Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 23

Sponsored Links

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

 

*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*

*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

 

*23*

 

To rayuwa taci gaba da garawa,yana iya bakin ƙoƙarinshi wajan ganin ya musu adalci tsakaninsu.

Fadeela ta sauke komai yanzu mijinta takebi sau da ƙafa dan murja tasata ta dawo daga rakiyar magungunan matan datake bankawa cikinta.

Yayinda ita kuma fareeda ƴar chadi ta ɗorata akan shan magungunan harda na masifa,azatonsu fadeelat yanzu ta dace,
.
Hajiya mahaifiyar labeeb sosai take nuna musu banbanci tafison fareeda,danko gidan taje part ɗin fareedar take sauka saidai ita fadeela tabita can su gaisa duk da itace babba.

**********

Yau tun safe fareeda ke fama da ciwon mata ga tashin zuciya komai taci sai ta dawo.

Sosai hankalin labeeb ya tashi,ya ɗauketa suka nufi asibiti dan duk ta galabaita.

Cikin gaggawa aka amsheta aka shiga bata taimakon gaggawa.bayan ta dawo hayyacinta suka fara gudanar da bincike inda gwajin farko suka ga tana ɗauke da ciki dan wata guda.

Lokacin da albishir ɗin ya isa ga kunnuwan labeeb kuka ya fashe dashi na farinciki ya rungumeta yanata sa mata albarka.

Itako wani irin farinciki take mara adadi dan tasan yanzu gida yagama zama nata tunda gashi itace zata fara haifar masa ɗa agidan.

Wayarshi ya zaro ya kira hajiyarshi,vata jima tana ringing ba ta ɗauka,kamar wanda zaa rigashi yace cikin muryar kuka.

“hajiya fareeda na ɗauke da juna biyu yanzu haka muna asibiti”

Wata kabbara hajiya tayi sannan ta rangaɗa guɗa,tace”nayi farinciki labeeb ashe inada rabon ganin ƙwanka aduniya,Allah na gode maka,labeeb ya jikin nata?”

“Da sauƙi hajiya,”ya bata amsa yana kallon fareeda dake ta faman sinne kai wai ita kunya.

“Gani nan zuwa asibitin yanzu,ka kira driver ka faɗa mishi inda kuken”tace lokacin data miƙe ta nufi cikin ɗakinta danta shirya.

*******

Ranar girkin fadeela ne kuma taji shuru be dawo ba,dan tana bacci yazo daga office ya ɗauki fareedar zuwa asibiti dan haka ita batasan wainar da ake toyawaba

Saida tags anyi sallar ishai be dawo bane yasa ta kira wayarshi dan be kai haka awaje.

Ya jima kan yaji ƙarar kiran dan tuni asibitin ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi anzo tayashi murna,kowa senan nan yake da fareeda kamar kwai.

Fita yayi daga ɗakin ya ɗaga kiran.

“prince lafiya kake ko najika shuru baka dawo gida ba”cewar fadeela cike da kulawa.

“ina asibiti tare da fareeda,batajin daɗi shiyasa ban dawo ba”ya bata amsa agajarce danshi beso ta kirashiba yana kusa da uwar ƴaƴanshi.

“me yasameta prince shine baa daɗamin bacin ciwon ƴa mace na ƴamace ne?”ta daɗi cike da kulawa.

“wani ciwon de,amma ita da take ɗauke da cikina fadeela taya zakisan kalar ciwon bayan ke baki taɓa ɗaukar cikin nawa ba”ta bata amsa batare da tunanin komai ba.

Wasu hawayene suka zubo mata,madu tsananin zafi da ƙuna,bana baƙin cikin fareeda ta samu cikiba,na gorin da labeeb ɗin yay mata da kanshi.

Kashe wayarshi yayi be jira tayi maganaba ya koma ɗakin ransa fess matarsa nada ciki.

Fadeela ranar yadda taga rana haka taga dare bacci ya ƙauracewa idanunta,kuka take tana kaiwa Allah kokenta.

*********

 

Sai washegari aka sallamosu,inda uwar siyayyar kayan haihuwa da akayi zaku ɗauka yanzu zata haihu.

Haka gidan suka cikashi maƙil anata murnar,haihuwar da zaayi nan da watanni tara tara masu zuwa.

A sanyaye fadeela ta shiga part ɗin na fareeda san mata sannu su kuma gaisa da hajiya.

Tunda ta shiga danginsa ke binta da kallon banza sabida kawai bata haihuba.

“sannu fareeda ya jikin Allah ya baki lfy”cewar fadeela asanyaye.

.Wata uwar shewa suka ɗauka sauran pan uwan labeeb ɗin sannan sukace”ay ciwone da akeso wannan bana fatan asamu sauƙi bane na fatan Allah ta inganta ya raba lafiyane muzo musha suna gidan ɗan uwanmu muzo da motar kwasar kashi akwashe kashin da akai shekara da shekaru anyi,dan yanzu permpers ɗin babybzamu dinga cika sokawen dashi.”ayko watacshewar suka sake sawa suna dariya gamida tafawa.

Bata kulasu ba ta gaida hajiya,da ƙyar ta amsa mata,sannan tace”ji yarda ta wani marairaice kamar wata ta kirki,kai kace itace me cikin”.

“yimata uzuri hajiya maybe kashi takeji kinsan nan tafi ƙwarewa”cewar ɗaya daga cikinsu.

Hawayen datake ɓoyewa ne suka shiga biyo idanunta da gudu tabar sashin tana kuka kamar ranta ze fita,uwa uba gashi agaban labeeb aka mata wulaƙancin amma be uya cewa komaiba se wasa take da hannun matarsa fareeda.

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button