HARSHEN HAUSA

KA’IDOJIN RUBUTUN HAUSA DA KALMOMIN HAUSA.#001

Sponsored Links

        KA’IDOJIN RUBUTUN KALMOMI DA 

    YADA KAMATA KA SANI, KAFIN RUBUTU       
                  CIKIN HARSHEN HAUSA.
                         KASHI NA FARKO
Gabatarwa 
   Daga 
Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.
  by
 msz
Tun lokaci mai tsawo da ya shude, na lura da kura-kurai wajen rubutu cikin harshen  Hausa. Na lura da hakan ne, sakamakon karancen mukalolin da aka rubuta cikin harshen Hausa, littattafan Hausa, littattafan hikayoyin da aka rubuta cikin harshen Hausa, wasikun da aka rubuto mini, rubuce-rubucen da ake yi a jikin motocin hawa, irin su manya motoci, misali, rokoki, Daf-Daf da dangoginsu. Bas-bas har zuwa mashina da kekuna da muke hawa. Na sake lura da kura-kuran ma a rubuce-rubucen da ake yi a gaban shaguna don talla, da kuma rubuce-rubucen da ake yi a jikin allunan kan hanya.

  Kura-kuran sun hada da: Rubuta kalmomin Hausa barkatai, hada kalmomin Hausa ba a wajen da ake hadawa ba, ko raba kalmomi ba a wajen da ake rabawa ba (Word margins and divisions), ko kuma kalmomin su kunshi bakake iri daban-daban, wanda a ka’ida ba haka ya kamata su zo a rubutu ba, da kuma cusa kalmomi ba a muhallin su ba, wani lokaci kuma rashin amfani da ka’idojin rubutu (Orthography) a wajen da suka dace, ko kuma rashin amfani da su ma kwata-kwata da matsaloli da suka yi cacukwi da rubutu cikin harshen Hausa.
   
  Kodayake wannan ya faru ne,
sakamakon ba asalin Hausawa ne, suka fitar da Manhaja ko Jadawalin rubutun Hausa ba. Idan aka koma ga tarihi za a ga irin su Farfesa Neil Skinner, Daraktan Hukumar NORLA da George Percy Bargery, Mawallafin Kamusun Hausa da Hanns Vischer, wanda ake kira Dan Hausa da Dokta R. M. East, Shugaban Hukumar Talifi da Mista. L. C. Giles, Editan farko Bature na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da sauransu, su ne suka fitar da yadda za a yi rubutun Hausa. 
 Kasancewar su ba Hausawa ba, bugu da kari ba su san furucin Hausa da kuma kalmomin sosai ba, sai rubutun Hausa ya taso cikin hajijiya da kuma rudani, wanda ya janyo har zuwa yanzu ake ta tafka kura-kurai, rubutun kuma ya ke ta tafiya da dingishi, face wadanda suka tashi tsaye, don fahimtar yaya ka’idojin rubutun Hausa suke kafin su yi rubutun Hausar.
       Sakamakon matsalolin da suka cunkushe rubutun Hausa, sai aka yi manyan taruka guda uku, domin daidaita ka’idoji da kuma kalmomin HaTawaon farko an yi shi ne, a Birnin Bamako da ke kasar Mali, daga 28, ga watan Fabrairu, zuwa 5, ga watan Maris a shekara ta 1966.
 Taro na biyu an yi shi ne, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a ranar 21, ga watan Yuni a shekarar 1970, 
Sai kuma na uku da aka yi a Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, a cikin Jami’ar Bayero da ke Kano, a watan Satumbar shekarar 1972. A cikin wadannan tarurrukan an yi gyare-gyare wa ka’idojin rubutun Hausa na cikin littafin ‘Hausa Spellings’, littafin da turawa suka dora Hausawa kansa a hanyar rubutu, wanda kuma shi ke dauke da Manhaja da Jadawalin rubutun Hausa.
Anan zamu diga aya sai kashi nagaba sai mu dora inda Aka tsaya.
                         Domin Karin
 Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 

shhanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

Leave a Reply

Back to top button