KUDIN RUWA DA BASHIN BANKI MUSULUN CI #006
KASHI NA SHIDA
Musulunci Da Matsalar Riba
Nau’o’in Riba A Musulunci:
A dabi’ar shari’ar Musulunci, duk wani abu da shari’ar
harammata ba wannan abin ne kawai yake zama haramun ba.
A’a hanyar duk da zata kai mutum ga yin wannan abin ita ma sai ta haramta .
A dalilin haka ne Riba a Musulunci ta kasu zuwa nau’i biyu fitattu.
(i) Riba Ta Lokaci: Ita ce wadda bayani ya gabata a kanta.
Watau karin da ake yi wa mai
karbar bashi saboda jinkirin da za
a yi masa. irin wannan nau ‘in na Riba shine, wanda haninsa ya zo kuru-kuru a nassin Al Rur’ani.
Ba a taba samun sabanin fahimta ba game da haramcinta ba .Watau( ijma’i)¹> a kan haramcinta ya faro tun daga kan Sahabbai, zuwa tabi’ai,²> zuwa malamai masu ijtihadi.
Kai har zuwa wannan zamanin da muke ba a sami sabani ba tsakanin Musulmi game da haramcin irin wannan Riba.
Ribar Musaya: Ita ce yin kari tsakanin abubuwa biyu masu nau’i daya yayin musanya.
Annabi (S.A.W.) shi ya haramta irin wannan nau’in na Riba domin gudun kada a fada wa wancan nau’in na farko.
Don haka yake cewa:
“Kada ku sayar da dirhami daya da dirhami biyu. Ina ji muku tsoron kada ku ci riba ”
Mun kuwa sani cewa Annabi (S.A.W.) shi yake bayanin abin da duk Allah yake nufi cikin umurninsa da haninsa. kamar yadda Ayoyin Alkur’ani suka tabbatar da haka.
Haramcin Riba A AlRur’ani
Akwai wata dabi’a da ya kamata mu sani game da Allur’ani, dangane da kafa dokoki na muhimman al’amura.
Wannan dabi’a ta Alkur’ani ita ce, idan zai yi wata doka ta umurni ko hani, ba ya kawo dokar gaba daya a lokaci daya. A’a, yakan raba abin ne zuwa matakai daban-dabam, har a kai ga cikakken umurnin ko hanin da ake nufi.
Wannan ita ce hanyar dà ya bi wa
jen kafa dokokin umurnin sallah da azumi da sauransu, ko kuma hani kan shan giya da ita cin Riba d’in, da sauransu.
Za mu ga cewa, yayin da Musulunci ya tarar da wannan cuta ta cin riba ta yi kanta a zukatan larabawa sai ya raba dokar haninta mataki- mataki, har zuwa matakai hudu.
Sai a mataki na karshe Alkur’ani ya hana ta gaba daya.
Ayar da aka saukar a makkah bayani tayi cewa, kudin ruwa (Riba) ba su da daraja a wajen Allah. Don haka ba su da sakamako a wajensa.
Amma kudin da aka bayar na zakkah suna nan Allah yana rubanya ladansa a wurinsa.
“Abin da kuka bayar na Riba don ya karo a cikin dukiyoyin mutane ba zai karu ba a wajen Allah.
Abin kuwa da kuka bayar na zakka kuna nufin Allah da shi su ne za a ninninka ladansu.”
A yoyin Madina kuwa, Ta farko bayani ta yi kan azaba mai radadi da za a yi wa yahudawa a dalilin hana su cin Riba da aka yi suka ki hanuwa, manufa a nan shi ne a jawo hankalin mumunai, a ba su tsoro don su bar wannan mummunar dabia da suka koya daga su yahudawa Allah Madaukakin sarki yana cewa:
“Saboda zaluncin Yahudawa sai muka haramta musu dadadan abubuwa wadanda da aka halatta musu, saboda kuma kare mutane da suke yi ga barin tafarkin Allah da kar bar Riba da suke yi.
Alhali an hana su ga barin ta. Da cin dukiyoyin mutane da sukeyi ta mummunar hanya. Mun tanadar wa kafirai daga cikinsu azaba
mai radadi.³
2- Ta biyu hani ta yi cewa kada a rika cin Riba ninkin ba-ninkin.
Watau kada ta kazanta. Ubangiji Madaukakin Sarki yana cewa:
“يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَأْكُلُوا الرِّبَا أَضْعَافًا مُضَاعَفَةً وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ “
“Ya ku wadanda kuka yi imani. Kada ku ci riba ninkin-ba ninkin, ku ji tsoron Allah ko kun rabauta.>5
3- Aya ta uku kuwa (watau aya ta hudu in aka hada da ayar da aka
saukar a Makkah), a ita ce aka saukar da hani na karshe kuma na gaba daya game da wannan mummunar d’abi’a. Allah Madaukakin sarki yana cewa:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَذَرُوا مَا بَقِيَ مِنَ الرِّبَا إِنْ كُنتُمْ مُؤْمِنِينَ فَإِنْ لَمْ تَفْعَلُوا فَأْذَنُوا بِحَرْبٍ مِنَ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَإِنْ تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُءُوسُ أَمْوَالِكُمْ لا تَظْلِمُونَ وَلا تُظْلَمُونَ وَإِنْ كَانَ ذُو عُسْرَةٍ فَنَظِرَةٌ إِلَى مَيْسَرَةٍ وَأَنْ تَصَدَّقُوا خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ .
[البقرة:278-280]
“Ya ku wadanda kuka yi imani. Ku ji tsoron Allah, ku bar duk wani abu da ya rage na Riba in kun kasance muminai. Idan kuwa ba ku yi haka ba, to ku shirya da yin (yaki) da Allah da Manzonsa. Idan kuwa ku ka tuba, to kuna da asalin dukiyarku. Ba ku yi zalunci ba, ba’a zalunce ku ba.
A wannan hani na karshe Ubangiji ya yi bayani bayyananne wanda babu wani loko da za A laBe A halatta wannan mummunar dabi’a. Domin ya bayyana mana cewa duk abin da ya doru a kan
asalin dukiyar bashi Riba ne.
Watau matukar mai bayar da bashi
ne ya shardanta wa mai neman bashi.
hujojin da aka kafa
(1) Ijma’i shi ne haduwar fahimtar malamai kan wani hukunci na shari’ar Musulunci.
(2) Tabi’ai Su ne muminai da suka sadu da sahabbai.
(3) Surah ta 4: Suratul Nisa’i Aya ta 160-161.
(4) Surah ta 3: Suratu Ali Imrana, aya ta 130.
Zamu tashi
Harmcin Riba A Sunna:….
Anan zu diga aya sai A kasan ce damu domin ka wo muku ragowar a shiri na gaba.
Allah ya datar da mu duniya da lahira ya Bamu kudi masu albarka na halal.
Domin karin bayani
Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu,
Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.