Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 50

Sponsored Links

CHAPTER 50

Jan hannunta laila tayi itako sai wani turjewa take cike da jarumtar da tanemo ta yafawa kanta amma ƙasan ranta fal tsorone dakuma fargaba dan cikin ta hautsina mata yake kaman zata saki zawo sabida tsorata da tayi da kalman wannan Alhajin na rashin imani.

Suna kaiwa bayan wasu motoci tasaki wani irin mahaukacin ajiyar zuciya tana dafe da setin ƙirjinta dake mata wani irin lugude sai numfashin wahala da take saukewa, akai akai saida ta seta nutsuwarta sannan ta ɗago da dubanta ga laila tace”kinceceni wallahi dakyar nasha.

Dariya laila ta fashe dashi saida tayi harda riƙe cikita tana mai nuna fuskar Aisha tace”kalli fuskarki gaki da tsoro amma bakin ki baya mutuwa nide abunda kawai zance dake ki kula ba ko ina zakina sake baki kina magana ba,irinsu Alh sunusi basu da imani wallahi zasu iya iyin komai saboda farin cikin su data iyalansu.

Ahmad dan sussunar da kansa yayi cike da ladabi yace”dan Allah daddy kai hakuri akwai yarinta tattare da ita be dace kaida kake babba kabiye mata ba,dan biyematan da kaine yabata daman sakin maganganu haka batare da ta tauna abunda zata faɗi ko kula da kaiɗin babba bane ba,daddy kasan sha’anin ƙuruciya”kai dallah rufama mutane baki anfaɗa maka ƙuruciya haukace toh nabi ƙuruciya dagudu ba wando nace nabi ƙuruciya dagudu ba wando tuntuni yariya tana ta zuba iya shegenta bakai magana ba sai yanzu zaka wani kashe murya kaman karuwa taso damfara kana wanu cewa sha’anin kuruciya.

To wallahi muddin bata farantawa shalelena rai ba kuwa itama bazata taɓa samun kwanciyar hankali ba,kwanciyar hankalin ta ɗayane kawai takawo kayan sannan tazo ta bani hakuri yanzun nan,ya kare magana yana huci kaman wani zaki.

“eh wallahi daddy sai takawo kayan nan kuma ta gogemun takalmi da hijabin ta sannan ta duƙa har kasa tabani hakuri basmace ke wannan magana shiko daddyn nata sai wani washe baki yake kaman gonan auduga,karshe Ahmad tafiya yayi ya barsu tsaye a wajen dan kansa har sara masa yake dan kwata kwata ya tsani tashin hankali da hayaniya arayuwar sa,ko meetin sukeyi da ma’aikata ko abokan kasuwancin sa yawanci khalid ke wakiltansa shike gudanar da komai.

Taku yasoma yi dan barin wajen cike da izza da ƙasaita kai kace jinin sarautane shiɗin”kai Ahmad Ahmad ina zaka baka kirata tazo ba,da karfi Alh sunusi yake kiran sunan sa yana masa magana dan ganin kaman yanufi parkin lot,bema nuna yaji shi yayi tafiyarsa yana isa wajen yabude motarsa ze shiga sai ya hangota duƙe dafe da kirjinta fasa bude motan yayi yanufi inda suke yana zuwa be tsaya yimata magana ba kawai ya damƙi hannunta yanufi bakin motarsa yabude yatura ta ciki da karfi sannan shima ya zagaya yashiga mazaunin driver key yama motan sannan ya figeta da wani irin karfi ya bar wajen wani irin tsorone yasake kama Aisha ji take kaman ta saki futsari awando tawani waro ido cikin in ina tasoma cewa”da Al lah kamun rai karage gudun nan dani wannan gudun wallahi banshirya mutuwa ba,akwai buruka da yawa da nakeson cikawa kafin mutuwa ta.

Banza yamata saima kara gudun motar daya sake duk inda motar su ta gilma sai mutane sun bisa da kallo masu abun hawa kan saide sune suke kauce masa hanya.

Ganin hakan da Aisha tayi sai yasake tsoratata dan Aisha duk jarumtarta da rashin bari takwanan ta amma akwi tsoro dan ko adaidaita ta hau idan taga driver na gudu sai tayi masa magana tayi yanda yaraje gudun dan ita anata ɗan ƙaramin tunanin duk wani hatsari dake faruwa gani take gangancin driver ke jawowa da suna kula da yin tuƙi cikin nutsuwa da hakan bazata yawaita faruwa.

HAJ MARIYA
tunda jiya dasukayi maganan nan da ƙawarta Haj balkisu hankalinta ba akwance yake ba,dan haka yau koda Alh sunusi yafita daga gidan ita ma shiryawa tayi ta nufi gidan kawartata dan tun daga bakin ƙofan shiga falon take ta ƙwaɗa sallama mai aikin gidan ne ta amsa mata tana mai bata hanya ta wuce a wulakance take kallon matar”hajiya fa?Tayi tambaya kaman wacce akace dole sai tawa matar magana.

“Tana ciki ƙaraso mana hajiya kya tsaya anan matar ke magana cike da girmamawa kaman bataga irin kallon da hajiya mariyan ke binta dashi ba.

“A’a lale marhabin kece tafe da sanyin safiyar nan shigo shigo da alama de akwai labari?hajia balkisu kenan dake zaune a falo hannunta riƙe da jarida take wannan magana.

Dan sakin fuska hajia mariya tayi tana ƙarasa shiga ciki nan suka shiga gaisawa inda hajia mariya ta kalli ƙawartata tace”ba dole kinganin nan ai tunda mukai maganar nan ta jiya hankalina ba aƙwance yake ba,kece ina can nasaki baki ina bacci ina baza izzar ƙarya inci in zubda masai ashe ku kuna nan kunama kanku tanadi kun barni baki hangame.

Dariya hajia balki ta kwashe mata dashi sannan tace”kai kawata ashede kanki na jaa yo aina dauka duk shekarun nan da mukai dake keɗin ƴar hannuce bansan ba haka kike ba ai da tuni munɗaura ki a network yanzu ma bata ɓaci ba inde kin shirya cin duniyarki da tsinke bismillah kafin nan zan gabatar miki da wata ƙungiya da muke da ita.

“Ƙungiya kuma?
Tafaɗa kaman maijin tsoro,cikin ko in kula da yanayin da taga hajia mariyar tashiga na shock tace”eh amma fa bata komai bace ta huce taƙaicine muna da ƴan shawalwalan ƴan mata da samari domin huce haushin ragon miji,ajiyar zuciya haj mariya ta sauke jin abunda ƙawartata ke fadi tace”yanzude ba wannan ba ai sai kanada yan canji zakaji daɗin huce haushin yande faɗamun hanya mafi sauki da zanbi dan ganin nima na yagi rabona kafin maganan wannan boka ta tabbata kinga ƙwara na tsira da wani abun nima dan gudun gori.

Aisha duk tasha jinin jikinta saima kanta data saka tsakanin cinyarta tasaki kuka bata yarda ta ɗago koda wasa ba amma tanajin yanda yake sharara gudu da kakkaucewa ababen hawa dakuma yawan horn dayake hakan na tabbatar mata da cewa haryanzun gudu yake,can aji yaci wata mahaukaciyar burki dasata furta”innalillahi shikenan yakashemu Allah yajiƙaina.

Maganar tata yaso bashi dariya duk da yanayin fushi dayake ciki amma ya danne bata ankara ba,taji an fuzgota da karfi har hannunta yana buguwa da murfin motan”shikenan wayyo Allah Anna gawani nan ze kashe miki ni takare magana cikin gunjin kuka.

Tsawa daya daka mata shiya nitsar da ita”dama kina da tsoro kika tsaya kinawa mutane rashin kunya ko,ɗan shiru yayi ganin de har yanzun kuka take kuma tamaƙi bude idonta ta kallesa.

A hasalale ya cigaba da cewa ba jininki rashin kunya ba,to kuwa zaki mutu ba tare da burukan naki son cika ba wawuyar yarinya dubeki mitsitsiya dake amma cikinki fal rashin kunya to kuwa inde irin su Alh sunusi zaki taɓa kuwa kishiryama mutuwa,yana kare faɗin haka yayi shige warsa motan ya baɗeta da ƙura,a rikice ta buɗe idonta ganinta ƙofan gida yasata sauke ajiyar zuciya tana murguɗa masa baki da cewa”oho de nasan kaji haushi daga kai har ita matar da zaka aura da ɗan tsohu wai harda wani cewa yi maza kije ki dauko kayan nan ki kawo yanzu ta kare faɗa tayi shigewarta cikin gida tana sake riƙe rigar da kyau ashe dama ɗamara tasha da rigan da zasu yin sallah.

Dariya tasake kwashewa dashi kamar wata mahaukaciya sabon kamu taƙara da cewa daman kaine Alh sunusin makashin iyayena to kashirya ma uƙubarka dan ina nan tafe gareka.

ALH SUNUSI
Bayan barin Ahmad m’aikata kiran Alh badamasi yayi cike da fushi yana dagawa yashiga magana”yanzu badamasi wai har kamata yaron nan ze wulakanta ya shanyamu a rana?

Alh badamasi jin abunda abokin nasa ke faɗi yamiƙe tsaye cikin rawar murya data jiki yace”wai wani yaro kake magana akaine? Alh dan Allah yi hakuri kamun bayani dalla dallah.

“Kabari kawai badamasi raina aɓace yake zucitarta sai tafarfasa yakemun yanzu kaman Ahmad wai shalele taga wani ɗinkin kaya daya ɗauki hankalinta tace tanaso amma yamurza toƙa a idon sa yanuna bema santa da ba.

“Shi Ahmad ɗinne yama haka Alh badamasi ya tambaya daga ɗaya ɓangaren”kwarai kuwa karya zanma ne badamasi kakira sheɗanin ɗan naka kaji inda yake”yanzu kuwa yafaɗa tana kashe wayan yashiga kiran Ahmad ɗin daya sauke Aisha yana hanyarsa ta komawa gida.

Saida yamasa kira uku sannan ya danna bluetooth dake maƙale a kunne sa dukda besan waye mai kiran nasa ba.

“Asslamu alaikum yafaɗa madadin amsa masa sallamar da yayi saijin saukar manyan boma bomai da mahaifin nasa keyi sauke masa,magana ta karshe inaso kakoma yanzu kayi masa duk abunda yake bukata inde kanason ganin farin cikina yana kaiwa karshe betsaya jiran jin ta bakin Ahmad ɗin ba yakashe wayansa yana sauke numfashi dacewa yaro anama gata amma baka gani.

Ahmad kuwa cike da ɓacin rai yakira wayan Basma wacce tacika tayi fam kaman zata fashe dan fushi ganin kiran nasa ta juya ta kalli daddyn nata dake tsaye yahaɗa zufa sai gogewa yaki da hancky tace”laa daddy kalli yakirani tafaɗa tana nuna masa scream ɗin wayan nata”dauka muji mai kuma zaice mana haɗa fuska tayi taɗaga madadi bata hakuri da tayi tsammani ko rarrashinta daga gareshi saɓanin haka tajj dan tana ɗaga waya yace”kiyi maza kija mahaifinki kibar wajen kafin nazo nasameki idan kuma muna abu kika sake saka iyayenmu ciki abun baze mana daɗi ba,idan ke bakisan girma da ƙimar naki iyayen ba ninasan nawa dan haka……sai kitt taji alaman ankashe waya sakato tayi tana karewa wayan kallon ganin yanda daddyn nata ya zubamata idon dan son jin meke faruwa sai cewa tayi”daddy yace mutafi gida kawai”dan abu kazan ubansa ni yaron nan ze nunawa duniyanci to wallahi yama ubansa badamasi dan ko shi daya kawoshi duniya be isa musamun magana ko na faɗi abu yaƙi yi ba to wallahi yama ubansa dan ni daidai nake da ubansa yi hakuri shalele mutafi kina zaune ubansa ze sakosa a gaba har gida zezo yabaki hakuri idan ko beyi ba to sunana ba sunusi ba…

 

Leave a Reply

Back to top button