Musabbabi Book 2 Page 3
https://chat.whatsapp.com/JUeJeOL9kA8AHOGOfXOnSZ
MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu Meyere)
Page 3
Karfe ɗaya saura minti uku na dare, Afrah na lafe a saman faffaɗan ƙirjin Musaddiƙ, gaba ɗayansu cike su ke da shauƙin son junansu, hakan yasa Afrah ta ƙara sunne kanta cikin kirjinsa, cikin sanyin murya ta kira sunansa, ya amsa yana ƙara matseta tsam, tamkar zai maidata cikin jikinsa, ta ɗan lumshe manyan idanunta tace “Ni ko yaya wata alfarma zan nema a wajenka, ina fatan kuma zaka yi min”. Da sauri ya amsa “Menene Afrah, bana jin akwai abinda zaki nema a guna matuƙar ina da halin yi miki na kasa yi, domin nasan ba zski taɓa yin abinda zai cutar da ni ba”.
Ta yi ɗan murmushi tace “yaya so nake ka barni na cigaba da karatuna”.
Ya numfasa gami da ɗago kanta, duk da babu wadataccen hasken da zai iya ganin fuskarta, sai yasa baki ya sumbaci saman goshinta, sannan ya maidata ya ƙwantar, yace “Dama na sani duk abinda zai fito a bakinki yana da muhimmanci, wannan tunanin ni ne yakamata nayi shi, saboda haka na yarda zaki cigaba da karatunki ni da kaina kuma zan samo miki makarantar”.
Cike da farinciki ta ƙara ƙwaƙume shi tana yi masa godiya.
Baisan dalilin da yasa a duk lokacin da ya faranta ran Afrah yake jin ya fita farincikin ba, domin dai ko yanzu ji ya yi wani daɗi na ratsa zuciyarsa, yadda ta ke jindaɗi ya fi masa komai.
Federal university of technology (F.U.T) Minna nan Murtala ya koma da aiki, Musaddiƙ yasan makarantar domin nan yake zuwa ya sami murtalan. Don haka shine mutum na farko da ya faɗo masa a rai wamda yake jin zai iya taimakonsa.
Hakan yasa washegari ya fita kafin lokacin fitarsa, amma fa sai da su kayi azkar shi da Afrah tun asuba, domin dai babu yadda za’ayi Afrah ta barshi ya fita ba tare da ya yi azkar ba. Ga ruwan ayatul sihir da kullum sai ya sha kafin ya bar gida. Haj kilishi na cikin zuciyarsa hakan yasa ya kasa fita har sai da ya shiga ya dubata, har yanzu cikin ciwon take sosai, domin nan ya tadda Hassana yadda ta gaya masa kuma tun asuba ta baro gidan mijinta ta taho saboda wayar da Haj kilishin ta yi mata cikin dare, cewar jikinta ya rikice.
Musaddiƙ ya matso sosai kusa da ita tama cikin bargo tana rawar sanyi.
Ya miƙa hannu ya taɓa saman wuyanta, zafi kamar wuta, da sauri ya cire hannunsa, ya dawo da kallonsa kan Hassana cikin damuwa yace “Ni ina ganin mai zai hana a koma asibiti”.
Hassana tace “Ni ma na yi tunanin hakan amma Haj ta dage ba zata koma ba sai ta gama shanye magungunanta, tunda dama ance maganin zai iya zafafa ciwon kafin daga baya ya dawo ya yi maganin ciwon”.
Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai, ya ƙara mata sannu sannan ya juya zai fita, duk da tana cikin wahala amma baƙar zuciyarta ba zata barta zama lafiya ba, da sauri cikin galabaitacciyar murya tace “Musaddiƙ ba zaka zauna tare da ni ba, tafiya zaka yi”, ta faɗi maganar tare da addu’ar Allah yasa ya yarda ya zauna ɗin, ko ba komai tasan zata sa ya makara wajen aiki, wanda hakan zai iya sawa ya sami matsala a wajen aikin, wanda dama burinta kenan.
Har ya dawo kamar zai zauna, harta fara jindaɗi sai kuma ya tsaya, ya ɗan dubeta yace “zan so na zauna kusa da ke Haj ko don na kula da ke, amma yau zamu tafi Abuja ni da Haj Hudah, zata halacci wani taro kuma yau zamu dawo, bana son na makara”, wani baƙinciki ya ƙara cika zuciyar Haj kilishi, ta maida idonta ta rufe, domin dai tasan kafiyar musaddiƙ tunda ya faɗi uzurinsa to bazai taɓa canjawa ba, don haka yi masa magana ma baida wani amfani,
Har ya fice bata buɗe ido ba, sai la’anta da tsinuwa da take masa. Da ta ɗan ji sauƙi amma yanzu ji tayi gaba ɗaya ciwon ya dawo mata.
Makaranta Musaddiƙ ya fara wucewa domin cika alkawarinsa ga Afrah. Ya sami murtala da maganar, cikin jindaɗi murtala ya gaya masa babu damuwa, domin an faɗa akan lokaci domin kuwa yanzu aka fara saida form.
Don haka murtala da kansa ya yi alƙawarin saya ma Afrah form ɗin, tare da neman taimakon malaman da ya sani a makarantar, domin su taimaka wajen samun admission ɗin.
Godiya sosai musaddiƙ ya yi ma murtala, a wajen kuma ya kira Afrah ya sanar da ita yadda su kayi da murtala, sannan ya bashi wayar domin ta yi masa godiya.
Daga wajen Murtala gidan Haj Hudah ya wuce.
Abinda ya ke gudu ne ys faru domin tuntuni Haj Hudah ta shirya, shi kaɗai ake jira. Meating ɗin da zata je yana da matuƙar muhimmanci, babu buƙatar ta makara, ba don ta ɗorawa kanta tafiya da musaddiƙ ba da tuni ta tafi ta bar shi. Sai da suka shiga mota sannan ta dube shi, bata iya yin fushi da shi, don haka ta sami kanta da yin ɗan murmushi tace “Ina ka aje wayarka?”, da sauri ya fito da wayar a bayan aljihunsa ya na dubawa, missed calls ɗinta ya gani har guda huɗu.
Ya yi saurin ɗagowa ya dubeta, yace “Banga kiranki ba Rankiyadaɗe, ayi haƙuri”.
Wani irin ƙayataccen murmushi ta jefe shi da shi, wanda nan da nan musaddiƙ ya ɗauke kansa, tace “Babu damuwa, amma dai kasan ka makara ko?”. Ba tare da ya kalleta ba, yace “ Na je yin wani uziri na matata ne”.
Ji ta yi kamar an watsa mata wuta a jikinta. Tayi danasanin tambayarsa, don da tasan irin amsar da zai bata kenan da bata tambaye shi ba. Dif ta yi har su ka kai Abuja bata ƙara magana ba. Wato musaddiƙ irin mazan nan ne masu ɗaukar matansu da muhimmanci, bayan irin ɗimbin son da ta fahimci ya na yi mata, har da kuma hidumta mata, lalle musaddiƙ irin su mata ke buƙata. Shin me ye matsayin musaddiƙ a wajenta? Da har ta ke shiga muguwar damuwa a duk lokacin da ta ga kusancin da ke tsakaninsa da matarsa, me yasa duk abinda yake ma matarsa take jin ina ma ita yake yi ma?.
Duk tafiyar da su ke yi, motsi kaɗan musaddiƙ sai ya kira Afrah ya ji halinda take ciki, Haj Hudah na jinsa yana roƙonta ta shiga ta zauna tare da Haj kilishi, duk da bata san wacece Haj kilishin ba, tayi mamakin yadda ta ji ya na yi mata magiya yana ƙasƙantar da kansa wajen roƙonta ta je ta zauna tare da ita. Nan ma ji ta yi wani abu ya tsaya mata arai, haka nan ta ji a ranta tana son ganin wannan matar ta sa, da ta fahimci bai hala kowa da ita ba.
Taso ace mijinta Alh yusuf sanda ne yake yi mata irin wannan tarairayar.
Ta maida bayanta ta kwantar a jikin kujera, ya zama dole yau dai ta gano dalilin irin wannan rikicewar da tayi akan musaddiƙ.
Har su kayi taron suka tashi Haj Hudah bata cikin nutsuwarta, hatta abinci juya cokalin kawai take yi, ta kasa cin komai. Sosai Musaddiƙ ya lura da halin da take ciki, ko kaɗan bai kawo damuwar al’umma bace kwance a fuskar Haj Hudah ya fi yarda da cewa damuwar mijinta ke nuƙurƙusar zuciyarta. Tabbas ko shi ya na jin tausayinta domin ba ko wace mace bace zata ɗauki wannan ƙasƙancin na wofintarwa daga mijinta, duk da dai baisan wane tsari suka tsarawa kansu ba, to amma a ganinsa tamkar akwai ɗaukar hakki.
Don dai magana ta gaskiya a ɗan zaman da su kayi bazai taɓa yi mata shaidar tana bin maza ba, don haka a matsayinta na cikakkiyar mace tana da damar da zata shiga damuwar rashin miji a kusa da ita. Sauri ya yi ya watsar da tunanin , don ɗabi’ar sa ce rashin son shiga abinda babu ruwansa. Kawai dai yasan shi wani irin mutim ne da baya son ganin ɗan’uwansa musulmi cikin damuwa.
Ƙarfe shida na yammaci su ka shigo minna, har kuma zuwa wannan lokacin Haj Hudah bata saki ranta ba, damuwarta na nan a maƙale a fuskarta.
Bayan isar su gida, sallama kawai su kayi ta shige gida da sauri, ta haye sama ta yaye labulen windo ta zubama musaddiƙ ido, yana ta wasa da dariya da masu gadi, komai ya yi burgeta yake yi, ta daɗe tsaye tana kallonsa har sai da ya yi sallama da kowa ya buɗe get ya fice sannan ta saki ajiyar zuciya, ta sulale ƙasa ta yi zaman dirshan.
Hakanan ta ji wasu sanyayan haeaye suna fita babu ƙaƙƙautawa, ta ɗora kanta jikin kujera tayi kuka mai isarta, har sai da jikinta ya ɗauki zafi, domin dai a yau a cikin kuma wannan lokacin ta tabbatarma kanta da cewa son musaddiƙ take, ta runtse idanunta tana girgiza kai, zuciya ba ta da ƙashi, baka sanin sanda so yake shiga cikinta, idan banda haka ta yaya tana matsayin matar aure amma ace zuciyarta tana son wanin mijinta, subhanallahi! Wace irin ƙaddara ce wannan, ta yaya zata ba zuciyarta abinda ta ke so bayan bai kasance na ta ba, shin ta yaya zata cire son musaddiƙ a cikin zuciyarta bayan tana jin tamkar zata zauce akan son na sa, ta ya ya zata iya ɓoye wannan nannauyan al’amarin bayan idan tana tare da musaddiƙ bata iya mallakar tunaninta balle kanta .
Tana son mallakar musaddiƙ ko da na yini ɗaya ne, wata zuciyar ta shiga kwaɓa mata, ta yaya zaki faɗa mummunan hanya wacce bata da wajen ɓullewa, kin san girman zunubin da ki ke ɗaukar ma kan ki kuwa na kawai kina son sa, balle kuma ta kai ga kin keɓe da shi, shin bakya ganin irin ɗimbin girma da kima da musaddiƙ yake baki, bakya tsoron duk ranar da ki ka ne me shi da wannan maganar duk girman ki zai xuɓe karshema ya na iya maida ke wata abin kyama yadda kuma yake son matarsa abu ne mawuyaci ya iya cin amanarta, ƙarshe babu abinda zata tsira da shi sai kiyayyarta da zai zauna a cikin zuciyarsa.
Duk wannan kashedi ne da tunatarwa daga zuciyarta, kawai Haj Hudah ji tayi ta ƙara rushewa da kuka mai tsanani, ita kanta tasan abar tausayi ce, domin duk wanda yake cikin saɓon Allah to lalle ya zama abin tausayi. A wannan daren duk abinda Haj Hudah ta saba yi bata yi ko ɗaya ba, hatta abinci bata iya fitowa ta ci ba, wanka kawai ta samu ta iya yi shi ma bata shafa ko mai ba, kayan bacci kawai ta zura ta haye gado ta ja bargo, wani ƙarin tashin hankali da zaran ta rufe ido babu wanda take gani sai musaddiƙ, karfe sha ɗaya da rabi na dare wayarta ta ɗauki ƙara , daƙer ta iya ɗago kai ta duba mai kiranta, ganin Alh yusuf sanda ne a hankali ta saki tsaki ta maida kanta ta kwantar.
Ji wani rashin adalci ba ka tare da mutum amma ka kira ka ji halinda matarka take ciki ya gagara, kira kawai fa, haba tun wayewar garin yau kwata kwata bai kira ba, itace dama ta saba kiransa to itama ta dake ta ƙi kira wanda hakan baisa shi ya kira ba, ta ƙara sakin tsaki a lokacin da ta tuna yadda yadda duk bayan awanni musaddiƙ ke kiran matarsa don kawai ya ji lafiyarta, tabbas da magidanta zasu san illar rashin kiran matansu a waya da sun daina. Ta yi zaton zai ƙara kira amma ga mamakinta bai ƙara kiranta ba. Ta maida idonta ta rufe tana addu’ar Allah ya kawo mata bacci.
Wasa wasa dai ciwon Haj kilishi sai gaba yake, bayan ciwon ƙirji da kai, yanzu harda ciwon ƙafa, kullum zuwa ganin likita wani lokacin ma har gado su ke bata na yan kwanaki kafin su sallameta, magunguna kuwa harda na banza, kuɗi take kashewa sosai akan neman lafiyarta, sai dai duk da tana cikin wannan halin ba ta yi tunanin saduda ba, domin tuni ta ɗora Haj Rakiya akan ta dinga wakiltarta a wajen boka Tsiduhu da mai Rakwacam, ita take ba duk kuɗin da ake buƙata ta kai to tana kai dai na Mai Rakwacam tunda shi Haj kilishi tana nambar wayarsa suna waya dole ta rufama kanta asiri ta dinga kai masa, sai dai duk da haka tana ƙarawa tana cire nata ta kai masa na shi. Na Tsiduhu kuwa sammasa take ta riƙe sauran, duniya ta zamar mata sabuwa, ta canja kujeru ta yi abubuwa da dama da zasu amfaneta, ta gane duk bin malaman da su ke yi ƙarya ce kawai sa’a ne , gaskiya ta dawo daga rakiyar abubuwa da dama.
So tari ma ji take kamar ta je ta raba kanta da nauyi ta hanyar tone asirin da su ka yi ma musaddiƙ, domin bata san dalilin da yasa take jin tausayinsa ba yanzu da zaran ta gan shi, domin yadda yanzu ya dage da yin yaƙi da ƙaddararsa ya sa ƙaimi wajen dawowa mutum nagari. Domin da kansa mai Rakwacam ya yi mata bayanin yanzu fa shi ma musaddiƙ tsaye yake da addu’a kuma akwai addu’ar da matarsa take bashi yana sha matuƙar yana sha kumq babu abinda zai iya yi masa, asalima idan ya cigaba da sha hatta asirin da aka taɓa yi masa da zai warware zai bar jikinsa ko da ba’ a tone asirin ba, me yiwuwa shi yasa a yanzu ake ganin canji a tattare da shi.
Alokacin da ta yi ma Haj kilishi wannan bayanin, hatta yawun bakinta sai da ya ƙafe, kirjinta ya shiga suya fiye da yadda yake yi. Afrah ta zamar mata ƙadangaren bakin tulu. Shin ina mafita, bata jin zata rungume hannu tabar abinda yake shirin faruwa ya faru, don haka ta dubi Haj Rakiya tace “ ki ƙara nemo min wasu gawurtattun malaman na yarda da ke da amanarki, yadda ki ke rike sirrina bana ɗar ko kaɗan wajen damƙa miki amanata, saboda haka ki je ki bincika min ko nawa ne zan iya kashewa don ganin bayan Afrah da musaddiƙ”. Haj Rakiya ta lumshe ido ji take kamar ta gama mallakar komai ta jinjina kai tace “zaki same ni me ƙara rike amanarki, zan kuma bincika miki kada ki damu ki kwantar da hankalinki kinga ba lafiya ce da ke ba”, kai ta haɗe da guiwa wasu hawaye masu ɗumi suna fitq matq, Haj Rakiya bata bata haƙuri ba barinta ta yi ta ci kukanta ta ƙoshi, ita kam babu abinda take saƙawa sai yadda zata dumbuli dukiyar Allah ya isan Haj kilishi, lalle an ba kura ajiyar nama, ta yi wani murmushi mai ƙayatarwa, lalle yadda musaddiƙ ya yi mata hanyar arziƙi, da zaran ta gama tatse Haj kilishi da kanta zata je ta haƙe asirin ƙasan kuka ta maida musaddiƙ yantacce, kamar yadda ya yi sanadoyyar maida rayuwarta yantacciya………………..
Yar gidan imam✍️