Inda rai 4
*INDA RAI*…🥰
*By*
*MARYAM ABDULLAHI*
💔💋(Oum Shaheed💔💋)
*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION*
Page 04
*Na sadaukar miki da wannan page ɗin ƙawa ta gari, Balkisu*🥰🥰
Bismilla’hirrahma’nirrahim
Sosai ƙirjin Barister Sudais ya ke ɗagawa da sauri sauri, wanda hakan ya haifar masa da matsanacin ciwon kai, saurin zama ya yi gudun kada ya faɗi a wajan, “Ambassador ne ya lura da halin da ya ronnasa yake ciki, “matsowa ya yi kusa dashi ya ce, “kana lafiya kuwa?”ɗago kai ya yi ya kalli mahaifin nasa ya ce, “eh Daddy, cikin ƙarfin hali ya sa kai yabar wajan, da kallo Daddy yabi ɗan nasa cike da kulawa, har sai da ya dena hango sa sannan ya ɗauke idonsa,
Gefe Maigari da Daddy suka je suka tattauna, bayan dogon lokaci aka ɗaura auran Maryama.
Barister yana shiga gida kai tsaye ɗakin kakarsa ya nufa ya kwanta akan kujera, ya rufe idonsa yana tuna farkon haɗuwar sa da Maryama.
“Tuƙi ya ke yi cikin ƙwarewa irin ta wa’ƴanda suka san mutumcin kare dukar ƙasa, amma duk da hakan bai hana hatsarin faruwa ba, “kawai gani ya yi yarinyar ta shigo gabansa babu zato bare tsammani, ya so ya kauce mata amma inaa,, saida ya bugeta a ƙafarta, cikin sauri ya parker motar a gefe ya fi to, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi ganin kamar ba ta motsi kwata kwata, jiki a mace ya ƙarisa har inda ta ke ya sunkuya a saitin kanta, maa shaa Allah, shine abun da yazo bakinsa, ya ƙura mata idanu, yarinyar da ke kwance a gabansa bazata wuce shekaru goma ba, fara tas, mai dogon hanci, bakinta ɗan tsurut ya ƙurawa idanu yanajin wani shok a jikinsa, zuciyarsa ta hau bugawa da sauri sauri, “ita kuma yarinyar jin shirun ya yi yawa sai ta buɗe ido ɗaya a hankali, so take taga ko mai motar ya tafi, ta tashi itama ta ƙarisa makarantar dama tuni ta yi latti, amma mai, tana buɗe idanun nata basu zame ko ina ba sai cikinna Barister Sudais Auwal, ƙiriiiii sukayi wa juna ko ƙiftawa babu, kamar daman can sun san juna, “Maryama ta ce” Malam lafiya kuwa? ka bugeni kuma ka tsaya kallona?? kwalelen karw da hantar kura, kabani hanya na wuce, daman nayi latti, sharrrrr sai ganin hawaye Sudais ya yi suna anbaliya a fuskarta, har wannan lokacin ya kasa cewa uffan. “Yaude Allah ya soni na yi addu’ar fi ta a gida, “bai san laoka in da dariya ta kwace masa ba, dan yagane mai ta ke nufi, wato ta yi addu’a bazai iya sace ta ba, “sannu baiwar Allah, fatan bakiji ciwo ba, tura ɗan ƙaramin bakinta ta yi a hankali ta ce”sai yanzu zai wani tambayeni, bayan da na karye yanzu da gurin ya yi tsami, wato saboda ba jikinka bane ko? ” kiyi haƙuri Beby, ai tunda naga kina tura baki babu kuka nasan bakiji wani ciwon kirki ba. “Da sauri ta kallesa saboda ba tayi tunanin zaiji abun da ta faɗa ba, “saka hannunsa masu taushi ya yi ya ɗago ta, ƙara ta fasa masa a dai dai kunnensa, saura kaɗan ya saketa ta kara faɗowa,”lafiya kuwa? bata kallesa ba taci gaba da kukanta harda sharce hanci, a hankali Sudais ya tsugunna dai dai kafafunta ya ɗaga yana dubawa ko zaiga in da taji rauni, amma baiga komi ba sai wani ɗan kujewa da yagani a wajan dunduniyar ƙafar, “ina ne yake miki ciwo? ko kallansa ba ta yiba, gani ta na ɓata masa lokaci kawai ya ɗauketa ya sa a motar ya nufi fadar mai gari, gidan kakansa, mahaifin Dadynsu, wanda yake zuwa dubasu duk ƙarshen wata.
Acan aka gama duba jikin Maryama bayan ya faɗa musu abun da ya faru, Naja’at, ƴar gidan ƙanwar Dady da suke Uba ɗaya, ita ta kama Maryama ta rakata har gida wanda kuma umarnin Barister ne.
Tun daga wannan ranar duk sanda ya shigo ƙauyen sai ya saka Naja’at ta kira masa Maryama sunyi karatu, a haka sukayi wani nugun sabo da juna wanda a ɓangaran Sudais kawai jira yake ta ƙara girma ya sanarwa kakansa mai gari. Wannan kenan..
Delhi
A hankali Imran ya ke buɗe idanunsa har ya samu suka gama wartsakewa, akan singalalin hanunsa da ya ke saƙale da ƙarin ruwan da abokinsa doctor Anwar ya saka masa, ya rabbi, wai maiyake faruwa danine kan? anya keɗin mutumce? Alhamdulillah ala lulli halim, ya Allah ka kawo mini agaji cikin lamurana, zare ƙarin ruwan ya yi ganin har ƙarfe 2:30 ko sallah baiyi ba, ya daɗe ya na addu’ah kafun ya mike ya nufi falo, kwance yaga Bhu-Ali, ya na bacci, kana ganin baccin kasan baya masa daɗi sam, a kasalan ce ya nufi hanyar dinning area, abinci ya ɗiba yaci kaɗan saboda sam bayajin daɗin bakinnasa, harya gama Aliyu bai ta shiba, a ransa yake tunanin dole zai koma gida cikin satinnan, dole zai tsananta neman ta kafun lokaci ya kure masa.
Ɗakin da yake zane ya nufa, komi ya na nan kamar yadda ya ajiyesa, ƙarisawa ya yi har gaban pic ɗin dayafi ko wanne girma a ɗakin, shafa fiskarta ya keyi ya na maganganu kamar yadda ya saba koda yaushe, ina kika shiga? a’ina zan ganki? kafun kace kat sai gani ya yi yana zubar da hawaye kamar wata mace, tabbas so masifa ne babba, musamma idan abunda kake so ɗin bakasan inda zaka same saba.
Ko sallama babu haka Malam Bukar ya shigo cikin gidannasa, kai tsaye ya nufi har ɗakin da yasan Maryama tana ciki, “kina ina? baƙar munafuka, algunguma, kekan bazakiyi albarka ba, wato saida kikasan yadda kikayi kika rusa auranki da ɗan ɗan uwana ko? kina ina nace? “rumtse idanu Maryama ta yi tanajin kanta na juyawa, duk da ya kamata ace farin ciki ta keyi, jin fasuwar aurannnata, amma kuma dawa kenan aka ɗaura mata aure? bayan ta gujewa auranta da Bello? maiyake bibiyar rayuwarta haka? “Allah yasa hakan shine mafi alheri a cikin rayuwarki Maryama, cewar Inna Rabi, kafun tace uffan har Malam bukar ya iso cikin ɗakin, “to maza ki tattara inaki ya naki zuwa ƙarfe biyar zaki bar mini gidana, ki manta kina da Uba kamar yadda kika rasa Uwa, ki ɗauka tare muka bar duniya, banza shasha, wato ke gaki baƙar munafuka, Allah ya raka taki gona, kuma ƙwandalata bazan kashe wajen saya miki ko tsintsiyaba, “sosai take son tayi kuka amma inaa, sam yaƙi zuwa, sai wani ɗaci da takeji acikin ranta, shin anya Baba shine mahaifinta.?
Zaune suke a gaban wata korama mai gudana, ruwane ya keta gudu fari tas, wasa ta keyi da ruwan tana zaune a kan wani dutse dake gefen ruwan gwanin ban sha’awa, “ta bayanta ya taho sannu a hankali harya ƙariso inda take, jin motsi a bayanta yasa ta juya da sauri amma me, wayan bata ganin fuskarsa, sai bayansa kawai, saka hannu tayi zata jawosa kawai taji an jata ta faɗa cikin ruwan tsumdum….
A firgice ya farka ga haɗa gumi sharkaf, addu’ad tashi a bacci yayi sannan ya tashi yaje yayi wanka yasa wando tree qwater da ƴar wata riga na shan iska Palo ya fi to ya samu angama gyara komi har Bhu-Ali ya tafi kenan? ya tambayi kansa, bayan ya gama diner ya kishin gida ya danna wayarsa sai gani yayi ta buɗe ƙofar ta shigo ko sallama babu, ɗauke idanu yayi daga kallonta yana ɓata rai kamar yaga makiyinsa, “ƙarisa shigowa matashiyar budurwar ta yi har kan kujerar da yake zaune tasamu waje daf dashi ta zauna, ko kallon inda take baiyiba balle tasa ran zai mata magana,itama de batace masa komi ba, a haka har suka shafe kusan minti talatin, sannan ya tashi a hankali kamar mai tsoron wani abun, ya ƙarisa kusa da ita ya saka hannu ya zame nata data ɗaura akan ƙafarta, sannan ya gyara ƙafarta data ɗaura ɗaya akan ɗaya, ya mqida kansa gurbin daya cire hannun nata, “murmushi Sakku ta yi dama tasan halin ƴan kayan nata, shiya idan taga yanayinsa take barinsa harya saƙƙo da kansa, ɗaura hannunta tayi akan kwantaccan kuma lallausar gashin kansa tana shafawa a hankali, sunkuwa ta yi dai dai kunnensa tana masa magana” i need you Beby, lumshe mata gajiyayyun idanunsa yayi ya kasa cemata komi, saboda yaji maganar har cikin kansa, ga wani ƙamshi datake fiddawa mai rikita lafiyar duk lafiyayye daga nan wasan ya fara, a hankali a hankali yaji komi najikinsa yana janyewa, lafiyar da yake murna yasamu ta fara tafiya, kuzarinsa ya kuma tankar na wanda ya shekara ɗari a duniya, kansa yaji ya sara da ƙarfi, ganin halittar jikinsa ta kuma ta lafe, ture Sakku yayi da ɗan sauran ƙarfin da ya rage masa, toilet ya nufa ya sakarwa kansa ruwan sanyi, amma maimakon yaji dama dama saiji yayi jikinsa ya fara wani irin kaɗawa, take wani zazzafan zazzaɓi ya kawo masa ziyara.
Cije baki Sakku ta yi tana jin baƙin ciki a cikin ranta, tuni duk wani gaɓa na jikinta ya mutu, tsikar jikinta ya mike sosai, sosai take buƙatar samun nutsuwa a halinda take ciki, taci alwashin sai ta samu kan Imran ko ta halin ƙaƙa.
Shigowar Inna ɗakin ɗauke da abinci shiya dawo da Sudais duniyar da tafi, “wai mijin anya kana lafiya kuwa? yau ɗin tun zuwanku mun kasa gane maka, gacan Naja’at sai ƙorafi ta keyi, “murmushin ƙarfin hali yayi yace, ” ina lafiya matar, kaina nane ya matsamin ɗazun, amma dana ɗan kwanta naji ya lafa, mai kika dafawa mijinnaki? ya ƙarisa tambaya yana mai saƙƙowa kasan kapet ɗin, “murmushi Inna tayi tace masa, mai zanko dafa maka idan ba abunda kafi soba? tuwon farar shinkafa ce,da miyar taushe, washe baki yayi ya hau cin abincin cikin nutsuwa.
A can fadar mai gari bayan kowa ya watse a ka bar ɗa da Uban suna ƙara tattaunawa, hmmm yanzu Abba taya zamu ɓullo wannan almari? ina tsoron kada su ɗaukeni a mara adalci? itw mahaifiyarsa tanada burin haɗasa aure da ƴar ƙanwarta Sahla, sannan ga ɗan uwansa, kuma yayansa, zai ɗauka babanci aka nuna masa, tunda shima bayi da auran. Murmushi mai gadi yayi yace” a kaf cikinsu akwai wanda ya isa yayi abunda Allah bai soba ne??idan har babu to ka kwantar da hankalinka kaji? ita mahaifiyar tasu kaji da ita, shikuma abokinnawa a duk sanda ya dawo ka turominshi da kaina zammasa bayani, yanzu zan tura Ramlatu ta taho da ita yarinyar, kafun mungama da shi lawwyer ɗin ko? “to abba.
Sosai yaji maganar kamar daga sama, mai kenan? wai an ɗaura masa aure da Maryama, ya Allah, maima ya kamata yace? ko ya aikata, su Daddy duk iya yinsu sun kasa gane asalin gane miye a ransa…
Writing by Oum Shaheed😍😍🥰🥰