmushi sukayi jin sigar da Abba yayi magana Cike da farin
ciki Abba ya cigaba da cewa.

“Idan yaso bayan an ɗaura auren da kaina zan Kai masa
matarsa da izinin Ubangiji sai dai yaga mata dan yanzu ya tafi yana rayuwa shi
kaɗai wasu sabbin damuwa zai sake sawa ranshi”.

 

Cikin sauƙe numfashi Malam Arɗo yace.

“Toh Alhamdulillah gamu da gishiri da goro na tambayar mu na
forko muka zo,”.

Sai kuma duk suka juyo suka kalli Malam Liman sayi gyaran
murya tare fuskantarsu da kyau cikin kamala da dottaku yace.

“Tunda ga yanayin yadda abin ya kasance, mu shammaci Adda
Nana, domin bata da alƙibila yanzu tace ta yarda zuwa anjima zata iya cewa ta
fasa, don haka mu ɗaura auren nan yanzu-yanzu ana da goron da kuka kawo in dai
akwai sadaki a hannunsu tunda ga waliyan yaro ga kuma nata waliyan”.

Ya ƙare mgnar tare da yin ƙasa da murya gudun kada Hajja
Nana taji mgnar.

Cikin tsanananin mamaki da farin ciki mara misaltawa Abba
Jameel yasa hannunshi cikin aljihunsa jiki na rawa ya zaro sabbin kuɗin yar
dubu dubu wanda ya dauko dan yin hisani. Bandir ɗaya ya ajiye a tsakiyarsu
wanda har jikinsa na rawa dan farin ciki yace.

“Gashi ina nemawa Aliyu Youseep Muhammad Mouley auren
Khausar bisa sadaki dubu ɗari”.

Da sauri Bappa Jimeta ya gyara zamanshi tare da cewa.

“Na bawa Aliyu Youseep Muhammad Mouley auren ƴata Fatima
Usman Abubakar Leewal bisa sadaki dubu ɗari.”

Cikin tsananin jin daɗin wannan al’amari da yazo musu da
sauƙin aka ɗauka Auren Khausar da Modibbo a yau Litinin a cikin rugar Jauro
yaya bisa shaidu Lamiɗo, Malam Arɗo, Malam Liman, da sauran ƙananan Hajja Nana
baki ɗaya.

Bayan sun gama gudanar da ɗaurin auren kamar yadda shari’ar
Muslunci ta tsara.

Cike da gamsuwa haɗin da tsananin jin daɗin ɗaurin auren
Baffa Jimeta yace.

“Toh ba matsala Insha Allah duk abinda ake ciki zan gayawa
Hajja Nana kuma zan taushi zuciyarta”.

Sai kuma duk suka juyo suka kalli Hajja Nana dake fitowa
daga cikin rumfarta tana mai cewa.

“Uhmmm ta yara kyau take bata ƙarko, ai duk abinda kuke cewa
dayi ina jinku badai kun ɗaya aurenba, toh ai hikenan maji magani”.

Cikin Sauri suka kuma kalli juna, ayi mace kunne kamar na
maciji duk ƙantar sauti sai taji.

Sai kuma suka maida kallonsu kam Malam Liman dake cewa.

“Toh kisanya albarka kawai”.

Kai ta gyaɗa cike da takaici tace.

“Hmmm Allah ya sanya al’khairi Allah yasa yadda muka ɗauki
mgnar marigayi da mahimmanci shima Modibbo a ɗauki mgnar da gsky”.

Bata jira cewarsu ba kuma ta juya cikin ɗakin,

Ida ta zubawa Khausar da tun lokacin da taji Hajja Nana
nacewa badai kun ɗaura aurenba ta daskare a zaune, yayinda Mommy mgnar ta daki
zuciyarta, dan batayi zaton abin da gaggawa haka ba. Sai kuma duk suka kalli
Hajja Nana dake cewa.

“Wlh kinyi asarar ƙuruciyarki da kyanki ji yadda aka ɗaura
aurenki kamar na bazawara mara gata”.

Zuwa yanzu Khausar kam bazata iya fahimtar kalaman Hajja
Nana ba bare ta bata amsa. Ita kanta Mommy abin ya sata tafiya dogon nazari.

 

A can waje kuma

Anutse Lamiɗo ya gyara zama kana yace.

“Toh Alhamdulillah dama kwanan ake batun auren Amina nanda kwana
goma, tunda an  auren Khausar za’a haɗa
bikin ayishi lokaci ɗaya, kana akai ko wacce gidan mijinta”.

Kusan a tare duk sukace.

“Allah ya kaimu lokacin”.

Amin Ya amsa tare daci gaba da cewa.

“Insha Allah zuwa gobe ko jibi Insha Allah zan dawo in muyi
magana mahaifiyar yarinya”.

Nan dai suka gaba da tsastsara duk yadda abin zai kasance.

 

Sai Misalin ƙarfe biyar suka bar Jauro yaya ahanya sukayi
sallar maghariba sai gab Isha’i suka isa gida.

Kasancewar ranan girkin Hajiya Bunayya ne yasa kai tsaye
Mommy ta wuce Sashen ta tare da Khausar wacce take tafiya tamkar kazar da ƙwai
ya fashewa, domin jin kanta take tamkar wacce aka rufe da ɗanyen fatan rago,
wasu abubuwa na musamman ne ke yawo a jiki da zuciyarta ita kanta ta rasa
yanayin da take ciki, kawai dai ta tsinci kanta da rayuwa da Modibbo a cikin
zuciyata tun lokacin da taji wai an ɗaura aurensu.

 

Suna shiga kai tsaye ɗalibta ta wuce, duk da tsalle da
Raudat keyi na ganinta ta gaza yi mata mgn.

Sai Mommy ce data ruggume Raudat ɗin.

 

Ita kuwa Khausar a hankali ta faɗa bisa gafonta, tare da
rumtse idanunta da karfi.

Sai kuma ta buɗesu ganin fuskar Modibbo a ranar da sukayi
robuwar ƙarshe jujjuya idonta tayi kamar yadda tayi mishi a lokacin, sai kuma
ta lumshesu jin wasu tafasassun hawaye dake kwaranyo mata ba ƙaƙƙautawa.

Kamar a Film haka yanayin da suke rayuwa dashi a makaranta
ya fara dawo mata, one by one, har zuwa ranar da suka kasance a mota, haka nan
taji wani murmushin da batasan manufarsaba ya kumce mata, wanda kuma ya korowa
hawayen da bata san ya kubce mata da kukaba.

Sai kuma ta saki sassayyan kuka jin Mommy ta zauna kusa da
ita tana mai cewa.

“Toh kuma kukan me kikeyi Fatima”.

Ta ƙare mgnar da kiran asalin sunanta wanda bata cika
kiranta da shiba.

Ita kuwa Khausar cikin ci gaba da sassayan kukan tace.

“Mommy kinaji fa wai sun ɗaura auren”.

Jawota jikinta Mommy da hawaye zubomata tayi tare da ɗaura
kanta bisa cinyarta tana mai danne kukanta tace.

“Ba komai Mamana kiyi shiru, ai ba yau za’a tafi da keba ki
share hawayenki, addu’arta bazata bari ki muzantaba a gidan aurenki”.

Ta ƙare mgnar tana share mata hawaye, daga nan taci gaba
tausarta da kwantar mata da hankali dan ta lura gaba ɗaya ta ɗimauce abin ya
daki zuciyarta ya kauda nitsuwarta.

 

Washegari Da safe Kai tsaye Bedroom din Mommy Lamiɗo ya shiga
tare da yi mata bayanin duk yanda sukayi a Jauro yaya bayan sun dawo Sallar
La’asar da batun auren da suka dauran.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe cikin sanyi ta ɗago kai tare da
kallon Lamiɗo kana tace.

“Toh yanzu har an ɗaura Auren kuma ba jan lokacin asan yaron
yana sonta, sannan kuma ace   za ayi
bikin cikin ƙankanin lokaci haka?”.

Ta ƙare mgnar cije da rauni.

Jinjina kai Abba yayi yana kallon yanayinta yace.

“Toh me za ajira Aysha ai abune na wasiyya kuma akwai damar
yi sannan Already Khausar ta gama Secondary kawai tayi Aurenta tunda Alh Bashir
yace a Marocco zasu zauna kinga shida kanshi yace zai kaita wurin mijinta”.

Kallonsa kawai Mommy keyi sabida tama rasa abincewa.

Ahankali Abba ya cigaba da cewa.

“Saboda ya lura yaron bayan son zaman nan sannan yana so
yabar masa ragamar Company ahannunsa kinga idan sunje can sai ta cigaba da
karatunta acan tunda dama yanayin makarantar su akwai cikekkiyar larabci kinga
zata iya karatu a can, ta kuma yi zaman aurenta cikin aminci”.

Sunkuyar da kai Mommy tayi tana wasa da yatsun hannunta
yayinda tausayin yarta yasa hawaye cika mata idanu A hankali tace.

“Kuma ba wanda ta sani a canfa, ya zatayi”.

Abba ya cigaba da cewa.

“Kada ki damu, ɗan naji Abban Jameel yace in Malam Ahmad ya
yarda da rakiyar Ummin Jameel da Asma’u zasuje, ga kuma Hajia Bunayyah itama
zan biya mata su kaita tare”.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.

“Hmmm abin ne naga kamar anyi sa da gaggawa Khausar fa
yarinya ce, wlh tsoron yaronan ne fal zuciyarta jiya kwana tayi batayi
bacciba”.

Murmushi Lamiɗo yayi tare da riƙe tafin hannunta acikin nasa
yace.

“A ba wani yarinta aciki ai
Insha Allah komai zai tafi dai-dai zakiyi alfari da Aurenta da Moddibo
ke lokacin da aka aurar dake ai bakima kaita shekaruba, mijinta kuma bar
tunanin tana tsoronshi a a bata sonshi ke dai ku zuba ido zakusha mamakin yadda
al’amarin zai kance in dai Khausar ta ɗauke ki ai kiyi shiru kawai yaro zayi
mubaya’a”.

Ya ƙare mgnar da cikin sigar wasa da son kwantar mata da
hankali.

Kai ta gyaɗa kana cikin sanyi tace.

“Allah yasa”.

Amin yace tare da miƙewa ya fita.

 

Acan ɓangaren Ummi kuwa bayan Sallar Azahar bayan Malam
Ahmad ya dawo daga gidan Abba ya zayyanewa Ummi duk yanda Abba ya faɗa masa.

Ajiyar zuciya mai nauyi Ummi ta sauƙe tare da fesar da
numfashi cikin tsananin jin daɗin kana tace.

“Alhamdulillah yau dai
burin Jameeluna ya cika sannan wasiyyar daya bari ta kasance kai baki daɗin
wannan al’amarin”.

Jinjina kai Malam Ahmad yayi cike da farin ciki yace.

“insha Allah”.

Numfashi Ummi ta fesar kana tace.

“Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kaimu lokacin
tafiyar, shiru zanyi bazan gayawa Asma’u ba tukun sai naga yadda Khausar ɗin ta
nufeta da mgnar”.

Ameen ya amsa kana ya fice.

 

Ahankali Asma’u ta fito daga Bedroom tare da kallon Ummi
kana tace.

“Ummi wai maganar me naji kuna yi kamar batun Aure?”.

Kai Ummi ta jinjina da alamun farin ciki afuskarta tace.

 “Hmmm”. Sai kuma tayi
shiru, ita kuwa Asma’u cikin son tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyemata
cike da kaɗuwa tace.

“Dan Allah Ummi ki gaya min na tuba”.

Cikin tsanananin jin dadin ɗaya kasa biya a saman fuskarta
tace.

“Eh maganar Auren Moddibo mukeyi”.

Zare ido Asma’u tayi kana tace.

“Ummi Yaya Moddibo zaiyi Aurene?”.

Jinjina kai Ummi tayi tana kallonta tace.

“Eh yanayi Aure dai”.

Murmushi Asma’u tayi cike da farin ciki tace.

“Ummi Wacece matar?”.

Ummi na murmushi tace.

“Aminiyar kice matar”.

Asma’u kuwa cike da matsanancin mamaki da al’ajabi ta zare
Idanunta waje kana tace.

“Khausar!?”.

Kai Ummi ta jinjina tare da faɗin.

“Tabbas kuwa da izinin Ubangiji Itace”.

Tafa hannu tayi tare da buga still da Mamaki da kuma
al’ajabi tace.

_“Lahailah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)”_ Yah
Moddibo da Khausar.

Kallon yanda ta zare ido da sallami Ummi tayi kana tace.

“Haƙƙun kuwa dan tuni an ɗaurama”.

Dafe kunci Asma’u tayi da matsanancin mamaki gani da kaɗuwa ɗoki
da bai sake taba tace.

“Dan Allah Ummi yaushe aka fara wannan maganar?”.

Hannunta Ummi ta riƙe tare da zaunar da ita agefenta yace.

“Ki nutsu mana Asma’u me wannan kamar wanda akace an haɗa
Auren mutum da Dodo!?”.

 

Sake baki Asma’u tayi cikin Mamaki tace.

“Tabb Ummi ai kusan Auren Dodo da mutum za ayi dan wallahi
Khausar matsayin Dodo take kallon Yah Moddibo”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kana tace.

“Aikuwa da saninta”.

Zare ido Asma’u tayi tamkar zasu zubo tace.

“Ummi Khausar ɗin ta sani?”.

Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.

“Eh”.

Dafe ƙirji Asma’u tayi Idanunta akan Ummi tace.

“Shine kuma bata faɗa min ba iyeee Kam bala’i bari Inje in
sameta”.

Ta Ida maganar tare da miƙewa.

 

Cikin sauri Ummi ta riko tsintsiyar hannunta tace.

“Zauna ai zuwa ta ƙarshe
naji tana cewa tazo kuyi wata magana kuma ta samu kuna aiki sannan
fitowar ku kenan taga Moddibo yazo kinga ai jikinta na rawa ta fita”.

Jinjina kai Asma’u tayi still Hannunta na cikin na Ummi
tace.

“Eh dan na kirata awaya ma nace ta faɗa min shine tace idan
inaso Inje gidansu inji labari ashe dama wannan ne maganar amma Ummi tasan
maganar kuma ta yarda?”.

Cikin sanyi Ummi tace.

“Eh ta sani ta yarda kuma ta amince”.

Dafe kunci Asma’u tayi kana tace.

“To amma Ummi garin ya akayi haka?”.

Kallonta Ummi tayi tare da gyara zamanta kana ta sauƙe
numfashi cikin sanyi tace.

“Wasiyyar Yayanki zata cika?”.

Cikin sauri Asma’u ta kalleta fuskarta ɗauke da mamaki tace.

“Wasiyya kuma Ummi ya bar mata?”.

Jinjina kai Ummi tayi tare da fesar da numfashi kana ta
jingina bayanta da jikin kushin ɗin tace.

“Idan baki manta ba Ranan da yazo gidan nan na ƙarshe itama
Khausar tazo sannan tare suka tafi”.

Cikin sauri Asma’u ta jinjina kanta kana tace.

“Ƙwarai kuwa Mommy na tuna aishine tace suna tafiya taga
wata mota na binsu”.

Kai Mommy ta Jinjina kana tace.

“To awannan ranan ne ya bar mata wasiyar. Mommy ta ke sanar
min  yanda suka yi”.

Jinjina kai Asma’u tayi cike da tausayawa Aminiyar tasan
yanda Khausar ke masifar tsoron Moddibo tabbas ta ɗauki al’ƙawari mai girma
cikin sanyin murya tace.

“Allah sarki Khausar!, Allah sarki Aminiya!!, Ubangiji Allah
yabar ƙauna Allah yabar ƙauna tsakaninta da Yah Moddibo”.

Sai kuma ta kalli Ummi da fuskarta ke ɗauke da murmushi
tace.

“Ummi inshirya inje”.

Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.

“Kije mana Asma’u wa zai hana ki zuwa wajen Aminiyarki”.

Cikin sauri Asma’u ta miƙe tashiga Bedroom ta sanya
hijabinta kana ta fito tayiwa Ummi Sallama.

 

Aɓangaren Hajiya Lami kuwa miƙewa tayi daga Bedroom ɗinta ta
nufi ɗakin Samira zaune ta sameta Idanunta sun kaɗa sunyi jawur tamkar garwashi
alamar tasha kuka sosai cikin sauri ta ƙarasa kana ta zauna gefenta cike da
kulawa tace.

“Samira wai lafiya yau baki fito ba meya faru?”.

Ahankali ta ɗago kanta Idanunta da suka sauya launi ta
kalleta Muryanta na rawa tace.

“Mommy ni baƙi ɗaya wari nake ji idan na tambaye ki kinajin
wani sai kice min bakya ji Mommy kullum warin nan ƙaruwa yake ya zanyi da
raina”.

Cike da tausayawa Hajiya Lami ta janyota jikinta cikin
sanyin murya tace.

“Haba Samira ki kwantar da hankalin ki mana idan ya dawo sai
mu sake komawa wajensa”.

Cikin raunin murya tace.

“Mommy wani irin in ya dawo zaku koma wajensa ni dai ina
ganin mutumin nan ya lalata min rayuwa ne yanzu ayanda nake warin nan ko
maigadin gidansu Modibbo ma zai yarda ya aurenki ne bare Modibbo da ɗan karen
tsabta”.

Sai kuma sharce hawaye masu masifar zafi kana tace.

“Yanzu Mommy wani namiji ne zai kalleni bare yace yana sona!
ga ruwa mai wari da ƙarni yana ta bina ko yaushe ina tare da ƙunzugu kamar mai
jego”

Cikin sanyi Hajiya Lami tace.

“Bakomai Samira kasa ki damu Insha Allah yana dawowa zamu
koma wajensa”.

Cikin muryan kuka da tashin hankali tace.

“Mommy Ni dai ina ji ajikina wannan al’amari ya zama min
bala’i arayuwata na saɓi Ubangiji gashi ya kamani tun ba aje ko ina ba Wayyo
Allah! Kaico na! Ni Samira”.

 

Asanyaye Hajiya Lami tace.

“Haba Samira kar ki karyar min da zuciyata mana Insha Allah
burinki zai ciki”.

Kai ta girgiza kana tace.

“Mommy ni kam hankalina bai kwanta ba burina inga na samu
lafiya wannan ruwan ya daina zuba shine kwanciyar hankalina”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafa shoulder ta tace.

“Kada ki damu Insha Allah Samira Zaki samu sauƙi”.

Jinjina kai tayi kana tace.

“Allah yasa Mommy Ina fatan hakan Allah na tuba Allah
kayafemin Allah kaji ƙaina ka gafarta min”.

 

Acan ɓangaren Lamiɗo kuwa bayan ya fita ɗakin Mommy Kai
tsaye sashen Gimbiya Dadu yashiga bakinsa ɗauke da sallama zaune ya ganta da
ƙanwarta Hajiya Kubra.

Anutse ya ƙarasa tare da zama kana da murmushi afuskarsa
yace.

“A Yafendo Kubra kin zo ne?”.

Kai ta gyaɗa tace.

“Eh Lamiɗo kana gida kenan?”.

Kai jinjina kana suka gaisa bayan sun gaisa Hajiya Kubra ta
gyara zamanta tare da kallon sa tace.

“Toh yau dai kam nazo da aiken Ƙaninka duk da yace min
iyayenshi maza sunzo”.

“Wanne ƙarin nawa”. Yayi tambayar a bauɗo domin babu wanda
ya taɓa mishi mgnar.

Shi kanshi mahaifin Naseru cewa yayi yaji suna mgnar ne
bakwai sun gaya mishi bane, to kuma shima sai abin ya kwanta mishi musamman da
yasan Nasiru na biye-biyen mata shiyasa ya nemi alfarma a bashi Amina kuma ayi
auren cikin gaggawa.

 

Murmushi tayi tare da Kallonsa tace.

“Naseeru mana”.

 

Kai ya jinjina kana yace.

“Ikon Allah Naseeru kuma ko ɗazun ma muna tare kuma bai faɗa
min ba shine sai ya aiko ki? ai da kin kirani ma zanzo har gida in sameki”.

 

Kai ta girgiza kana ta kalli Gimbiya Dadu sai kuma ta kalli
Lamiɗo tace.

“A’a ai aiken ne dole muzo da kan mu tunda iri muke nema”.

Jim yayi kana yace.

“Ikon Allah wani kalar iri kenan?”.

Ƴar dariya tayi ta gyara zamanta kana tace.

“Iyeee al’amarin ne ya sauya sheƙa”.

 

Gyara zama Gimbiya Dadu tayi kana tace.

“Eh aihakama shi yafi alkhairi Hausawa sunce naka sai naka
daɗin zama sai bare gwara dai kome za ayi ace na kane” .

Ido kawai Lamiɗo ya zuba musu cikin rashin fahimta ko kaɗan
bai taɓa fuskantar alaƙar dake tsakanin Amina da Naseer.

Ganin yanda yake kallon Hajiya Kubra tayi murmushi tayi kana
tace.

“Akan al’amarin Naseeru ne da Amina”.

Cikin sauri ya kalleta ya girgiza kai kana yace.

“Ba dai Amina da Naseeru ba saidai Nasseru da Khausar dai
ko?”.

Dariya tayi tare da gyara dankwalinta tace.

“A’a da Aminar dai”.

Ido ya zuba mata cike da son nazartansu  yace.

“Da Amina dai?”.

Jinjina kai tayi ta kalli Gimbiya Dadu kana tace.

“Tabbas da Amina”.

Jingina Lamiɗo yayi da jikin kujeran kana yace.

“A’a baki fahimci maganarsa da kyau ba da Khausar ce kuma
al’amarin ma dai gashi nan yanda yazo abirkice”.

Fuska Gimbiya Dadu ta ɓata kana tace.

“Babu abinda ya birkice sai dai sune ya birkice musu acan
tunda Khausar ta nuna bata sonsa ai Alhamdulillah ga ƴar Uwarsa ta soshi”.

Cike da Mamaki Lamiɗo ya ɗago kansa ya kalleta yace.

“Da ita Aminar kenan?”.

Jinjina kai Hajiya Kubura tayi kana tace.

“Eh ai Amina da Nasseru sun daɗe da haɗa kansu  soyayya suke sosai basu dai fito sun faɗa
maka bane suna so sai angama shirya abubuwa komai ya kankama”.

Jinjina kai Lamiɗo yayi still da mamaki atare dashi yace.

“Allah mai iko shi kuma Naseeru ƴarsa zai Aura?”.

Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.

“Ya haramta ne?”.

Murmushi yayi tare da girgiza kai yace.

“A’a a’a bai haramta ba na isa in haramta abinda Allah ya
halatta ba wai ya haramta bane amma da yake tana sunan ƴarshi ce”.

Baki Gimbiya Dadu ta taɓe kana tace.

“To wannan dai ba wani abu bane aciki ka dai kayi fatan
alkhairi Allah yasanya albarka acikin al’amarin”.

 

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

“Kuma haka abin ya zama kenan?”.

Kallonsa Gimbiya Dadu tayi kana ta kalli Hajiya Kubura dake
murmushi tace.

“Sosai ma tunda naji Kakar Khausar tana cewa ba zata bawa
Zuri’ar Mayu ba tana ƙananun surutai shiyasa nace ya janye da nemanta ya nemi
Amina ƴar Uwarsa shiyafi mana kwanciyar hankali”.

Ahankali Lamiɗo ya sunkuyar da kansa ƙasa batare da yace
Uffan ba.

Dariya Hajiya Kubrua tayi kana tace.

“Ai shiyasa nace bari nazo da kaina muyi magana”.

Anutse ya ɗago kansa ya kalleta ajiyar zuciya ya sauƙe kana
yace.

“Toh Yafendo Kubura ai wannan al’amarin Aure magana ce ta
maza bata mata ba ai da Babban Naseeru ne zaizo muyi magana zai fiko sai insamu
gamsuwa da sahalewar sa za ayi dukkan maganar?”.

Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.

“Ai zaizo amma dai ta fara zuwane ta sanar maka saboda
bakasan da Maganar ba”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

“Toh shikenan Ubangiji Allah ya mana zaɓin alkhairi”.

Gimbiya Dadu kuwa cikin sauri ta tari numfashi ta hanyar
cewa.

“Shine ma alkhairi Nasseru ya auri ƴar uwarsa ita kuma taje
can ta ƙarara ta auri duk wanda taga dama da masifaffiyar Kakarta”.

Murmushi yayi kana yace.

“To Allah ya kyauta”.

 

Miƙewa yayi ya fita kai tsaye sashen sa ya nufa zaune ya
samu Hajiya Bunayya da waya maƙale akunnenta tana magana da Hajiya Lami ganinsa
yasa tayi saurin cire wayar kana ta katse ta juya ta kallesa zama yayi tare da
tsira mata ido tamkar shine rana ta farko da yafa ganinta acikin rayuwarsa.

Ganin kallon da yake bin ta dashi ne tace.

“Ya dai Mai martaba naga kana ta kallona lafiya kuwa?”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe kana cikin tsira mata Ido yace.

“Wai me yake faru tsakanin Naseeru da Amina ne?”.

Cike da farin ciki tace.

“Meye kuma yake faruwa Lamiɗo banda lamarin Aure da muke
fatan zai tabbata tunda sun daidaita kansu”.

Wani irin kallo ya watsa mata kana yace.

“Sun dai-dai-ta kansu Meyesa ban sani ba”.

Zare ido tayi tare da ɗage hannunta sama tace.

“Lalala nima Wallahi ban saniba sai kwanan nan bai kai sati
ba Amina take cemin wai zai aiko ya gama haɗa kayan Aure su goro da kayan
gishiri da kuma sadaki”.

Ido kawai Lamiɗo ya tsira mata bako ƙyaftawa ta cigaba da
cewa.

“Hatta kayan rufi ya gama haɗa komansa yana so ayi auren nan
da mako biyu nanne nasan da maganar toh tsoron yi maka magana nake ta yanda zan
tunkare ka da maganar”.

Cikin wani irin yanayi Lamiɗo ya tsira mata ido tamkar mai
son fahimtar wani abu.

Marerece fuska tayi kana tace.

“Ya dai ka zuba min ido
Lamiɗo ka yarda dani ai danasan da maganar dana faɗa maka nima abin ya
daure min kai shiyasa ban faɗa maka ba”.

Sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa kana ta cigaba da cewa.

“Domin nasan da farko Khausar Naseeru yake so to amma shi
Naseeru da kansa ya sameni yace Khausar tace bata sonsa  to shi ya hakura sannan Gimbiya Dadu ma tace
ya nemi Amina ƴar Uwarfashi Lamiɗo ya fesar kana yace.

“Allah ya kyauta amma batun kice baki sani ba zancene
Bunayya magana kike”.

Cikin sauri ta kallesa kana tace.

“Wallahi tallahi Lamiɗo ban saniba”.

Cikin yanayin ɓacin rai da takaici yace.

“Dakata Bunayya kada ki rantse dan na lura kamar baki san
girma da darajar rantsuwa ba idan kika ce baki sani ba magana ya ƙare”.

Cikin tsinkewar zuciya take kallonsa.Cike da ɓacin rai ya
cigaba da cewa.

“Idan kika faɗa kona yarda ko kar nayarda wannan tsakanina
ne dake akan abinda kinsan ƙaryane kinsani sannan nasani kuma inada tabbaci da
yaƙinin ke kika ƙulla wannan alamarin”.

Cikin yanayin tashin hankali da damuwa tace.

“Fisabilillah taya zan ƙullah”.

Ƙwaffa yayi kana yace.

“Bunayya gani kike kamar bansan komai akanki ba ko?”.

Atake zuciyarta ya tsinke zufa ya fara wanke mata fuska duk
da sanyin irin na garin Gembila cikin sauri tace.

“Toh yanzu dan Allah ni menayi?”.

 

Kai ya girgiza still Idanunsa na kanta yace.

“Hmmm jiki magayi tunda haka kika zaɓawa kanki, duk abinda
ya kasance ku kuka da kanku acikin al’amarin nan ya kamata ace komai zakiyi
kiyi shawara dani”.

Kasa cewa komai Hajiya Bunayya tayi sai zufa dake wanketa
cike da takaici ya cigaba da cewa.

“Amatsayina na mijinki kuma Uba ga Amina amma bakuyi shawara
dani ba sai kuka tura Iyayena ta yanda zasu tsareni acikin maganar tunda haka
kuka zaɓa magana ta ƙare, kowa ya ɗeɓo da zafi bakinsa!!!”.

Cikin ɓoye tsoronta tace.

“Naseeru fa shiyace ya daina son Khausar”.

Cikin sauri ya katseta ta hanyar cewa.

“Khausar ko baice ya dena sontaba Ni kaina inada nufin bazan
bashi Auren Khausar ba, tunda kuma yazo ya zagaya kukayi haka ke kika sani ƴa
ƴarki ce shi kuma ɗan uwana ne babu abinda zance”.

Marerece murya tayi kana tace.

“Ni dai wallahi babu abinda na sani aciki kuma itama Amina
tace in faɗa maka Babansa yace zai zo gobe”.

Wani kallo ya watsa mata Afusace yace.

“Idan kinga dama kice masa yanzu yazo aɗaure ba haka kike so
ba?”.

Asanyaye ta kallesa kana tace.

“Toh fisabilillah dan Amina za tayi Aure shine zai zama
laifi ko kuma so kake itama tayi ta zama kamar yanda Asiya take zaune?”.

 

Cikin tsawa ya ɗaga mata hannu kana yace.

“Ki kiyayi kanki kada ki yarda kijefi Asiya da mugun furuci,
Insha Allah Asiya Ubangiji zai jiɓanci lamuranta Asiya zatayi Aure aure mai
daraja da izinin Ubangiji baza ta taɓe ba”.

Kallon yanda yayi kicin-kicin da fuska Hajiya Bunayya tayi
cikin fushi ya cigaba da cewa.

“Da yardan Allah tunda tayi haƙuri da jarabawar da Ubangiji
ya mata za taci nasara baya ga haka duka-duka nawa Asiya take bare Amina dududu
ba shekaran daya gabata bane ta gana Secondary ba?”.

Uffan batace ta lura aharzuƙe yake cikin rashin walwala ya
miƙe yashiga Bedroom ɗinsa.

 

 *MOROCOW*

 

Aɓangaren Moddibo Baki daya kansa ya ɗauki zafi aiki suke
gadan-gadan Anutse ya fito daga masallacin dake cikin Company ya nufi ainihin
inda ake buga Abaya, kama daga Dubai Abaya, Morocco Abaya, Saudia Abaya, da
kuma Turkiya Sai kuma Veils,Bags,shoes da sauransu.

Babba wajene sosai ankafa manyan ijinina sabbi ana ta haɗa
su ga manyan-manyan AC dake aiki kana ga sanyin garin dake sauƙa wajen ya ɗauki
sanyi baki ɗaya aiki suke gadan-gadan babu kama ƙafar yaro da alama nan da
Kwanaki biyar za’a haɗa komai  gashi an
dakatar da aikin komai sai sabbi dake aiki Saboda sabunta Injina da akayi
Ma’aikatan na ganinsa suka nufo sa suna Cikin harshen larabci suke masa Barka
cike da mutuntawa da kuma girmamawa shima sannu yake musu yana yaba aikin da
suke.

 

Ɗaya daga cikin ma’aikatan wanda yake shine Babba yace.

“Alh aiki na kyau yanda ake
buƙata insha Allah nan da kwana biyar za’a gama daddasa Injinan da za’a
gama aikin”.

Kallon yanayin wajen Moddibo yayi kana yace.

“Masha Allah abu yayi kyau sosai”.

Kai Engineer ya Jinjina kana yace.

“Sosai ma ai saboda ansamu zaƙaƙuran ma aikata kuma baki ɗaya
cikin kwanaki Ukun nan da aka dakatar da buga Abaya’s,Veils,Jakankuna da
Takalma *BASJAM”.*

Ahankali Moddibo ya lumshe Idanunsa Aransa yace Allah sarki
Abba gashi ya haɗa sunan sa dana J ɗina a Company sai dai bashi da ikon aiki a
Company Engineer ya cigaba da cewa.

“Baki ɗaya har abin ya fara ƙaranta zuwa ƙasashen da ake
kaiwa danma ansamu antanadi masu yawa suna zaune amma Alhamdulillah aikin zaiyi
gaggawa tunda ansamu  zaƙaƙuran
ma’aikata”.

Jinjina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa  saboda sanyin da wajen ke dashi kana yana jin
yanda Kasan mararsa ke murɗawa ahankali ya ɗaura tafin hannunsa na dama akan
maransa ya danna sai kuma ya cije Lips ɗinsa na ƙasa cikin dauriya ya kalli
Engineer tun jiya ya kwana da ciwon cikin kana har yau bai lafaba na awa ɗaya
mai kyauba da zaran yayi minti talatin zai sake murɗa masa ahankali ya cije
Lips ɗinsa kana yace.

“Abu yayi kyau Allah yatemaka insha Allah nan kusa zamu
kammala akoma bakin aiki a cigaba da aiki gadan-gadan”.

 

Ya ida maganar tare da juyawa ya nufi gefen dama wanda
office, Office ne awajen wani Corridor ya shiga tare da buɗe makeken Office da
yafi sauran kyau da tsaruwa sosai Office din ya haɗu table ne kansa ɗauke da
system da takardu sai flowers kana daga jikin bango kujera ce mai juyawa daga
gaban table ɗin kuma kuma jeru biyu ne sai Cottons sky blue da fari daga gefen
dama Ac ne daga ɗaya gefen kuma tamkar falo ne manyan kujeru ne guda bakwai
suma Sky blue sai Tv Plasmer ajikin bango da frigde sai kuma showglass dake ɗauke
da kofuna ahankali ya ɗauki remote din AC yaƙara gudu duk da kuwa sanyin da ake
stugawa yayin da zufa ya shiga tsats-tsafo masa agaba ɗaya ilahirin jikinsa
kana maransa na cigaba da murɗawa jikinsa sai zufa yake karyo masa rintse
idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda mararsa ke murɗawa tamkar zai fita ahankali ya
zauna kana ya ɗaura kansa akan Center table dake tsakiyar falon ya lumshe
idanunsa sai kuma yayi saurin buɗewa kana ya lashi busassun laɓɓansa  baki ɗaya jikinsa ya fara rawa jin yanda
maransa ke dunƙulewa yana tsikarinsa cike da damuwa da rauni ya soma faɗin.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

Kana yaja wani numfashi me nauyi ya yunkura da niyyar miƙewa
ji yayi bashi da kuzarin da zai iya tsayawa ji yayi tamkar an haɗa maransa da
bayansa ana dinkewa ga wani irin harbawa da zuciyarsa keyi da Masifar ƙarfi
kwanciya yayi akan 3sitter yayi rub da ciki baki daya ilahirin jikinsa rawa
yake ga zufa dake tsats-tsafo masa tamkar babu Ac saboda yanda azabebben ciwon
cikin ke gallazarsa yakai kimanin minti talatin yana murƙususu akan kujera
kafin ya fara lafawa sannu Ahankali ya fara maida numfashi yana fesaewa.

 

 *Gembila*

 

Asma’u kuwa ta daɗe tsaye aƙofar gida bata samu Adaidaita ba
jin kiran sallar La’asar yasa ta juya da niyyar koma gida tayi Sallah kuma sai
tasamu adaidaita shiga tayi tana isa gidan Kai tsaye falon Mommy ta shiga
bakinta ɗauke da sallama zaune ta samu Khausar da Haiydar tana riƙe da hannunsa
tana yanke masa Farce.

Haiydar kuwa kallon Khausar yayi kana yace.

“Nifa ki kula kar ki yanke min hannu”.

Hararansa tayi sai kuma ta cigaba da yankewa kana tace.

“Tunda dai baka iya ba kona yankekama kai ka jawa kanka”.

Ta ƙarasa maganar tare da sauke Idanunta akan Asma’u data
gama shiga falon da sauri ta sake masa hannunsa tare da miƙewa da sauri ta
Rungume Asma’u cike da farin ciki tace.

“Oyoyo Asmeey ta”.

Zare ido Haiydar yayi tare da yarfe hannunsa yace.

“Wayyo ta yankeni Wayyo ya tsana”.

 

Da sauri Mommy ta fito daga Bedroom ɗinta Idanunta akan
Haiydar tace.

“Lafiya kuwa”.

Yarfe hannu Haiydar yayi kana ya Marerece fuska yace.

“Mommy ki kallafa Addah Khausi ta yanke min yatsana daga
kallon Asma’u”.

Langwaɓar da kai Asma’u tayi kana tace.

“Ayyah Haiydar Sorry sannu bata sani bane”.

 

Hararansa Khausar tayi tace.

“Rabu dashi ƙato dashi tunda dai har yanzu bai iya yanke
Farce ba sai dai in yanke masa aikuwa nata yanke masa hannu”.

Kallonta Mommy tayi kana tace.

“Wato ma da saninki kika yanke sa?”.

Cikin sauri ta girgiza kai tare da langwaɓar da kai tace.

“Wallahi Mommy ban sani ba ganin Asma’u ne yasa na tashi da
sauri ashe na yanke sa”.

 

Kai Mommy ta gyaɗa tare da kallon Haiydar tace.

“Sannu Babana mu gani”.

 

“Mommy Ummina tace in gaisheki”

 

Jinjnna kai Mommy tayi kana tace.

“Ina amsawa”.

Hannun Asma’u Khausar taja suka shiga Bedroom ɗinta suna
shiga Khausar tace.

“Fisabillah baki zoba sai yanzu ko dai kwana zamuyi?”.

Zare ido Asma’u tayi kana tace.

“Mu kwana kuma wa zai taya Ummina aiki da safe?”.

Langwaɓar da kai Khausar tayi sai kuma tace.

“Don Allah Asmeey mu kwana zan kira Ummi mu roƙeta”.

Kai Asma’u ta girgiza kana tace.

“A’a keto muje mu kwana mana”.

Ware ido Khausar tayi tare da sanya dariya tace.

“Caɓɓ lallai kam”.

Murmushi kawai Asma’u tayi kana ta zauna abakin gadon.

Khausar kuwa fridge ta buɗe ta ɗauki Plate ta sanya Faro
water da Ayaba ta mikawa Asma’u.

Karba Asma’u tayi tana ɓare Ayaban tace.

“Ke dai bakya rabuwa da Ayaba aɗaki kina nan kamar biri”.

Murmushi Khausar tayi kana tace.

“Wallahi kuwa Ina son Banana yana min daɗi”.

Jinjina kai Asma’u tayi tare da faɗin.

“Ai lallai dai kam”.

 

*Morocco*

 

Aɓangaren Moddibo kuwa haka yaita fama bayan minti talatin
cikin yake sake Murɗansa yana kallon gari yayi duhu maghariba ta kawo kai har
wasu massallatai sun fara kiran sallah amma ya kasa miƙewa saboda yanda ciwon
cikin ke kartansa jin ciwon ya lafa yasa ya miƙe tare ya fita yaga wajen shiru
alamar duk ma aikata sun tattafi sai
securities da mai bawflowes ruwa kasancewar karfe biyar da wasu Mintuna
ake tashi ma tsaye wajen motarsa yashiga yaja ya fita a gate one.

Ya miƙe titin ya fito gate ɗin La riva restaurant dake
Opposite da Company yazo Dai-dai wajen Traffick sun tsaida shi saboda sauran
motoci da suke wucewa ahankali yasa hannunsa ya dafe fuskarsa ta gefe yatsunsa
na dafe da kuncinsa ya tsansa ɗaya kuma na cikin bakinsa kana ya fito da
fuskarsa ta wajen motar yana ɗan shan Iska jikin katangar Company sa yana
shaƙan iskar bishiyar dabino dake zagaye da Company wanda ta ko ina sune da
gudu yaga wata mota ta gilma ta gabansa wacce ta fito daga gefen yamma zata yi
gabas kana shi kuma yana gefen kudu ne idan ya samu dama zaibi arewa ganin
wulgawar motar yaga fuskar J ɗinsa ne aciki cikin sauri ya zare Idanunsa
sakamakon kallon fuskar J ɗinsa aciki Motar cikin wani irin sauri ba tare da
anbasa hanya ba ya figi motar ya karya kwana yabisa har ya kusa bige wata mota.

 

Da mugun gudu yake bin motar kana ga cunkoson ababen hawa
kasancewar maghariba ta kawo kai ƴan kasuwa sun taso ga kuma ma’aikata sun
tattaso daga Office kowa na burin komawa gida wasu kuma na ƙoƙarin su samu
masallacai dan kada su rasa jam’i hakan yasa cunkoso yayi yawa ga kuma duhun
gari gudu yake yana bin bayan motar ga kuma cun kuson motoci da suka taresa ya
cusa ta nan yaga antaresa baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake tun lokacin daya
zare idonsa har yanzu bai maidasu daidaiba saboda idanunsa sun gane masa Allah
ya nuna masa fuskar Jameel ɗin sa ne yasani Koda amagagin mutuwa yake ya
tabbatar fuskar Jameel wulgawa daya zaiyi ya gane yasani wannan fuskar
Jameel  ɗinsa ne baki ɗaya ilahirin
jikinsa rawa yake kana yana maimaita kalmar Innalillahi wa’inna ilahi
rajiu’n  yana cigaba da dannawa motocin
gabansa hon baki daya mutane Kallonsa suke wasu kuma na cewa wannan kam
lafiyarka ina zakaje haka kamar zaka tashi sama shidai haka ya cigaba da tafiya
ya kutsa tanan ya kutsa tacan garin hakane ya bigewa wani motarsa mutumin na
cewa Kai lafiya amma ina tuƙi kawai yake da gudu baki ɗaya hankalinsa baya
jikinsa wani mai Napep ne ya tare gabansa madadin ya kalli gabansa amma baki ɗaya
idanunsa na kan motar daya yaga J ɗinsa aciki yana samu ƙaramar ɗin ya kauce
masa ya cigaba da bin bayan motar yanda yake gudu da masifaffen ƙarfi haka
zalika motar da yake bi ɗin ma take gudu hakan yasa yasake tabbatarwa kansa J
dinsa ne kenan gudunsa yake ko kuma yaya ahaka suka isa wani roud about nan
yaga ya ɗauki hanyar da zata sa dashi da flyover gudu yake da ƙarfi haka shima
wancen ke gudu duk da gudun da yake amma ya kasa kamo wancan motar saboda shima
gudun yake ga kuma motoci dake tsakaninsu amma yana iya hangosa kasancewar be
wuce motoci biyu zuwa uku bane agabansa sunzo daidai kan Flyover yasamu yabi
sama Shima Moddibo cikin sauri yabi sama kasancewar ba cunkoso sosai numfashi
mai karfi ya sake kana ya hau kan Flyover yabi sana kafin ya isa tsakiyar
Flyover shi kuma wannan har ya sauƙa ya ɗauki hanyar Unguwar Mellila shima
Moddibo cikin sauri yabi wannan hanyar tafiya kaɗan sukayi yaga motar ta wuce
wani asibiti cikin gudu shima ya wuce tafiya kaɗan suka ƙara yaga motar taja
kwana adai-dai wani tamfatsetsen gini mai masifar kyau da girma bisa duk kan
alamu asabiti ne saboda sunan dake manne asaman ginin idanunsa ya ɗaga yaga
sunan dake manne ajikin ginin *Youssef Mouley Hospital*.

Mai motar kuwa yana danna hong aka buɗe masa gate yashiga
kafin ya juya akalar motarsa ya ƙarasa wajen kuma a maida gate din ana ƙoƙarin
rufewa da wani irin sauri ya danna hancin motarsa cikin gate din.

 

Cikin sauri securities dake bakin gate din suka taso suka yo
Kansa.

Shi kuwa mutumin cikin motar tuni yayi Parking ya buɗe motar
ya fita da sauri Norses biyu suka biyu bayansa suna faɗin.

“Welcome Sir”.

Security din kuwa kan Moddibo suka nufa suna faɗin.

“Lafiya kuwa?”.

Shi kuwa Moddibo gadan-gadan ya nufi kan security din da
sauri suka kauce masa yana shiga yayi Parking kana ya fito da sauri security
suka yo kansa suna faɗin.

“Lafiya kuwa?”.

Bai tanka suba yabi bayan mutumin yana cewa.

“J!,J!!,J!!!,”.

Shikuwa Mutumin gaba yayi Norses na biye dashi jin hayaniya
yasa ya juya ya kalli bayansa gani yayi Moddibo ya nufo kansa yana cewa.

“J”.

Security kuwa ƙoƙarin riƙesa suke suna faɗin.

“Malam lafiyar ka kuwa ina zaka je?”.

Cikin sauri Moddibo ya hankaɗesu kana cikin fushi yace.

“Ka matsa min anan ka bani hanya, J!J!!”.

Wata matace ta fito daga cikin Hospital din ta ƙaraso kusa
da wannan mutum kana tace.

“Dan Allah Dr Jameel kayi sauri kaceci rayuwar ƴata tana
cikin hatsari”.

Jin haka ne yasa Mutumin da takira da Dr Jameel ya juya ya
nufi cikin asibitin.

Moddibo kuwa da gudu yabi bayan Dr Jameel da already ya
shiga cikin reception tamkar wani zautacce haka ya dawo baki daya bashi da wani
cikakkiyar nutsuwa Akuma dai-dai lokacin yaji cikinsa ya sake kartawa da masifaffen
ƙarfi da gudu ya nufi kan Dr Jameel yana cewa.

“J!,J!!,J!!! Ina zaka je”.

Afusace Dr Jameel ya tsaya tare da juyawa yace.

“Wai lafiya Malam Security ku fita dashi mana me kuke jira
ha’a ya zaizo yana mana ihu yana firgita mana marasa lafiya”.

Baki ɗaya Norses da sauran mutanen ido suka zubawa Moddibo.

Cike da girmamawa security yace.

“Yallaɓai munyi ƙoƙarin korinsa amma yaƙi tafiya sai turemu
yake”.

Juyawa Moddibo yayi jin J ɗinshi na mgn da larabci wai a
koreshi, da sauri ya buga hannunsa aƙirjin Dr Jameel Cikin juya harce zuwa
larabcin  yace.

“J ni kake cewa akaro?,J nine fa A.J ɗinka ni kake cewa
akaro?”.

Cikin fushi Dr Jameel ya fincike hannun Moddibo ajikin
rigarsa yace.

“Ka sakeni wanene kai a ina na sanka kaji yanda kake ihu
kana gigita mana mutane”.

Ya ƙare mgnar yana yiwa Modibbo wani irin kallo mai cike da
tarin mmki da kuma son nazartan abubuwa da yawa musamman kamaninsa.

Shi kuwa Modibbo Cikin rauni da tsanananin tashin hankali da
azabebben ciwon ciki Moddibo ya sanya tafin hannunsa ya dafe maransa muryarsa
na rawa yace.

“J Nine fa J A.J ɗinka kake cewa baka gane ba Innalillahi
wa’inna ilahi rajiu’n J nine yau kake cewa baka sani ba?”.

Akuma dai-dai lokacin cikinsa ya sake murɗawa da masifaffen
ƙarfi cike da ɓacin rai Dr Jameel ya Kalli security kana yace.

“Ku fitar min dashi”.

Norses ɗin kuwa cikin alamun damuwa suka ce.

“Dan Allah Dr muje ka duba matarnan”.

Juyawa Dr Jameel Yayi Moddibo kuwa ganin haka yasa Cikin
wani irin rauni ya kallesa  muryarsa na
rawa kana numfashinsa na fusga yace.

“Jameelu nine fa aduniya Koda baza ka gane kowaba amma Ni da
Ummi da Abba bamu cancanci kamanta damu ba kuma ko me yafaru da kai aduniya Ni
dai da Ummi da Abba bamu cancanci ka ce baka gane muba A.J dinka nefa”.

Yana gama faɗar haka ya yanke jiki yayi baya…

Leave a Reply

Back to top button