Kanwar Matata 6
🦜 *_K’ANWAR MATATA_*🦜
_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_
☀️ *ZAFAFA WRITER’S ASSOCIATION*☀️
Page 6
“Ni kai min shuru da wannan zancen banzan naka. Sam Khalil baka k’aunar gudun b’acin raina ko? Kafi kowa sanin su wanene y’an uwan mahaifinku, sam basu raina abun magana. Mahaifin naku ya kwanta dama, amma duk da hakan baza’a bar ni na sarara ba. Menene a ciki idan ka auri Nina d’in. Kuma da kake zancen y’ar iska ce, kai ka tab’a kamata red-handed ne? Nifa bani son sharri da k’azafi.” Mik’ewa Khalil yayi tare da fad’in, “I love you Hajiya. Sai na dawo. Ki cewa Laure taje laundry ta kwaso min kayana ta kai d’akinki. Kada ta sake ko wajen k’ofar d’akina taje.” Yana gama fad’in haka ya nufi k’ofa. Aunty Maryam sai k’umshe dariyarta take yi ganin irin uban tagumin da Hajiya ta buga tana k’arewa Khalil kallo har ya gama ficewa daga d’akin. Mai do da dubanta ga aunty Maryam tayi tare da fad’in, “Saki, saki dariyarki Maryam.” Dakyar aunty Maryam ta iya gimtse dariyar tare da fad’in, “Hajiya ba dariya zan yi ba.” Gyad’a kai Hajiya tayi tare da fad’in “Uhm, Maryam ban san mai Ibrahim ya maida ni ba. Gaba d’aya ya mai dani kakarsa. Kina ji a gabanki ina yiwa yaron nan magana amma don tsabar wulak’ancin sai ce min yayi wai wani I lobiyu sai na dawo. Har da bani sak’o in fad’awa Laure. Dani yake zancen. Allah ko yak’i Allah sai yayi aure nan kusa. Idan har yace bai son Nina, ba zan takura masa ba, amma kuma dole ne ya fiddo wacce yake so. Na gaji da zagin da iyayensa suke min a kansa. Shekaru talatin da biyar, yana da aikin yinsa, to uban mai yake jira kuma. Muhalli dai ga b’angarensa nan kullum cikin kwaskwarima da gyararraki yake yi. Yaron sai shegen k’arya da kashe kud’i kamar bai san zafin nema ba. Kina gani akan dank’on da kullum bashi da aiki sai na taunawa kamar tsohuwar karuwa sai yayi takakka ya biya kud’in jirgi har wata k’asar. Zai ci gidansu dani yake zancen.” Fad’in Hajiya tana mai jawo kulan ramar dake gabanta ta bud’e ta soma ci. “Hak’uri za ai Hajiya. Addu’ar tagari za kiyi masa ya zab’o tagari a hankali.” Rama cike a bakinta tace, “Rabu dashi Maryam. Idan ya kai ni bango, bazawara shikan wawa zan samo masa kuma sai ya aure ta.” Dariyar da aunty Maryam keta rik’ewa ta kufce tare da fad’in, “Lallai Hajiya kin so rigima. Tun Khalil na yaro ke kike bamu labari komai sabo yake so. Duk wani abu da wani ta riga sa amfani dashi bai tab’a amfani da abun balle kuma ace matar da zai aura wani ya riga sa auran ta. Lallai Hajiya kin d’auko da zafi. Har na hangi Khalil gashi can da auran bazawara. Kin san Allah Hajiya barin garin nan zai yi baza ki sake ganinsa ba sai an d’ebi shekaru.” Rufe kulan Hajiya tayi tare da fad’in, “To ya tafi mana Maryama. Ni na huta ma da magana. Ni da na san haka zai rika jawo min zagi, da ban takura sai ya bar wannan k’asar ya dawo Nigeria da aikin sa ba. Sai shegen kwalliya da fesa manya-manyan turaruka masu shegen k’amshi da tsada, amma duk uban kwalliyar nan abokansa sunce min ko hakoransa y’an mata basu gani a waje. Ni ko ya yake kula da marasa lafiyan oho! Kin tuna wannan yarinyar Salma da ta mak’ale masa daga ya dubata a asibitinsa? Yarinyar arziki har gida nan take zuwa gaishe ni. Amma yaron nan sai da ya koreta ta daina zuwa. Kai ni lamarin Khalil na ban takaici. Ni ko dai aljana ce ta aure shi?” Aunty Maryam gyara zama tayi tare da fad’in, “Hajiya babu wata aljana lokacine kawai bai yi ba. Amma idan yayi shi da kansa zai kawo maki budurwarsa har gida.” “Allah ya amsa Maryamu ko na huta da mita da kiraye-kirayen wayar dangin ubansa.” Fad’in Hajiya. B’angaren Sarah kuwa, ko da ta koma d’akinsu, can k’uryan gado ta hau ta nannad’e cikin bargo sabida wani zazzafan zazzab’i daya lullub’eta. Can kamar kusan mintuna talatin, lokacin zazzab’in ya k’aru sosai taji shigowar Hassana wacce dawowarta kenan daga yawon ta zubar d’inta. Zama tayi a bak’in gadon ba tare da ta lura da Sarah dake kwance cikin bargo ba can k’arshen gadon. “Honey wai kana nufin baka gaji dani ba? Mu kwana muna abu d’aya amma ace ka kasa gajiye dani.” Wani dariya Hassana ta saki har da kwanciya flat tana kallon ceiling ga dukkan alamu taji dad’in amsar da wanda take waya dashi ya bata. Don har da wani mik’a tayi. “Kamar ka sani kuwa. Wallahi duk ka tada min da sha’awata. Kasan fa muryanka kad’ai ma kawai na sakani haniniya.” D’an shuru tayi sai kuma tace “Allah ko! To ban mintuna uku kacal zan kira ka yanzu.” Tana gama fad’in haka ta yanke wayar tare da mik’ewa ta cire kayanta gaba d’aya har da P&B. Kasancewar idanun Sarah a kulle suke, bata san abunda Hassanar ke aikatawa ba. Sai bayan kamar mintuna goma ta jiyo nishi sama da kuma maganganun batsa. A hankali ta bud’e idanunta tare da d’an d’ago kanta da take jinsa kamar zai tsage. Gabanta ne yayi wani irin mugun fad’uwa ganin yar tata tsirara da wani abu mai shape d’in al’aurar namiji yana wani irin k’ara ita kuma tana turawa tare da gogawa a gaban nata. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel! La’ilaha illallah Muhammadur Rasulillah!! Allahumma arji’ini fi musibati.” A razane Hassana ta d’ago ta kalli Sarah, ita kuma Sarah saurin kawar da kai tayi saboda ganin al’aurar wanda take video call dashi ta cikin wayar don lokacin da Hassanar ta razana wayar ta fad’i kuma ba kifawa tayi ba. Mugun tsaki Hassanar taja ganin Sarah ce, don ta d’auka wani abun tsoro ne. D’aukar wayarta tayi tare da fad’in, “Baby mu cigaba. Wannan banzan K’anwar tawa ce da nake baka labari ce.” Fad’in Hassana. Sarah kuwa duk da rashin k’arfin jikinta da kuma sarawar da kanta yake yi, haka nan ta mik’e ta dafa bango ta fice daga d’akin don baza ta iya wannan mummunar ganin ba. Tana fitowa daga d’akin wani irin yunk’uri ya taso mata na amai, cikin sakwanni biyu ta soma kakari tana kelaya wani irin amai mai mugun wuya kasancewar ba wani abun kirki bane a cikinta. Don hatta ruwa idan tasha dawowa yake yi. Ruwan bohol ko kuma fanta mai mugun sanyi ne kawai yake iya d’an zama a cikinta. Shima kuma sai tana sha tana hutawa. Lami, Aina’u da Nuratu na tsakar gidan amma babu wanda ya iya mik’ewa yazo domin taimakonta. Tsabar yanda take amai d’in hatta fitsari zuba yake yi a jikinta. Tun tana amai a duk’e har ta zauna dirshan a k’asa tana bubbuga kanta da hannunta amma babu wanda ya tanka balle ya kawo mata d’auki. Nuratu ma Wak’a ta soma yi na habaici da isgilanci. Azaba ya ishi Sarah, bata san lokacin da ta soma d’aga hannu tana fad’in, “Babu mai taimako nane? Lami ki taimaka min dan girman Allah. Nuratu, Aina’u, ku taimaka min zan mutu, wallahi mutuwa zanyi.” Lami ce ta soma magana, “Dan ubanki ki mutun mana. Kowa da kike gani a cikin gidan nan kud’insa yake cirewa ana yi masa hidima. Kema da kin cire mugun hali sa son kin fad’i uban cikin dake jikinki, da yanzu shalele kike a cikin gidan nan. Amma tunda kince mugun hali kika saka a ranki, mugun halin ya cece ki.” Tana gama fad’in haka ta sab’a Yabo d’an wajen Na’ima a baya, shi kuma ya tak’ark’are ya ganna mata wani arnan cizo a tsakiyar bayanta sakancewar baya k’aunar goyo, ita kuma Lami burinta tayi ta kima sa a baya don Na’imar tace tana kula dashi sosai. Don duk cikin y’ay’anta, tafi k’aunar Yabo. Zafin cizon ya saka Lami tafiya ta gaba a gigice ta had’a kai da wani dogon k’arfe dake kan barandar d’akinta sai da goshinta ya k’umu kuma yayi k’ulu k’atoton. Dariya Aina’u ta fashe dashi tare da fad’in, “D’an bura uban yaro! Kema ai Allah ya k’ara Lami. Kin fi kowa sanin Yabo bai k’aunar goyo amma sabida naiman suna kika kima shi a baya. To ai ga babbar Yabo nan kin samu a kan goshin ki.” Kwance zanin Lami tayi ta sauke sa tare da dungure masa kai, aikuwa take ya b’are baki ya fashe da kuka. Da sauri Lami ta saka tafin hannu ta rufe masa baki tare da fad’in, “Na shiga uku zai jawo min jidali da safen nan. Yi hak’uri d’an lele. Yanzu zan shiga d’aki na d’auko maka sweet mai tsinke.” Sarah kuwa dake jibge a k’asa tana ta faman bugun goshi kamar zata fita hayyacinta, kira sunan Aina’u ta shiga yi tana fad’in, “Aina’u dan girman Allah ki taimaka min, Wallahi zan baki dubu d’aya.” Mere baki Aina’u tayi tare da fad’in, “Now you’re talking. Amma kuma yasin dubu d’aya tai min kad’an, dubu biyu zaki bani.” Dai-dai nan Baba ya fito da sandarsa a hannu ya kalli inda Sarah take tausayinta ta kashe sa a tsaye, mai da dubansa yayi izuwa wajen Aina’u tare da fad’in, “Aina’u yanzu taimakon y’ar uwar taki ce sai da kud’i?” Mik’ewa tayi tare da fad’in, “A’a fa Baba! A’a! Walleh gwamnati ta hana aikin banza. Ta biya yanzu taga aiki da cikawa. Don ma ta samu zan karb’i kud’in in taimaka mata. Duk cikin gidan nan waye zata bawa kudi ya amsa don taimakonta idan ba niba. Idan zata bada 2k ta bayar a taimaka mata, idan kuma baza ta bada ba, ta sha zamanta.” Girgiza kai Baba yayi tare da fad’in, “Ungo nan gashi ni zan cika mata. Karb’i ki taimaka mata ta gyara jikinta ku tafi asibiti.” Wani kallo tabi baban dashi tare da fad’in, “Oh wai har da su zuwa asibiti? To lallai kud’i ya k’aru. Ni na d’auka taimaka mata kawai zanyi ta d’auraye jikinta ta koma d’aki! To kud’in ku dubu uku, idan kuna dashi, a cika aiki, idan babu, in koma in zauna.” Shuru Baba yayi yana kallon Aina’u, sai kuma ya mayar da dubansa ga Sarah yaga halin da take ciki. Sai ya koma d’akinsa, bayan kamar mintuna biyu ya fito tare da fad’in, “Zo Aina’u, ga dubu uku kamata ki taimaka mata ta wanko jikin nata sai ku tafi asibitin.” Mik’ewa Aina’u tayi don har ta zauna tare k’arisawa ta amshi kud’in sannan tace, “Ko kai fa d’an tsoho. Tsohon nan kud’i fa gare ka naga alama!” K’ala bai cewa Aina’u ba, sai ma kallon Sarah da yayi tare da fad’in, “Allah ya baki lafiya.” Sannan ya juya ya shige d’akinsa. Aina’u kuwa, k’arisawa wajen Sarah tayi ta kamata ta mik’e ta kaita har gindin pamfo ta wanke mata jiki. “Aina’u taimaka min da fanta mai sanyi a shago dan Allah. Akwai naira dubu d’ari biyu, ki d’auki d’ari biyun ki sayo min.” Matsawa baya kad’an tayi tare da fad’in, “To ki tabbata shima akwai kud’insa daban. Don yasin ban aikin banza.” Sarah na nishi tace, “Naji ji ki sayo min. Idan muka fita zan cire kud’i a POS sai in biya ki.” Ba tare da Aina’u tace komai ba ta juya ta nufi d’akinsu Saran ta d’auko d’ari biyun ta fito ta nufi waje don sayo Fantan. Sarah kuma da kyar ta iya jan jiki ta koma d’akin. Sai da ta d’an yi jimm kamun ta tura k’ofar ta shiga saboda bata son ganin abunda ta baro a cikin d’akin. Alhamdulillah Hassanar ta gama abunda take yi, kwance ma same ta tana kwasar barci. Kai tsaye wajen wardrobe ta nufa ta canza kayan jikinta ta zauna a k’asa tana nishi. Don wani irin juwa take gani. Aina’u ce ta hankad’o labulen ta shigo d’akin tare da dire mata kwalbar fanta a gabanta mai sanyi. “Nagode Aina’u!” Shine abunda Sarah ta fad’i tare da kai kwalbar bakinta ta cire kwankwalatin ta hau shan fantar. Kad’an tasha taji kamar za tayi amai sai ta mayar da kwankwalatin ta rufe ta ajiye a gefe tare da mik’ewa ta d’auki hijjab ta saka ta cewa Aina’u, “Muje Aina’u. Zamu d’an tsaya a shagon Nura zan cire kud’i, taimaka min ki d’au min jakata.” Jakar ta d’aukar mata suka fita daga d’akin. “Lami mun tafi.” Fad’in Aina’u. “To sai kun dawo. Ki tabbatar kin karb’i kud’inki.” Wani murmushi Aina’u tayi tare da fad’in, “Kin san wannan dole ne Lami, sai dai mun dawo d’in.” Ita dai Sarah bata ce komai ba ta nufi hanyar k’ofar gida. Sai da suka biya ta shagon Nura Sarah ta cire 11k ta bawa Aina’u 1k na sayo mata fanta da tayi sannan suka tsari napep suka shiga. “Ina zamu je Hajiyoyi?” Fad’in mai napep. “Ka kai mu wani asibiti mai kyau da kasan sun san aikin su sosai.” “An gama Hajiya!” Fad’in mai napep d’in. Sun d’an yi tafiya mai tsayi mai napep d’in ya tsaya a bakin wani katafaren asibiti kamar ba a k’asar Nigeria ba, a saman asibitin an rubuta *_Khalilullah Specialist hospital_* “Kai! Kana hauka ne da zaka kawo mu wannan asibitin? Shin baka san tsadar asibitin bane?” Fad’in Aina’u. Ko kamun mai napep yace wani abu, Sarah ta sauko daga keken tare da zaro dubu d’aya ta mik’a masa ya cire kud’insa ya bata canji. Sai a sannan ya kalli Aina’u tare da fad’in, “Ai gani nayi kunyi kalar asibitin shiyasa na kawo ku nan d’in.” Harara ta zabga masa tare da bin bayan Sarah da har ta kusa shiga cikin gate d’in. Sai da ta d’an had’a da gudu tukun ta isketa tare da fad’in, “wannan wani irin iskanci ne haka zaki wuce ki barni? Don kin samu na rakoki ko? Gobe rana ce ai!” Ba tare da Sarah ta kalleta ba tace, “Yau d’in ma kud’i nane dana Baba ya sakaki taimako na, gobe ma idan kika ga kud’in, biyo ni za kiyi.” Aina’u bata kuma cewa komai ba har suka shiga reception d’in asibitin. Gaba d’aya numfashinsu ya kusa d’aukewa sabida tsabar had’uwar da asibitin yayi. Aina’u kuwa baki bud’e take bin lungu da sak’on asibitin da kallo. “Baiwar Allah dan Allah Ina zan je na bud’e file?” Fad’in Sarah bayan ta tab’o wata nurse da tazo wuce wa. Da hannu nurse d’in tayi mata nuni da wajen sannan ta wuce. Sarah kuwa k’arisawa tayi tare da yin sallama ta gaishe da saurayin da ta gani a wajen sannan tace, “File nake so a bud’e min. Ina son ganin doctor.” Wani file ya d’auko tare da kallonta ya mik’a mata wani k’aramar paper tare da fad’in “Je ki biya wannan a wajen cashier sai ki dawo min da receipt d’in.” Karb’a tayi tare da fad’in, “Ina ne wajen dan Allah?” Shima da hannu ya nuna mata wajen. Tana zuwa ta mik’a masu papern, matar dake wajen ta d’ago ta kalleta tare da fad’in, “Kud’in ki dubu bakwai. Don kinyi sa’a babban doctor ne zai duba ki. Bud’e file dubu biyu, sai kud’in ganin likita dubu biyar. Shuru Sarah tayi, domin idan ta bada 7k saura 2k a jikinta. Da mai zata biya kud’in scanning? Don ta san tabbas za ayi mata scanning. Aina’u ce tazo wajen ta tsaya, Sarah tayi saurin cewa, “Dan girman Allah Aina’u aramin dubu hud’un hannunki, idan mun koma gida zan baki.” Ciro kud’in Aina’u tayi ta mik’a mata tare da fad’in, “Amma fa ki sani, wallahi sun haifu. Ba dubu hud’u zaki mayar min ba.” Komai Sarah bata ce mata ba. Sai mik’awa cashier kud’in tayi tare da mik’a mata receipt ita kuma ta karb’a ta koma wajen wanda ke bud’a file ta mik’a masa. Sunanta ya tambaya tare da age, adresss da kuma phone number sannan ya nuna mata inda zata je tare da shaida mata ya turawa doctor file d’inta ta computer. Consultant room taga an rubuta a sama. Har zata murd’a sai kuma ta d’an tsaya jim ta juyo ta kalli Aina’u dake zaune a kan kujera ta d’aura k’afa d’aya a kan d’aya tana danna waya. Ajiyar zuciya ta sauke tana fatan ace wannan karon idan an dubata ace wani ciwo ne daban a jikinta ba ciki ba. Kwankwasa k’ofar tayi sannan ta tura ta shiga. Wani gaurayayyen sanyi Ac taji ya ratsata mai tafe da wani k’amshi mai shiga zuciya da b’argon d’an Adam. Har sai da Sarah ta lumshe idanu tana mai fatan ace ta cigaba da jin wannan k’amshi har abada saboda yanda yayi mata wani irin dad’i da salama a cikin zuciyarta. Ba tare da ya d’ago kai ba yayi mata nuni da kujerar dake gaban teburinsa. Zama tayi tana mai wasa da hannunta. Shi kuwa doctor wani rubuce-rubuce yake yi a jikin wani file. Ya d’auki mintuna uku kamun ya ajiye file d’in ya zare glasses d’in dake fuskansa sannan ya juyo da computer yayi danne-danne tare da fad’in, “Saratu Nuhu ko?” Ya fad’i hakane tare da juyowa ya kalleta dai-dai lokacin da itama ta d’ago kai idanunsu suka sark’e dana juna. A mugun firgice Sarah ta mik’e tare da tura kujeran da take kai baya gabanta na wani irin mugaba kamar yanda dak’ik’an agogo yake bugawa. Bakinta na rawa tace, “kkkk…. Kai!” Shima da matuk’ar mamaki ganinta ya furta, “Ke ce?” Da sauri ta juya ta fita daga office d’in har tana k’ok’arin kifawa tayi saurin dafe bango. Aina’u dake charting ganinta kawai tayi ta fito kamar wacce aka biyo ta tayi waje da sauri. Ita ma mik’ewar tayi tana fad’in, “Sarah! Sarah!! Lafiya?” Dai-dai lokacin ya fito shima ya bita a baya, Aina’u na ganin haka ta rufa masu baya amma suna isa wajen gate d’in suka ganta har ta hau napep, napep d’in ya wuce. Juyawa Aina’u tayi ta kallesa tare da fad’in, “Lafiya? Mai ka mata? Ko HIV kuka gano tana d’auke dashi?” Wani irin kallo Khalil yayi mata tare da fad’in, “Ni ko dubata ban yi ba. Kin santa ne?” Ya tambaya duk da kuwa yana ganin kamannin jini a fuskar Aina’un. “K’anwarta ce ni. Ni ke binta.” Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad’in, “Ko zaki shigo mita muje in sauke ki sai in san gidan naku daga nan.” Wani kallon up and down tayi masa, ganin babu k’arya sai tace, “To amma kai mai yasa kake son zuwa kaga gidan mu?” Kai tsaye ya bata amsa da, “Saboda ina son had’uwa da yayarki. Auren ta nake son yi. Na jima ina naimanta sai yau Allah ya had’a ni da ita.” Wani dariya rainin hankali Aina’u ta kwashe dashi tare da fad’in, “Lallai! To ka ko san abunda ya kawota nan asibitin? To bud’e kunnuwanka da kyau in fad’a maka. Ciki ne da ita har na tsawon watanni uku, kuma zuwa tayi nan domin a zubar mata da cikin. Mu gidan mu bamu aure. Kar ka wahalar da kanka don baza ka tab’a samun Sarah matsayin mata ba. Ko da yake, ban san tsananin son da kake mata zai saka kayi auren ragowar wani ba. Ni na barka lafiya.” Tana gama fad’in haka tayi gaba. Shi kuwa Khalil mutuwar tsaye yayi kansa na wani irin juyawa jin wai wacce yake matuk’ar k’auna ce take d’auke da juna biyu. Tirr ya auri mazinaciya a rayuwarsa. Idan kuma hakan ta faru, daran ranar da ya fahimci haka, a ranar zai korata gidansu. Don ya san zama da zargi babu aure, shi kuma ba zai tab’a iya auren yarinyar da zuciyarsa zai rik’a kokwanto a kanta ba. Har ya fara tafiya ya tsaya cak tare da maimaita abunda Aka Aina’u tace masa cikin zuciyarsa “Ciki wata biyu? Kai ba zai tab’a yuwuwa ba.” ya fad’i a bayyane tare da bin bayan Aina’u da sauri………….
_AKWAI FA SAURAN CHAKWAKIYA A GABA SOSAI. DON HAR YANZU BA’A SOMA LABARIN BA. SHIN TA YAYA SARAH TA SAMU CIKI BAYAN TAYI RANTSUWA DA ALLAH BATA TAB’A SANIN D’A NAMIJI BA, WANENE DOCTOR D’IN DA SARAH TA GANI HAR TA TSORATA DA GANINSA TA GUDU BA TARE DA TAYI ABUNDA YA KAITA ASIBITIN BA? MAI DOCTOR KHALIL YAKE NUFI DA YACE BA ZAI YUWU BA ACE SARAH NA D’AUKE DA CIKIN WATA BIYU? A INA YA SAN SARAH, KUMA MENENE ALAK’ARSU? WACECE LAMI? WANENE BABA NUHU? SHIN MAI MAI K’ANWAR MATATA YAKE NUFI? TUN FA DA AKA SOMA LABARIN BAMU GA MATAR BA, BAMU GA MIJIN BA, BARE KUMA K’ANWAR. HMM WALLAHI Y’AR UWA KAR KI BARI AYI WANNAN LABARIN BABU KE. DOMIN AKWAI CHAKWAKIYA MAI ZAFI A CIKINSA._
*_A NAN NA KAWO K’ARSHE. FREE PAGES, GA MAI BUK’ATAR KARANTA LITTAFIN K’ANWAR MATATA, SAI YA TURO D’ARINSA BIYAR ZUWA WANNAN ASUSUN BANKIN 0592412800, ZULFAU SAID GT BANK, SAI KI TURO DA SHAIDAR BIYANKI DA WANNAN NUMBER 08128755583_*