KUDIN RUWA DA BASHIN BANKI

KUDIN RUWA DABASHIN BANKI A MUSULUNCI .

Sponsored Links

         KUDIN RUWA DA BASHIN BANKI 
                          A MUSULUNCI

                           Kashi na hudu 

Gabatarwa

    Daga 

musa s zage 

                  Haramcin Riba Tsakanin 

                      Al’ummomi Na Dá:

 Tsofaffin al’ummomi a duniya kamar Girkawa, Misirawa da Romawa, sun yi ta fama da wannan matsala ta Riba a tsakanin-su. 

  An yi ta samun hautsini da tashin hankali a tsakanin masu kudi da talakawa a wadannan al’ummomi, saboda irin wannan bashi. Wannan shi ya sa a wadansu lokatai shugabannin wadan- nan al’umomi sukan kafa dokoki don rage yawan ruwan bashi

(Interest) ko kuma ma soke shi dungurungun.

 Misali, akwai Sarkin Masar daya gidan saraula na ishirin da hudu (24) wanda ake kira Yokhoriyas, wanda ya kafa dokar cewa, komai dadewar bashi kada karinsa ya yi daidai da asalin kudin.

Idan muka ga al’umma girkawa da Romawa za muga cewa, tunshekaru dari biyar kafin haihuwar Annabi Isa,  shugabanninsu suka kafa dokoki, kan cewa ; karin da za a yi kan bashi kada ya wuce kashi sha biyu cikin dari na yawan asalin dokiyar.

   kafin wadannan dokoki. bashin ruwa kan sa  mutum ya zama bawa a wadannan al’ummomi. Watau saboda karuwar da bashin yake yi, wata rana shi kansa wanda ake bi bashin ya zama shine ruwa.

Masu hikima  Na Da Sun La’ance Ta :

    Masana na da can wadanda suka dogara da tonani wajen gano abubuwa kamar su Afladon (Palaton) da Arasdo (Aristote) duka sun la’aci (Riba). Misali ,  shi Afladon wanda ya rayu 247-430 kafin haihuwar Annabi ISAH (As) . ya bayyana a littafinsa mai suna {Alkanun} cewar bai halaita a bayar da bashi da ruwa ba. Shi kuwa dalibin sa Arasdo wanda ya rayu 322-384

kafin haihuwar Annabi Isa, kasa hanyoyin neman kudi ya yi zuwa kashi uku:

(i) Hanyar ciniki ta musaya. Watau kamar a bayar da tufafi

karbi abinci. Wannan ita ya kira da cewar ta dace da dabibi’a.

Da ita ake amafani kalin a san kudi

 (Da Hausa ana kiransa cinikin urfure).

(ii) Hanyar yin musanyar wani abu da kudi. Kamar a bayar daTufafi a karbi nairori. ita ma wannan  ya yarda da ita. Kuma ta fara ne bayan dan Adam ya fara samun ci gaba.

(iii) Saikuma hanyar da ya kira da cewar ba ta dace da dabi’a ba. Watau hanyar nan ta a sayar da kudi a ci riba. Ya ki yarda da wannan hanya ne sabo da kudin ne kansu suke janyo wasu kudin, ba tare da mai kudin ya yi aiki wani aiki ba kamar yadda asara ba zata shafe shi ba .Anan ne yake cewa: ” Kudi basu taba haihuwar kudi ba.

Haramcin Riba A Yahudanci Da Kiristanci

Tun asali Yahudawa sune da alhakin yaduwar wannan mu’amala ta bayar da bashi da ruwa (Riba). Sune suka rubuta a

littarinsu (Attaura), a gyaran da suka yi na 23 kamar haka:

“In za ka bayar da bashi ga wanda ba Bayahude ba, ka ba shi da ruwa (Riba).

  Amma idan za ka bayar ga dan uwanka bayahude kada ba shi da ruwa 

” (Attaura sashi na 23.  sakin layi na 20).

   A saboda haka ne suka yi ta kokarin cin riba ga wadanda ba Yahudawa ba. Wanda daga karshe ma sai suka rika. sanya ta harkan ‘yan uwan nasu yahudawa.

Dangane da addinin Kirista kuwa su sai mu ce an yi sa’a. A duk gyare-gyaren da suka yi ba su halatta ta a kansu ba. 

 haramcinta ya zo a cikin Injila (New Testiment) fasali na 6 sakin layi na 34 dana 35 cewa: “Idan har za ku bayar da bashi ne ga wadanda za ku saurari sakamako, wace falala ke nan za a samu daga gare ku?

 Abin da ya fi shi ne ku yi alheri. Ku bayar da bashi ba tare da kuna sauraron wani abu da zai biyo baya ba. In kun yi haka za ku samu lada da yawa”

Malamai da shugabanni na coci-coci, da kuma dukkan Ma- jami’u sun hadu a kan cewa Annabi Isa (A.S.) ya haramta Riba.

Har ma wadansu daga cikin malamansu suna cewa duk wanda ya halatta Riba ya fita daga kiristanci. Wadansu kuwa cewa ma suka yi idan maciya Riba suka mutu kada a yi musu jana’iza. Saboda ba su da wata daraja.

                       Domin karin bayani

Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 

Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

written by ceo

       Page 

musa s zage

Leave a Reply

Back to top button