ILIMIN HADISI A SAUKAK
ILIMIN HADISI A SAUKAKE KASHI NA BIYU
Sponsored Links
بسم الله الرحمن الرجيم
(2) MENENE HADISI?
Hadisi dai shine abin da dangata shis ga anabi (S. W. A) kuma, kan Sharadi (3) Na farko Abin ya fada. (2) Abinda Ya aika (3) Abinda Ya tabbatar (Wato abin da akaiyi a gabansa bai ce komai ba).
(3) MENENE HADISI KUDISI?
Hadisi kudisi, shi abin da Annabi Yace Allah Yace, Kamar Wanda yace, ” ya ku bayina na haramta zalunci a kaina na sanya shi abin haramtawa a kanku kada kuyi zulunci” To wannan shine Hadisi kudisi. kuma yanada banbamci da Alkur’ani, saboda shi Alkur’ani. malai’ka yake saukar da shi daga AllaA zuwa ga Annabi. Amma Hadisi kudisi ba wani tsani, wato daga Allah zuwa ga Annabi.
(4) MENENE HADISI SAHIHI?
Hadisi Sahihi yana da sharadi (5) biyar kafin ya cika Sahihi, na farko (1) Isinadin Hadisi (Wato jingine) ya zamu ya sadu har zuwa ga Annabi. wane yaji daga wane, wane yaji daga wane. (2)Mai ruwaito Hadisin. ya zamo adalai ne. na (3) ya zamo mai hadane. wato duk abinda yaji baya mantawa. kuma babub kokwanto ga yawan haddar hadisai. na (4) Ya zamo babu wanda ya saba, ko ya baude cikin masu ruwayar hadisin. na (5) Ya zamo bashi da wata illa ta fuskar mallaman hadisi. kuma kubutace ga barin kowane irin sako.
اولها الصحيح وهو ما اتصل
إسنا دو ولم يشذ او يعل
يرويه عدل صابط عن مثله
. معتمدفى صبطه و نفله
(5) MEMENE HADISI HASANI?
Hadisi hasani shi ne wanda isinadin sa ya sadu da Annabi (Munifa. wane yaji ga wane) amma ya tara sharudan Sahihi. sai dai karan cin hadasa baibkai na Sahihiba. shima yana sharudai guda 5 biyar. na farko (1) saduwarsa (wane yaji ga wane) na biyu (2)adaline mai ruwayar. na uku (3) karan cin haddar mai ruwayar, wadda batakai ta Sahihi bab. na hudu (4) Ya zamo bashi da wani kauciya, wato sabani ruwayar. na biyar (5) ya zamo bashi da wata illa. kamar samun wanda ba adaliba a cikin masu ruwayar.
والحس المعروف طرقا وغدت
رجاله لا كالصحيخ اشتهرت
Sai a taremu a kashi Na (3)
Daga dalibin ku
Musa s zage .