Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 24

Sponsored Links

Chapter 24

Yanda nake sauri har bana iya ganin gaba araina kuwa faɗi nake mai wannan tsohon yake nufi dani ne,shiɗin saurayin ƙawatace wanda take mutuwar so sabida ƙudin sa to wai meke shirin faruwa danine kode yafaɗi wani abu akaina ne yasa ta zaɓin yimun rashin mutunci ranan kuma tasaka mahaifiyarta tazo har gida taci mana mutunci harda yi mana gorin alherin da sukai mana abaya,idan kuwa hakane haƙiƙa sunyi kuskure daga shi har ita dan ni rayuwata ba soyayyar mai kuɗi acikin.

Banyi aune ba sai jin na bugu da abu nayi taga taga nayi kaman zan faɗi runtse idona saboda na gama saddakarwa faɗiwa kawai zanyi,jin ban kai ƙasa ba yasani buɗe idona da sauri na sauke a fuskar wanda ya rikoni yana kallon cikin idanuna wani irin ajiyar zuciya na sauke tare da yin saurin zame jikina daga nashi ina daidaita zaman hijabina ba tare da nasake kallon inda yake tsayen ba,jikina sai ɓari yake saboda yaune karon farko da wani ɗa namiji ya taɓa taɓa riƙemun hannu.

Wuce shi nayi ba tare da nasake waiwayo shi ba,kawai de inaji ajikina kaman ana kallo na,harna wuce nayi shigewata hall ɗinda muke ɗinki.

Fadila jiki a sanyaye ta dawo gida dan jinta take wani iri tunda shugaba yace mata jinin innarta dodo yakeso kawai taji duk wani abun duniya da take da burin tasamu ya fita mata a rai.

Jiki ba ƙwari haka ta shigo gidan cikin sanyi jiki da ta shigo gidan innarta sar zuba take tasaka ƙanwar fadila mai suna harira ta kawo mata jalof ɗin macarooni da yasha bandan kifi sai turirin yake tashi da kunun aya mai sanyi,kasaci fadila tayi,sai kallon innarsu take cike da so.

Kallonta mama rabi tayi tana ta washe baki dan yanzu fadila bata lefi a gidan tunda tana da ɗan abu a hannun ta”kici abinci mana kin zauna kin tasa abinci a gaba sai ya huce tukunna ta kare maganar cike da kulawa”mama wallahi bana jin cin komaine mama wallahi raina a ɓace yake yau ta amsa mata batare da kalli inda mamar take zaune ba”me yafaru?
Waye taɓa mun ke ƴar albarka,duk kusan a tare jero mata da tambayan.

hmmm tasauke ajiyar zuciya ganin yanda mama rabi ta ruɗe yasa tayi ƙokarin ɓuye tata damuwar ta tace”bafa wani abunda zaki tada hankali akansa bane kawai Alhajina ne yace yanason Aisha kinji…..”kan bazawara ba gashi mama rabi ta katseta da fadi yo akwai abunda yafi wannan tashi hankali ne amma anyi tsinanniyar yarinya yanzu duk jan kunne dana musu ita da uwarta saida tabi ta ƙarƙashin ƙasa danta rabamu da farin ciki kawai dan anga canji a rayuwarmu to wallahi bazata tsaɓo ba sai naje har gidan nasu na cicci musu mutunci wallahi takare magana tana hucin ta ƙaici.

Dama tun fil azal saida namiki magana akan ƙawancen ku kikace ba komai yo ina kika taɓa ganin inda abotan ƙyakkyau ya ɗaure data mummuna,ai duk wanda zece yana sonki da zaran ya ɗaura ido akanta sai yaji hankalin sa ya karkata gun,haka mama rabi ta karaci faɗanta karshede taji bazata iya hakuri batare da taje ta sami maman Aisha tamata jan kunne ba,idan ko ta ƙiji to wallahi bazata ƙi gani wallahi ko tsirara zatayi yawo a doron duniya ƴarta bazata bari ƴata tashiga damuwa ba.

Ahmad office ya koma ya zauna duk yarasa abunda yake masa daɗi,kawai maganan wannan mutumin ke zo masa cikin kunnen sa inda yake cewa,Aisha inasonki kuma aurenki zanyi.

Watse yayi da duk kayan da ke saman table ɗin dake office ɗin nasa sai huci yake yadafe kansa dake sara masa da hannu,jin kaman fashewar abu yasa khalid daya hana Alh shehu bin bayan aisha shigowa daga ciki dan ce masa nan wajen aikine alh ba dandalin soyayya ba dan haka kayi hakuri idan ta koma gida kasameta a can wannan ba girman kane ba.

Gaskiya abunda khalid ya fadamasa da alama ya shige sa dan shi ko ɗaya be kawo hakan a ransa ba kawai aisha dake gaban sa idon sa yake gani gani yake kaman shigan da tayi bazata fito ba haka yakeji a ransa.

“Bro lafiya kuwa?
Ya tambaye sa lokacin da ya faɗo cikin office ɗin a guje,turus yaja yatsaya ganin yanda ya maida office din.
Meke fatuwa anan?
yasake tambaya cikin sanyin murya sanda ya karaso tsakiyan office ɗin sosai,zama yayi saman kugera yana ta maida numfashi ba tare da ko kalli khalid dake juro masa tambaya ba.

Ruwa mai sanyi khalid ya dauko masa daga cikin freezer sai da yabude goran ya miƙa masa karɓa yayi ya kafa kansa saida yama goran tass sannan yayi jifa da goran ya jinjina da kujeran da yake zaune yamai da idon sa ya lumshe kaman mai bacci amma duk yanda yaso ya ƙice fuskan wannan banzan mutumin a ransa kasawa yayi,dan Allah mai zatayi da wannan tsohun dawani tumbi kaman randa”au bro to kai ina ruwanka da tsufan sa da tumbinsa tunda ba sonta kake ba,kumama ai farare bugun abuja.

Bude idonsa dake lumshe ya zubasu fess saman fuskar khalid daga masa gira khalid din yayi haka ya tabbatar masa da zance zuci dayake yafito fili.

Leave a Reply

Back to top button