Hausa Novels

Kanwar Matata 5

Sponsored Links

🦜 *_K’ANWAR MATATA_*🦜

_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_

 

☀️ *ZAFAFA WRITER’S ASSOCIATION*☀️

Page 5

A gigice Sarah ta d’ago tare da dafe kuncinta tace, “Farouuuuq.” sai da ta ja sunan cike da tausayi tana kallon fuskansa hawaye na shatata a idanunta. Bakin Farouq har rawa yake yi wajen fad’in, “Kar ki kuskura ki k’ara kiran sunana anan wajen idan ba haka ba karya ki zan yi billahil lazi. Wawuya shashasha mai fuska biyu. Ashe watsatsatsiya ce ke kamar sauran y’an uwanki. Kin cucuni Saratu da har kika saka ni na d’auki dakon sonki a cikin zuciyata har tsawon shekara. Allah ya isa tsakani na dake. Kuma ki sani, ko da ace daga ni sai ke muka rage a duniya, har sai dai na mutu babu aure. Banza budur-bazar.” Kuka Sarah ta fashe dashi jin zafafan kalaman da Farouq ke fad’a mata. So take yi ta bud’e baki tace wani abu, amma rawar da bakinta yake yi ya hana ta iya furta ko kalma d’aya. Ji tayi an watso mata papers a fuska. Bin papers d’in tayi da idanu, sai kuma ta kai hannu ta dake rawa ta dauki paper d’in ta bud’e. Waro idanuwa tayi ganin papers d’in scanning d’inta ne har guda uku wanda tayi jiya. Bata iya cewa komai ba don ta san babu abunda zata fad’i wanda zai saka Farouq ya yarda da ita. Tsirtar da miyau Farouq yayi tare da kama hannu aunty Luba yace, “Aunty mu wuce anan kada amai ya kama ni dan Allah. Don ganin fuskan yarinyar nan kawai yana saka ni tashin zuciya.” Rintss idanu Sarah tayi tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa tamkar yanda jirgin k’asa ke malala gudu akan titinsa. Bata iya tashi a wajen ba sai da ta kwashi mintuna kamun ta mik’e, shima sabida mutanan da suke wucewa suna zund’enta ne ya saka tayi k’arfin halin tashi ta tura k’ofar gida ta shiga. Kai tsaye d’akin mahaifinsu ta wuce duk da maganar da Lami take mata a tsakar gida tana yiwa yaran Na’ima wanka, amma bata kula ta ba. Tana shiga dakin ta zube a k’asa sai da guiwowinta suka bugu da k’asa, amma bata damu da zafin da taji ba. Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi tare da fad’in, “Wallahi, tallahi, billahil azim Baba ban tab’a sanin wani d’a namiji a rayuwata ba. Baba namiji da na tab’a bawa kaina. Ban san ta yanda akayi ciki ya shiga jikina ba. Na shiga uku na lalace Baba. Shikenan nima ba zanyi aure ba?” Sunkuyar da kai Baba yayi yana mai zubar da hawayen tausayin Sarah. Dakyar ya iya d’ago kai ya kalleta tare da fad’in, “Saratu da badin manzon Allah SAW yayi hani da d’auke mace a burni a kaita k’auye ba, da nace ki tattara kayanki ki koma _Wamba_ kiyi auren ki acan. Amma kuma Saratu babu ta yanda za ayi ki samu ciki ba tare da d’a namiji ba. Kin tabbata baki tab’a zuwa wani waje ba an baki abun sha kin sha ba? Watak’ila ta nan aka yaudare ki.” Girgiza kai Sarah tayi tare da fad’in, “Baba ban tab’a zuwa party ba. Ko k’awaye bani da balle su gayyace ni.” Shuru Baba yayi na kayan tsawon mintuna biyar sannan ya nisa tare da d’agowa ya kalleta yace, “Jeki d’akin ki Saratu. Allah shi yasan abunda ke b’oye. Duk wanda yake k’ok’arin cutar dake, in Sha Allah, Allah ba zai bashi dama ba. Kina gani da idanunki Saratu, kina ganin irin wulak’ancin da mahaifiyarku da sauran y’an uwan ki suke min a cikin gidan nan. Kina tunanin ko ban bud’e baki nayi masu baki ba, Allah ba zai tsine masu ba. Ni dai Sam ban yi sa’ar mace ba. Haka zan koma ga Allah da bak’in cikin Lami da y’ay’anta. Sai da y’an uwana suka yi min gargad’i, amma kuma nayi kunnar uwar shegu dasu. Gashi yanzu ina girbe abunda na shuka.” Baba ya k’arisa yana mai fashewa da kuka. Itama Saratu kukan ta fashe dashi tare da fad’in, “Kayi hak’uri Baba. Dan Allah ka cigaba da hak’uri dasu kamar yanda ka saba.” Bai d’ago ba ya ce, “Saratu y’ay’an ciki na suke duka na! Wallahi tallahi har mahaifina ya koma ga ubangiji, bai tab’a fad’i na fad’a ba balle har in d’aga in kallesa inyi masa k’unk’unai. Wannan jarabta ce kawai daga Allah!” Shuru Saratu tayi tana mai jin k’una sosai a cikin ranta. “Na’ima y’ay’anta uku babu aure, dan ma Allah yayi wa d’ayan cikawa da yanzu y’ay’anta hud’u duk babu uba. Nuratu biyu, Marfu’a nada d’aya, Hassana kuma tayi y’an biyu, ko wata uku ba’ayi ba da d’aya daga cikin y’an biyun ya koma. Wannan bak’in cikin kawai ya isa ya kashe ni Saratu. Gashi itama autar taku Aina’u tana so ta fad’a cikin halakar da y’an uwanta suke ciki. Yanda idanunta suke a tsatstsaye, wallahi ni sai nake ganin ma kamar sai tace duk abunda y’an uwanta suke yi basu yi komai ba akan wanda zata yi ita.” “A’a baba, addu’a zaka yi mata. In Sha Allah hakan ma ba zai faru ba. In Sha Allah Aina’u baza tayi halin su Na’ima ba.” Girgiza kai Baba yayi tare da fad’in, “Uhm! To Allah yasa. Amma da kamar wuya. Hatta shi kansa namijin da Allah ya bani tilo, sakarai ne. Tunda shima shaye-shaye babu wanda bai yi da kuma d’aukar kayan mutane. Jiya da daddare, ina jin lokacin da wannan yaron wa yake da suna?” ” *_Naliliyo_*” Fad’in Sarah. “Yauwa eh shi! Ina jinsa yana karta adda a k’asa yana zage-zage. Kuma uwar na d’aure masa gindi. Ya Allah idan wani laifi nayi maka kake min wannan jarabawar, Allah na tuba ka yafe min dan tsarkin mulkinka.” Da “Ameen.” Sarah ta amsa tana mai jin tausayin kansu ita da mahaifin nata. “Tashi kije Sarah. Kije kiyi ta addu’a. In Sha Allah, Allah zai kawo maki mafita. Ki k’addara dama can Umaru ba mijinki bane. Idan kuma mijinki ne, wallahi duk wannan abun da ya faro, babu makawa sai anyi wannan auren.” Share hawaye Saratu tayi tare da fad’in, “Nagode Baba. Amma dan Allah idan ka yi min izini, zan koma asibiti domin ganin likita.” Sai da ya gyara k’afarsa sannan yace, “Saratu ki bari gobe kyaje. Yanzu ki koma d’akinki ki huta.” Mik’ewa Saratu tayi tare da fad’in, “To Baba, nagode Allah ya baka lafiya.” Da Ameen ya amsa, ita kuma ta fice daga d’akin. Sanye yake cikin jeans d’in _Secret Circus_ da shirt na kamfanin _Saint Laurent_, sannan ya sanya takalmin _Stuart Weitzman_. Babu abunda ke tashi a jikinsa sai turaren _Imperial Majesty_, kallon kansa yayi a cikin k’aton madubin dake d’akinsa ya saki lallausar murmushi ganin irin kyawu da yayi. Juyawa yayi ya nufi wani katoton showglass wanda ba komai bane a ciki sai mahaukantan expensive sunglasses, wani waje ya danna sai ga glass d’in ya zuge, rabi yayi sama, rabi yayi k’asa. Sai da ya k’arewa glasses d’in idanu sannan ya kai hannu ya d’auko _Bulgari Flora_ wanda duk cikin sunglasses d’insa yana matuk’ar k’aunar wannan. Madannin ya kuma dannawa glass d’in ya rufe sannan ya juya ya koma wajen madubi ya d’auki Microfiber cloth ya goge glasses d’in sannan ya saka a fuskansa. Yanda yayi matuk’ar yi masa kyau, zaka d’auka dan shi kawai aka yi glasses d’in. Sai da ya k’ara kallon kansa from head to toes yaga he’s perfectly dress sannan ya d’auki iPhone d’insa a kan bed ya nufi k’ofa ya murd’a ya fito. “Barka da fitowa ranka ya dad’e” Shi gaba d’aya tsorata yayi don bai tsammaci ganinta a k’ofar d’akinsa ba. “Laure! Kai Inna lillahi wa’inna ilaihir raju’un. Wai ni Ibrahim ya zanyi dake ne wai dan Allah? Sau nawa zan fad’a maki ki daina zuwa kina tsayuwa a k’ofar d’akina kamar wata security. Dan Allah, dan Allah Laure ki daina firgita ni. Ni wallahi babu abunda ke tada min hankali da tsoro kamar wad’annan kacakoren hakwaran na….” Tun kamun ya kai k’arshen zancen ta fashe da dariya wanda ya bayyanar da manya-manyan hakwaranta na sama guda hud’u da suka turo suka yi curko-curko a waje. Sam bata iya rufe bakinta ruf saboda hakwaran. “Precious Lord in heaven! Laure bar nan wajen tun kamun na zubar da wad’annan kacakoren hakwaran wallahi.” Ja da baya tayi tare da fad’in, “Ni hwa tsaya kaji Ya Khalif (Khalil), Hajiya ce tace nazo nayi kiranka tana can parlor kai take jira. Kuma ni kayi mani wanin (warning) akan kar ba kuskura na kuma shigar maka d’aki kai tsaye. Kuma nayi k’ok’arin danna wanna madannin amma na kasa. Kasan ni d’in ce kamar a duk’e aka haifo ni sabida rashin tsaho.” Harara ya maka mata tare da fad’in, “To naji bar nan wajen.” Washa bakin ta kuma yi sai da ya matsa baya don da gaske shi hakoran nata tsoro suke bashi. Gaba tayi kad’an, sai kuma ta juyo tare da fad’in, “Nace dan Allah yaya khalif ko zaka d’an sammun wannan turaren naka mai shegen k’amshi anan, ko baka cika min ba wallahi nagode.” Ta k’arisa maganar tana mai ciro wata k’aramar kwalba irinta fiya-fiya a k’ark’ashin zaninta. Yunk’urowa yayi kamar zai kai mata duka ta juya a guje ta nufi dogon corridor d’in da zai fitar da kai katoton parlorn gidan. Tsaki yayi sannan ya jawo k’ofar d’akina nasa ya murza key tare da saka key d’in cikin aljihun wandonsa ya soma tafiya majestically har ya iso parlor. Tsaye yaga Laure da mopa a hannunta, maimakon tayi abunda za tayi, sai ta b’ige da kallon katoton tv na bango dake manne a jikin bango. Wani film d’in India mai suna *_Sultan_* ake haskawa d’ai-d’ai inda yake gudu domin kamo jirgin leda. Babu abunda Laure kayi sai kyalkyalewa da dariya. Khalil na k’arisowa ya d’auki remote dake hannun kujera ta jefi Laure dashi a goshi, don Hajiya tayi kiran sunanta har sau hud’u amma film ya d’auke mata hankali. Kuma ita ta zubar da juice d’in da Hajiya ke sha sabida rawar kanta. Saurin susa goshin Laure tayi tare da fad’in, “Laa! Wallahi kuma naji kamshin turaren ka, wata zuciyar tana ce min kai ne ka k’ariso, amma wanna gayen ya tafi da imani na. Dan Allah Hajiya zaki biya min kud’in jirgin inje indiya mu gaisa tare da d’aukar hoto dashi? Na san wallahi zai ji dad’i idan ya ganni. Na san har fim sai mun yi tare in fito a budurwarsa.” Harararta Khalil yayi tare da fad’in, “To dan gidan ku matsayin saka ki a cikin keji ana zuwa ana ganin ki ba zaki samu ba, shashasha kaiwa. Za kiyi abunda ke gabanki ko sai na isko ki nan wajen.” Marairaicewa tayi tare da fad’in, “Allah sarki yaya khalif. To na rantse maka fad’in k’asar indiya samu mai kyawuna abune mai matuk’ar wuya. Ko kai d’innan da kad’an ka fini kyawu.” Zama yayi kuwa da Hajiya yana mai fad’in, “Tabbas, babu shakka. Dama ai samun irin ki a indiya ai sai an tona. Don ko namun dajinsu sun fiki kyawun gani.” Turo baki tayi tare da fad’in, “Kina dai jin sa ko Hajiya!” “Kar ma ku soma saka ni cikin shirmen ku. Ke da Khalil dai kamar kuna ganin hanjin juna.” Fad’in Hajiya dai-dai lokacin da Maryam matar wan Khalil tayi sallama ta shigo d’akin hannunta rik’e da wani kyakkwar kula. Dai-dai inda Hajiya take ta ajiye kulan tare da fad’in, “Tom and Jerry! Kun soma fad’an naku ko.” Kallon kukan da aunty Maryam ta ajiye a gaban Hajiya yayi sannan ya kalli aunty Maryam d’in tare da fad’in, “Ai kin san Allah, sai na kori yarinyar daga gidan nan. Ni da gidanmu amma bani da sakewa. Babu ranar duniya da wannan yarinyar bata tsora tai da muggan hakwaran nan nata.” murgud’a baki Laure tayi tare da fad’in, “Halittar Allah kake zagi. Idan ka isa halicci kiyashi anan wajen mu gani. Sai rowar tsiya, d’an turaren da mutum zai baka kad’an cikin kwalba amma ya kiya sabida rowar tsiya. Wallahi Hajiya dai kowa ya san ita d’in hannunta a bud’e yake kamar kasuwar kwari ta Kanon mu. Ko ina kayo rows oho! Kuma Hajiya kice ya bani makulli in tai in gyara masa d’aki.” _Mastika gum_ da yake matuk’ar k’aunar ya fiddo daga aljihunsa ya jefa a baki ya hau tauna a hankali yana lumshe idanu. Allah ya had’a wani strong love tsakaninsa da chewing gum. Da yuwa kaga bakin Khalil babu gum a bakinsa. Kuma gaba d’aya chewing gum d’in da yake ci daga waje ake kawo masa. Yasan expensive gum da yawa. Yana biyan kud’in jirgi ya keta hazo kawai domin sayo chewing gum. Kullum cikin browsing yake domin ganin sabon chewing gum d’in da aka yi. Hajiya tayi-tayi har ta gaji akan yi masa fad’a ya daina ci amma Sam yak’i bari. Har hak’ori an tab’a cire masa tsabar cin chewing gum amma hakan bai saka ya daina ci ba. “Dan gidan ku ina yi maka magana shine ka d’auki d’an iskan abun nan da ba tsana ka jefa a baki kana tauna.” Tsayawa da taunar yayi tare da fad’in, “Dan Allah Hajiya ki daina saka damuwar uncle Ridwan a zuciyarki. Ya kamata ki saba da riginarsu yanzu. Wai shi so yake na auri Nina, ni kuma da in auri wacce wani namijin ya riga ni saninta, gwara na mutu babu aure. Na tsani mace mara kamun kai. Hajiya Nina fa bata san iya adadin mazan da ta kwanta dasu ba………..”

 

 

 

08128755583

Leave a Reply

Back to top button