Matan ko Mazan 28
MATAN?? Ko MAZAN??
M SHAKUR
EPISODE
I am a certified Cosmetologist and I help women of color attain Clean, Clear and Brighter looking skin through supplements.
Bari na muku gwari gwari mutanena itadin certified wato tayi graduating a harkan cosmetologist, kwararriya ce, duk wata matsala dakikeda shi afata tanada maganinta kawai ki sameta, discoloration, kyasfi, dry skin, ke ko baturiya kikeso ki zama zata maidaki yesss kuje page dinta na IG kusha kallo, sannan ga number ta ku danna kumata magana a whatsapp ku fadi matsalan ku.
We treat skin conditions like hyperpigmentation, uneven skin, dark spots, skin discolorations and skin aging through beauty supplements that work from the inside.
My handle is
www.instagram.com/gimigimoraskin
Contact Number:
wa.me/+2347062972229
28
Ba karamin batama su Nura lokaci akayi ba, shi yana zaune bayan kanta kaman criminal, Alhaji Musa da Lawyer shi ke shiga da fita, ganin yanda suke da kudi aikuwa sun tatsu a hannun yan sanda dan kusan 650k suka kashe wanda duka Alhaji Musa yabiya daga pocket nashi, sannan aka sallamesu Nura yayi signing a some files haka sannan suka baro wajen sukai sallama da Lawyer Nura suka wuce, Alhaji Musa ke tuki bini bini yana kallon Nura, ganin baya iya magana ma yasa yace “nakira Maman Humaira tana gidan tareda su Aman da Amali tun dazu, koda school bus yakawo su already tana gidan” gyadamai kai Nura yayi ahankali, juyarda kanshi yayi yana kallon titi bayako kyafta idanu sunyi nisa sosai ahankali yace “Musa park the car please” parking motan Musa yayi yace “lpy”? Ahankali Nura yacemai “ina zuwa” bude motan yayi yafita yafara tafiya zuwa gefen titi, saida yadanyi nisa sai kawai ya tsugunna yabawa titi baya, Musa dake kallonshi ta cikin mota Nura ya bala’in bashi tausayi dan Nura is hurt da yanda Hadiza ta makashi a kotu dakuma mishi shairi, da wulakanta shi datayi, badadan lawyer shi ba da har handcuff za’a samai a hannu fa, he’s heart broken sosai.
Wayanshi daya bari kan kujera ne yahau ruri hakan yasa ya kalli screen din ganin Hajiya ne yasa yadauki wayan tareda saukowa daga mota yawuce inda yake aduke yadafash tareda bashi wayan yace “koma mota kayi waya da Hajiya ita ke kira, bari na shiga super market din chan nasamo mana ruwa, ba ruwa a motan da dan abinci bamuci komiba tun safe” karban wayan Nura yayi yawuce mota tareda zama abaya shikuma Alhaji Musa yawuce super market.
Daukan wayan Nura yayi kafinma yayi magana yaji unsettle muryan Hajiya tace “Nura I’ve been calling you tun dazu wayanka baya shiga kana ina” cikeda dauriya gudun kada ta gane komi yace “inda nake ba network ne Hajiya” dan shiru Hajiya tayi jin muryanshi kafin tace “kanin yaron nan dake neman auren Meena yakira yayanshi yake fadi yaganka a kotu matarka takawo karanka shi yana aiki a Admin office ne kaman ku wai dayagani da Meena yasa yakira yayanshi, what is happening Nura? Kaine aka gani a kotu”? Dan lumshe idanu Nura yayi wato babu abinda yakai bad news spreading, jin yakasa magana yasa cikeda damuwa sosai Hajiya tace “what happen talk to me Nura, kasan how worried sick nake kuwa tun dazu nake kira waya ka baya shiga, meke faruwa Nurudeen”? In a very weak voice yace “Hajiya Hadiza takai karana kotu sabida na mareta shekaran jiya…….” Da kyar dai ya iya bama Hajiya labarin sama sama, Hajiya tai shiru kaman wacce ruwa ya cinye tanajin muryanshi dake breaking sosai, ance tsakanin d’a da uwa sai Allah dudda he’s trying to show her he’s fine but she could feel pain din danta piercing through every organ na jikinta, she feel yanda voice nashi is so weak, shaking with lots of sorrow atattare dashi, cikin dauriya da kokarin so tabashi karfi dakuma tsananin so irin wacce mahaifiya kema danta tace “are you okay yanzu? Kun gama zancen kotun? Hope babu abinda ya sameka? Did anybody hurt you Nura? Tell me wani abu yasameka kun gama da kotun, are you fine Son?” Hajiya ya jeromai tambayoyin cikeda damuwa, da tausayi dakuma matukar son danta, baki Nura yabude zaiyi magana sai yaji abu ya tokaremai wuya, dagewa yayi cikin karfin hali irin na maza zaiyi magana yakasa sai hawaye sharrrr, duk yanda yaso ya danne kukan yakasa abinda he can’t remember the last time yayi arayuwanshi sai kawai kukan yashiga flowing, cikin murya mai bala’in rauni da bata nuna kaman mutum na kuka but at the same time kuka yake yace “Hajiya I don’t know why all this is happening to me?” Yadanyi shiru cus muryanshi na rawa kukan dayake yazama so obvious yace “Hajiya Hadiza hurt me deeply, she crushed my ego today, laifine dan na sota? Hadizan danai soyayya da ita harna aura was a hardworking obedient wife, muna dawowa Abuja ta chanza, I put up with every attitude nata cus idan akwai soyayya dole akwai sacrifice da hakuri da juriya, she did so many mistakes ina yafemata and overlook nama manta something like that ever happened, all because of one slap Hajiya wanda in all this years da muna tare ban taba mata ba can’t she forgive me, I am human Hajiya, I get angry too, banfi karfin kofsawaba haka banfi karfin aikata kuskure ba babu abinda fushi baya sawa, but sabida a single slap ta makani a kotu tabatamin suna batare datayi tunani how this action will affect me ba, or my children, Hajiya mata yakamata tazama mai rufawa mijinta asiri, idan yamata kuskure ta rufamai asiri, tanuna min cewa ita ba matan da zata iya rufamin asiri bane and bata damu da self respect dina ba, I love Hadiza alot, I’ve done all I could but tunda abin yakai ga haka gwara na hakura da ita for good!” Hajiya jitayi kaman tayi kuka sabida yanda taji Nura is seriously crying, bazata iya tuna the last time da Nura yayi kuka ba maybe tun yana primary school, Nura grew up as a strong hardworking man, baida magana, ita badadan tazo Abujan nan sabida ciwon taba batasan kalan rayuwan dayakeyi da iyalinshi ba, ko sunzo kano babban salla Hadiza bata zama gidanta gidan su take zuwa to ta ina zata gane wani kalan rayuwa suke ciki? Nura ba gayamata zaiyiba, banda hakama is not proper tasa kanta arayuwan gidanshi, datazo Abuja taga zamansu saisa dayazo mata da maganan auren Ummi bata hanashi ba, saisa take sonshi da Ummi dantaga itane yarinyar dazai iya tankwarawa dan ayanda taga Hadiza wlh wlh tafi karfin danta, babu yanda zatayi ne dan yana sonta amman babu mahaifiyar da zataso taga mata na ganama danta azaban da Hadiza kewa danta, tun ranan farko data shigo Abuja taga kallan zaman dasuke ta dage sosai da yima danta addu’a kan Allah yakawo mai karshen wahalan nan, idan aurensu akwai alkhairi to Allah ya daidaitasu idan babu Allah yakawo musu mafita su biyun. Anatse dakuma soft tone ganin danta is weak tace “Nura bazan maka karyaba auren ku dakai da Hadiza has become toxic, the space will do the two of good, burina shine Allah ya zaba maka abinda yafi maka alkhairi, Allah ya takaita muku wahala, ka kawomin yaran nan kano gobe” kaman maraya Nura yace “tohh” Hajiya jitayi zatamai kuka tadai daure no one can understand the pain of a mother idan taga danta na wahala, Nura is suffering sosai cus yanason Hadiza, Hadiza kuma ta maida Nuran kaman abokin fadanta, Nura yabata tausayi sosai daurewa kawai tayi hatası ta fashe da kuka damuwan takaramai yawa, ahankali tace “kazo kano gobe Ummi na nan wajena” dasauri cikin muryan da ba karfi har lokacin yace “eh”? Ahankali Hajiya tace “Ummi na gidana bataje kauyensu ba” lumshe idanu Nura yayi ahankali saikuma yabudesu baice komiba, Hajiya tace “you will get true this Nura, duk abinda bai ragazaka ba will only make u stronger, rayuwa yagaji haka, Allah ya kyauta ina kuma yima Hadiza fatan shiriya, Allah ya shiryata, Allah ya ganar da ita, sai kazo gobe kaji, Allah tamaka albarka Allah ya rage maka zafin dakakeji azuciyanka, May Allah grant you comfort my Son” ahankali Nura yace “Ameen Hajiya” Ahankali tace “kagama da kotun gabaki daya yanzu?” Gyadamata kai yayi yace “eh ina tareda Alhaji Musa ne zamu tafi gida” Ahankali Hajiya tace “to kuje gidan first I will call u later, don’t forget ka kira mahaifin Hadiza koka turamai sakon message” gyadama Hajiya kai yayi ya katse wayan yashiga aikama Mahaifin Hadiza message dan baijin zai iyamai magana yanzu ba.
Hajiya jitayi kaman akwai dutse akan zuciyanta duk yanda zatai bayani bazaku fahimta ba Nura is her only son, shine amatsayin mahaifi ga duka kannenshi mata, shine komi nasu, shine school nasu, shine kayan dakinsu, shine komi, shine abincinta, maganinta daidai da electric bill na gidan nan da swan bottle water datake sha da komi ma shine and Hadiza is trying to kill her son for her, bawai ta tsani Hadiza bane but zuciya batada kashi, datake Abujan nan taga abinda ke faruwa Hadiza ta siremata tatas daga zuciya babu uwar dazatazo matar dake wulakanta mata dan datasan zafin haihuwan shi, Hadiza fitinanniyan mata ce ta fitini danta haba! Aisha takira wacce itace gist partner Hajiya dan banda Nura itace yatta tabiyu kuma kunsan mata da iya relating to pain din maman su.
Aisha na kiran Hajiya back Hajiya tafashe da kuka tace “Aisha Hadiza zata kashemini yaro wannan wani kalan abune me d’a yamata? Aisha cikinku babu wacce kema mijinta yanda Hadiza kema Nura, kunama mazanku girki, kuna girmamasu, why is my son so unlucky da mata eh? Kashemin yaro takeso tayi? Zata haifamin waninshi ne eh? Yarona sai kuka yake all because of her, why are so women so heartless? I know babu excuse na marin mace, Nura was very very wrong daya mari Hadiza, mari ba kyau musulunci yahana amman akwai forgiveness a aure, tsakanin mata da miji yakamata akwai yafiya, jinkai tausayi wanda duka naga Nura nama Hadiza, what’s the point na makashi a kotu uban yaran dakika haifa aduniya fa, sabida ya mareki? Idan ma so take abimata hakkinta for marin daya mata she can call me wlh saina sabamai, zata iya kiran mahaifinta takai karan Nura akira amai kashedi kada ya kara taba lafiyanta, kotu all sabida mari is too harsh, so take Nura ya wulakanta aduniya dayau beda kudin bail da yana gidan yari yanzu haka, ga yarinya mai ladabi da biyayya ya aura amman hankali shi baya kanta yafison wacce ke bashi kashi wai yaya kan maza yake ne mesa sun fison abinda ke cutarda su? Hadiza ce kadai mace aduniya akan wani dalili zata dinga wulakanta min da shirun dataga nayi ta dauka tsoron ta nakeji koko ta dauka bansan darajan dan cikina bane”? Cikeda lallashi ganin ran Hajiya na tafarfasa Ya Aisha tace “Hajiya please stop crying is not good for you kada su Meena su jiki suzo suna kuka suna duk hankalinsu yatashi” cikin kuka Hajiya tace “basanan sun tafi lesson din da Meena keyi da ita da Ummi, Aisha I don’t care Nura ya haihu da Hadiza sunada yara all I know shine ko yau Allah zai dauki yara koda Ummi bata karbesu ba ku zaku amshesu bazasu taba wulakanta ba Aman da Amali, wlh wlh idan yarinyar chan takaini bango karshen auren su kenan koda Nura zai maidata saina hanashi, if she’s not ready ta zauna da yarona let her go gabaki daya” calming Hajiya down Aisha tayi sosai, tadinga bata hakuri da kyar tashawo kan Hajiya ta huce tayimata hira har saida su Meena suka dawo gida sannan tabarta tamata sallama.
Saida sukai magrib suka wuce gida, Nura na sallama su Amal da Aman dake wasa da yaran Alhaji Musa afalo suka taho da gudu suka rungumeshi suna oyoyo Dady, yaran Musa ma haka boye duk wata damuwarshi yayi yayi murmsuhi suka daddauki yaran suka shigo gidan cikeda girmamawa Maman Humaira ta gaida Nura ya amsa Humaira ma ta gaidashi cikeda girmamawa Nura ya shafa kanta yace “Humaira is now a big girl fa yaushe aka haifi Humaira nazo na dauketa a baby showel a hospital” akunyace Humaira ta rufe fuskanta duk akai dariya, abinci Maman Humaira takawo akaci suka fice dan yin isha’i Humaira ta wanke komi da sukai amfani dashi suna dawowa daga mosque suka tafi gidan yarage daga Nura saisu Aman dake wasa da toys akan rug, dago kanshi Aman yayi yakalli Babanshi saikuma yabar toys din yahayo kan kujeran yazauna kusadashi ahankali yace “Daddy are you fine?” Dasauri Nura yakalleshi saikuma yamai murmushi ganin yanda yaron ke kallonshi yace “yes Dady is fine” dasauri Amal itama tabar wasan ta hayo kujeran ta zauna kan cinyanshi takai hannunta ta taba fuskanshi tace “Dady you look very sad today right Ya Aman?” Gyadamata kai Aman yayi yana kallon Baban nashi shima, murmushi Nura yamusu baice komaiba sai kawai ya kama kansu ya manna musu peck cikeda so, ahankali Aman yace “Dady where is Mom? Bata dawoba” shiru Nura yayi yana kallonsu they have the right susan meke faruwa dudda yarane, anatse yana kallonsu duka biyun dake kallonshi kur kaman tv saikuma yakama hannunsu cikin tsantsan so da kamanta magana ta yanda yara zasu fahimta yace “Mommy will not be living with us again, Daddy is not together with Mommy” Sosai yaran ke kallonshi sukai shiruu dukansu biyun suna kallon fuskanshi chan Aman yace “Momy started doing those bad things again right Dad? Is that why your eyes are read”? Dasauri Amal abunku da yarinyar takai duka hannayenta kan kumatun Babanta tajuyo da fuskanshi saitin nata tawani leka idanunshi kaman wacce ke leka rijiya, cikin muryan yara tace “Mommy hurt my Dad, Aman daddy eyes are red like he criedddddd” taja cried din tana sakin kuncinshi tai kwaba kwaba da fuska zatai kuka da sauri Nura yace “no Amali don’t cry ni banyi kuka ba, Dady ai baya kuka, idanuna na ciwo ne saisa sukai ja” ahankali Aman yakama hannun Babanshi shima kaman zai fashe da kuka yace “Dady I promise I will never hurt you like Mommy does, and we will never ever yelled at you or scream or be stubborn ko Amali”? Gyadamai kai Amali tayi ashagawabe tace “I love my Dady very much Ya Aman I hate seeing my Daddy looking sad” ta rungumeshi, Aman shima ya rungumeshi yace “Dady you are my superhero and I love you alot Dad, you are the best Dady don’t be angry kaji Dady, kayakuri, Anty Ummi said Innallaha….” Dasauri Amali ta taso daga jikin Baban tace “ma’a sabireen” atare suka hada baki sukace “lalle Allah yana tare da mai hakuri, Dady kayakuri kaji” gyadamusu kai Nura yayi yanaji kaman yayi kuka maganansu ya mugun sosamai zuciya kawai ya rungume yaranshi kowanne side side gam gam, arayuwanshi yanason yaran nan, su biyun nan are his soul, yaranshi are just so adorable and sweet kuma suna sonshi sosai, sai yaji Ummi takara shiga ranshi, akwai some small small abubuwa datake koyama yaran da he so much appreciates, kaman son junansu tanunama yaran su biyu are one and Aman should always take care of Amali, wlh dawuya kaga Aman da Amal nafada ko sunyi sharp sharp zakaga Aman ya rungume Amali ya lallasheta he’s so protective of little sister nashi and is all thanks to Ummi da yan tatsuniya da labaran datake basu. Banda haka kana ganin kaman basusan meke faruwa ba they understand everything, saisa ko fada bayaso yanayi da Hadiza agabansu especially Aman dan yaron is very smart.
Sun dade ahaka saida yaji dukansu sunyi bacci sannan ya daddaukesu yaje ya kwantar da su adakinsu, wanka yayi anan bayin Aman yafito yaje dakin Ummi yadauko wani jallabiya yasaka yadawo dakin Aman ya kwanta yayi shiruuu sai chan hawaye ya gangaro daga gefen idanunshi dasauri yasa hannu ya share tareda fuzar da iska yace “enough!” Tashi yayi yadauki wayanshi yaciro number Hadiza yayi deleting, yashiga files nashi yashiga deleting komi nata messages, pics, yashiga whatsapp yayi blocking nata ta ko’ina, ya maida settings na wayanshi ta yanda unknown number bazai iya kiranshi ba, yanaso from daren yau yarufe babin Hadiza gabaki daya and just move on with his life, harga Allah he wish her well koba komi itane mahaifiyar yaranshi he wants her to get everything datakeso in this life to tayi rayuwan datakeso, he wants her to excel and attain success in business nata, but for him ya yafe Hadiza koda zai mutu he don’t wanna ever be together da mace kalan Hadiza ma balle Hadiza, he just wanna live his life yanzu da wacce keda opposite of all abubuwan da Hadiza kedashi.
Washegari as usual da wuri ya tashi yana dawowa tea yashiga kitchen yamusu yayi microwaving abincin da Maman Humaira ta dafa yayi arranging komi a dinning yaje sama yatadasu ya musu wanka brush yasa sukai salla yafito yabasu abinci tsaf suka cinye daidai wata babban mota na zuwa gaban gidan, sama yakai yaran dakinsu yabasu iPad nasu sannan yafito ya shigo da maza su 7 aka shiga kwashe kayan gidan ana fitar da su, dudda duka kayan gidan na Nura ne, dasukai aure da kayanta aka kawota gidan su na Kano dazasu dawo Abuja yasa ta kyautar da komi yamata komi sabo but he wants her to have it dan Allah yasani da sunanta yasai everything agidan kap, kayan dakin Ummi da gadajen dakin yaran ne kawai ba’a taba ba but hatta kujerun falon sama tass aka fitarda komi gidan looks empty yar kayan kitchen, frames menene menene, address na gidan iyayen Hadiza yabasu a kano yariga yabiyasu kudinsu aka tafi sosai ya tsaya yana kallon gidan da babu komi ciki banda pentin bango, kawai yawuce sama dakin yaran ya shiga yahada kayansu tsaf a akwatinan su dan idan yabar gidan nan sabon gidanshi zasu koma next time, shima ya tattara kayanshi awani akwati yasauka kasa shida mai gadi suka ijiye a boot already yaran sun gama exam badai suyi closing school ba tukunna amman yakira school nasu yagayamusu tafiya takamashi yadawo yadaukesu suka sauko yasasu amota ya kulle gidan yashiga mota office yaje yayi some ayyuka da komi yabarma manager shi aikin sannan by 2:00 suka tafi airport dan 2:45pm jirgin zai daga, yaran were so happy zasuyi tafiya they’ve missed traveling daganan sukai flying sai kano inda direban Hajiya ke jiransu already.
Kuna ganin Nura made the right decision na rufe chapter Hadiza gabaki daya in his life??
Koko kuna ganin is not the right decision daya kamata yadauka??
Me aganinku yakamata yayi??
In his statement “I want mace complete opposite na Hadiza” yana nufin wacce is not as educated as Hadiza, expose as Hadiza dadai sauran su, kuna ganin that’s the best thing for him??
What are the perks na auren educated independent woman??
And what are the perks na auren uneducated uncivilized lady???
Don’t forget ku shigo class dina na matan Aure with just 2k chat me up today wa.me/+2347012181461