Hausa NovelsHausa NovelsTabarmar Kashi Book 2

Tabarmar Kashi Book 2 Page 5

Sponsored Links

Book 02 Page 05

********Tunda suka taho a hanya yake mata hira cikin nutsuwa tare da son janye hankalinta,dukka a qoqarinsa na ganin ya kafa kansa cikin zuciyarta yadda ya kamata.
Kaf tsahon hirar da yake mata tun daga thairaphy beaty saloon din har yanzu da suke gab da shiga unguwar su bata amsa masa sau hudu ba. Ta cika tayi fam,tasan tabbas afifa ta gayawa mahmud inda taje. Tun jiya sukayi zata rakata ta wanke kanta,ayi mata gyaran fuska a kuma saka mata jan lalle iya yatsun qafa dana hannu,tayita jiran afifan bata dawo ba,daga qarshe sukayi waya tace tana da patient data kusa haihuwa,so saidai taje,ta sameta acan saita daukota su dawo tare. Maimakon taga afifa sai taga mahmud,hakanan don babu yadda zatayi ta shiga motar,saboda idanu sunyi yawa a kanta sanda take fitowa,dole ta shiga din ya rufe ya jasu,ranshi fari qal,yana jin dadin yadda a yau ta aminta ta yarda ya dawo da ita gida.

Zata iya cewa tsahon rayuwarta,tun Karin ma aurenta na farko yaushe ne ta shiga motar wani d’a namiji ba banda yayunta maza,don haka ko a yanzun jinta take a takure qwarai.

Taso ya ajjiyeta daga gofar gida amma sai ya giya

“Wannan ladan dole na garasashi” ya fadi yana murmushi,da kansa ya buda mata qofar ta fito ya mayar ya rufe

“Yanzu sai yaushe kenan ranki ya dade?”

“Zan duba” kawai tace dashi tana yin gaba.
Kansa ya girgiza,shi sam abinda takeyi bai dameta ba,yasan with time zata daina komai idan ta shiga gidansa,ya soma amfani da kyautatawarsa a kanta wajen kafa kansa.

“Madam,oga muhyiddeen yace ki sameshi a dakin baqi idan kin shigo” cewar jamilu yana dan rusunawa. Duban jamilun tayi,kamar zatayi magana sai kuma kawai ta sauya akalarta zuwa can din,wataqila vana wani aiki ne da yasa ya kebe a can,tunda time to time yana yin hakan,sai ya baro gidansa vazo nan yayi aikinsa a nutse,saboda su khalipha basa barinsa.

Har zata daga curtains din masu kauri da girma sai ta dakata,saboda wani bagon qamshi da ya shiga hancinta,cikin iiki da zuciyarta takejin kamar tasan qamshin,amma ta kasa banbancewa. Ta kauda tunanin ta sanya hannu ta budesu.

Shine yake fuskantar gofa,wannan yasa tana budewar dashi suka fara hada idanu,kwantattun sexy eyes dinsa da yau suke cikin wani irin nutsuwa wadda damuwa kadan ta cakuda dasu. A tare dukkansu suka janye idanun nasu,kowa yana jin zafin dan uwansa a qasan ransa. Itakam sãahar sai da taja siririn tsaki qasan ranta,cikin zuciyarta tana tunanin me kuma yazo yi a gidan nasu?,saboda ita dai ta riga ta yiwa kowanne zuwa nasa gidansu fassara da zuwan da baida alkhairi.

“Yauwa kin dawo?,qaraso ciki kinyi bago” ya muhyiddeen ya fada. Cikin nutsuwa take takowa da wani irin rashin sakewa da batasan meye dalilinsa ba,saidai tanajin kamar ido ne a kanta. Tabbas batayi qarya ba,can gasa gasa toufeeq yake qare mata kallo,yanason ya gano meye ne tafi kowa dashi har Dr da maii suke iya magana da bada umarni a kanta? saidai idanunsa basu gano masa komai ba face zara zaran yatsun gafafunta da suka sha jan lalle da yayi radau,suka fito fes gwanin sha’awa.
Daga bisani dole ya zare idanun nasa yana sakin tsakin da baisan anji ba ko ba’a ji ba.

Yaa muhyiddeen din ta gaisar,can qasan ranta tana juya ta yadda zata gaida toufeea din don batajin zata iya gaidashi sam sam.
Kallon da yaa muhyi yayi mata yasa don babu yadda zatayi ta waiwaya sashensa ba tare data dubeshi ba tace

“‘Barka da yamma”

“‘Barka” ya furta da gasaitacciyar muryarsa,idanunsa nakan wayarsa da yake qoqarin sanyata a flight mode.
“Sun kawo drinks sun wuce,kiyi serving nasa,idan kin gama ki jirayeni wajen maama” yawu ta hadiye sannan ta gyada kaitana qyashin yadda zata yiwa wannan mutumin hidima,wanda baisan mutunci da darajar kowa ba. Dole ta zamo ta sauko qasa daga saman lallausan sofa din,dai dai sanda ta fara serving din nasa yaa muhyi ya juya ya fice daga falon.

Mutum ne shi mai kaifin karantar mode din mutum,koda bakayi magana da bakinka ba,yana da saurin fahimtar yanayinka koda ta cikin qwayar idanu ne. Tsaf ya fahimci akan dole take zuba masa komai,saboda mugunta kuma sai daya cika kome taf har bakin cup,ta mige ta koma kan kujerar tayi zamanta ba tare da tavi masa tayin sha ba.

Ya fahimci Allah Allah take ya fadi uzurinsa ya tafi,hakane kam a zuciyarta,don ji takeyi kamar ta zura da gudu tabar dakin. Yana sane shi kuma yaqi cewa komai,yanata danna wayarsa ba tare da yace ta tafas ba,yavin da ita kuma keta murza yatsuntsa da sukasha lalle,ranta yanata quna,hancinta yanata zugo mata qamshinsa yana watsa wani irin abu ilahirin jikinta ta kowanne sashe. Kamar ta yayyaba masa magana kan yadda ya barta a zaune haka taji,saidai ta kanne ta cije,don batason yaci gaba da sanin abinda yake bata mata rai.

Sai daya mula don kansa,yanata tauna yadda yau a karon farko zai furtawa wata diya mace kalmar ban haquri,bayan maji dinsa da hajiya qarama. Sai daya sauke gafafunsa dake harde ya gyara zamansa yana zuba mata narkakkun idanunsa. Ba abinda yake hangowa saman fuskarta sai tsiwa fal,shi kansa bai san me yasa duk sanda zai dubeta ba yakejin kallon kamar ya bambanta da sauran kallon da yakewa kowa.
Kalmar haqurin tana masa maqaqi a wuya,musamman idan ya tuna da kalmar data jefeshi dashi shima. To amma sajjad ya gaya masa tun a hanya,mai nema baya fushi,kuma zaiyi komai ne for the sake of fadeela,indai da gaske yana son diyar tasa.

“I hope zaki manta da komaiina neman alfarmar ki dawo kici gaba da zama da angel” yayi maganar da wani irin softness.

har yanzu izzarsa tana nan cikin maganganunsa.

Nata idanun ta zube masa tana gyara zamanta

“Ba komai kudi ke iya bayarwa,kamar yadda ba komai ne darajarsa take hawa mizani daya dana kudi ba. Komai ya wuce a gurina saboda fadeela da nadeeya,but am sorry…..bazan iya dawowa gidanka ba,infact ma am getting married in the next month” abinda ta fada kenan ta miqe tsam tana daukar hand bag dinta.

Wani rudu ne ya shigeshi,a hankali yaji zuciyarsa ta motsa da wani irin qarfi ta matse guri daya

“Aure zatayi?” Ya tambayi kansa,kamar ba yanzun nan kunnuwansa suka jiye masa abinda tace ba

“Idan tayi aure ta tafi,yaya makomar rayuwar fadeela?” Muhimmiyar tambayar data tilasta masa furta abinda ko a mafarki bai taba zaton zai furta ga kowacce diva mace a doron duniya ba

“Will you marry me?”. Wannan kalmar idan ta kirata da saukar ajali lokacin mutuwar fuju’a a kunnuwanta to batayi kuskure ba. Kalmar data ji girmanta ya wuce girman dutsen dala a kanta. Kunnuwanta suka bada wani shuuu,sai ta kasa daga qafafunta daga gurin,kamar an dasata

“Will you marry me?” Ya sake maimaita maimaitawa a karo na biyu. Wannan karon wata faduwar gaba da sautinta yakai har ga kunnuwanta taji,numfashinta yadan so ya fara fita da sauri amma saita yi qogarin saitashi. A nutse ta waiwayo tana dubansa kai tsaye

“Absolutely no” ta zare idanun nata daga kansa tana qoqarin ci gaba da tafiya. Saidai taku biyu kacal tayi ya cimmata,ta fahimci hakanne ta hanyar qamshin turarensa da ya mamayeta,taja baya da sauri tana rabewa gefe,saboda yadda yayi bake bake a bakin gofar,kwarjininsa ya daketa da wani qarfi,ya sanya wannan magnet din sosai a kanta da ya sanya ta kasa duban idanun nasa a yanzu.

Nasa kallon ya dauke daga kanta yana zaro complimentary card dinsa,yayi taku biyu zuwa inda take,abinda ya kusa dauke numfashinta kenan,saboda bata ga card din hannunsa ba,saura qiris tace masa ya dakata, Allah yasa batakai ga fada din ba ya zura mata card din a gefen jakarta dake maqale a hannunta

“Idan kin canza shawara you are always welcome,zamuyi aure don ki kula da fadeela kawai, wannan shine manufar,ni kuma zan baki dukkan ‘yanci da mafakar da kike nema” daga haka ya juya a cikin nutsuwa da kamewa ya fice.

A qalla sai da yabar gidan ta motsa daga gurin,ta gama tsorata da yadda ya kafeta da kallomsa,batajin ya taba mata irin wannan kallon kai tsaye,yadda ya nufota kanshi tsaye baya ma ko tsoron ya muhyiddeen ya dawo ya ganshi ya bata mamaki. Tsaiwarta ta gyara tana kallon card din, butter milk color da aka yiwa ado da ruwan gold. Tsaki taja,ta sanya hannu ta zaro card din ta watsar a wajen. Wai ta aureshi saboda ya raina mata wayo,shi baisan ko bashi bama ba zata iya auren kowanne namiji ba? ta rasa ma wa zata aura saishi? har abada,Allah yayi mata tsari.

Dukka ta gama wadan nan maganganun cikin banbami a ranta ita daya,ba tare da tasan gaddara tana sauya komai cikin qasa da sakanni ba kamar dai qiftawar ido. Kusan hakance ta sameta,bayan ta samu yaa muhyiddeen kamar yadda ya umarceta,ya kuma shaida mata a satin nan mahmud zai turo magabatansa da komai nasu,aurenta duka duka bazai wuce watan gaba ba,so basa son mata auren da bataso,idan tana da wanda takeso tayi gaggawar gabatarwa da abban nasu. Tashin hankali,shin a dazu ta gayawa toufeeq wannan maganar kenan da harshen malaiku? ,wata gudan data ambata shine ke neman tabbata a kanta cikin mintunan da basu wuce talatin ba?.

Fadin irin mawuyacin halin data fada ma bata bakine idanunta suka soye sai qirjinta dake zafi, batasan me yasa suka dage sai sun aurar da ita ba,bayan har yanzu bata gama healing ba,tana buqatar lokaci sosai,a galla shekaru goma ma a gaba idan sun bata dama.

Ita dava cikin dakin,qarfe biyu na dare tazo ta risketa ba tare da bacci ya ziyarceta ba,sai tarin fargaba da kalmar auren da yaa muhyi ya furta mata daketa yawo a saman kanta. Ta wacce hanya zata samu ta kubcewa wannan qaddararren auren?,dama dukkan wani aure a nan gaba har sai lokacin da taji zuciyarta ta gamsu ta aminta da aure?.

“Akwai” taji zuciyarta na gaya mata,amsar da taja hankalinta ta kuma sanyata neman baasin maganar

“zamuyi aure don ki kula da fadeela kawai wannan shine manufar,ni kuma zan baki dukkan ‘yanci da mafakar da kike nema” kalamansa suka dawo tarwai cikin kunnuwanta,kamar a sannan yake furta mata
SU.
[12/09, 5:41 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*

 

Leave a Reply

Back to top button